السبت، 13 يونيو 2020

Sunan Allah "Al-Hakim" Mai Hikima

اسم المترجم : أمين سعد عبد الله

اللغة  : الهوسا

التاريخ : 13/10/1441هـ

 

 

Hudubar Masllacin Annabi na SheikhAbdulmuhsin Bin Muhammad Alkasim 13-10-1441AH / 5-6-2020 AH

Hudubar farko

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna gode maSa kuma muna neman taimakonSa

Muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu  da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, wanda ya batar kuma babu mai shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya,kuma na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa. Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa.

Bayan haka, ku ji tsoron Allah -ya ku bayin Allah-cancancin tsoronSa ku yi riko da igiya mai karfi na musulunci

Ya ku musulmai

Fidira ta shaida duniya na da Ubangiji Mai kamala a zatinSa da sifofinSa, yana siffantuwa da dukkan sifa ta kamala mafi kamalarta da mafi girmanta da gayarta, dukkan yabo da godiya da kyautata ambato na shi ne, na daga cikin girmama Allah tabbatar masa da siffofinSa ta kamala da daukaka.

Sunan Allah "Al-Hakim" yazo cikin littafin Allah sama da gurare casa'in (90).

Allah Mai hikima ne yana sanya abubuwa bigirin su yana saukar da su a wurarensu da ya dace da su a cikin halitta da umarninSa yana da cikakken hikima wacce ke hade da daukaka Mabuwaya da ilimi da gwanancewa da kuma yalwa da kuma tuba da godiya, hikimarSa ta kai kololuwa da ta gagari hankula iyakancewa a hakikaninta harsuna sun kasa furta hakikaninta bayani game da ita , da hikimarSa ne ( Abin da ke cikin sammai da kasa suka yi tasbihi zuwa ga Allah).

Tsarki ya tabbata a gare Shi Mai hikima ne abin bauta a sama da kasa (Lallai shi ne abin bautawa a sama kuma Shi ne abin bautawa a kasa yana da hikima kuma Masani ne) ya godewa kansa da kansa saboda shi Mai hikima ne (Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ke cikin sammai da abin da ke cikin kasa duka nashi ne kuma yana da yabo a lahira kuma Shi Mai hikima ne Gwani) Allah ya yabi kanshi tsarki ya tabbata gare Shi lallai cewa yana da girmame - girmame kuma ya cikamake ayar da cewa Shi Mai hikima ne  (Yana da girmame - girmame a cikin sammai da kasa kuma shi Mabuwayi ne Mai hikima) kuma yana da rundunoni a sama da kasa yana gudanar da su kaman yanda ya so shi Mai hikima (Allah na da rundunan sammai da kasa kuma Allah ya kasance Masani ne kuma Mai hikima) ya kirayi Musa Alaihissalam ya sanar da shi da zatinSa cewa shi Mai hikima ne  (Ya musa lalle ne Ni Mabuwayi ne kuma Mai hikima).

Ya kyautata yabo ga littafinSa cewa lallai ya zo ne daga wurinUbangiji Mai hikima yana sanya ko wani abu a bigiren Shi kuma ya saukar da shi a wurin shi matsayin shi sai ya kasance littafi ne gamamme da ya kunshi cikakkiyar hikima Allah subhanahu wa ta'ala ya ce :(Littafi ne da an kyautata ayoyinsa kuma aka yi bayanin shi daki daki daga wurin Mai hikima Mai labartawa) da hikimanSa subhanahu ya bude arziki ga mutane kuma ya ke rike ta (Ba wani abin da Allah ya ke budewa mutane na arziki na rahama ko kuma ya rike face da abin da Allah ke bude wa mutane na rahama ba mai rike haka nan kuma abin da ya ke rikewa ba mai turo ta bayan Shi  lallai Shi Mabuwayi ne mai hikima) , Mala'iku suna matsayi na yarda da gazawa da kuma kasawa a ilimi sun tabbatar da ilimin Allah suka mika wuya ga al'amarinSa (sai suka ce tsarki ya tabbata a gare Ka ba mu da ilimi sai abin da ka ilmantar da mu lallai kai din nan Masani ne kuma Mai hikima) masu daukan al'arshi da wanda ke kewayenta suna adu'a wa musulmai da gafara da shiga gidajen aljannah kuma da cikamake addu'ansu cewa lallai shi din nan da sunan shi  tsarkakakke kuma Mai hikima  (Ya Ubangijinmu ka shigar da su gidajen Aljanna na adn wanda ka yi alkawarin shi gare su kuma ka gyara daga cikin iyayen su da matayen su da kuma zuri'an su lallai kai din nan Mabuwayi ne Mai hikima) .

Allah ya ce ga dukkan Manzannai cewa wahayin da ya ke saukarwa daga gun Shi ne Mai hikima (Haka nan ne ya ke wahayi zuwa gareka da wadanda su ke kafun kai Allah Mabuwayi Mai hikima) Annabawa amincin Allah su tabbata a gare su sun kasance suna rokon Allah ne wurin tabbatar da fatan su da kuma burace - buracen su da sunan Shi tsarki ya tabbata a gare Shi Mai hikima , Ibrahim Alaihissalatu wassalam ya roki Ubangijinsa da sunan Shi Mai hikima da ya turo zuwa gare mu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi (Ya Ubangiji ka turo a cikinsu manzo wanda ya ke karanta a gare su ayoyinKa kuma yana sanar da su littafi kuma da hikima yana tsarkake su, lallai kai din nan Mabuwayi ne Mai hikima) Ibrahim amincin Allah su tabbata a gare shi ya zo garin shi ya yi hijira zuwa ga Allah sai ya ce lallai Allah Mai hikima ne (sai ya ce lallai ni zan kaura zuwa Ubangijina kuma lallai shi din nan shi ne Mabuwayi Mai hikima), zamani ya tsawaita ga Ibrahim amincin Allah su tabbata a gare shi bai haihu ba ba a haifa mishi ba, sai mala'iku suka yi wa matarsa  albishir da wani da wanda  a halin ita tana tsohuwa kuma bakarariya, sai ta yi mamakin haka sai mala'iku suka ce da ita lallai Allah Masani ne Mai hikima (sai suka ce haka nan ne Ubangijinki ya ce domin lalle Shi Mai hikima ne kuma Masani) Yakubu alaihissalatu wassalam tare da hakurin shi da sauraron yaye bakin ciki sakamakon rasa yusuf da ya yi da dan uwan shi ya tabbatar da ilimin Allah a cikin zaben zamani da ya dace saboda abin da ya ke fata a gare shi na yaye bakin ciki ya sakankance da hikimar Allah wurin shirya sabuba na yaye bakin ciki sai ya fiskanci Allah da sunan shi Mai hikima tare da fatan shi da addu'a (To hakuri  abu ne  mai kyau ya wuci Allah ya  kawo mini su gaba daya lallai  shi din nan Masani ne Mai hikima) bayan yayewan bakin ciki daga Yusuf alaihissalatu wassalam da tsawon musibu da wahalhalu wanda ya hadu da su ya tuna ni'imomin Allah da falalanSa sai ya tabbatar da su tare da tabbatar da ni'iman Allah a hakan sai ya ke cewa (Hakika ya kyautata mini tunda ya fitar da ni daga kurkuku ya zo mini da ku daga kauye bayan shaidan ya shiga tsakani na da 'yan uwana lallah Ubangijina Mai ludufi ne ga abin da ya so kuma lallai Shi Masani ne Mai hikima).

Kuma sunan Shi Subhanahu Mai hikima ya kumshi hikimomi a halittanSa da umarninSa wurin iradarSa ta adiini da kuma ta duniya , Ibnul kayyim Allah ya mishi rahama ya ke cewa tare da izza kamalar kudurarSa da hikima kuma kamalar iliminSa wadan nan siffofi biyu Allah kan hukunta abin da ya so  kuma ya umarnin abin da ya so ya yi hanin abin da ya so kuma ya kyautata yabo kuma ya bi kadu wadan nan siffofi ne da su ke masdarin su shi ne halitta da umarni.

Da hikimansa ne Allah subhanahu wa ta'ala ya halicci halittu gaba daya da tsari mafi kyau ya jera su mafi kamalan jerawa ya kyautata gudanar da su ya kyautata kaddara su ya bawa ko wani mahaluki halittarsa da ta dace da shi ta dace da shi (Ya bawa kowa halittar da ta dace da shi san nan ya shiryar) Allah ya kalubalanci halittu cewa su kawo ko da halitta daya ne wanda akwai tawaya cikin halittarSa, Allah ya kalubalanci da su samar da cikin halittanSa guda daya wanda akwai rashi daidaitu (ka sake dubawa da gani shin za ka ga akwai wani abu na tsagewa?) Da a ce hankulan halittu gaba daya za su hadu domin su bada shawara ga misalin halittan Mai rahama ko kuma abin da ke kusantan shi ko kuma abin da ke kusa da shi ko kuma abin da Allah ya sanya cikin halittan Sa abubuwa na rayayyu na daga kyau da kuma tsari da kyautatawa ba za su iya ba saboda haka Allah ya umarci halittu da su wadatu da ta'ammuli da lura cikin abin da Allah ya halitta Mai hikima cikin halittunSa tare da tsinkayan bisa wasu abin da ke ciki na daga kyau da kyautatawa (ka yi dubi me ke cikin sammai da kasa) da hikimarSa ne Subhanahu ya samar da bayinSa da zatinSa tsarkakakka da kuma mika wuya da umarninSa da haninSa, ya saukar da littafinSa kuma yana so da ya karbi tuban mu kuma ba gyaruwa game da al'amuran duniya sai da addini haka nan kuma wasu magabata suke cewa (Ba don a cikin umarninSa da shari'ansa ba sai wannan hikima mai girma wanda ita ce tushe na alheru da kuma kamalan zatinSa da hakan ya kasance abu ne cikakke kuma mai waraka).

Shi ne wanda tsarki ya tabbata a gare Shi Mai hikima cikin  umarninSa a cikin duniya  wanda ya ke jarabta bayinSa da shi domin ya gyara su  ya daga darajar su ba wani abu da bawa zai kasance yana da shi na zabi kaman nufin rashin lafiya da tawayan arziki kawai abin da zai yi to ya yi imani ne kuma ya yarda  kuma ya riki abubuwa na sababi wanda aka  shar'anta da kuma abubuwan da suke na halal sai ya tunkude kaddaran Allah da abin da ke gudana wa bawa ba tare da zabin shi ba wanda ba yi da karfi wurin tunkude shi sai ya yarda kuma ya mika wuya ya shaida izzan Allah ne a cikin hukuncinSa da kuma a'adalcinSa da kuma abin da ya hukunta.

HikimanSa na gudana a gare Shi kuma lallai duk abin da ya same shi bai kasance da ya kuskure shi ba abin da kuma ya kuskure shi bai kasance da ya same shi ba lallai hakan ke wajabta masa a'adalcin Allah da hikimanSa lallai Allah Mabuwayi hakika ya bayyana wasu hikimomi ga bayinSa sai ya bada labari cewa saukar da littafi da ya ke yi don tabbatar da mumunai ne ya shiryar da su kuma da yin albishir a gare su (ka ce ruhi mai tsarki ya sauka da shi daga Ubangijinka (Mala'ika Jibril) da gaskiya domin ya tabbatar da wadanda suka yi imani kuma da shiriya ne da albishir ga musulmai) ya tura manzanni domin kada wani ya zama yana da hujjar cewa shi ya jahilci addini (Manzanni ne masu albishir kuma da gargadi domin kada ya zamana mutane suna da hujja a kan Allah bayan zuwan manzanni ) Hakika kuma Allah ya jarabci mutane yana kuma yi musu ibtila'i kuma zai sake yi musu ibtila'i  domin ya duba ya ga gaskiyan ta'allukin su da Shi Allah(Wai mutane suna zaton za su ce sun yi imani ne a kyale su a halin kuma ba a'a jarraba su) Allah ya shamake ilimin gaibi ga bayinSa sai ya kebantar da shi ga kansa saboda hikima , (Masanin gaibi abin da ya faku da kuma shahada Shi Mai hikima ne kuma Gwani).

Bayan haka ya ku musulmai:

Lallai Allah Shi kadan shi halitta da umarni na Shi ne yana aikata abin da ya so a cikin duniyarSa, a cikin shari'arSa yana hukunta abin da ya ke so abin da ya nufa , ba a fiskantar da tambaya gare shi, ba a suka cikin hikimanSa da wata magana (Ba a'a tambaya don me ya ke aikatawa amma su (halittu) ana tambayan su )

Musulmi yana bautawa Allah ne da abin da sunan Alhakimu ya kumsa na ma'ana, idan bawa ya sakankance da hikimar Allah sai ya ji dadi da halittan Allah wanda ya ke Albadi'u da aikin Shi wanda akwai kyautatawa a ciki da kwarewa da kuma girmama shari'an Allah ya ji tsoron shi Allah Madaukaki, ya ji kunya daga  saba mishi ko ya ji kunya daga kurakuran shi, ya mika wuya ga umarnin shi da hanin shi ya tsananta farin ciki da cewa Allah ya shiryar da shi zuwa ga wannan addini saboda hikimanSa da ya nufa da ita game da shi kuma lallai shari'a daga mai hikima ne ta zo domin ya sanya dan adam cikin walwala ko da bala'i ya sauka a gare shi sai ya yarda da abin da Allah ya hukunta ya kaddara masa ya mika wsuya cewa hakan Allah ya hukunta a gare shi cikin gyara da kuma alheri (Ya wuci ku tsani wani abu kuma sai ya zamana alheri a gare ku) kuma ya sakankance cewa bayan hakan akwai hikima  da bai santa ba  kuma lallai yana  kai komo cikin ni'iman Allah ne a halin yalwa kuma da halin cuta , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke cewa: (Mamaki da ala'amarin mumini, lallai dukkan ala'amarin shi alheri ne a gare shi hakan baya kasancewa ga wani sai ga mumini idan alheri ya same shi sai ya yi godiya sai hakan ya zama alheri a gare shi idan kuma cuta ta same shi sai ya yi hakuri hakan sai ya zama alheri a gare shi) Muslim ne ya rawaito.

Ina neman tsarin Allah diga sharrin shaidan abin jefewa.

(Yana gudanar da ala'amura ba wani mai ceto face bayan izinin Shi wancannin ku Shi ne Allah Ubangijin ku, ku bauta miShi, ba za ku yi tunani ba ?) Allah ya sa mini albarka ni da ku a cikin Alkur'ani mai girma.

 

Huduba ta biyu:

  Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa kyautatawanSa, godiya a gare Shi bisa datarwanSa da kuma baiwanSa, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya ina mai girmama sha'aninSa na shaida Annabin mu Muhammad bawanSa ne kuma Manzon Sa ne tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa da aminci tabbatacce mai kari.

Ya ku musulmai:

Allah ya gina al'amuran bayinSa da ya sanar da su wasu ma'anoni  na dalilin halittansu  da umarninSa ba tare da zurfafawa cikin su ba da kuma bayanin su daya bayan daya ba, wan nan abu ne da ke faruwa a cikin ala'amura a tushensu da kuma rassansu abin da ba ya boyuwa ga bayi wasu ma'nonin na hikimanSa cikin abin da ya kirkira haka nan kuma da umarninSa da shari'anSa da kuma abin da ke kasancewa a duniya na kaddara ya ishesu cikin saninSa ta fiska na gaba daya abin da ya kumsa na hikima  da ya kai kololuwa su fahimci hakikanin bayaninSa daki daki ba ko hikimansa daki daki ba daya bayan daya hakan kuma yana daga cikin ilimin gaibi ne wanda Allah ya barwa kanSa shi .

 sannan ku sani lallai Allah ya umarce ku da salati da aminci ga AnnabinSa sai ya ce: a cikin littafinSa mafi hikima da ya saukar (Ya ku wadanda suka yi imani lallai Allah da mala'ikunSa suna salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce mai yawa).     

   

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق