خطبة عيد الأضحى
لفضيلة الشيخ أحمد طالب
اسم المترجم : أمين سعد عبد الله
اللغة : الهوسا
التاريخ : 10-12-1441هـ
Hudubar babbar
sallah na masallacin Annabi tare da Shaikh Ahmad bin Hamid Al dalib 10-12-1441AH / 31-7-2020AD
Hudubar farko:
Allahu Akbar
Allahu Akbar Allahu Akbar
Allahu Akbar
Allahu Akbar Allahu Akbar
Allahu Akbar
Allahu Akbar Allahu Akbar
Allahu Akbar
kabiran , walhamdu lillahi kasiran , wa subhanallahi
bukratan wa asila.
Allah Mai girma Abin
girmamawa.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Abin
daukakawa kuma tsarki ya tabbata ga
Allah abin tsarkakewa kuma ba abin
bautawa da gaskiya sai Allah Abin kadaitawa
babu dabara ko karfi sai ga Allah Abin dogaro, abin fauwalawa na shaida
ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya muna masu
tabbatarwa da kuma kadaitawa, na shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma
ManzonSa ne tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi da aminci mai kari.
Tsarki ya
tabbata ga Allah kuma godiya ta tabbata
ga Allah ba abin bautawa da gaskiya sai
Allah , kuma Allah mai girma ba
dabara ko karfi sai ga Allah Madaukaki
kasaitacce .
Mafi soyuwan
magana zuwa ga Allah kuma mafi soyuwan
magana zuwa ga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bisa duk abin da rana ta fito a kan shi wanda
take mafi daukaka wanda aka 'yanta kuma mafi kyau akan dawakai masu linzami da
sirdi da kuma mafi tsadar raguna da aka
sa musu alama na hadaya karbabbiya
Allah Mai girma
wanda zai cika tsakanin sama da kasa ya
kankare zunubai ko da ya kai tarukucen kumfan kogi ne da fadowansu zuwa kasa kamar yanda 'ya'yan
itace ke zuba .
Allah mai girma
……su ne dashen aljanna kuma masu tseratarwa
kuma garkuwa kuma Albakiyatussalihatu wanda ladan su ke wanzuwa sakayyan
su ke dauwama .
Allah mai girma…
suna shawagi a kewayen al'arshi mai
rahama suna da sauti kaman sautin kudan zuma suna
tunatarwa game da sahibinsu ba zai gushe
ba yana da abin da ake ambatonsa da shi gaba ga UbangijinSa, kuma Ubangijin ka bai kasance mai mantuwa ba.
Kuma ba wani
mutum da ya fi daraja a wurin Allah akan mumini wanda ya yi tsawon kwana a musulunci yana yawaita ambaton Allah .
Allah mai
girma…..
Sune sadaka na
gangan jiki kuma masu nauyaya
mizani kuma masoya zuwa ga Mai rahama
kuma da su ne ake nade sunayen Allah kyawawa da siffofin shi Madaukaka su ne masu tattaro abin da suka tarwatse kuma su ne matattara na yin da'a.
Allah Mai
girma….
(Ya
ku wadanda suka bada gaskiya ku ji tsoron
Allah ku fadi magana da take dai-dai, zai gyara muku ayukan ku kuma ya
gafarta muku zunubanku, duk wanda ya ke yiwa Allah biyayya da ManzonSa to
hakika ya rabauta, rabauta mai girma ) Ahzab 71
(Ya
ku wadanda suka yi imani ku ambaci Allah ambato mai yawa, ku yi masa tasbihi
safiya da maraice , shi ne wanda ya ke salati a gare ku da mala'ikun sa domin
ya fitar da ku daga duhu zuwa haske kuma ya kasance mai rahama ne ga muminai, gaisuwan su ranar haduwan su
da shi shi ne aminci , kuma ya tanada musu lada mai girma ) Ahzab 44.
Da shaidawa da
salla da azumi da zakka da jahadi da
hajjin dakin Allah ba wani abu ba
ne sai wasu sifofi ne na girmama Allah
da kuma wasu dalilai ne na ambaton Allah ba wanda zai samu daukaka da talbiya
ko ya koshi da tarwiya ko ya yi arfa da taskiya, ko ya tsaya wurin
girmamawa ko kuma ya kusanto da mika
wuya ko ya yi jifa da walaha ko ya yi
dawafi da hantsi, ko ya yi suka da kabbara
ko ya yi jifa da garji, face wanda harshen sa ya kasance danye ne daga amabaton Allah.
Allah mai girma.
HUDUBA TA BIYU
Allah Mai girma
Allah Mai girma Allah Mai girma Allah Mai girma Allah Mai girma Allah Mai girma
Allah Mai girma
(Ya
ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku lallai girgizan kasa wani abu ne mai girma, ranar da za ku ganta duk wata mai shayarwa
takans ingije abin da ta ke shayarwa, duk ma'abociya ciki zata sauke cikinta za
ka ga mutane cikin maye alhali ba maye ba ne suke ba face azabar Allah ce mai tsanani).
Haj 1-2.
Allahu akbar kabiran,
walhamdulillahi kasiran, wa subhanallahi bukratan wa asila,
Na shaida ba
abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya na
shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi da iyalan shi.
Ku yi laiha ya
ku bayin Allah –Allah ya karba muku laihanku ba wani abin da mai bauta zai
kusanci Allah da shi a ranar laiha da ya kai zubar da jinin dabbobin gida ga
Allah Ubangijin talikai ya ci ya yi
kyauta ya yi sadaka ya bayyana manyan
alamomin addinin Allah sunnan baban ku
Ibrahim amincin Allah ya tabbata a gare
shi da Annabinmu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi .
Ku sani cewa
baya inganta a laiha a yi da mara lafiya
wacce rashin lafiyanta ya bayyana ko
makauniyar dabba wacce makantanta ya bayyana
ko gurguwan dabba wacce bata iya
tafiya tare da masu lafiya, ko kuma mai
gutsurarriyar kunne wanda sama da rabin
kunnen ta ya gutsure ko kahonta , haka
nan banda ramemmiya wanda babu bargo a kashin ta , haka nan kuma ba a so a yi
da mara hakori wanda hakwaranta na gaba
suka cire daga asalin su ko kuma wacce
nonon ta ke motse kuma ya bushe tare da girma
haka nan kuma ba a so a yi da wacce ta kamu da cuta, cuta mai raba.
Ba ayi da
rakumi kasa da shekaru biyar , ko saniya
sai wacce ta kai shekaru biyu ba ayi da akuya sai wacce ta cika shekara ko rago sai wanda ya
cika wata shida rakumi na iya
isarwa mutane bakwai saniya ma na isarwa mutum bakwai abin da yake sunna shi ne a soke rakumi a
tsaye an daure hanun shi na hagu , a yanka saniya kuma da dabbobi a baryan su
na haku suna fiskantar alkibla kuma za a
ce ya yin yanka ''Bismillahi'' , bisa wajabcin
''wallahu akbar'' bisa mustahabbanci .
Abinda yake
sunna shi ne ya ci sulusi daga namanta ,
ya yi sadaka da sulusi yayi kyauta da sulusi.
Kada ya saida fatan ta ko wani
abu na daga gare ta kada kuma ya bawa mahauci
ladansa daga cikinta .
An sanya lokacin
yanka tun daga kare sallan idi har zuwa karshen kwanaki biyu bayan sa .
Allah mai girma Allah
mai girma ba abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Allah mai girma Allah mai girma dukkan yabo da godiya na Allah ne.
(Kuma
rakuman, mun sanya su a gare ku, a ibadojin Allah kuna da wani alheri babba a
cikin su . Sai ku ambaci sunan Allah a kansu suna tsaye akan kafafu uku sa'annan idan
sasanninsu suka fadi , to, ku ci daga gare su , kuma ku ciyar da mai wadar
zuci da mai bara . kamar haka muka hore
muku su, tsammaninku, kuna godewa .
Namomin
su ba za su sami Allah ba, haka jinainansu, amma takawa daga gare ku tana samun
Sa. Kamar haka ya hore su sabo da
ku, domin ku girmama Allah sabo da shiriyar da ya
yi mu ku . Kuma ka yi bushara ga masu kyautata yi.)
Ya ku bayin
Allah ku riki mai daga adua mai bude kofofin sama …salati da aminci ga limamin Annabawa
kuma shugaban masu takawa.
Adu'a.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق