اسم المترجم : أمين سعد عبد الله
اللغة : الهوسا
التاريخ : 12-11-1441هـ
Hudubar Juma'a a
masallacin Annabi na Shaikh Aliyu Bin Abdurrahman Al-Huzaifi 12-11-1441AH / 2-7-2020AD
Hudubar farko
Dukkan yabo da
godiya sun tabbata ga Allah, Majibinci abin godiya, Ma'aboci al'arshi mai
girma, wanda ake fata don yaye dukkan bakinciki mai tsanani, ina kyautata yabo
ga Ubangiji kuma ina gode masa bisa ni'imominSa ba mai iyakance su face shi
cikin wadanda muka sani da wadanda ba mu
sani ba, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi
da abokin tarayya, Mai aikata abin da ya so, na shaida Annabinmu kuma
shugabanmu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne. abin koyi a dukkan al'amura na
shiriya, Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka ga bawanka Muhammad da
iyalansa da sahabbansa wadanda suka taimaki musulunci da aiki da shi da kuma
kira zuwa gare shi da jahadi don daukaka kalmarSa har zuwa lokacin da tauhidi
ya wargaza duhun shirka,
Bayan haka ku ji
tsoron Allah Ubangijinku, ta hanyar tashi da wajibabbu, da kauracewa muharramai
za ku rabauta da daddadar rayuwa da
kyakkyawan karshe. Allah Madaukakin Sarki yace : (wancan
gida na lahira muna sanya ta ne ga wadanda ba su son dagun kai a doron kasa ko
barna, akiba na ga masu takawa).
Ya ku musulmai!
Hakika Allah ya
halicci wannan duniya ne don ya cika al'amarinSa a ciki kuma mashiarSa ta zartu a cikinsu ya yi hukunci a cikin Su da hukuncinSa da ba mai bin
sawu, kuma ya gudanar da su da gudanarwarSa wanda ke cike da hikima da iliminSa
da hikimarSa, da rahamarSa da kudurarSa, halittu na sanjawa ne daga wani yanayi
zuwa wani yanayi ne tsakanin falalarSa da rahamarSa da adalcinSa da hikimarSa.
Duk abin da ya samu
halitta na yalwa da alheri to fa tsaban falalarSa ne da rahamarSa, Allah
Madaukakin sarki ya ce : (Duk abin da ya
same ka na kyakkyawa to daga Allah ne) kuma Mai tsarki yace : (Duk abin da
Allah zai budewa mutane na rahama to ba mai rike ta kuma abin da ya rike to ba
mai turowa bayanSa kuma shi Mabuwayi ne
Mai hikima) Allah Madaukakin sarki ya ce : (Ashe baku gani
cewa Allah ya hore muku abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin kasa kuma
ya yalwata muku ni'imominSa bayyanannu da na boyayyu). Allah Madaukakin sarki ya ce
: (kuma duk
abin da ke gare ku na ni'ima to daga Allah ne). kuma Allah Mai
tsarki ya ce : (kuma idan kun kidaya ni'imar Allah ba ku iya lissafa ta,
lalle ne Allah Mai yawan gafara ne Mai jinkai).
To ni'imomi
mafarinsu daga Ubangiji ne,Mabuwayi da daukaka kuma karshen su ma daga gare Shi
ne ba wani da ya cancanci ni'ima daga gare Shi , na daga cikin rahaman Allah ga
bayin Shi da ya umarci bayi da su yi godiya bisa ni'imomi domin su wanzu su
karu, ya gargadi daga rashin godiya game da su domin kada su gushe ko su kauce,
sai Allah Mabuwayi ya ce (ka ambata yayin da Ubangijinku
ya ce muddin ku ka gode to lallai zan kara muku idan kuma ku ka butulce , to
lallai azabaTa na da tsanani)
Godiya wa
ni'imomi ana yi ne ta hanyan tashi da farillu da kuma rashin aikata alfahasha
da munkarai , ya kuma tafiyar da ni'imomi cikin abin da zai yardar da Allah
Madaukaki da kuma girmama Mai ni'ima Mabuwayi da daukaka , Allah Mai tsarki ya
ce :(ku godewa ni'imar Allah in kun kasance Shi
kadai ku ke bautawa) kuma Allah Madaukakin sarki ya ce :(ku yi aikin godiya ya iyalan Dauda , kuma kadan ne daga cikin
bayi Na masu godiya) wasu ma'abota ilimi suka ce ''Ba wani lokaci da zai zo a dare
ko wuni face a iyalan Dauda akwai mai ruku'i ko sujada ko kuma wani mai aikin da'a"
To ka tuna ya
kai musulmi ni'imomin Allah a gareka ka yi tunani yanda Ubangijinka ya fari
wadannan ni'imomi a gareka alhali kai kuma ba ka cancance su ba a gare Shi , ka
yi godiya game da su ga Ubangiji Mai tsarki , kamar yanda Annabi Muhammad tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi godiya ga Ubangijin Shi da su a fadinsa (Ya
Mai yalwan gafara : ya Mai shimfida hannaye biyu da rahama , Ya Ma'aboci dukkan
ganawa ya Makura na dukkan kokawa ya mai karamcin rangwame ya Mai girman kyauta
ya Mai fara ni'imomi tun kafin cancancanta ya Ubangijin mu ya Shugabanmu Majibincinmu
ya makuran bukatanmu ina rokon Ka ya Allah kar ka soya halitta ta da wuta)
Hakim ne ya rawaito a cikin Al- mustadrak daga hadisin Amru dan shu'aibu daga
babansa daga kakansa kuma ya ce hadisi ne ingantacce .
Tuna ni'imomi da
girmama su yana haifar da kaunar Allah da jin kunyarSa, ta yaya zai kasance daga mai hankali ya
fiskanci Mai kyautatawa da muzgunawa, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi ya ce (ku kaunaci Allah saboda kalace
da ya ke baku, na daga ni'imarSa , kuma ku kaunace ni saboda kaunan Allah, ku
so iyalan gidana saboda kaunata) Tirmizi ne ya rawaito kuma ya
inganta shi da Hakim kuma ya ce sahihi ne daga hadisin Ibnu Abbas Allah ya kara yarda a gare su , wannan na
daga cikin gudanarwan Allah da kyautanSa da alherori da albarkatu da kyawawa ga
bayi ba wani da ya isa ya cika ni'imomin Allah da da'a domin falala dukkan shi
na Allah ne Madaukaki sai dai Allah yana
yafiya kuma yana rahama yana bada falala kuma yana yarda da kadan na daga
ayyuka na kwarai da iklasi da kuma bin sunnah annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce (aikin dayanku ba zai
shigar da shi aljanna ba sai aka ce : ko kai ma ya Manzon Allah ? sai ya ce ko
nima sai dai Allah ya lullubeni da rahamarSa) Ahmad ne ya rawaito
daga hadisin Abu Huraira Allah kara yarda a gare su , Ibnu Rajab Allah ya mishi
rahama ya ce game da bayi na kwarai : sun kasance suna tuhuman ayyukansu da
kula da ayyukansu da tuban su kuma suna tsoron kada a ki karba musu sai hakan
ya kasance yana sanya musu tsananin tsoro , da yawan kokari cikin ayyuka na
kwarai , Hasan dan basari Allah ya mishi rahama ya ce '' na riski wasu mutane
da dayansu ya ciyar da abin da ya kai cikin doron kasa to da bai amunta ba
saboda girman zunubi a cikin zuciyansa''
ta tike.
Kamar yanda
alheri da ni'imomi da yalwa da hukuncin Allah ne da kaddararSa da falalanSa da
rahamarSa haka nan musibu da sharrori da
ukubobi duka da hukuncin Allah ne da kaddararSa da a'adalcinSa da
hikimarSa , Allah Madaukakin sarki ya ce :(Allah ne Mahaliccin
dukkan komai kuma Shi wakili ne ga dukkan komai) An karbo daga
Abdullahi dan Amr Allah ya kara yarda a gare shi shi da mahaifin shi daga
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (lallai Allah ya rubuta kaddarori na halittu kafin ma ya
halicci sammmai da kasa da shekara dubu hamsin , al'arshinSa kuma yana kan ruwa)
Muslim ne ya rawaito da Tirmizi .
Allah Mabuwayi
da daukaka ya halicci sabuba kuma ya halicci abin da ya ke bayan sabuba , Ubangiji
yana halitta da sababi kuma yana halitta ba tare da sababi ba , abin da ya so
shi ke kasancewa , abin da bai so ba baya kasancewa , yana yin jarabawa da
alheri kuma yana yin jarabawa da sharri , Allah Madaukakin sarki ya ce:(Hakika muna jarabtan ku da sharri kuma da alkairi a matsayin
fitina kuma gare mu ne za ku koma) , sai ya bada lada ga masu yin
da'a masu godiya kuma ya yi ukuba ga masu sabo masu juhudi (musanta ni'ima)
dukkan duniya na gudana ne bisa sunnar Allah yanda Allah ya so kuma ya bayyana
a cikin littafinSa to Allah mai girma Mai iko Mai tausayi Mabuwayi ,Mai hikima Shi
ne wanda ya kyautata duniya kuma ya ke tunkude shi Allah Madaukakin sarki ya ce
:(Yana gudanar da al'amari kuma yana saukar da ayoyi
daki daki ko za ku samu sakankancewa game da haduwa da Ubangijinku) AllahMai
tsarki ya ce :(Yana gudanar da al'amura ba wani mai
ceto face bayan izininSa , wancannin ku Shi ne Ubangijinku ku bauta miShi shin
ba za ku yi tunani ba?) Allah Mabuwayi ya ce:(Wanda ke cikin sammai da kasa suna tambayan Shi a ko wani
rana kuma yana cikin sha'ani)
An karbo daga
Abu Darda'i Allah ya kara yarda a gare Shi ya ce : Annabi tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Dukkan ko
wani rana yana cikin sha'ani na daga cikin sha'anoniSa ya gafarta zunubai ya
yaye bakin ciki ya amsa mai roko , ya dauke wa wasu mutane kuma ya sanyawa wasu
mutane) Bazzar ne ya rawaito .
Da duniya na tafiya ne a cikin zamaninta
kaman yanda mutane suke so da jarabawa bai faru ga Annabawa ba amincin Allah su
tabbata a gare su da kuma bai kasance suna da kyakkyawan akiba ba su da
mabiyansu da kuma wanda suka saba musu ba su kasance suna da nau'o'i na ukubobi ba sai dai hukunci na Allah ne Shi
kadan Shi , Allah Madaukakin sarki ya ce :(ka ce
lallai al'amari duka naShi ne) Allah Madaukakin sarki ya ce: (wadanda suke bautawa wani koma bayan Allah ba wani abin da
suka mallaka ko da tantanin kwallon dibino ba).
Musibu na
kankare laifuka ga musulmi kuma suna daga darajojin shi,
An karbo daga
Abu Huraira daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Bala'i ba zai gushe ba ga mumini da mumina a cikin
rayinsa da dansa kuma a dukiyarsa har ya hadu da Allah bayi da wani kuskure)
Tirmizi ne ya rawaito kuma ya ce hadisi ne hasanun sahihun da Hakim kuma suka
inganta shi.
An karbo daga
Muhammad dan Kalid Assulami daga babansa daga kakansa ya ce: na ji Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa : (lallai bawa idan wani matsayi ya tsere a gare shi daga
Allah to bai riske ta ba da aikin shi sai Allah ya jarrabe shi a jikinshi ko
kuma a dukiyansa ko kuma a dansa sannan Allah ya hakurtar da shi a kan haka har
ya riski wannan matsayi din da ya tsere mishi daga Allah Madaukaki)
Abu dauda ne ya rawaito shi da Ahmad da Abu ya'ala.
Bala'i na zuwa
ne gwargwadon karfin addinin mutun da kuma raunin shi, An karbo daga Mus'ab dan
sa'ad daga babansa ya ce : na ce : ya Manzon Allah : a cikin mutane wanene ya
fi bala'i sai ya ce: (Annabawa sannan sai
wadanda suka fi riko sai wadanda suka fi riko, ana jarabtan mutun ne gwargwadon
addininsa idan har ya kasance addininsa nada karfi to sai bala'insa ya yi karfi
idan ya kasance a cikin addininsa yana da rauni sai Allah ya jarrabe shi
gwargwadon addininsa bawa ba zai gushe ba yana haduwa da bala'ai har ya bar shi
yana tafiya a doron kasa bai da wani laifi tare da shi) Tirmizi ne
ya rawaito kuma ya ce hadisi ne hasan sahihi kuma Ibnu Maja ma ya rawaito shi.
Musibu kuma da bala'o'i da annobobi suna sauka
ne gamagari ; domin a bada lada ga al'umar musulmi saboda hakurin da suka yi da
neman lada a wurin Allah kuma abin lura ne ga mutane don su yi tunani cikin kofofi
na zunubai da suka aikata domin kada su maimaita irin zunuban saboda su aikata abin
da ya fi girma kuma saboda kada a yi musu ukuba da abin da ya fi girma domin su
wa'azantu da abin da suka kasance a ciki na daga ni'imomi kafin saukar bala'i
domin waraka ko lafiya ta tabbata a cikinsu da aminci da yalwa ta hanyar da'a, Allah
Madaukakin sarki ya ce: a cikin sunnoninSa (ya wuci Ubangijinku
ya muku rahama idan kun koma kuma muma mu koma)
Allah Mabuwayi
da daukaka ba ya dawwamar da annoba sai dai yana dauke ta idan ya so, ku jira
yayewa daga Allah , ku fiskanci bala'i da addu'a da kuma komawa zuwa ga Allah
domin lallai Ubangiji tsarki ya tabbata a gare Shi Mawadaci ne daga azabtar da
mutane sai dai Shi Allah Madaukaki yana so musu ne don su yi aiki na kwarai
kuma su kauracewa munanan laifuka, Allah Madaukakin sarki ya ce :(Idan bayiNa suka tambaye ka game da Ni ka ce: lallai Ni iNa
kusa kuma Ina amsa kiran mai kira idan ya kiraye Ni , to su amsa kira Na kuma
su yi imani da Ni ko za su samu shiriya) Allah Madaukakin sarki ya
ce: ( lallai rahamar Allah kusa ta ke ga masu
kyautata wa).
Allah ya sa mini
albarka ni da ku a cikin alkur'ani mai girma .
Huduba
ta biyu :
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai na shaida
ba abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi
kadai ya ke ba Shi da abokin tarayya Mai karfi kuma AlMatinu na shaida Annabinmu
kuma shugabanmu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne amintacce , Allah ka yi
dadin tsira da aminci da albarka bisa ga bawanKa da kuma ManzonKa Muhammad da iyalanSa da
sahabbanSa baki daya.
Bayan haka : ku ji tsoron Allah cancancin takawa ku yi riko da igiya mai
karfi na musulunci, ya ku bayin Allah ku sani lallai wadatuwan bawa
da kuma sa'adarsa yana cikin bukatuwansa
zuwa ga Ubangijinsa ne da yakininsa da hakan , Allah Madaukakin sarki ya
ce: (Ya ku mutane ku talakawa ne zuwa ga Allah kuma
lallai Allah kuma Shi Mawadaci ne abin godiya).
Lallai dukkan tabewa ga bawa da hasararsa da halakarsa gurin zatonsa
cewa ya wadatu daga Ubangijinsa kuma ya rudu da kansa da abin da Allah ya bashi
Allah Mai tsarki da daukaka ya ce: (lallai wanda ya
yi rowa kuma ya wadatu ya karyata kyakkyawa da sannu za mu kama shi da tsanani
ba zai amfane shi ba dukiyansa idan ya halaka) , an karbo daga
Abdullahi dan Abbas Allah ya kara yarda a gare su shi da mahaifinshi ya ce:
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (Ni'imomi guda biyu mutane da yawa suna hasara a cikinsu :
lafiya da kuma zama haka) Bukari ne ya rawaito .
Ya ku bayin Allah lallai Allah da mala'ikunSa suna salati ga Annabi ya
ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce mai yawa
.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق