الثلاثاء، 14 يوليو 2020

DARUSA DAGA SULHUN HUDAIBIYYA A WANNAN YANAYI NA KORONA

اسم المترجم : أمين سعد عبد الله

اللغة : الهوسا

التاريخ : 19-11-1441هـ

Hudubar Juma'a a masallacin Annabi na Shaikh Abdulbari dan Awad Assubaiti 19-11-1441AH / 9-7-2020AD

 

Hudubar farko

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah, bayan haka.

Tarihin Annabi kan haskaka mana hanyar tafiya a rayuwa. Na daga cikin shafuka na sira masu kamshi akwai tarihin sulhun Hudaibiyya da darusansa da  mawakif na sa da abin da ya faru a ciki Allah ya ambace shi da budi Allah Madaukakin sarki ya ce:- (Lalle Mu Mun yi ma budi wanda yake budi bayyananne).

Sahabbai sunyi bushara  da mafarkin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya gani cewa za su shiga Makka kuma su yi dawafi  a dakin Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Lalle ne Hakika Allah ya gaskata wa ManzonSa mafarkinsa da gaskiya: Lalle  za ku shiga masallacin Harami in Allah ya so,  kuna  amintattu kuna masu aske kawukan ku da  masu saisaye , ba ku jin tsoro).

  Mutum dubu da dari hudu  daga cikin masu umra suka tafi  tare da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  suna da kuzari game da abin da suke ji  na karfin guiwa,  zukatan su na cike da  shu'uri  suna masu nufan dakin kaba  bayan yankewan shekaru da  wannan wurin din mai albarka  wanda zukata ke karkata zuwa gare ta  wanda ta kasance kuma bata gushe ba  kuma baza ta gushe ba  wato shudewan zamani da kuma lokaci , alkibla ne da zukata kuma  wurin karkata ne da zuciya  rayuka kan samu natsuwa a farfajiyan ta  kuma   ta dauki ibra a kasanta kuma  ta zubar da hawaye   Ibrahima alaihissalam  ya mata adu'a (Allah Ubangiji lallai na zaunar daga cikin  zuri'a ta  a  kwari wanda ba yi da shuki  a wurin dakin ka mai alfarma , Ya Ubangijin mu domin su tsaida sallah ka sanya  zukata na mutane na karkata zuwa gare su )

Shauki zuwa ga masallaci mai alfarma  da kwadayin wurare na alheri da ibada  dalili ne na rayuwan zukata  kuma dalili ne na hasken zuciya da kuma lafiyan ta  Allah Madaukakin sarki ya ke cewa (Lallai kawai masu raya masallatan Allah su ne wadan da suka yi imani da Allah da ranar lahira  kuma suka tsaida salla  suka bada zakksa  ba su ji tsoron kowa  ba sai Allah  to, ya wuci wadannan su kasance cikin shiryayyu) Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi harama  daga zulhulaifa  ya fara talbiya  asaniyya  kusa daga makka  asaniyya kusa da makka taguwar sa ta durkusa wato alkasuwa wato ta kwanta taki ta tafi  daga wurinta   sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :-( Ba kin tafiya ta yi ba  kuma wannan ba dabi'arta ba ne sai dai akwai abin da ya  rike ta ne  wanda ya rike giwa ,)Buhari ne ya rawaito

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tunkude daga  taguwarsa alkasuwa  yayin da aka tsarge ta ta yi tirjiya  da fadin sa cewa a'a wannan ba dabi'ar ta ba ne  wannan baya cikin halinta  domin ya bada hanzari ga dabba wanda yake ba magana take yi ba  sabo da sanin halin ta na asali  da kuma wato siranta mai kyau  domin ya koyar da al'umar sa darasi wurin mu'amala da  hukunci mai kyau bisa ga maukifi da aka samu  akai da kuma  cikin dauke  laifi da samar da uzuri da mutumin da yake da  wasu abubuwa da suke abun shaida na alheri  da falala a baya  Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tura Usman  Allah ya yarda  da shi da sako na musulunci  wato ita ce zaman lafiya ba kiyayya ba  ya basu labari cewa mu ba mu zo don yakan wani ba  Usmanu sai ya zo garin makka ya gayawa Kuraishawa  game da sakon Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cewa sun zo ne suna masu ziyaran dakin kaba  suna masu girmamawa da alfarmarsa da kuma dawafi da shi  sai suka ki , aka samu kai komo tsakanin Manzon Allah da kuraishawa  Annabi ya yi amfani da tausayawa  a cikin al'amura  da kuma dauke kai cikin abin da ba zai cutar da addini ba  wanda kuma ba zai bata sha'ani  na hakkin Allah ba Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke cewa (Na rantse da wanda raina yake hanun sa  ba za su tambaye ni wata khudda ba wanda suke girmamata  na alhurmomin Allah face na basu ita) Buhari ne ya rawaito .

Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya rinjayar da  bangare na maslahan kare jinayen musulmai   da kuma  kubutar rayuka kuma yayi dubi zuwa ga karshen al'amari  a assasawa al'uma fikhu na manufa  da kuma gaya  ya kasance a makka a hudaibiyya  mutane dayawa daga cikin muminai  da kuma masu rauni daga maza da mata  da 'yan yara , da'ace  sahabbai sun shiga makka aka samu yaki a tsakani da ba wanda zai aminta da  ya kubuta  daga a taba shi  kamar yanda Allah mai tsarki da daukaka yake cewa :-(Kuma ba domin wadan su  maza muminai da wadan su mata muminai ba  ba ku sansu ba,  ku taka su  har wani aibi ya same ku daga gare su ba  ba da sani ba  (da Allah ya yi muku izinin yaki )

Amfanin sulhun ya bayyana  karara  da kuma fa'idoji na zahiri wanda  ya kasance karshen shi bude  garin makka da kuma musuluntar mutanenta  da shigan mutane addinin  Allah  tawaga-tawaga.

 Na daga cikin dubi zuwa ga makoma na al'amura kasancewan haji a wannan shekara  wani nau'i ne daban, an kebe shi da wani adadi iyakantacce da wasu ka'idoji  da aka shar'anta  a karkashin wannan yanayi na korona ,  da cutarwanta ya game komai  annobanta ya taba ko wani abu ,  wannan matakin mai hikima wanda    jagorori suka dauka  na mamlakar arabiyya saudiyya  ita ta dace wato tana cikin abubuwa da suke mafi muhimmanci  yana tafiya tare da manufofi na shari'a  kuma yana fadawa ne akan maslahan musulmai  wurin kiyaye rayuka da kuma tunkude duk wani abu da   zai ka ga hadari  wanda yake tabbatacce , ko kuma wanda aka fi  rinjayin zato akan shi  da kuma yin taka tsantsan  wurin yaduwar wannan annoba din  da kuma cututtuka  masu yaduwa.

 Tattaunawa da aka yi  ya haifar da  ittifaki da tarihi ya ambace shi  da sulhun hudaibiya  wanda sahabbai suka koma zuwa garin madina  ba tare da sun yi dawafi a dakin ka'aba ba  sai dai Allah ya girmama su ya  yalwata musu lada  ta inda ya yarda da su sai  yake cewa  hakika Allah ya yarda da muminai  ya yin da suke mubaya'a  a gare ka  karkashin bishiya shi ya san abin da ke cikin zukatan su  sannan ya saukar da natsuwa a gare su kuma  ya basu ladan budi a kusa,  da wannan ne zai bayyana wa musulmi  cewa idan yayi iya kokarin shi  ya yi iya abin da zai iya  wani abu ya yi shamaki tsakanin shi da ibada  don sauke wannan ibadan  to kada ya yi fushi kuma kada ya yi bakin ciki domin za a maida mishi abin da ya rasa  ladan shi kuma yana rubuce falalan Allah kuma yana da yalwa  an karbo daga Abdullahi Dan Abbas  Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :- Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:-(Cikin abin da ya ke rawaitowa daga Ubangijin shi  mai tsarki da daukaka  lallai Allah ya rubuta kyawawa da munana  sannan ya bayyana haka  duk wanda ya nufi aikata kyakkyawa bai aikata ba to za a rubuta  mishi ladan shi cikakke   idan kuma ya nufi aikatawa sai ya aikata  to za a rubuta mi shi ladan shi guda goma  har zuwa  dari bakwai  zuwa ga ribi mai yawa  idan kuma ya himmatu da mummuna bai aikata ba to Allah zai rubuta mishi kyakkyawa guda cikakke,  I dan kuma ya himmatu da ita sannan ya aikata ta to  za a rubuta mi shi  mummuna guda daya) Buhari ne ya rawaito da muslim.

Madalla da irin wannan falala mai girma  wanda mai jinkai mai rahama ya ke kwaranyo da shi  zuwa ga bayin shi muminai  yayin da aka gama sulhu tsakanin Manzon Allah  da kuraishawa  Manzon Allah ya tashi sai ya ke cewa  ku tashi ku soke  abin yankan ku  kuma ku aske kawunan ku , ya fadi haka  har sau uku ba daya daga cikin su da ya tashi  sai wani alamomi na bakin ciki ya bayyana a gare shi  a zaton wasu daga cikin su wannan sulhun ci baya ne  sai ummu salma ta yi nuni  zuwa ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tace ya Annabin Allah kana so a yi hakan? To ka fita kada ka ka fadi ko kalma ga daya daga cikinsu, har sai ka soke rakuminka, ka kira mai askinka ya maka aski, sai ya fita bai yi wa kowa magana ba daga cikinsu ya aikata haka ya soke dabbarSa kuma  ya kira mai askinSa ya masa aski yayinda suka ga haka kowa sai ya tashi ya soke dabbarsa sai wannan yayiwa wannan aski wannan ma ya yiwa wannan aski har sashinsu ya kusa ya ti fada da sashi saboda bakinciki ) Bukari ne ya rawaito

Shawara mai zurfi daga ummu salama Allah ya kara yarda a gareta ga Annabi manzo wanda ya canga akwalar abinda ya faru na waki'I a wannan mawuyacin yanayi wannan maukifi da waninsa da yawa yana tabbatar da matsayi da daukaka irin na mace a musulunci da karrama musulunci gareta da kuma karfafanta ga sakon musuluncin lallai mace mai hankali mai tunani mai ra'ayi da ayyukanta na da dauri wurin sana'anta wato rayuuwa da gina shi da kuma habaka shi .

Ummu salama  Allah ya kara yarda a gareta ta raya da shawaranta daya daga cikin mafi rukunnai na tarbiyya abun koyi a aikace wanda ita ce mafi yawan amfani a dasa ginshiki kuma dabi'u da kuma gyara halaye .

Yana bayyana a sulhul hudaibiya kaunar sahabbai ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wanda ba a kwatanta shi da kuma daukaka wanda ba irinsa , abin da ke nuni ga haka Urwa daya daga cikin jakadun kuraishawa zuwa ga Annabi  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi fadinsa ga mutanensa kaman yanda ya zo a cikin Buhari sai Urwa ya koma ga mutanensa sai ya ce ya mutane na: '' wallahi ; hakika naje wurin sarakuna naje ga kaisar da kisra da Najashi wallahi ni ban taba ganin wani sarki ba ko da su daya wanda mutanensa ke girmama shi kamar yanda mutanen Muhammadu da sahabban Muhammadu suke girmama shi ba wallahi in da zai fitar da majina to face sai ta fadi a tafin hanun daya daga cikinsu ya shafe a fiskansa da kuma fatansa , idan ya umarce su gaggawa suke yi don su aikata umarninsa idan ya yi alola suna dab da su yi fada da juna wurin ruwan alolansa, idan ya yi magana sai su sassauta muryansu gaba gare Shi ba sa iya daga ido su yi dubi zuwa gare shi saboda girmama shi lallai shi yabijiro muku da wata hanya ta shiriya to ku karbeta''. 

 

Huduba ta biyu :

             

Yayinda Suhailu dan amru ya zo don tattaunawa da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ga jakadan kuraishawa manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai ya ke cewa: (hakika al'amarinku ya saukaka) Bukari ne ya rawaito ,

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi tafa'a'ul wannan abin nanatawan  musulmi a cikin al'amura masu jujjuyawa zai yi fatan alheri kuma ya kyautata zato ga Ubangijinsa a irin wannan yanayi na annoba muna kyautata zato ga ubangijinmu muna sakankancewa cewa lallai  yaye bakin ciki na tahowa bala'i kuma na gushewa kuma komi zai koma daidai iska a bigire mai tsarki ya kwanta ya tsarkaka ya yi dadi zukata su je su yi dawafi da jikunkuna a ka'aba sannan kafafuwa su taka su yi sa'ayi tsakanin safa da marwa ba da jimawa ba mu'munai za su yi farin ciki Allah Madaukakin sarki ya ce : (Hakika Allah ya gasgata ManzonSa da mafarki da suka yi na gaskiya cewa za ku shiga masallacin alharam in Allah ya so kuna cikin amunci kuma kuna masu aske kawunan ku kuna masu gajarta gashinku ba kwa tsoro).      

     


ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق