السبت، 13 يونيو 2020

BUKATUWARMU GA FADAKA

اسم المترجم : أمين سعد عبد الله

اللغة : الهوسا

التاؤيخ : 20-10-1441هـ                                                                                                                            

 

Hudubar farko

Ya ku musulmi!

 Fadaka na daya daga cikin manyan abubuwa masu kima, da kuma abu mafi tsarki da ya dace a dasa shi , ba aminci sai da shi  babu zaman lafiya kuma sai da kulawa da shi   da bin shi ; fadaka; shi ne kiyayewa  daga duk wani abubuwa kanana da fahimta mai zurfi    an karbo daga Aisha Allah ya kara yarda a gare ta ta ce :- Manzon Allah tsira  da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce gamae da saukar wahayi :- (Sai ya tafiyar da ni da hankali na  a halin na kiyaye abin da ya fada ). A wani lafazi (sai na kiyaye abin da ya ke fadi ) Buhari ne fito da shi

Katada Allah ya mi shi rahama ya ce :- (Kunnuwa na ba za su ji wani abu ba face zuciya na ta kiyaye shi )  fadakakkiya ita ce wacce  ta hankalci abin da yake daga  Allah madaukaki da kuma amfana da abin da ta ji  na daga littafin Allah da sunnar Manzon sa  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce :-(Kunnuwa masu fadakuwa) ya kawo shi bisa ga tankiri  bai kawo shi a sigar jam'i  ba  sabo da karancin masu kiyayewan da fadakuwa.

An karbo daga Zaid dan sabid Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :- na ji Manzon Allah tsira  da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa:- (Allah ya haskaka fiskan duk mutumin da ya ji magana ta sai ya kiyaye ta  ya fadaku da ita  sannan ya sadar da ita zuwa ga wanda bai ji ta ba ,  sau da yawa  wanda ke dauke da  fakihu  alhali shi ba fakihi ba , sau da yawa  kuma wani kan dauki  fikihu zuwa ga wanda  ya fi shi fahimta ) Tirmizi ne ya rawaito).

Ramah Ramazi  Allah ya mi shi rahama ya ce :- ( Sai Annabi ya bambance tsakanin mai nakalto sunna da mai fadakuwa da ita ya  yi nuni zuwa  ga falalan mai fadakuwa a fadin  shi , sau da yawa wani kan dauki fikihu amma shi ba fakihi ba sau da yawa kuma wani  kan dauki fikihu zuwa ga wanda ya fi shi fikihu ).

 Ya ku musulmi:

Jakar mutum ita  ce :- zuciyarsa da  hankalinsa  da suke tattaro iliminsa da kudurinsa da kimarsa  da tunaninsa  da jinsa (na jiki), kar ka sanya a jakar ka sai abin da ya dace da  addininka  da hankalinka da dabi'unka .

Alheri wanzuwa yake ko da zamani ya yi nisa sharri kuma shi ne kazanta mafi muni da ka kiyaye na guzuri .

Ubangijin mu ya ce:-  game da  kafiraia masu girman kai   (Kuma Allah shi ne mafi sanin abin da suke tarawa ) wato  ya san  abin da suke tattarowa su boye a cikin zukatan su  na kiyayya ga Manzon Allah da muminai .

Abdullahi Dan Mas'ud Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :- (Lallai wadannan zukata jaka ce, to, ku shagaltar da ita da  Alkur'ani, kar ku shagaltar da ita da wanin sa   ko wani abu  wajen shi na buso da abin da ke cikin  shi  ne,  harshen sa kuma na furta abin da ke zuciyar shi )

Abin da ke  zuciya ya ki sai ya bayyana *** Kuma dukkan kwano   yana nason abin da ke cikin shi ne

 Wanda asalin shi bai kasance tsarkakke ba *** To ba zai fitar da abu mai tsarki ba daga bakin shi.

Dukkan mutum aikin shi na kama da shi *** kofi na kamshin abin da ke cikinsa ne.

 

                           Ya ku musulmi:

Ana samun fadaka ne ta hanyar ilimi da natsuwa da fahimta   da bincike  tana karfafuwa kuma ta hanyar abota da masu yalwan hankali wanda  ya goge a harkar yau da kullum ya san jiya da yau.

 Hakika ance abin da ya rage  ya isa mai bada labari game da abin da  ya wuce, abin da suka jarraba  ya isa abin lura ga masu hankula, fadakuwa   na karuwa ne ta hanyar tambayan ma'abota ilimi  da gogewa a rayuwa  da basira a al'amura  da shekaru  da kuma sani. 

An tambayi Dan Abbas Allah ya kara yarda a gare su ya ce:- (D a harshe mai yawan tambaya da zuciya mai yawan hankalta  da rayi wanda  bai gajiya).

Fadakuwa  na habaka  ne ta hanyar shawara da ma'abota hankula da basira  da kuma tattaunawa da masu hikima  da ma'abota hankula .

Mai hankali idan al'amura suka rikice mi shi *** Sai ya hade al'amuran  ta hanyar tattaunawa da kuma neman shawara

Amma ma'abota jahilci yana fandarewa da ra'ayin shi*** Sai ka ganshi yana taran  aradu da ka    

  Abin sani fadakuwa na iya karuwa kuma yana iya raguwa , hakika ance musharaka cikin al'amura yana bawa mutum  goge , atisayi kuma yana daga ma'abocin shi  zuwa ga  darajoji na kamala

 

 Mai hankali fadakakke  yana gane  nauyin da ke wuyansa, kuma  yana dubi zuwa ga karshen al'amura kafin su bayyana  ya kiyasta wani abu da makamancin shi  kuma ya dauki izina daga wanin sa  ya kiyaye daga sharri kafin ya same shi .

Mai basira ne da karshen al'amura  kai ka ce **** yana dubi ne  da ra'ayin sa na dai-dai zuwa ga abin da ya ke aukuwa

Huzaifa Dan Yamani Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :- (Mutane sun kasance suna tambayan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  akan alheri , ni kuma na kasance ina tambayan shi game da sharri, tsoron

Mai hankali fadakakke  yana kiyayewa daga  abin da akwai kaskanci  ko tawaya  kuma yana taka tsantsan cikin abin da akwai aibi  akan shi , ko kuma akwai cutarwa ga wanin shi, kuma yana tsarkaka daga abin da yake akwai kazanta , ya kuma kauce daga abin  kyama ya kuma kare kan shi daga abin da bai dace ba,  kyau da kawa  daga  gare  shi ya ke fitowa,  alheri kuma daga gare shi ya ke gangarowa.

 Ya ku musulmi:

Karancin fadakuwa  musiba ce  da ta tsaya akan kwabri na jahilci,  da kuma  raunin hankali da wauta  da karancin gogewa,  kuma yin ko inkula  na daga cikin  bala'in da ya ke kasancewa ra'ayi , ga wanda yake da iko ba ga wanda ya ke kallo ba, ta yaya mutum zai musanta abinda ya ke hakika ne  ya kuma gaskata abinda ya ke na bata ne ko karairayi , ya maida abubuwan da  suke ana ji  ana gani   ya rasa rarrabewa  , zane da layi suka rikirkice mi shi  ya kasa rarrabe tsakanin zare da abawa   da kuma tsakanin gaskiya da wasa   da kuma abu mai kyau da mara kyau  bai yi dubi ba zuwa ga karshen ala'amura  ,  bai gano girman hadarin ba  kuma bai yi riko da azama ba , bai dauki mataki na kariya da iyakancewa ba  da farkawa  ba , ya bi son rai  ya kosar da zuciyan sa sha'awe-sha'awen sa  ba tare da yayi dubi zuwa ga makomar al'amura ba, to ta yaya zai zamana ya amsa kiran mai nasiha ko ya damu da  abin da   yake cewa.

Na daga cikin musiba zargin wanda  ba zai gargadu ba*** dabga zaluncin shi  da kuma magana da wanda bai fahimta

Ba wani abu ba ne cuta  sai dai ka ilmantar da wanda yake jahili *** Shi kuma yana zato cikin jahilcin shi  cewa ya fi ka sani

Ya ku musulmi:

Ku gyaru da ilimi , ku amsa kira da fahimta ku ja damara da basira, ku sa rigar kariya  da fadaka.

Fadakuwa abu ne   na dole *** ba mai rabauta sai mai yi da gaske

Tir da wanda ya san abu na gaske kuma  ya ki ya ki ya tafi akai , muna jin  radadi a yayin da muka ga wanda ya ke jin koyarwa na kariya  da kuma abubuwa da aka yadawa na fadakarwa da dalilai na shiryarwa  da kuma tsari na kare kai da ke fitowa daga  bangaren jami'an tsaro da jami'an lafiya musamman daga abin da ya shafi korona  sai ya yi kunnen uwar shegu , kamar bai ji ba  ya rinka fiskantar su da izgilanci  da ko inkula  ya doge yana mai sabawa  da musu  ya haifarwa kansa da iyayensa da 'ya'yansa da iyalansa  ya jawo bala'i da cuta ya raba musu a tsakiyar gidansu ya bude mu su kofofinta ya dauke musu shamakinta , ya rinka kuma kashewa mutane gwuiwa daga  bin matakan kariya , ya kuma yada tsakanin mutane cewa korona karya ne  da yaudara, ya makance daga dubannin matattu da wadan da suka kamu, wadan da suka dandani daci da tsananin cutan .

 

Yana tinkaran dukkan kokari da kasashe ke yi na iyakan cewa da yin galaba da yaduwan shi , to ku kiyaye daga raunin hankali  da raunin alkalami  da magana  ku sake bitan hankula ku yi lura cikin tunanin da kuke yadawa da lafuzan da kuke saka  da abubuwa da kukle yadawa , ku ji tsoron Allah cikin abin da kuke fadi , ku bar abin da ba ku  iya  kyautata  kada ku kusa cikin abin da ba ku sani ba , kar ku yi amfani da jahilci wurin yakar ilimi da zato wurin yakini ,  da abin da yake na shirme  da karairayi wanda ba su da  makama ,   ku kyautata  al'amarin ku , ku shiga taitayin ku, hakika ance   .

Ra'ayi mai gudana da idanuwan mutane  na bacci***Ra'ayin da ya kaddamar da takatsatsan  baya jinkirta azama. Ina fadan abin da kuke ji kuma ina neman gafaran Allah kuma kuma ku nemi gafarar shi lallai shi ya kasance ga masu  yawan komawa gare  shi mai yawan gafara ne .

 

Huduba na biyu

Ya ku jama'ar musulmi :

Hakika  abubuwan da suka faru na wannan yanayi da ake ciki na korona   da abubuwan da suka auku ya bayyana  bukatuwanmu zuwa ga sake gina fadakarwa , ga 'ya'ya da kuma al'uma da mata da maza ,  da yawa mun gani na daga dajjalanci  da karairayi  wanda suke amfani da wannan annoban  wurin cimma  kazantattun manufofin su  da neman abin duniya walakantacce , wofantacce mai da'awan karyan da bayi da ilimin likitanci  ko kuma ba yi da wani  abu da zai taimaka mishi wajen tabbatar da binciken ilimi mai zurfi , ba kuma na'ura  da zai yi amfani da shi wurin gano maganin korona , amma zai yi da'awan ya gano maganin cutar korona , mutumin da yake likitanci na karya  da yaranta da yaudara zai bada magani na kwayar cuta da ta gagari center ta bincike na duniya. Shi mai kwadayin abin duniya mai son handama, maras dabi'u masu kyau zai boye kayaki da sumbattoci   da kuma ababan tsabtace wuri da magungunan kashe koyoyin cuta , domin ya rinka wasa da farashin su ,    da kuma ,mai yin algus da dabaru yana mai sana'anta magunguna na karya da  da abubuwan kashe koyoyin cuta na boge wacce ke iya yin illa wa lafiya  kuma yakan taba lafiyan jiki  da mai karyan ilimi rudadde , wanda yake  bushewan ido da bada fatawa  da yin ijtihadi a cikin abubuwa da suke sabbi, da matsaloli da suke da alaka da korona  , yana mai fiskantar da mutane ta yanda za su yi salla su tsarkaka su yi ibada alhali kuwa bai mallaki cancanci na ijtihadi ba ko fatawa .

 Za ka ga wawa yana kaucewa duk wani abu na mutunci*** yana sauraron duk wani abu na wauta.

Ba mai aminta da masu wadannan da'awar sai mara fadaka da ganewa da lafiyayyen hankali.

Ku ji tsoron Allah ya ku musulmi  ku hanu ku kame kai daga abubuwan aibi da laifi da abin kunya, ga Al-kur'ani da suna gaba gare ku, suna cike da hikima da hukunce – hukunce da ka'idoji da wa'azuzzuka, da laduba da wadanda su ne shugabannin ilmuka kuma mabubbuga ne na fahimta kuma hanya ce ta samun daukaka da ake nema, to ku kiyaye su,ku yada su, da wahayi ne da fadaka hankula ke cika, shakku da wahami ke gushewa.duhu ke yayewa,

Ku   farkar da zukata  daga gafala ku tuba daga zunubai da kusakurai, bala'i bai sauka sai da zunubi, ba a daukewa sai da tuba, ku nemi saukar rahama da adu'a, duk wanda ya nuna talaucin shi zuwa ga Allah  to Allah ya wadata shi, duk wanda ya nemi mafaka a wurin shi Allah sai ya daukaka shi duk wanda ya nemi kariya daga gun shi sai Allah ya kare shi idan har bayan jirkicewa ne to sai Allah ya bashi kwanciyar hankali idan bayan ruwan sama ne kuma sai ta yi fayau, rana tana buya kuma tana hudowa , fure kan yankwane sannan kuma ya yi 'yaya , dukkan wani tsanani to zuwa ga sauki ,dukkan kuma wani wahala to zuwa ga yayewa, ku yawaita kankan da kai da adu'a da fatan alheri.

Waka :

***duk wanda ya ke neman mafaka kuma yana fata ***

 annoba ya bayyana sai gashi matambayi ya zo zuwa gare ka***

*** idan ka bada taimako to dukkan bala'ai zai yaye ***

Idan ka kwarara to dukkan alheri zai sauka ***

***idan ka yi rahama to dukkan cuta zai katse ***

Idan ka warkar to dukkan cuta zai sushe ***

*** kasa idan ta yi fari a shekara to zai tafe ***

To wanene mai karanci a gare mu mai yawan yawan kyauta mai yawn zubar da ruwan sama ***

*** idan annoba ya taho a kan guiwansa a kwangwan nin mu ***

To wanene mai jin kai a gare mu ko a'agajin gaggawa ***

*** idan ya yafe to Shi Mai karamci Mai yalwa ***

Idan Ya yi hukunci to Shi ne mai hukunci na a'adalci

Ku yi salati da  sallama ga  Ahmad  mai shiriya mai ceto ga halittu.          

  

 

 

  

 

 

 

 

 

 

 

 

 

  

  

 

 

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق