اسم المترجم : أمين سعد عبد الله
اللغة : الهوسا
التاريخ : 3-12-1441هـ
Hudubar Juma'a a
masallacin Annabi na Shaikh Abdul Muhsin
Al kasim 3-12-1441AH / 24-7-2020AD
Hudubar farko:
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah
Madaukakin sarki muna gode mishi kuma
muna neman taimakonsa , muna neman gafarar sa, kuma muna neman tsarin Allah
daga sharrin kawunanmu , da munanan ayyukanmu , duk wanda Allah ya shiryar da
shi babu mai batar da shi , duk wan da ya batar kuma babu mai shiryar da shi,
na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin
tarayya, kuma na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne, tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa
da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa.
Bayan
haka: ku ji tsoron Allah-
Ya
ku bayin Allah,- cancancin tsoronSa, ku yi murakabarSa a boye da bayyane.
Ya
ku musulmi!
Allah
na zaba a cikin halittun shi wanda ya so
kuma ( Ubangijinka na halittan abin da ya so
kuma ya zaba) sai ya zabi manzanni
daga cikin mala'iku, da mutane, ya zabi ambatonSa daga cikin magana,
kuma ya zabi dakunanSa daga doron kasa. Ya zabi ramadana da watanni masu
alfarma daga cikin watanni, Jahiliyya sun kasance suna kari a kwanaki ta
jinkirta don bin son rai, azuminsu bai zama a lokacinsa ba, hajjinsu kuma ba a
kan lokacinsa ba, kuma Allah ya yi mana falala da turo Annabinmu Muhammad tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma ga zamani ya zagayo kamar yadda ya
ke, hajjinsa ya kasance a zulhajji, ya fada a cikin hudubarsa : Lalle zamani ya kewayo kamar yadda ya saba a sifarsa tun
randa Allah ya halicci sammai da kasa)Buhari da Muslim.
Sai
adadi ya cika kidaya ya inganta al'amari ya koma bisa yadda ya gabata a
littafin Allah a farko.
Fifiko
tsakanin dararraki da ranaku na kira ne zuwa ga ribatan alherin da ke cikinsu,
kuma Annabinmu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kwadaitar bisa
ribatar ni'imomi da za su gushe ba makawa, sai ya ce : (Ka
Ribaci Abubuwa Biyar Kafin Zuwan Biyar :
Ka Ribaci Ƙuruciyarka Kafin Tsufanka, Ka Ribaci Lafiyarka Kafin Rashin
Lafiyarka,Ka Ribaci Wadatarka Kafin Talaucinka, "Ka Ribaci Lokacinka Kafin
Zuwan Shagula, Ka Ribaci Rayuwarka Kafin Mutuwarka) Nasa'i ne ya
rawaito.
Ga
goman zulhijja ya shigo mana Allah ya yi rantsuwa da dararrakin su sai ya ce (ina rantsuwa da Alfajir)(da dararraki goma) , su ne ranakun Allah masu
alhuruma , kuma cikamakin watanni sanannu wanda Allah ya ce game da su, (Hajji watanni ne sanannu).
Wuninsu
ya fi daraja akan wunin goman karshe na Ramadan , Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce: (mafificin
ranakun duniya su ne ranaku goma) Ibnu Hibban ya rawaito,
falalan
goman Zulhijja ya samu ne sakamakon tattaruwan manya manyan ibadoji a cikinta
na daga salla – da azumi – da sadaka – da hajji – wanda hakan baya samuwa a
waninta.
kuma
dukkan ayyuka na kwarai a cikinta ya fi soyuwa zuwa ga Allah na daga irin
wannan aikin idan ya faru a waninta.
Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Ba wasu ranaku wanda ayyukan alheri a cikin su ya fi soyuwa ga Allah
irin wadannan ranaku) wato
yana nufin ranaku goma, sai suka ce ya Manzon Allah ko da jihadi a tafarkin
Allah? Sai ya ce: (ko da jihadi a tafarkin Allah sai dai mutumin da ya fita
da rayinsa da dukiyarsa bai dawo ba da wani abu na daga wannan) Abu
Dawuda ne ya rawaito asalinsa na Bukari.
Ibnu Rajab Allah
ya kara yarda a gare shi ya ce '' kuma wannan hadisi yana nuni da cewa aiki na kwarai
a wannan kwanaki goma ya fi soyuwa ga
Allah akan aiki a sauran kwanakin duniyaba tare da toge wani abu ba daga cikin
su ''
Magabata
Allah ya musu rahama sun kasance suna kokarin ayyuka na kwarai a cikin su '' Sa'id binu
jubair Allah ya mishi rahama ya kasance idan goman farko na Zulhijja ya shigoya
ya kan yi kokarin da ba za a'a iya ba ''
Na daga
cikin falalan Allah da karamcin Sa Ya sanya
nau'uka na da'a daban daban a ciki na daga cikin abin da aka shar'anta
akwai yawaita ambaton Allah , Allah subhanahu wa Ta'ala ya ke ce:(kuma su ambaci sunan Allah a ranaku sanannu) Ibnu
Abbas Allah ya kara yarda a gare shi, shi da mahaifin shi ya ce:<< wadan
nan kwanaki goman>> ambaton shi Allah Subhanahu wa Ta'ala a ciki na daga
cikin ibadodi na kusanci Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya
ce; (Ba wata rana da tafi girma da soyuwa wurin
Allah aiki a cikin su a wurin Allah irin ranaku goma to ku yawaita a cikin su
halala da kabarori Da kuma godiya wa Allah) Ahmad ne ya rawaito,
Imam Annawawi Allah ya mishi rahama ya
ce:<< mustahabbi ne yawaita zikiri
a wadannan goma kari akan su, mustahabbi ne na daga haka a ranar arfa fiye da
sauran kwanaki goman, mafificin zikiri karatun littafin Allah shi ne shiriya
kuma da haske bayyananne >>
Kabbarori
wanda suke na saki wzaiwai ba kaidi a dukkan lokaci yana cikin manyan alamomi a
watan zulhijja Ibnu Umar da Abu huraira Allah ya kara yarda a gare su sun
kasance suna fita kasuwa a cikin ranakun nan guda goma suna kabarbari mutane
suna kabbara da kabarbarin su , an shar'anta yin kabbara mai kaidi karshen
salloli tun daga asuban ranar arfa ga alhazai da wasun su shehul islam Allah ya
mishi rahama ya ce mafi ingancin zantuka a cikin kabarbari wanda jamhurin magabata
suka yi da fukaha'u da sahabbai da limamai shi ne ayi kabbaran tun daga asuban
asuban arfa har zuwa karshen ranakun attashrik karshen ko wani sallah.
Na
daga cikin abin da ya ke mustahabbi a ranaku goma azumtan su, rana na tara shi
ya fi dacewa a cikinta , Imam Annawawi- Allah ya mishi rahama- ya ce '' lallai mustahabbi
ne mustahabbanci mai karfi '' .
Yin
sadaka aiki ne na kwarai wanda ya ke yaye bakinciki ya ke tafiyar da bacin rai ,
mafi alheri ta kasance a lokacin bukata
da kuma lokaci mafi daukaka na zamani.
Tuba
matsayinta a addini na da girma da daukaka domin ita ce sababi na samun rabauta
da kuma samun sa'ada, Allah ya wajabta ta ga dukkan al'umma daga dukkan
zunubbai. , sai ya ke ce ga wanda ya yi da'awan mata da da ga Allah (ase ba za su tuba zuwa ga Allah ba su nemi gafaran Shi ?)
kuma ya ce ga muminai (ku tuba zuwa ga Allah gaba
daya ya ku muminai ko za ku samu rabauta) , Annabi tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi yana rokon Allah a wuni so dari , kuma ya tuba zuwa
gare Shi , Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke cewa: (ya ku mutane ku tuba zuwa ga Allah domin ni ina tuba zuwa
ga Allah sau dari a wuni) Bukari da muslim suka rawaito , mu muka fi
dacewa da bukatuwa zuwa ga tuba , mafi alherin ranaku ga bawa shi ne ranan da
ya tuba , Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da Ka'ab
binu Malik Allah ya kara yarda a gare shi (Albishirinka
da mafi alherin rana albishirinka da mafi alherin ranan da ya zo a gareka
tunda mahaifiyarka ta haife ka) Bukari da Muslim ne suka
rawaito .
Abin
mamaki da kyan tuba mutun zai tuba a mafi kyan ranaku zuwa ga Allah duk wanda
ya yi gaskiya a tuban sa to darajarsa zata daukaka Allah zai canja mishi munanan
shi ya maida su kyawawa .
A
cikin ranaku goma na Zulhijja ana nufan dakin Allah da aikin haji daya daga
cikin rukunnan musulunci kuma ginshikan shi masu girma Allah Subhanahu wa
ta'ala ya ke cewa (Allah ya wajabta fiskantan
daki ga mutane duk wanda ya samu iko na
zuwa) , wanda ya gaza yin hajji saboda wani uzuri to shima yana tarayya da alhazai a cikin lada idan ya
gaskata niya, ta iya yuyuwa ma mutumin da ya tafi da zuciyarsa sai ya riga
wanda ya tafi da jikinsa .
A
goman farko na Zulhijja akwai ranar arfa azumtansa yana kankare zunuban shekara
guda da kuma shekara mai zuwa (Ba wata rana da
Allah ya fi yawaita 'yanta bayi daga wuta kamar ranan arfa) Muslim
ne ya rawaito.
A
ciki ne akwai ranan suka mafi alherin ranaku na yanka kuma shi ne mafi bayyana
kuma shi ne mafi yawan tara jama'a shi ne ake cewa yaumulhajjil akbar (ranan
hajji mai girma) Allah Madaukakin Sarki ya ce: (
shelantawa daga Allah da ManzonSa zuwa ga mutane ranan hajji mafi girma)
.
Shi
ne mafi girman ranaku a wurin Allah Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi ya ce:(lallai mafi girman ranaku a
wurin Allah shi ne ranan suka sa'an nan kuma sai ranan sha daya) Abu
dauda ne ya rawaito.
Kuma
daya daga cikin I'idi ne na musulmai , rana ne na farin ciki da annashawa ta
hanyan sauke wani rukuni daga cikin rukunnan musulunci, wasu mutane suna gafala
tare da farin ciki daga ambaton Allah to ya kasance ambato a wannan ranaku yana
da daraja , Allah subhanahu wa Ta'ala ya ce:(ku
ambaci Allah a cikin ranaku kididdigaggu) – wato sune ranakun nan na
Tashrik - , Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Ranakun Tashrik ranaku ne na ci da sha da ambaton
Allah) Muslim ne ya rawaito.
Ibnu
Hajir Allah ya mishi rahama ya ce: '' Ya tabbata falalan wadan nan ranaku goma , saboda
haka wadan nan ranaku na ayyamuttashrik falalan su ya tabbata ''
A
cikin ranakun suka akwai ibada ta dukiya da kudi kuma ita ce mafi soyuwar
ayyuka zuwa ga Allah, Allah ya hada su da sallah sai ya ce:(ka yi salla ga Ubangijinka kuma ka yi suka) ,
Allah ya kwadaitar bisa ga ikhlasi a wurin suka, kuma ya kasance Allah aka nufa
a ciki Shi kadai ba alfahari ko riya ko kuma neman a ji ko kuma ya zama kwai
tsurar al'ada ce, Allah subhanahu wa Ta'ala ya ce :(naman
shi baya riskan Allah ko jinin su saide tsoron Allah ne ya ke riskan Shi)
kuma << Annabi ya yi laiha da raguna biyu
masu fari da baaki a kahgon su ya yanka su da hanun shi >> Bukari da Muslim ne suka rawaito. ''al'amlah '' (shi ne baki wanda saman shi akwai
fari) "al'akran"( kuma shi ne mai
kaho) , babu laifi mutun ya yi bashi don ya yi laiha kuma ya nemi mayuwa
a wurin Allah kada ya rika zambo sakamakon tsadanta , domin ladan ta wurin
Allah yana da girma duk wanda ya nufi ya yi laiha to ya haramta a gare shi a
cikin ranaku goman nan da ya dauke wani abu na daga gashin shi ko farcen shi ,
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke cewa (Duk wanda ya kasance yanada abun yanka zai yanka to idan
jinjirin watan zulhijjah ya kama to kada ya dauki wani abu na daga gashin shi
ko kkuma kumban shi har sai ya yi laiha) Muslim ne ya rawaito.
Bayan haka ya ku
musulmai:
Wanda
ya samu sa'ida shi ne wanda ya ribaci lokutan nan na watannin nan da ranakun
nan da sa'o'in nan ya kusanci Allah Majibincin shi da abin da ya ke na ayyukan
da'a , ya wuci wani abu ya riske shi na wannan alheru ya samu sa'ada wanda zai
aminta da su bayan haka daga wuta da abin da ke ciki na daga alheru kuma ya
rabauta da aljanna wanda fadinta ya kai sammai da kasa .
Ina
meman tsarin Allah daga shaidan abin jifa
(Ku yi gaggawa zuwa ga Uban gijin ku da aljannah wanda fadinta
ya kai sama da kasa an tanadeta ga wanda suka yi imani da Allah da ManzanninSa
wannan falala ne na Allah ya kan bada shi ga wanda ya so Allah Ma'aboci falala
ne Mai girma).
Allah
Ya sa mini albarka ni da ku a cikin alkur'ani mai girma.
Huduba ta biyu :
Dukkan yabo da
godiya sun tabbata ga Allah bisa kyautatawanSa dodiya a gare Shi bisa datarwan
shi da baiwan Sa na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai Ya ke
ba Shi da abokin tarayya ina mai girmama Sha'aninSa , na shaida Annabin mu
Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi da sahabbansa da aminci tabbatacce mai kari.
Ya
ku musulmai:
Addinin
musulunci addini ne mai girma da an gina shi akan janyo maslahohi da kuma
tunkude barna saboda wata hikima da Allah ya ke nufi da ita, ya shafawa mutane
a doron kasa gabacin kasa da yammacinta da wata annoba wanda ba a taba irinta
ba a tarihin doron kasa ko da sau daya kuma da boyuwarta da yaduwarta da
gazawan samo maganinta wanda yana kama wanda ya kiyaye daga gareta a wani
lokaci kuma ya kuskure da umarnin Allah wanda ake zaton zai kamu da ita.
Hakika Allah ya kebance wannan gari (Alharamain
Ashsharifain) da wasu darajoji kuma ya daukaka darajan jagororinta ta hanyan
hidima da kuma kaunan su ga musulmai a dukkan doron kasa da kuma tsorace musu abin da zai faru gare su na daga cutuwa,
saboda haka ne jagororinta suka dauki matakai na hana yaduwar wannan cuta na
annoba domin fatan gushewarta ba tare da an samu cakudayyan mutane ba sashin su
ga sashi musamman a hajji tunda ana tafiya ne zuwa gare shi kuma ana zuwa a
dawo yana karuwa a garuruwa, sai suka maida karin alhazai zuwa ga shekara mai
fiskantowa domin fatan alheri da neman yayewan Allah da rahamarSa, Allah ya
saka musu da alheri bisa ga musulunci da musumai.
Allah Subhanahu
wa Ta'ala Ya siffantu da falala da karamci da rahama na daga wanda ya nufi
hajji ya gazara yi to za a rubuta mishi ladan shi Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce: (lallai a cikin
Madina akwai wasu mutane da baza ku yi wasu tafiya ba ko ku yanka wani kwari ba
face sun kasance tare da ku) sai suka ce ya Manzon Allah : alhali
suna Madina sai ya ce:(iye, uzuri ne ya tsare su)
Bukari ne ya rawaito .
Sannan ku sani
Allah Ya umarce ku da salati da aminci
ga AnnabinSa.