الأربعاء، 11 ديسمبر 2019

HUNTURU LOKACIN KAKA NE NA MUMINI


Hudubar Masallacin Annabi na shaikh Abdullah Bin    Abdurrahman Albuaijan 9-4-1441AH/6-12-2019AC
Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah masanin gaibi Mai suturce aibi mai yaye bakinciki Mai yafe zunubai Mai tsinkayan dukkan sirri da ke zukata, muna gode masa kuma muna neman taimakonSa muna neman gafararSa muna kuma tuba zuwa gare shi.
Muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu, muna riko da shi (Allah) a dukkan al'amuranmu da yanayinmu.
Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake ba shi da abokin tarayya.
Kuma na shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, ya isar da sako kuma ya sauke amana.ya yi nasiha ga al'uma ya yi jahadi don Allah cancancin jahadi har mutuwa ta zo masa. Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalanSa da sahabbanSa baki daya.
Bayan haka,
Mafi alherin zance shine maganar Allah, mafi alherin shiriya shi ne koyarwar Annabi Muhammad, mafi sharrin al'amura shine fararrunsu, kuma dukkan bid'ah bata ce, kuma dukkan bata na wuta.
Ya ku bayin Allah ku ji tsoron Allah cikin umarninsa ku hanu daga abin da ya yi hani a kai ya kuma tsawatar. (ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah cancancin tsoronSa kada ku mutu face kuna musulmi)
 Ya ku bayin Allah!
Lallai ga karewan kwanaki akwai abin lura, ga abin da ya shude kuma a kwai tunatarwa da izina (Allah na juya dare da wuni, lalle ga hakan  akwai abin lura ga ma'abota basira).  
Ranaku da watanni da lokutan shekara, da shekaru na shudewa suna bin junan su, burace – burace da ajali na karewa, wasu al'uman na riskan wasu,  (Duk wanda ke kanta zai kare sai fiskar Ubangijinka ma'aboci daukaka da karamci zai wanzu).
 Ya ku jama'ar Musulmai!
 Hakika lokacin hunturu ya fiskanto ku, sanyinsa mai gargadi ne, Allah ya yiwa jahannama izini da ta numfasa a cikinsa, An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi yace :Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( wuta ta koka zuwa ga Ubangijinta sai ta ce :" sashi na ya ci sashi, sai Allah ya sanya mata numfasawa biyu :numfasawa daya a lokacin hunturu,dayan kuma a lokacin bazara, shi numfasawarta na lokacin hunturu to shine jaura, na lokacin bazara kuma shine wannan iska mai tururi)Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
An rawaito daga Umar dan khaddabi cewa idan hunturu ya zo sai ya bibiyi talakawansa sai ya rubuta zuwa gare su : "Lalle hunturu ya zo kuma shi makiyi ne to ku masa shiri na daga fatu da hoffofi da safanni, ku riki fatu a matsayin riga 'yar ciki da ta waje, domin sanyi makiyi ne mai saurin shiga (jiki) mai dadewa bai fita ba".
  To ku bibiyi bayin Allah -masu rauni- ku taimaka musu bisa sanyin hunturu, ku bibiye su don basu abinci da tufafi da mayafi, ku nemi ladan su gurin Allah a ranar gamuwa, (Duk abin da ku ke ciyarwa na alheri to don kan ku ne, ba wani abu da za ku ciyar face don neman yardar  Allah, ba wani abu da zaku ciyar na alheri face an cika muku shi, a halin ku ba zaa zalunce ku ba.)


Ya ku bayin Allah!
Ku yi lura da wadannan zamuna da lokutan shekara da abin da ke cikinsu na maslahohi da hikimomi, da ace zamanin gaba daya lokaci guda ne cikin lokutan shekara da wasu maslahohin an rasa su wato na sauran fasalin, kamar da dukkan shekara bazara ce to da an rasa amfani da maslahohin hunturu, haka ma in da kaka ne gaba dayansa ko   damina  dukaninsa.
Abin mamaki ta yaya zaa sabawa Ubangiji***
                     Ko ta yaya wani mai korewa zai kore shi*
Cikin komai akwai alama tasa***
                    Da ke nuni cewa shi kadai ne*

Ya ku jama'ar Musulmai!
Hunturu ya fiskanto, to maraba da ganimar masu bautan Allah, da kuma kaka ta muminai, dare na tsawaita cikin shi sai su samu rabon su na barci, sannan hakarkarinsu na yin nesa daga makwanci, don su yi tsayuwan dare, wuninsa mai sanyi na gajarta don ya saukake musu wahalar azumi.
Allah Madaukakin sarki ya ce : (lallai masu tsoron Allah suna cikin lambuna da maremari. Suna masu dibar abin da Ubangijinsu ya ba su, lallai su sun kasance masu kyautatawa a gabanin haka(a duniya). Sun kasance a lokaci kadan na dare suke yin barci. Kuma a lokutan asuba suna ta yin istigfari.)
Lokacin Hunturu -Ya ku bayin Allah! - Lokaci ne na kaka ga muminai, suna kiwo cikin gonakan da'a ga Allah. Suna shakatawa a fagage na ibadoji zukatansu na walwawa cikin dausayin kusantar Ubangiji, an samu saukin wahala da gajiya, azumin bai gajiyar da su, ko dare ya kuntata gare su ga barcinsu ko tsayuwansu na  dare.
An rawaito daga Amir dan Mas'ud Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :"Azumi cikin hunturu wata ganima ce na ruwan sanyi)Ahmad da Tirmizi ne suka rawaito.
Abdullahi dan salam ya ce :A yayin da Annabi ya zo garin Madina mutane sun yi cacarindo zuwa gare shi, Sai na shigo cikin mutane don na gan shi, a yayin da na samu ganin fiskar shi sai na tabbatar wannan fiskar ba na makaryaci ba ne,farkon maganar da ya fara da ita ya ce  : (ya ku mutane ku yada sallama ku ciyar da abinci, ku sada zumunci, ku yi salla a halin mutane suna barci za ku shiga Aljannar Ubangijinku da aminci).Ahmad da Tirmizi ne suka rawaito,kuma ya inganta shi.
Yayin da mutuwa ta zo wa Mu'az Bin Jabal sai ya ce ga kuyangarsa : "kaiton ki shin gari ya waye? Sai tace : a'a, sai ya kyale ta zuwa bayan wani dan lokaci sai ya ce: ki duba, da ta duba sai tace ; "e"  sai ya ce : Ina neman tsarin Allah daga safiyar da za ta kai zuwa ga wuta, sannan sai yace : Maraba da mutuwa, maraba da bakon da yazo ana halin talauci, duk wanda ya yi nadama ba zai rabauta ba, Allah ka san ba wai ina bukatar zama a duniya ba ne sabo da tona sabbin rami na koramai ba, ko dashen itatuwa ba, sai dai ina son zama ne don na dage da kokari a daren hunturu mai tsawo, da kuma fiskantar kishin garji a lokacin tsananin zafi, da kuma gogayya da malamai a sahun halkan ambaton Allah."

Ya ku bayin Allah!
A lokacin hunturu ne dare ke tsawaita wuni ke gajarta, Hakika Allah ya sanya dare sutura, ya sanya barci kuma hutu, wuni kuma don neman abin rayuwa.
(Allah ne wanda ya sanya muku dare domin ku natsu a cikinsa, da rana mai ganarwa, lalle Allah hakika Ma'abocin falala ne a kan mutane, kuma amma mafi yawan mutane ba su godewa.)
 Hakika dimantan kwana ba barci wata cuta ce mai tafiyar da nashadi, mai kashe jiki,  mai hana neman arziki da aiki, kuma yana banzatar da lokuta, kuma yana shagaltarwa daga da'a, kuma ya sabawa sunna.
Allah Madaukakin sarki ya ce :(kuma na daga cikin ayoyinSa barcinku a cikin dare da wuni, da neman ku ga falalarSa, lalle a cikin wannan akwai ayoyi ga mutane masu saurarawa.)
 Annabi ya kasance yana kin barci kafinta da zance bayanta –wato sallar lisha-
Ina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan abin jefewa. (kuma shi ne wanda ya sanya muku dare ya zama tufa, da barci ya zama hutawa, da yini ya zama lokacin tashi).
Allah ya sa min albarka ni da ku a cikin Alkur'ani.

Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa datarwarSa da kyautatawarSa, tsira da amincin Allah su tabbata ga Muhammad Mai kira zuwa ga yardarSa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalanSa da sahabbansa, da 'yan uwansa.
Ya jama'ar Musulmai!
Lalle ba abin da musulunci ya bari a halin rayuwa , ya yi la'akari da sanjawar zamani da lokuta sai ya shar'anta hukunce –hukunce na azima da sauki a yayin larura.
Na daga cikin abin da Allah ya ke daga darajoji da shi, ya kuma kankare kusakurai da laifuka akwai gaggautawa zuwa ga tsarki, wanda sharadi ne na ibadoji, kuma rabi ne na imani, kuma sharadi ne na salla wanda yake rukuni ne na musulunci. To dagewa  da jurewa da hakuri ga abin da aka ki, da bauta ta hanyan amfani da ruwa a lokacin sanyi a hunturu, na cikin masu kankare zunubai, An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :"Ase ba zan nusar da ku ga abin da Allah ke goge zunubai da shi ba, kuma ya daga darajoji da shi? Su ka ce : E ya Manzon Allah,sai yace : Yalwata alwala a halin ba a so, da yawan taku zuwa ga masallatayya, da jiran salla bayan idar da salla: Wancannin ku shi ne Ribadi )Muslim ne ya rawaito.

Ya ku bayin Allah
Na daga cikin sauki irin na shari'a da hikima na musulunci da rangwami da saukakawa mutane a yayin wahala mai bijirowa, da cutuwa da ake tsammani  (kuma bai sanya muku wani abu na kunci ba a addini)
  Duk wani abu mai wahala na janyo  saukakawa, (kuma Allah bai dora wa rai sai abin da ya ba shi, Allah zai sanya sauki bayan tsanani.
   Musulunci ya shar'anta sauki  yayin kunci da whala  da larura, na daga ciki akwai mara lafiya,
Kai har ma mai laifiyan idan ya  tsoracewa kansa, amfani da ruwa to an shar'anta masa taimama da kasa, kamar yadda a ka shar'anta wa wanda ya ji ciwo da ya yi shafa kan abin da ya rufe ciwon ko ma a kan maganin.

  An karbo daga Jabir Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Mun fita a wata tafiya  sai dutse ya samu wani mutum ya mishi rotse a kai, sai ya yi mafarki sai ya tambayi mutanensa sai yace : ko ina da sauki ko zan iya na yi taimama? Sai suka ce ba ka da wani sauki tunda za ka iya amfani da ruwa, sai ya yi wanka sai ya mutu. Yayin da suka zo gun Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare sai aka bashi labarin hakan sai ya ce:  sun kashe shi Allah ya kashe su, me ya sa ba za su tambaya ba idan basu sani ba, ba komai ba ne maganin jahilci sai tambaya. Ai daya yi taimama kawai da ya isan masa ya matse ko ya daure ciwon nasa da tsumma, sai ya shafa kan ciwo ya kuma wanke sauran jikin nasa )
An karbo daga Amru dan As  Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Na yi mafarki a dare mai dari a yakin zatus salasil, sai na tausayawa kai na na yi taimama don in nayi wanka zan halaka.sai na yi (jagorancin ) salla ga mutane na sallar asuba, sai su ka ambaci hakan ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai yace : ya Amru ka yi limanci wa mutanenka a halin kana janaba? Sai na gaya mishi abin da ya hana ni wanka nace ni na ji fadin Allah da ya ke cewa : (kuma kada ku jefa kan ku ga halaka lalle Allah ya kasance mai tausayi ne a gare ku),sai Manzon Allah ya yi dariya bai ce komai ba. Abu Dauda ya rawaito Albani kuma ya inganta shi.
   

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق