الجمعة، 31 يوليو 2020

YALWAR AFUWAR ALLAH

اسم المترجم : أمين سعد عبد الله

اللغة : الهوسا

التاريخ : 10-12-1441هـ

Hudubar Juma'a a masallacin Annabi na Shaikh Abdulbari dan Awad Assubaiti 10-12-1441AH /31-7-2020AD

 

Yalwar afuwar Allah

 

Hudubar farko

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wadda ya sanya aljanna sakayyar hajji  mabruri,    ina kyautata yabo gare shi, tsarki ya tabbata a gare shi   kuma ina gode mishi  bisa dukkan falala da alheri  da ya saukake na  shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya  shi ne Mai yafiya kuma Mai gafara,  shi ne Mai yawan yafiya kuma Mai gafara  kuma na shaida shugaban mu kuma Annabinmu  Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne  ya bautawa UbangijinSa da yakini zuciyarsa  sai ta zama tana farin ciki   da kaunarsa  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabban shi, duk wanda ya kaunace su  shine abin taimakawa kuma mai samun lada.

Bayan haka;  

 Ina muku wasiya da ni kaina da tsoron Allah, Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Ya ku wadan da suka yi imani ku ji tsoron Allah cancancin  tsoron shi kada ku mutu face kuna musulmai ).

Yafiyan  Allah kalma ce da take jefa natsuwa a cikin zuciya  da kwanciyan hankali a cikin zuciya  da kuma sika cikin abin da yake  wurin Allah.

(Hakika Allah ya kasance Mai yafiya ne kuma Mai yawan gafara yana  yafewa wanda yayi zunubi  kuma ya gafartawa wanda ya yi laifi kuma yana rangwantawa wanda yayi kuskure) ( shi ne wanda ya ke karban tuba daga bayinSa kuma yake yafewa daga kusakurai  kuma ya san abin  da kuke aikatawa ).

 

Na daga cikin kyawun afuwar Allah yana son  masu tuba  kuma yana farin ciki da komawa zuwa gare shi

Na daga cikin yalwan afuwar Allah da ribanya kyawawa da yake yi da kuma bada lada bisa ga nufan yin abu  ba tare da munana ba.

 Na daga  cikin kyakkyawan afuwan Allah shi ne yakan canza munanan  ayyuka ya maida su  kyawawa  bayan tuba  na gaskiya, idan bawa ya daina aikata aikin haramun  ya fiskanci sabuba na tuba  da da'a  ya kara imani tare da imaninsa  sai ya karfafi dalilai na imani  a cikin zuciyarsa, sai Allah ya karrama shi  da  kyakkyawan yafiyarSa.

Abin mamaki da yalwa da kuma kawa irin na afuwar Allah  Mai tsarki da Daukaka,

 Allah ya ce :- (sai wanda ya tuba ya yi imani kuma ya yi aiki , aiki na  kwarai to wadannan Allah zai canza musu laifukan su kyawawa, Allah ya kasance Mai gafara ne Mai jin kai) .

Na daga cikin yalwan afuwar Allah  cewa rahamarSa tana rigayar fushinSa  yafiyarSa kuma tana riga ukubarSa,  Buhari ya rawaito shi daga Hadisin Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :- Na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa :- (Lallai  Allah yayin da ya yi halittan halitu  ya rubuta a wurin shi a saman al'arshin shi, lallai  rahama ta ta rigayi fushi na ).

Na daga cikin yalwar afuwar Allah  shi ne jinkirtawa bayinSa da yake yi  kafin ya kama su domin  Allah Mai tsarki da daukaka shi  yana fiskantar jahilcin bayi da hakuri  sa'annan kuma zunubinsu yana fiskantar sa da gafara,  sannan bayyana sabo kuma yana fiskantar shi da suturtawa, kafurcewa ni'ima  kuma Allah yana fiskantar ta  da ni'imtarwa.

    Na daga cikin yalwar afuwar Allah da ya sanya masu kankare zunubai nau'uka daban –daban, na daga cikin masu kankare zunubai akwai yalwata alwala, da ambaton Allah karshen farillu, da yawan taku zuwa masallatayya, da azumin ramadana da azumin ranar Arafa da azumin ranar Ashura., da adu'ar kaffatul majlis da umara da Hajji da sauke sallolin farilla. Da sadaka da hakuri da halartan majlisai na zikiri, da salati ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Na daga cikin koyarwar Annabi kwadayin neman afuwa da yafiya yana rokon Allah a lokacin da ya wayi gari da lokacin yammaci (Ya Allah ina rokonka afuwa da waraka a addini na da duniya ta da iyalai na da dukiya ta).  

Allah ka sa min albarka ni da ku cikin Alkur'ani mai girma.

 

HUDUBA TA BIYU

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga wanda  da ni'imarSa ce kyawawa ke cika  ina kyautata yabo a gare shi kuma ina gode mishi bisa kyautarSa  masu yawa,  na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya  Abin bautar halittu na shaida  shugabanmu Muhammad bawanSa ne kuma Manzon sa ne , shi ne abin koyin mu a duk wani yanayi da aka shiga na tsanani  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  da sahabbansa ma'abota falala abin girmamawa.

  Bayan  haka, ina muku wasiyya da kaina da tsoron Allah  duk  wanda ya dimanci da'a ga Allah  to zai rabauta da afuwar Allah.

 

Tare da wannan falala mai girma da kuma yafiya mai yawa,  mutum zai kiyaye daga ruduwa da afuwar Allah  da girman karamcinSa  Allah Madaukakin sarki ya ce :-(Ya kai mutum  mai ya  ruda ka  game da Ubangijin ka Mai karamci ).

 Ya dace a wadannan kwanaki a bayyana manyan alamomi na musulunci na daga ciki akwai  kabbarori  wanda suke masu kaidi  karshen salloli na farilla,  wanda ke farawa tun daga safiyan ranar arfa  har zuwa faduwan ranar karshe na ayyamut tashrik .

 Allah Mai girma ba abin bautawa da gaskiya sai Allah  kuma Allah Mai girma  ba bu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma  Allah Mai girma dukkan yabo da godiya na shi ne.

  ku saurara kuma ku yi salati  ya ku bayin Allah bisa ga Manzon nan na shiriya  hakika Allah ya karrama ku a littafinSa.

     

 

 


ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق