الخميس، 2 يوليو 2020

FALALAR SALATI GA ANNABI

اسم المترجم : أمين سعد عبد الله

اللغة : الهوسا

التاؤيخ : 26-10-1441هـ                                                                                                                            

 

Hudubar farko

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga wanda ya cike manzancin sama da shari'armu,ya sanya Annabinmu ya zama cikamakin Annabawa da Manzanni ya sanya al'umarmu ta zama tsaka – tsakiya kuma mafi alherin al'uma da  a ka fitarwa mutane, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, yana halittan abin da ya so  ya kuma zaba, na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne  Al Musdafa Zababbe, daga cikin zababbun zababbu .

Ya shugabanci halittu ba ja ,  to shi ne bayyananne halittu na baya.

Annabin gaskiya wanda ya zo da gaskiya  mafificin halittu  kuma mafi kyaun su a dabi'u da halitta , kuma mafi fasahan su a wurin furuci.

Hakika ya isar da sako ya sauke nauyin amana kuma ya yi nasiha wa al'uma  ya yi jahada a tafarkin Allah cancancin jahadi har mutuwa ta zo mishi  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  da iyalan shoi da sahabban shi da wanda suka bisu  da kyautatawa har zuwa ranar sakayya .

 Bayan haka.

Bayan haka, lalle mafi alherin zance shine maganar Allah, kuma mafi alherin shiriya ita ce shiriyar Annabinmu Muhammad, kuma sharrin al'amura sune fararrunta, kuma dukkan bidi'a bata ce, kuma dukkan bata na wuta.

(Ya ku wadanda suka bada gaskiya ku ji tsoron Allah cancancin tsoronSa kada ku mutu face kuna musulmai)

Ya jama'ar musulmi!

Allah ya kan zabi Manzanni a cikin mala'iku da mutane,   hakika ya zabi Muhammad tsira da amincin Alla su tabbata a gare shi,  daga mafi tsada da kima na ma'adanai  kuma ya  girmama shi ya fifita shi akan sauran mutane ya sanya shiryarwar sa  shi ne ma'auni na fifiko kuma da kiyasi  bai bata ba , kuma bai ketare  haddi ba ,  kuma baya yin magana daga son zuciyar sa , (maganarsa)  bata zamo ba , face wahayi ne da ake aikowa, (mala'ika) mai tsananin karfi  ya sanar da shi ,  Ma'abucin karfi da kwarji sa'annan ya daidaita .

 Allah ya tsiratar da dan -adam ta dalilinsa  daga duhun shirka, da kudurkumin jahilci  da zurfin duhu, daga kuma tabarbarewan halaye da  dabi'u , da juyawar fidira  da kekkecewa  da radadi da zunubai da karkasuwa , sai ya kasance mai kwadayin shiryar da mu da tseratar da mu  da kuma samun walwalar mu Allah Madaukakin sarki ya ce :- (Lalle ne hakika Manzo daga cikin ku ya je muku .  abin da kuka wahala da shi mai nauyi ne a kansa. Mai kwadayi ne sabo da ku. Ga muminai mai tausayi ne,  mai jin kai .)

An karbo daga Abdullahi dan Amr dan As Allah ya kara yarda a gare shi cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya karanta fadin Allah a cikin sha'anin Ibrahim (Ya Ubangiji lalle su dinnaan sun batar da dewa daga cikin mutane  duk wanda ya bi ni to lallai shi, yana tare da ni )

Isa alaihissalam  ya ce :- (In za ka azabtar da su to bayin ka ne in kuma za ka gafarta musu to kai mabuwayi ne mai hikima ) sai Manzon Allah ya daga hannayen sa sai ya ce:- (Ya Allah al'uma ta  al'umata) sai ya yi kuka  sai Allah mabuwayi da daukaka ya ce ya Jibrilu tafi zuwa ga Muhammad ka ce  lallai mu za mu yardar da kai game da sha'anin al'umar ka  ba za mu musguna  maka ba)

An karbo daga Jabir  Allah ya kara yarda a gare su, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :-(Misali na da misalin ku kamar misalin  mutum ne ya kunna wuta  sai  kwari da fari suka rinka kokarin fadawa a cikin ta , shi kuma ya na kokarin tare su daga gare ta  to ni ina kokarin katange ku ne daga wuta  alhali ku kuma kuna kokarin ficewa daga hanuna ) Muslim ne ya rawaito

Na daga cikin bada kulawarsa ga al'umarsa akwai adana musu adu'arsa da yayi  a ranar  da mutum zai gujewa dan'uwansa da mahaifiyarsa da mahaifinsa, da matarsa da yaransa, kowane mutum a wannan rana da shanin da ya ishe shi.    An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  yace : ( ko wani Annabi na da adu'a karbabbiya, to ni na adana nawa don nemawa Al'umata ceto , za a bada ta in sha Allahu ga duk wanda ya mutu cikin al'uma ta bai hada Allah da wani). Tirmizi ne ya rawaito.

 


 

Ya ku bayin Allah!

Hakika Allah ya umarce mu da mu sakawa duk mutumin da ya kyautata mana, sai yace : (shin akwai wani abu ga sakayyar kyautatawa face  kyautatawa).

(To duk wanda ya yi muku wani alheri to ku kyautata masa).

Ku saurara! lalle na daga cikin hakkin Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da ya ke kan mu shine mu saka masa bisa kyautatawarsa gare mu, da falalarsa da ke kan mu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, to yin salati a gare shi na daga cikin mafi girman hanyar tsira. Da kuma sadarwa mafi kima, da kusanci mafi girma da da'a mafi tsarkaka. Kuma yana cikin mafi girman abin da mutum zai raya lokuta da shi. A ribanya kyawawa da shi, a daga darajoji da shi, a kankare laifuka da shi, a yaye bakinciki da bacin rai da damuwa, tare da ribin gomomin salati daga Allah.

AlHaitami yace hadisi ne mai daraja ta biyu wanda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : ( Ba wani bawa da zai tuna ni sai ya min salati face  Allah ya rubuta masa kyawawa goma ya kankare masa laifuka goma, ya kuma daga daraojinsa guda goma.

An karbo daga Ubayyu dan ka'ab Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: na ce ya Manzon Allah  ni ina yawaita salati a gare ka kamar nawa ne zan sanya na daga salati na ? sai ya ce:- '' iya abinda ka so'' sa ya ce: '' kamar rubu'i daya bisa hudu yayin da ka so  idan ka kara akan haka to, ya fi alheri a gare ka  , sai na ce kamar rabi fa sai ya ce : '' iya yanda  ka so idan ka kara akan haka ma  ya fi alheri a gare ka  sai na ce to zan yi biyu bisa uku  sai ya ce ka yi iya yanda ka so idan ma  ka kara akan hakan alheri ne a gare ka  sai naq ce to,zan sanya salati na gaba daya a gare ka ,  sai ya ce  : - '' to in dai haka ne za a dauke damuwan ka  a yafe ma zunuban ka  Tirmizi ne ya rawaito kuma ya ce hadisi ne mai daraja na biyu).

Ya ku jamaa'ar musulmi:

 Lallai Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi shi ne mafi karamcin  mutane , Allah ya hada imani da shi da imani da  kansa da biyayya gare shi da kuma biyayya ga kansa  da kaunar sa da kaunar Allah  da ambaton  Allah da ambaton sa , shaidawa na tauhidi  shi ne  daya daga cikin alamomi masu girma na musulunci ,  adireshin  imani  kuma shi ne ramzin  zaman lafi  kuma jumla na kiran salla ana maimaita shi a  wurin kiran salla a ko wani rana bisa kunnuwa  na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah na shaida Annabi Muhammad Manzon sa ne  imani ba ya kulluwa da daya daga cikin  shahada guda biyu sai an hada  ta da daya  sabo da haka ya wajaba a gare mu da shari'a na Allah da kuma hakkin sa  da ke kan mu  da kwadayin sa bisa  siran mu  da mu cika zukatan mu  da kaunar sa  da kimanta shi da girmama shi  da bin sunnar sa da tafarkin sa  .

Ku saurara lallai ne  yana daga cikin babbar  alama ta kaunarsa    da kuma wajibi na hakkinsa da sunnarsa da yake mafi karfi  da da'a ga Ubangijinsa   yawaita salati a gare shi (lallai Allah da mala'iku suna salati ga Annabi,  Ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce ) .

To ya bayin Allah : Ku yawaita salati ga Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ku motsa harsunan ku da shi  ku danyaya labban ku da shi .

Ya bayin Allah:  lallai Allah  hakika ya ribanya  ladan salati ga Annabi  ya girmama ma'abotansa da masu yin sa. An karbo daga Abu  Dalha Al-ansari Allah ya kara yarda a gare shi ya ce ( Manzon Allah ya wayi gari wata rana  zuciyan sa tsarkake cikin dadin rai ana gani a fiskan sa da walwala sai suka ce ya manzon Allah yau ka wayi gari cikin annashawa a cikin dadin rai  ana ganin haka a fiskarka sai ya ce :- haka ne  wani mai zuwa ya zo min daga wurin Ubangiji na mabuwayi da daukaka sai ya ce duk wanda ya ma salati guda a cikin al'umarka  , to Allah  zai rubuta mishi kyawa guda goma da ita kuma zai goge mishi  guda goma na laifuka da ita  zai daga darajojin shi guda goma kwatankwacin su.)

  An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara mishi yarda  ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a garew shi ya ce:- (Mafi dacewan mutane gare ni  ranar alkiyama shi ne wanda yafi  yawaita min salati )  

Ku raya zukata ya ku bayin Allah da ambaton sa  ku yi salati a gare shi don bin umarnin Allah  da koyi da sunnarsa da wafa'I da hakkin sa  da kusanci zuwa ga  Allah da girmamawa  da kauna da girmamawa ga Manzon Allah tsira da amincin  Allah su tabbata a gare shi  da kari wurin kyawawan ayuka da kuma kankare laifuka .

Ina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan abin jefewa (lallai Allah da mala'iku suna salati ga Annabi,  Ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce mai yawa.

HUDUBA  TA BIYU

 Dukkan yabo da godiya sun tabbata  ga Allah Ubangijin talikai wanda ya turo cikin ummiyyai  Manzo a cikin su wanda yana karanta musu ayoyin sa  kuma yana tsarkake su yana sanar da su littafi  da hikima ko da da can sun kasance kafin  haka cikin bata bayyananne .

Ya ku taron Musulmi:

Lallai yana daga cikin mafi tsadan adu'o'i da  zikiri kayan ado mafi haske  shi ne yawaita salati da aminci ga Annabi zababbe  a safiya da maraice  da hantsi da yammaci  ana yinta ne ga masu kauna  alama ce wata sima ce  wata shi'ar ne kamar a ranar Juma'a domin shi ne mafificin ranaku  , an karbo  daga Aus dan Aus Allah ya kara yarda a gare shi  ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :- (lallai na daga cikin mafificin ranakun ku shi ne ranar juma'a  a ciki ne aka halicci Adamu  kuma a ciki ne aka dauki ransa  a ciki ne kuma za a yi busa  a ciki ne kuma za a yi tsawa  to, ku yawaita salati a gare ni , domin salatin ku ana bijiro min da ita  Abu Dauda ne ya rawaito Albani ya  kyautata shi)

Duk wanda yake son Allah ya yabe shi kuma ya  girmama shi  kuma ya daukaka shi ya kambama shi  Mala'iku masu daraja   su ambace shi  a daga ambaton shi da darajojin shi da kuma matsayin shi to ya yawaita salati ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a ko wani yanayi  da ko wani lokaci da sauran ranakunsu , musamman idan ya zo wurin ambaton shi a magana ne . An karbo daga Aliyu dan Usaini daga Baban sa  cewa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce  :-  (lallai mai rowa shi ne wanda aka ambace ni a gaba gare shi bai yi salati a gare ni ba Tirmizi ne ya rawaito )

Ya ku bayin Allah:

Lallai salati ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  kusanci ne ba tare da kaidi  da lokaci ko kuma wuri ba, sai dai  tana wajabtane a  wasu lokuta daga ciki akwai  lokacin da aka ambaci sunan shi  a harshe  ko kuma lokacin da ka ji ya yin kiran salla. An karbo daga Abdullahi dan Amru dan As  cewa ya ji Manzon Allah tsira  da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa  (idan kun ji mai kiran salla na kiran salla to ku fadi abin da ya ke fada ,  sannan ku min salati ,    duk wanda ya min salati Allah zai mishi salati da ita guda goma  sannan ku nema min wasila  domin wani matsayi ne a aljanna domin  bata dace ba ga kowa sai wani bawa daga cikin bayin Allah  ina fata kuma in kasance ni ne shi  wanda ya roka min wasila  to cetota ta tabbata a gare shi   Muslim ne ya rawaito)

 

An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara mi shi yarda  ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :- ( Hancin shi ya dumbuli kasa duk mutumin da aka ambace ni  bai yi salati a gare ni  ba Tirmizi ne ya rawaito.

Ya ku bayin Allah:

Yin salati ga Annabi yana zama dole a wurare da dama daga ciki akawai  tahiyan karshe ,da  yayin shiga masallaci,  da kuma yayin fita daga gare shi  da yin adu'a da kuma  yayin musiba  na bakin ciki da yayin haduwa  da mutane  da taruwan mutane da kuma  tsakanin kabbarori na idi , da bayan kiran ladani, da wasu wurare daban da ba wannan ba  da lokutan da aka samu ya zo daga sunna .

Ya ku bayin Allah!

Salati ga Annabi na yiwuwa da ko wace siga aka yi, da kuma kowace jumla aka hada shi, sigogi daban- daban sun zo kuma dukkansu suna isarwa ga abin bukata, kuma sun gamsar wurin salati ga Annabi abin kauna,

    An karbo daga Abu Mas'ud Al0Ansari Allah ya kara mi shi yarda  ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya zo mana muna majlisar sa'ad bin Ubada, sai Bashir bin Sa'ad ya ce :Allah ya mana umarni da mu maka salati ya Manzon Allah, to yaya za mu maka salati? Sai ManzonAllah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi shuru har muka yi fatan ina ma da baa tambaye shi ba, sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :  ku ce ya Allah ka yi dadin tsira ga  Muhammad da iyalan Muhammad, kamar yadda ka yi dadin tsira ga iyalan Ibrahim ka yi albarka ga Muhammad da iyalan Muhammad kamar yadda kayi albarka ga iyalan Ibrahim a cikin talikai,  kai abin godewa ne kuma abin girmamawa, shi kuma sallama shi ne kamar yadda kuka sani )   

 

  An karbo daga Abu Humaid Assa'idi  cewa sun ce ya Manzon Allah, yaya zamu  yi salati a gare ka sai ya ce ku ce:- '' Ya Allah ka yi dadin  tsira ga Muhammad da matayen sa da zuri'ar sa ,  kamar yanda kayi dadin tsira ga iyalan Ibrahim ka sa albarka ga Muhammad da matayen shi da zuri'ar shi , kamar yanda ka sa albarka ga iyalan Ibrahim lallai kai abin godiya ne abin girmamawa .)

 Ya ku masoya ga manzon Allah :

Lallai salati ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na da faidoji da basa kididdiguwa suna da kuma tasiri da amfani da ba a iya iyakance su, a ciki akwai maslahohi na duniya da lahira wanda ba a  iya kwalkwale su  a duk lokacin da masoyi ya yawaita ambaton abin kaunarsa da halarto da shi a zuciyarsa da bijiro da kyawawan sa  da ma;anonin sa masu janyo kaunarsa , sai son ya ribanya , sai shaukinsa kuma ya karu  hakan sai ya kasance abu ne mai karfafa guiwa  zuwa ga binsa  , ba abin da ya fi kawo sanyin ido ga masoyi kamar ganin abin kaunarsa, ba abinda ya fi kawo mishi kwaciyar zuciya  kamar ambaton shi da halarto  da kyawawan sa .

Kuma duk lokacin da mutum ya juya baya daga ambaton sa sai kaunar sa ya ragu daga zuciyarsa.

Sa'annan ku sani  cewa salati ga Annabi tsira da amincin  Allah su tabbata a gare shi  kusanci ne da  da'a  da ake bijiro da shi gare shi  ku yi fatan su kasance sun dace da manhajinsa wurin bi ,  ku yi nesa daga wuce gona da iri da bin son rai da kirkiran bidi'o'i,  duk wanda ya yi wani aiki wanda babu umarnin mu  a ciki to an maida mishi.        

   

 

 

 


 


 

 


 

 

 


 

 


 

 


 

 


 

 


 


ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق