السبت، 13 يونيو 2020

Allah Abin godiya

                                                                                                     

ترجمة الخطبة

اسم المترجم :أمين سعد عبد الله

اللغة : الهوسا

التاريخ : 6-10-1441هـ

 

Hudubar Juma'a a Masallacin Annabi Na shaikh Ahmad Dalib 6/10/1441AH/29/5/ 2020AC

Hudubar farko

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah muna gode masa kuma muna neman taimakonsa da gafararsa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi, kuma duk wanda ya batar babu mai shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, na kuma shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma manzonSa ne. tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da aminci tabbatacce.

(Ya ku wadanda suka bada gaskiya ku ji tsoron Allah cancancin tsoronSa kada ku mutu face kuna musulmai)

(ya ku mutane ku ji tsoron Allah wanda ya halitta ku daga rai guda kuma ya halitta matarsa daga gare shi ya yada daga gare su mazaje masu yawa da mata, ku ji tsoron Allah da ku ke roko da (sunan) shi. Da zumunci, lalle Allah ya kasance mai tsaro ne a kan ku.)

(ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah ku fadi zance na daidai. zai gyara muku ayyukan ku kuma ya gafarta muku zunubanku, duk wanda ya ke yi wa Allah biyayya da ManzonSa to ya rabauta rabauta mai girma.)

 

Bayan haka, lalle mafi alherin zance shine maganar Allah, kuma mafi alherin shiriya ita ce shiriyar Annabinmu Muhammad, kuma sharrin al'amura sune fararrunta, kuma dukkan bidi'a bata ce, kuma dukkan bata na wuta.

Lalle ni ina muku godiya ga Allah Ubangijin talikai. Mai rahama Mai jinkai.Mai mulki ranar sakayya.

(Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya halicci sammai da kasa, kuma ya sanya duhu da haske, sannan wadanda suka kafirta suna karkacewa Ubangijinsu).

(Wanda ya saukar da littafi ga bawanSa bai sanya karkata ba gare shi.madaidaici domin ya yi gargadi da azaba mai tsanani daga gare shi. Kuma ya yi albishir ga muminai wadanda suke aikata ayyuka na kwarai da (cewa) suna da wata lada mai kyau. Suna masu dawwama a cikinta har abada).

(Wanda bai riki da ba. Kuma bai da abokin tarayya, kuma bai da wani majibinci da zai taimake shi daga walakanci).

 (wanda yake abin da ya ke cikin sammai da kasa nasa ne.godiya tasa ce a lahira, kuma shi Mai hikima ne Mai labartawa. Ya san abin da yake shiga cikin kasa da abin da ya ke fitowa daga gare ta, Shine Mai rahama Mai gafara).

(Wanda ya fari halittan sammai da kasa,Mai sanya mala'iku manzanni masu fukafukai bibbiyu da uku-uku da hurhudu, yana kara abin da yaso cikin halittar, lalle Allah Mai iko ne ga dukkan komai).

(Wanda ya sanya muku kasa tabbatacciya, da sama ginanniya kuma ya suranta ku, sa'annan ya kyautata surorinku, kuma ya azurta ku daga abubuwa masu dadi. Wancan shine Allah Ubangijinku, albarkar Allah Ubangijin talikai ta bayyana.(Shine rayayye ba abin bautawa face shi, ku kira shi kuna masu tsarkake addini a gare shi, Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu).

   To yabo da godiya sun tabbata ga Allah,wanda ya ke ciyarwa ba a ciyar da shi, ya mana baiwa sai ya ciyar da mu ya shayar da mu, dukkan wani abu mai kyau na jarabawa Allah ya mana.

Godiya ga Allah ba irin na mai bankwana, ko wanda ake sakawa ba ko mai butulcewa ba ko kuma wanda ya wadatu daga gare shi ba Ubangijinmu.

Godiya tasa ce bisa halittanmu da azurta mu da shiryar da mu da yayi, godiya gare shi bisa ilmantar da mu da ya yi, ya kuma tseratar da mu ya yaye mana bakinciki, ya bamu mafaka, godiya gare shi bisa imani, godiya gare shi bisa musulunci, godiya gare shi bisa Alkur'ani. godiya gare shi bisa iyalai da dukiya da waraka, ya wulakanta makiyinmu ya yalwata mana arziki ya bayyana amincinmu ya hada rarrabarmu,ya kyautata samun lafiyarmu, kuma ya bamu dukkan abin da muka roke shi to dukkan yabo da godiya na shi ne mai yawa mai tsarki mai albarka a cikinsa kamar yadda Ubangijinmu ya ke so kuma ya yarda.

(Sabo da haka godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin sammai kuma Ubangijin kasa, Ubangijin halittu. Kuma gare shi ne girma ya ke a cikin sammai da kasa, kuma Shi ne Mabuwayi Mai hikima). Dukkan yabo da godiya ta sa ce kamar yadda muke fadi, dukkan yabo da godiya ta sa ce sama da yadda muke fadi, dukkan yabo da godiya ta sa ce har sai ya  yarda, dukkan yabo da godiya ta sa ce har bayan  yarda, kuma godiya tasa ce a farko kuma godiya tasa ce a karshe, kuma godiya tasa ce a bayyane kuma godiya tasa ce a boye, kuma dukkan godiya tasa ce a kowane hali, Mai girma Madaukaki.

Ya samar da mu kuma ya tattale mu ya taimake mu,to godiya tasa ce, ya datar da mu ya fahimtar da mu ya mana ilhama, to godiya ta tabbata a gare shi,ya shaidar da mu kuma ya shiryar da mu ya sanya mana walwala, to godiya ta tabbata a gare shi.

Ya tsaida mai shaidar rahama cikinmu sai ya kubutar da mai lafiya ya warkar da mara lafiya, ya zabi wanda ya kai ga ajalinsa cikinmu zuwa kusancinSa. Ya katange zukata daga firgici da gazawa da kwadayi.

ya bibiye mu da yalwan falalolinSa, bai muamalance mu da tsagoron adalcinsa ba, ya isar da mu zuwa watan ramadan ya jiyar da mu alkur'ani daga kwarin daki mai alfarma da kusa da raudan abin girmamawa.ya tsaida wanda ya so a cikin su daga bayinSa a matsaya na salihai masu azumi da tsayuwa da tilawa da ambato da tadabburi da tafakkuri da tuntuntuni da godiya, kebantar da su ya tabbata fatan ka sa su cikin kebabbunka.

Allah ya yawaita mana juma'o'i a cikinsa ya bibiyar da alherori a cikinsa ya kwarara mana albarkokin sama, sannan Allah ya cika mana da kammaluwan ranakunsa da dararakinsa, da halartan girmama Ubangijinmu. Da daukaka daren ja'izozi da wayan garinsa da taimakonsa ga shan ruwa da da buda baki da cin abinci, to godiya ta tabbata a gare shi.

 Godiya ta tabbata a ga Allah da ya nunawa musulmai alheri mai yawa a kansu sau da yawa aka kammala karatun Alkur'ani a gidaje, raka'o'i da dama an sallata a dakuna, littafi mai amfani nawa aka karanta,darusa nawa aka yada su kuma suka amfanar kuma wa'azuzzuka nawa ne aka yada su ta gidajen radiyo suka fadakar.

Godiya ta tabbata ga Allah da ya bayyana boyayyen imani daga gurin da aka manta shi, kur'anai da dama an kaurace musu sai gasu an fito da suka ga haske,zukata nawa ne suka kakashe sai ga su sun lausasa, idanuwa nawa ne da suka bushe sai gasu suna zubar da hawaye, rayuka nawa ne suka saba sai gasu sun hada kai, mutum nawa ne suka juya wa juna baya sai gasu sun fiskanto juna, ruhi nawa ne suka yanke zumunci sai gasu sun sadar,

Godiya ta tabbata  ga Allah da ya sanya musulmai a cikin miskinai kamar Ansar a cikin Muhajirun, wadanda suka bayar da masauki suka yi taimako, suka karfafe su suka karbe su kuma suka yi shafa'a suka bada shafa'a. suka tattaro suka rarraba, suka ciyar suka fifita, arziki nawa suka raba,da basuka da aka biya, mata nawa ne da suka rasa  mazajensu suka rufa musu asiri, marayu nawa aka dau nauyi, bukatu nawa aka biya, kwanukan abinci nawa aka shimfida, tafuka nawa aka hana roko, gidaje nawa ne aka cika su da alheri,basu kasance da su kauracewa sunnonin Manzon Allah ba ko su bar koyarwarsa  ba, gari mai kyau tsirransa na fita da izinin Ubangijinsa.

Godiya ta tabbata ga Allah da ya nuna mana tausayi irin na jagora da nasiha irin na mataimaki, da shiryarwa irin na alami,da agazawa na likita,da kulawa irin na mai tsaro, da tausayi irin mai nasiha, da daukaka kiran sallah, da walakantuwa irin na fajirci da fasikanci da sabo.

Godiya ta tabbata ga Allah da ya shafe mu da rinjaye irin nasa.sabo da horarwa, ya zartar da ludufi na kudurarSa a cikinmu domin ladabtarwa, da ya so da ya kama mu da fushinSa ya azabtar da mu azabtarwa. (kuma da Allah yana kama mutane saboda abin da suka aikata, da bai bar wata dabba ba a kanta(kasa) amma yana jinkirta musu zuwa ga ajalin da aka ambata, sa'anan idan ajalin su ya zo to lalle Allah ya kasance Mai gani ga bayinSa).

             (To shin  kuna fatan idan kun juya (daga umarnin)  za ku yi barna a cikin kasa kuma ku yanke zumuntan ku )

Shin ya wuci idan kun samu dama da ku yi barna a  bayan kasa ,   ku watsar da littafin Ubangijin ku  a bayan bayan ku ! shin kuna fatan idan kun samu aminci da ku yi barna a doron kasa kuma ku aminta da makirci na Ubangijin ku  shin kuna fatan idan kun bayyana da ku yi barna a doron kasa  kuma ku bi soye-soyen rayukan ku, shin kuna fatan  idan kun sauka kasuwannin ku da kuma makwancinku,  da ku bayyana abin da aka ki ku bi sha'awe-sha'wen ku! Shin kuna fatan idan  mai kiran sallan ku idan ya kira salla da ku yi barna a doron kasa! Ba za ku amsa zuwa ga abinda zai rayar da ku ba .

YA KU BAYIN ALLAH :

Idan kun tsoraci talauci to ku nemi wadata cikin talakawan ku, idan kun tsoraci galaba to, ku nemi taimako cikin  masu raunin ku , domin da su ne ake azurta ku kuma ake baku nasara , da zaluntan su kuma da fin karfin su da'ira take juyawa akan ku  sa'annan ayi galaba akan ku   a rinjaye ku .

Zaku sulale daga shari'a ne a sadade  idan musiba ta sauka sai  ku ce daga ina ne wannan! (Ka ce shi daga wurin kawunan ku ya  ke lalle Allah mai iko ne ga dukkan komai )

Ku sani lallai izza na cikin da'a , kaskanci kuma na cikin sabo

(Wanda ya kasance yana son daukaka to daukaka a wurin Allah ne yake  gaba daya zuwa gare shi magana mai dadi ke hawa , kuma aiki na  kwarai yana dauka ta ,  kuma wadan da ke yin makircin munanan ayuka  suna da wata azaba mai tsanani  kuma makircin wadannan yana yin tasgaro ).

(Izza na Allah ne da Manzon shi da muminai sai dai munafukai ba su sani ba )  

Ba makawa  a samu mai shaida a halittu bisa kalmar gaskiya ,  cikin  ma'abota rarrabuwa da ,munafunci , sai su ambaci irin jinsin fadin masoyan su na daga kafurai da mushirikai , (Hakika cututtuka da sauki  sun shafi iyayen mu) har su yardar da rayukan su shakiyyai  kame da ayukan su masu halakarwa , sai wasu mutane su riske su -muna neman tsarin Allah daga halin su  sun yi alkawari da Allah a lokacin cuta to idan ya yaye azaba sai su saba alkawarin ,  (Sai ya biyar mu su da munafunci a cikin zukatan su  har zuwa ga ranar da su ke haduwa da shi  sabo da sabawa Allah ga abin da suka yi masa alkawari, kuma sabo da abin da suka kasance suna yi na karya shin  ba su sani ba cewa lalle ne Allah yana sanin asirin su da ganawan su Kuma lalle Allah ne  Masanin abubuwan fake?  ) (Ka da ranka ta tafi zuwa gare su kana mai hasara ) ( Kada ka yi bakin ciki a gare su kuma  kar ka kasance cikin kunci bisa abin da suke yi na makirci , lalle Allah  yana tare da wadan da suka yi takawa  , kuma yana tare da masu kyautatawa).

Amma ma'abota imani  sun gaskata  abin da suka alkawartawa  Allah a gare shi  a cikin su akwai wanda ya biya bukatan sa  akwai kuma wanda ya ke jira basu sanja ba .(Kuma da  wadan su, sunyi furuci  da laifin su sun hada aiki na kwarai da wani mummuna, akwai tsammanin Allah ya karbi tubansu, lalle Allah Mai gafara ne Mai jinkai ).

Suna cewa:-  (Ya Ubangijinmu mun zalunci kawunanmu to muddin ba ka gafarta mana ba ka jikanmu ba zamu kasance cikin hasararru)

Suna cewa :-(Ya Ubangijinmu ka gafarta mana zunubanmu da barnanmu a cikin al'amarinmu, kuma ka tabbatar da digadigan mu , kuma ka taimake mu akan mutanennan kafurai).

Suna cewa:- (Ya Ubangijinmu kar ka rike mu idan mun yi mantuwa ko kuskure, Ya Ubangijin mu  kuma kada  ka aza nauyi a kan mu kamar yanda ka aza nauyi akan wadanda suka gabace  mu .  Ya Ubangijin mu kada ka sanya mu daukan abin da babu iko gare mu  da shi, kuma ka yafe mana , kuma ka gafarta mana  kuma ka yi jinkai  a gare mu kai  ne Majibincinmu sabo da haka ka taimake mu akan mutanennan kafurai).

Misalin tawaga biyu kamar makaho da kurma   da mai gani da mai ji shin za su yi daidai ase ba za ku wa'azantu  ba (Godiya ta tabbata ga Allah sai dai mafiya yawan su ba su sani ba ..

 

 

   HUDUBA TA BIYU

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah kamar yanda ya dace da girman  fuskanSa  da kasaitan ikon sa  kuma  godiya na sa ne kamar yanda ya dace  da  yalwan afuwar sa  da kayun kayutatawanSa kuma kyakkyawan yabo na shi ne kamar yanda ya dace da girman rahamar sa da yalwan gafararSa.

Yana da godiya na har abada , godiyan da  adadi bai iyakance shi ,  kuma har abda ba zai katse shi ba , kamar yanda ya dace da a gode mi shi.

 Dukkan godiya na shi ne bisa ga ni'imomi  wanda ba sa kidanyuwa da da falalolin da  ba sa iyakantuwa , da kuma hukuncin da ba a maidawa , godiya na  shi ne bisa ga  rahamarsa wacce ta yalwaci dukkan komai na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah majibincin salihai, na shaida kuma shugabanmu Muhammadu bawan sa ne kumsa Manzon sa ne  shugaban masu takawa

(Ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah ku kasance tare da masu gaskiya ) ku tuna ni'imomin Allah  kuma ku tuna ranakun Allah  ku kiyaye ni'imomin ; ta hanyan da'a  wa Allah , kuma ku nemi karin su ta hanyan godewa Allah , ku dauki izina a cikin halittun Allah da kuma abin da aka nuna muku na daga ayoyin Allah , ba abin da ya fi zama wa'azi a gare ku kamar maganan Allah .

Allah yana cewa:- Ka ce: « Godiya ta tabbata ga A1lah, kuma aminci ya tabbata bisa ga bãyinSa, waɗanda Ya zãɓa. » Shin Allah ne Mafi alhẽri koabin da suke yin shirki da Shi?
60. Kõ wãne ne Ya halitta sammai da ƙasa kuma Ya saukar muku, daga, sama, wani ruwa, Muka tsirar, game da shi, gõnaki mãsu sha'awa, ba ya kasancẽwa gare ku, ku tsirar da itãcensu? Shin, akwai abin bautãwa tãre da Allah? Ã'a, sũ mutãne ne suna daidaitãwa ( Allah da wani ) .
61. Kõ kuwa wãne ne Ya sanya ƙasa tabbatacciya, kuma Ya sanya kõguna a tsakãninta kuma Ya sanya mata manyan duwãtsu tabatattu, kuma Ya sanya wani shãmaki a tsakãnin tẽkuna biyu? Shin akwai wani abin bautãwa tãre da Allah. Ã'a, mafi yawansu ba su sanĩ ba.
62. Kõ wãne ne yake karɓã , kuma ya sanya ku mamãyan ƙasa? Shin akwai wani abin bautawa tãre da Allah? Kaɗan ƙwarai kuke yin tunãni.
63. Kõ wãne ne yake shiryarwa a cikin duffan ƙasa da tẽku,kuma wãne ne Yake aikõwar iskõki dõmin bãyar da bushãra a gaba ga rahamarSa? Ashe akwai wani abin bautãwa tãre da Allah? tsarki yã tabbata ga Allah daga barin abin da suke shirki da Shi.

64. Kõ wãne ne yake fã ra halitta sa'an nan kuma ya mayar da ita,kuma Wãne ne Ya azurta ku daga sama da ƙasa? Ashe, akwai wani abin bautãwa tãre da Allah? Ka ce: « Ku kãwo dalĩlinku idan kun kasance mãsu gaskiya. »
65. Ka ce: « Bãbu wanda ya san gaibi a cikin sammai da ƙasa fãce Allah. Kuma bã su sansancẽwar a yaushe ne zã a tãyar da su. »
66. Ã'a, saninsu ya kai a cikin Lãhira Ã'a, sunã cikin shakka daga gare ta. Ã'a, sũ da gare ta makãfin zũci ne.
67. Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: « Shin idan mun kasance turɓaya, mu da ubanninmu, shin, haƙĩƙa, waɗanda ake fitarwa ne? »
68. « Lalle ne, haƙĩƙa, an yi mana wa'adi ga wannan, mũ da ubanninmu, daga gabãnin haka. Wannan bã kõme ba ne fãce tãtsũniyõyin farko. »
69. Ka ce: « Ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba, yãya ãƙibar mãsu laifi take? »
70. Kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma kada ka kasance a cikin ƙuncin rai daga abin da suke ƙullãwa na mãkirci.
71. Kuma sunã cẽwa, « A yaushe wannan wa'adi ( zai auku ) , idan kun kasance mãsu gaskiya? »
72. Ka ce: « Akwai fatan sãshen abin da kuke, nẽman gaggãwarsa, ya kasance yã kuturta ( 1 ) a gare ku. »
73. Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa Mai falala ne a kan mutãne kuma amma mafi yawansu, bã su gõdẽwa.
74. Kuma lalle Ubangijinka, haƙĩƙa Yanã sanin abin da ƙirãzansu suke, ɓõyẽwa, da abin da suke hayyanãwa.
75. Kuma bãbu wata ( mas'ala ) mai bõyuwa, a cikin sama da ƙasa fãce tanã a cikin littafi bayyananne.
76. Lalle ne wannan Alƙur'ãni ( 2 ) yanã gaya wa Banĩ Isrãĩla mafi yawan abin da sũ suke sãɓa wa jũnansu a ciki.

77. Kuma lalle shi haƙĩƙa shiriya ce da rahama ga mũminai.
78. « Lalle Ubangijinka Yanã yin hukunci a tsakãninsu da hukuncinsa, kuma Shi ne Mabuwãyi, Masani. »
79. Sabõda haka, ka dõgara ga Allah, lalle ne, kai ne a kan gaskiya bayyananniya.
80. Lalle ne kai, bã ka jiyar da matattu, kuma bã ka sa kurãme su ji kiranka, idan sun jũya sunã mãsu bãyar da bãya.
81. Kuma kai ba ka zama mai shiryar da ɗimammu daga ɓata ba. Bã ka jiyarwa fãce wanda yake yin ĩmãni da ãyõyinMu. To, sũ ne mãsu sallamãwa ( al'amari zuwa ga Allah ) .
82. Kuma idan magana ta auku a kansu, Munã fitar musu da wata dabba ( 1 ) daga ƙasa, tanã yi musu magana, cẽwa « Lalle mutãne sun kasance game da ayoyinMu, ba su yin ĩmãnin yaƙĩni. »
83. Kuma a rãnar da Muke tãrãwa daga kõwace al'umma, wata ƙungiya daga waɗanda suke ƙaryata ãyõyinMu, sai ga su anã kangesu. ( ga kõra )
84. Har idan sun zo, ( Allah ) zai ce, « Ashe kun ƙaryata ãyõyinNa, kuma ba ku kẽwaye su da sani ba? To, mẽne ne kuka kasance kunã aikatãwa? »
85. Kuma magana ta auku a kansu, sabõda zãluncin da suka yi. To, sũ bã su da ta cẽwa.
86. Shin, ba su gani ba, cẽwa, lalle Mũ, Mun sanya dare dõmin su natsu a cikinsa, kuma da yini mai sanya gani? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi! Dõmin mutãne waɗanda suka yi ĩmãni.
87. Kuma da rãnar ( 2 ) da ake hũsa a cikin ƙaho, sai wandayake a cikin sammai da waɗanda suke a cikin ƙasa su firgita, fãce wanda Allah Ya so, kuma dukansu, su je Masa sunã ƙasƙantattu.
88. Kuma kanã ganin duwãtsu, kanã zaton su sandararru, alhãli kuwa sũ sunã shũɗẽwa shũɗewar girgije, bisa sanã'ar Allah wanda Ya kyautata kõwane abu. Lalle Shi, Mai lãbartãwa ne game da abin da kuke aikatãwa.

89. Wanda ya zo da kyakkyawan aiki guda, to, yanã da mafi alhẽri daga gare shi. Kuma sũ daga wata firgita, ( 1 ) a yinin nan, amintattu ne.
90. Kuma wanda ya zo da mugun aiki, to, an kife fuskõkinsu a cikin wuta. Ko zã a sãka muku fãce da abin da kuka kasance kũnã aikatãwa?
91. ( Ka ce ) : « An umurce ni, in bauta wa Ubangijin wannan Gari, ( 2 ) Wanda Ya mayar da shi Hurumi, kuma Yanã da dukan kõme. Kuma an umurce ni da in kasance daga mãsu sallamãwa. »
92. « Kuma inã karanta Alƙur'ãni. » To, wanda ya shiryu, yã shiryu ne dõmin kansa kawai. Kuma wanda ya ɓãce, to, ka ce: « Ni daga mãsu gargaɗi kawai nake. »
93. Kuma ka ce: « Gõdiya ta tabbata ga Allah. Zai nũna muku ãyõyinSa, har ku sansu. » Kuma Ubangijinka bai zama Mai shagala daga barin abin da kuke aikatãwa ba.


ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق