اسم المترجم : أمين سعد عبد الله
اللغة : الهوسا
التاؤيخ : 5-11-1441هـ
Hudubar Juma'a a
masallacin Annabi na Shaikh Husaini Al-Assheikh
Mafi girman
ni'imomin duniya ita ce ni'imar lafiyan jiki, ba wata ni'mar da ta ke daidai da ita na daga cikin
ni'imomin duniya duk yanda ta yi dadi ,
Allah ya azurta mu gaba daya da lafiya da waraka saboda haka ne ba wanda ya san
dadin lafiya sai wanda ya dandani dacin cututtuka da rashin lafiya Allah ya
kare mu da ni da ku daga su Manzon Alla tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi ya ce : (Ni'imomi guda biyu mutane na hasara a cikinsu, shi ne lafiya da kuma zaman
banza)Buhari ne ya rawaito
'yan
uwa a musulunci :
Mai samun farin
ciki, wanda aka datar da shi , shi ne wanda ya san ni'ma yayin samuwanta ya
kuma tashi da hakkin ta , ya kuma ji kimanta a jikin shi , mafi wajabcin godiya
ga ni'ma na lafiya shi ne ka hakabata ya kai musulmi wurin da'a ga Allah na
sauke wajibabbu da kiyayewa bisa ga umarce umarce, da yin nesa daga bakaken
abubuwa da mununan laifuka , da gaggautawa zuwa ga ayyukan nafilfilu da kuma
ayyuka na kwarai Allah Madaukakin sarki ya ce:(ku yi
gaggawa zuwa ga gafara daga Ubangijinku da aljanna wanda fadinta ya kai sammai da
kasa an tattaleta ga masu tsoron Allah),
Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke cewa (ku gaggauta da ayyuka kafin abu guda bakwai, shin akwai
abin da ku ke jira ne face talauci abin mantawa? Ko wadata abin da ke sa
dagawa?, ko kuma rashin lafiya da ke yin barna?, ko tsufa da ke kararwa? ko
kuma mamaci abun shiryawa?,ko kuma dajjal? to sharrin abin da ya ke boye da ake
jira ko kuma tashin alkiyama? kuma tashn alkiyama shi ya fi tsanani shi ya fi
daci)Tirmizi ne ya rawaito kuma ya ce hadisi ne hasan .
'yan
uwa na musulunci :
Musulmi a ko wani halin da ya ke ciki yana cikin alheri
ne mai girma da lada mai yawa a duk lokacin da ya yi ikilasin niyarsa ga Allah
ya yi gaskiya a wurin biyayyan sa , duk wanda aka jarabce shi da rashin lafiya
ya yi hakuri ya nemi lada to hakan zai zamo mishi daukaka ne a darajojin shi
kuma da kankara ne ga laifukan shi , Allah Madaukakin sarki ya ce : (hakika za mu jarabe ku da wani abu na tsoro da yunwa da
tawaya na daga dukiya da rayuka da 'yayan itace ka yi albishir ga masu hakuri)
(wadanda idan musiba ta same su sai su ce lallai
daga Allah mu ke kuma gare Shi za mu koma) (wadannan suna da kyakkyawan ambato daga wurin ubangijin su
kuma da rahama kuma wadannan su ne shiryayyu) , Manzon Allah tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:(ba
wata musiba da zata samu musulmi na rashin lafiya ne ko wani abu koma bayan
haka face Allah ya kankare mishi laifukan shi kamar yanda ganyen itace ta ke
karkadewa diga itaciya) Muslim ne ya rawaito.
Annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya shiga wa Ummussa'ibsa ya ce :(mai ke
gare ki ne ya ummussa'ib kina karkarwa ? sai ta ke cewa zazzabi ne , kar Allah
ya mata albarka sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :
kar ki zagi zazzabi domin tana tafiyar da kusakuran bani a'adama kamar yanda
zugazugi ke tafiyar da kazantan karfe) Muslim ne ya rawaito.
Na daga cikin
mafi girman ni'imar Allah cewa Allah yana gudanar da lada ga bawa mai rashin lafiya irin ladan aikin da yake yi a
halin yana mai lafiya, kamar yadda ya zo a sahihul Buhari Annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shiya ce : (Idan bawa ya yi rashin lafiya ko tafiya to Allah
Madaukaki zai ci gaba da rubuta masa
ladan aikin da ya saba yi a halin yana da lafiya mazaunin gida).
Ka sani ya kai
wanda a ka jarabta da rashin lafiya
Allah na kusa da bawanSa to ka nemi mafaka a gare shi, ka roke shi
waraka da lafiya kana tsayuwa a kan sabuba na jinya wadanda su kansu suna cikin
hakikanin dogaro ga Allah Mabuwayi da
daukaka, da Allah ne kadai bakin cikinka ke yayewa kuma cutarka ta tafi ( kuma idan na yi rashin lafiya to shi ke warkar da ni).
Ka kasance bisa yakinin rahamar Allah da falalarSa, kuma shi ne Mai warkarwa kuma Isasshe, (
kuma lalle tare da tsanani akwai sauki. To kuma lalle tare da tsanani akwai
sauki)
Huduba ta biyu
Duk yadda dan adam ya kai da karfi da bunkasa da
tunbatsa a fagen ilimi to fa sifa ta rauni na damfare da shi, Allah Madaukakin
Sarki ya ce ( kuma ba a baku wani abu na ilimi ba
face kadan). Kuma Mai tsarki yace : (Kuma an halicci mutum da rauni).
To cikakken Karfi
na hakika sifa ne ga Allah Alkawiyyu Al
Matin Mamallakin dukkan komai bisa hakika, Mai gudanar da al'amura kuma Mai
tunkude su, kowani abu na faruwa ne da hukuncinSa da kaddararSa. Kuma karkashin
gudanarwarSa da ganin damarSa (Mashi'arSa) ( Ya ku mutane ku
talakawa ne zuwa ga Allah, kuma Allah shi Mawadaci ne Abin godiya).
To mu yi kokari wurin bauta masa, mu kafu wurin masa
biyayya kuma mu kankan da kai a gare shi mu nemi mafaka daga bangarenSa. Allah
Madaukakin Sarki yace :( ku tuba zuwa ga Allah
Ya ku wadanda suka yi imani ko zaku rabauta)
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق