الجمعة، 29 نوفمبر 2019

HUKUNCIN SHAFA A KAN HUFFI A MUSULUNCI


Hudubar Masllacin Annabi na shaikh Muhammad Salah Al-budair 2-4-1441AH/29-11-2019AC

Hudubar farko
Ya ku musulmai!
Ku ji tsoron Allah, duk wanda ya ji tsoron Allah Matsayinsa zai daukaka har ya haura nisan taurari ya taka tsanin da zai kai shi kololuwa.(ku ji tsoron Allah zai ilmantar da ku,kuma Allah Masani ne ga dukkan komai).
 Fikihu guzuri ne na mai bautan Allah, kuma taimako ne ga mai neman shiriya. duk wanda fikihunsa ya karanta to aikinsa zai munana,  jahilcinsa kuma ya halaka shi  , idan hunturu ya zo  mutane sukan yi amfani da  huffi  da safa   da  mayafi  da abin dumama jiki .
Shafa akan huffi guda biyu abu ne da ya halatta ba mai musun haka sai dan bidi'a, mai sabawa jama'ar musulmai da malaman fikihu da hadisi.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya kasance yana shafa akan huffi, ya tabbata shafa akan safa daga wasu sashi na daga sahabbai Allah ya kara yarda a gare su .
 Halaccin shafa  a kan huffi biyu sauki ne  da kuma dadadawa da yalwatawa da  saukakawa   a cikin shari'a   sabo da bukatuwar  sanya shi   sannan kuma   za a hadu da wahala wurin  yawan cire shi.
Wanda ya ke son shafa a kan huffi to ya wajaba ya nemi sanin hukunce- hukuncensa  da  sanin tsawon  mudda (lokaci) da sifarsa da sharudan halaccinsa, da abin da ke warware shi  da hukuncinsa idan ya warware  da wanin haka na daga matsaloli .

YA KU MUSULMAI:
Huffi abu ne da aka sana'anta shi daga fata  ana ambaton shi  da huffi ne sabo da  rashin nauyinsa  ko kuma  kamar yadda  wasu suka ce '' sabo da hukunci ya yi sauki na in an sanya shi a yi shafa a madadin wankewa, ''
Amma ita safa aba ce da ke rufe kafa wanda aka sana'anta ta daga auduga ko gashi ko jawazkar gashi, ko kyalle, wanda aka fi sani a yau da Shurrab.
.
 An shardanta su zama suna da tsarki kuma sun suturce dukkan kafofi biyu da idon sawu, kuma su zama suna da kauri basu bayyana jiki, to idan huffi ya zama mai bayyana jiki, kuma danshin shafan da aka yi yana jika kafa, kuma yana bayyana launin fata, to bai halatta a yi shafa a kansa. idan ya kasance ba shara-shara ba ne kaurinsa bai barin ruwa ya jika kafa to ya halatta a yi shafa a kansa, a daya daga cikin zantuka biyu na malamai.
Kuma an shardanta ya sanya su bayan ya yi cikakken tsarki na ruwa, idan ya yi shafa akansu ba tare da yana da dahara cikakkiya na ruwa ba kafin sa su to alolarsa da sallarsa basu inganta ba.
Idan ya wanke daya daga cikin kafafuwarsa sa'anan ya sanya safa sannan ya wanke daya kafar kuma ya sanya ta cikin huffi ko safa to baya halatta ya shafa akanta a zance mafi inganci cikin maganganu biyu na malamai sabo da hadisin Abu bakrata -Allah ya kara yarda a gare shi-  ya zo cikin shi (Idan yayi tsarki sai ya sanya huffinsa biyu, to ya yi shafa a kansu) to harafin  Fa a hadidisin yana hukunta bin juna take hade da jerantawa : sabo da haka ya wajaba ya kammala tsarkinsa ya kuma kammala alolarsa ya kuma gama wanke kafafuwansa biyu sa'annan sai ya shigar da su cikin huffinsa biyu ko safarsa biyu.
Mazaunin gida na iya shafa akan hufi tsawon wuni da dare, matafiyi kuma zai iya shafa bisa huffi har tsawon kwanaki uku dare da wuninsu.
Muddar shafan na fara wa ne tun daga shafar farko bayan ya yi karamin hadasi a zance mafi inganci cikin maganganu biyu na malamai,
To zai yi ta shafa a kan su tun daga shafan farko bayan hadasi karami har zuwa misalin wannan lokaci na  washegari idan mazaunin gida ne. in kuma matafiyi ne to har zuwa kwatankwacin wannan lokaci na rana ta hudu.
Umar dan khaddabi Allah ya kara yarda a gare shi yace: zai shafa a kan su har zuwa kwatankwacin wannan sa'a  na wuninsa da darensa) Abdurrazak ya fitar da shi.
To idan Muddar ta kare to dahararsa ta warware a gun wasu malaman fikihu, wasu kuma suka ce: a'a, alolarsa bata warware ba ko da kuwa lokacin shafa ya kare ne a halin yana cikin salla to zai karasa sallarsa don karewar mudda baa sanya ta cikin masu warware alola, amma maganar farko ta fi zamewa Ahwad iyakantacciya don fita daga sabani ga sallar. Kiyayewa da yin taka tsantsan shi ya fi dacewa bisa a rasa tabbacin sharadi na inganci.
Idan ya yi hadasi bayan karewar muddar to ba zai yi shafa a kansu ba har sai ya cire su, ya yi cikakken tsarki sannan ya sa su.
Zai iya shafa cikin muddar muddin ba janaba ya yi ba, to idan ya yi janaba ta hanyar jima'i ko mafarki ko waninsu, to ba zai yi shafa akan su ba har sai ya wanke dukkan jikinsa, har da kafafuwarsa biyu, An karbo daga Safwan bin Assal Allah ya kara yarda a gare shi yace: (Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana umartanmu in mun kasance muna halin tafiya da kada mu cire huffinmu har tsawon kwanaki uku da dararrakinsu, sai dai don janaba, ba bahaya ko fitsari ko barci ba.
     Idan yayi shakku bisa muddar shafan to ba zai shafa ba tare da shakku, sabo da rashin tabbacin sharadin halaccin shafar.
  A duk lokacin da ya cire huffinsa biyu ko safanninsa biyu, ko kuma ya cire huffin daya daga cikin kafafuwa biyu to shafarsa ta warware alolarsa kuma ta baci, wanke kafafuwarsa ba zai isar masa ba da ya ci gaba da shafa a kansu, sai dai ya wajaba a gare shi ya sabonta tsarki na ruwa kafin ya halatta a gare shi ya yi shafa a kansu a   zance mafi inganci cikin maganganu biyu na malamai.
Don kiyayewa da iyakancewa ga salla, sabo da kuma mustahabbi ne fita daga sabani.

Ya ku masallata masu tsarki!
Idan har a huffi ko safa akwai huji ko yagewa ko kecewa wanda bigere na farilla ke bayyana to in har ya yi girma sosai to ba ya halatta a yi shafa a kansa sai in ya kasnce kadan ne. idan kecewar daga saman idon sawu ne to haka ba zai cutar da shi ba.
Abin da ya ke wajibi shine shafa a saman huffi ba kasansa ba, ko dunduniyarsa ko kwabrinsa ba,
Sifar shafar ita ce : ya dora jikakkun hannayensa yana mai bude yatsun hannayensa bisa yatsun kafarsa sai ya tafiyar da su tun daga saman  tsintsiyar kafar  har ya isa ga makyangyamarsa, ba sunna ba ne ya shafa kasansa ko dunduniyarsa ko kwabrinsa, a zance mafi inganci sabo da hadisin Aliyu Allah ya kara yarda a gare shi yace:(Da a ce addini ra'ayi ne da shafa kasan huffi shi ya fi dacewa a kan shafa samansa, hakika na ga Manzon Allah yana shafa bisa saman huffinsa) Abu Dawuda ne ya rawaito.
    Wanda ya bar shafar saman huffi to alolarsa bata inganta da ijma'in malamai, kuma ko da ya yi salla to sallar ta baci.
Wani mai waka ya ce : Mai barin shafan sama (huffi)  ka bata ,   zai yi shafa ne gaba daya dama akan dama hagu akan hagu  wasu suka ce :- sunna ne a gabatar  da dama .
       Imamu Ahmad  Allah ya mishi rahama ya ce:-
( Duk yanda ka yi ya halatta  da hanu daya ko hannaye biyu).
Ba mustahabbi ba ne maimaita  shafa  sabo da rashin zuwan hakan , ba a shafa akan huffi mai najasa .
     Ya ku masallata matsarkaka : wanda ya kasance matafiyi ya kuma fara shafan a muddar halin tafiya, ya yi shafa  kasa da  wuni da dare  sa'annan ya dawo garin  shi   zai cika wuni da dare.  idan ya yi shafan a halin tafiya wuni da dare  zuwa sama sa'annan ya dawo garin su zai cire safar sa biyu bisa wajabci, sabo da karewar lokacin shafa  da isowar sa zuwa garinsa, to idan kuma mazaunin gida ya yi shafa sai ya yi tafiya  kafin karewar muddar shafar  to sai ya cika shafa irin na matafiyi.
 ya ku masallata matsarkaka:
 Idan ya yi alola da ruwa cikakken alola sannan ya sanya safa  ba tare da yayi hadasi ba har ya sake dora wani safan daban  akan shi   to ya halatta yayi shafa akan safan saman ,  idan ya yi shafa akan safan saman sa'annan ya cire shi to alwalan sa ya baci .
   Idan ya yi alola cikakken alola da ruwa sannan ya sanya safansa , sannan ya yi hadasi sai kuma ya sanya safa a sama bayan yayi hadasin  to  baya halatta a gare shi ya yi shafa akan na saman,  sabo da ya sanya shi ne a halin bai da  tsarki , wato yana mai hadasi   to idan ya shigar da hanunsa   kasan safan saman   to ya halatta,  idan ya sanya safa a halin yana mai tsarki  na ruwa cikakke  sannan ya yi hadasi   ya kuma shafa akan shi  sa'annan ya sanya wani safan akan shi   to baya halatta yayi shafan akan  na saman  sabo da  ya sanya shi ne a halin yana da tsarki na shafa ba tsarki na ruwa ba.  wanda ya sanya safa a halin yana da tsarki na ruwa cikakke  sannan ya sanya  takalmin sau-ciki  mai tsawo a kan shi  ko but ko kambas, wanda duk sun rufe idon sawu, to zai iya shafa a kan su, idan ya cire  takalmin sau-ciki  mai tsawo  ko but ko kambas, bayan ya yi shafa a kan su to alolarsa ta baci.
 Idan ya sanya takalmi wato sau ciki wanda bai suturce idon sawu ba, to shafa a kanta ba zai isar mishi ba.
Idan a kasan akwai safa da ta rufe idon sawu kuma ya sanya ta da takalmin kafin ya yi hadasi zai shafa bisa takalmin da abin da ya bayyana na safanni biyu, saman gurin da ake wankewa ya kuma yi salla a cikinsu gaba daya, to idan ya cire takalman to alolarsa ta baci, sallarsa kuma bata inganta ba da safa kadai sabo da shafa ya ta'allaka da su.
 Allah ya sanya ni da ku cikin wadanda suke bautawa Allah bisa ilimi da basira.
Ina fadin abin da ku ke ji, ina nema mana gafaran Allah kuma ku nemi gafararsa, madallah da da rabauta irin na masu neman gafara.

Huduba ta biyu
Ya ku musulmai!
Ya wajaba ga mai salla ya rika bibiyar safarsa don tana da saurin yin wari, to a duk lokacin da safa ta yi wari ko doyi  to ya wajaba ya cire ta don kar ta cutar da mai salla ko musulmi da warinta.
Ko mutanen da sukan yi karin magana da warinta inda suka ce (ya fi wari a kan warin safa).sun yi zambo da shi sai dayan su yace :
Ibnu Umair ya yi yakin da ya bar suna  na yabo irin warin safa ketacciya.
Wani kuma ya ce :
Ki yi yabo a gare ni da abin da ki ka sani domin ni * ina yabon ki kamar yadda ake yiwa iskar safa.

Ya ku musulmai !
Muna nasiha da fadi da ya fi iyakancewa ga salla a babin shafa bisa huffi, idan ba wasu nassoshi na yanke ko bayyane, in har ba kunci  ko wahala mai tsanani da ke wajabta sauki wurin amfani da  Ahwad din sannan kuma in wurin amfani da Ahwad din akwai karin bauta da lada.
Hakika malaman fikihu sun nassanta cewa fita daga sabni abu ne mustahabbi.
Hakika Annabi ya yi amfani da Ihtiyadi  kuma ya yi hukunci da shi a waki'i da ya shahara
Na daga ciki akwai abin da Buhari da Muslim suka rawaito daga Anas dan Malik Allah ya kara yarda a gare shi yace:(Annabi ya wuce ga wani dabino ya fado sai yace : (Ba don ina tsoron kar ya zama cikin na sadaka ba da na ci shi).
  . Muna kira ga musulmi da zuciyarsa ta bude ta karbi sabani a irin wadannan mas'aloli, to in ba haka ba sai su zama sababi na sabani da kauracewa juna da fada da kiyayya da yankewa juna,   
. Ya ku musulmai ! ku godewa Allah bisa ni'imarsa mai yawa da falalarSa mai yawan zuba, ku tuna yadda mutane su ke tafiya huntaye ba takalma suna rasa abin jin dumi suna barci bisa duwatsu da safa, sannan kun wayi gari a bayan su kuna rayuwa mai yalwa.da gurin noma mai yawan alheri da 'ya'yan itace nunannu masu ganye, ku godewa Allah bisa yalwan falaloli da ni'imomi, to mai biyayya mai godiya yana ci gaba ne cikin falala da habaka da albarka, kuma mai sabo mai gujewa Allah na tafiya ne zuwa ga walakanci da talauci da halaka.
Ku yi salati da aminci ga Ahmad.


ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق