الاثنين، 30 ديسمبر 2019

SABUNTA IMANI


Hudubar Juma'a  a Masallacin Annabi na shaikh AbdulBari Subaiti 1-5-1441AH
HUDUBAR FARKO
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, wanda ya halicci sammai da kasa, ya sanya duhu da haske  ina kyautata yabo a gare shi ina gode  mishi da  yammaci da safiya  da lokacin sammako, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah  shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, wanda yace : ( kuma rayayyu ba zasu yi daidai da matattu ba Allah na jiyar da wanda ya so, amma kai ba za ka jiyar da wanda yake cikin kabari ba)
 Na shaida shugabanmu Muhammad bawansa ne kuma manzonSa ne, ya yi gargadi a kan gafala da gajiyawa, tsira da amincin Allah su tabbata gare shi,da iyalan shi da sahabbansa wadanda suka samu babban falala da lada Bayan haka.
Ina muku nasiha da ni kai na da jin tsoron Allah Allah Madaukakin sarki ya ce:-(yA ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah cancancin tsoronSa kada ku mutu face kuna musulmai).
 Bibiyar imani da ba shi kulawa na daga cikin sifar musulmi kuma abin nanatawar masu hankali, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :(Imani na tsufa ya kode a cikin dayanku kamar yadda tufafi ke tsofewa ya kode, to ku roki Allah Madaukakin sarki : da ya sabunta muku imani a cikin zukatanku).
Kamar yanda tufafi ke tsofewa,  ai wato kamar yanda  sabon  tufafi yake tsofewa  sabo da dadewa ana amfani da shi, Manzon Allah tsira da amincin  Allah su tabbata a gare shi ya ce :- (An ambaci zuciya ne  kawai da zuciya  sabo da  jujjuyawa da yake yi ,  misalin zuciya kamar misalin gashi ne  da aka rataye ta a wani itaciya iska na kada ta  cikinta  da wajenta)
  Mumini na sabunta imaninsa , sabo da imani ba ya tabbatuwa a hali guda,  sai dai yana gajiyawa sabo da dadewa  ya raunana sakamakon gajiyawa a bangaren ibada , ko daina ibada ko kuma gafala daga Allah, da dulmuyar rayi a cikin sha'awe-sha'awensa  to mutum wani halitta ne da ke da iyaka a ikonsa, yana da rauni a fidirarsa  yana tsakanin gajiyawa da gajartawa  Allah Madaukakin sarki ya ce:-(An halicci dan adam a halin yana mai rauni).
Duk wani abu da zai sami musulmi na yanke ibada daga wani lokaci zuwa wani lokaci ko kuma zamewar kafarsa , to hakika baya kubuta daga hukunci na Ubangiji  daga ciki akwai komawa zuwa  ga Ubangiji da fadakar zuciya  Allah Mai tsarki da daukaka yana son masu yawan tuba yana farin ciki da tubarsu, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:-
  (Na rantse da wanda raina ke hanun shi  da badon kuna aikata zunubai ba  da Allah ya tafiyar da ku ya zo da wasu mutane masu yin zunubai , kuma suna neman gafara sai ya gafarta musu.)
  Imani na karuwa yana raguwa , yana karuwa da biyayya kuma yana raguwa da sabawa Allah , idan zuciyar dayanku ta farka daga gafalarta,  ya rika ayyuka na da'a ya riki sabuba na imani to imaninsa  zai karu ya yi karfi ko yakininsa ya yi karfi  idan ya yi dubi zuwa ga ni'imomin Allah  a  gare shi  sai kaunar sa ga Allah ta karu   sai ya yi  lafazi na ambaton Allah ya gaggauta cikin tuba da  ayyuka na alheri  domin ya riski abin da ya gajarta da abin da  ya tsere mishi a dalilin  gafala  sabo da haka ne lalle abin kwadayi ne   kwarai wurin bibiyan imani  da kuma aiki bisa  daga darajar shi  na daga cikin sifa na salihai  , Abu Darda Allah ya kara yarda a gare shi yana cewa: "Na daga cikin fikihun bawa  ya rinka bibiyan imaninsa da abin da ya tawaya daga gare shi , na daga cikin fikihun bawa  yasan cewa    yana karuwa ne shi ko yana raguwa". 
Umar Allah ya kara yarda a gare shi ya kasance yana cewa sahabban shi , ''  ku zo mu kara imani '' sai su ambaci Allah Mabuwayi .
Ibn Mas'ud Allah ya kara yarda a gare shi yana cewa a cikin adu'arsa (Ya Allah ka kara mana imani da yakini da  fahimta).
 Mu'az  bin Jabal -Allah ya  kara yarda  a  gare shi - yana cewa wani mutum (zauna tare da  mu , mu kara imani na wani lokaci).
Duk yanda imanin mumini  ya kai kololuwa a daraja to ba zai aminta wa kansa ba, tafarkinsa shi ne komawa zuwa ga Allah yana neman tabbatuwa a kan tafarki, Allah Madaukakin sarki yace a harshen bayinSa muminai: (ya Ubangijinmu kar ka karkatar da zukatanmu bayan ka shiryar da mu).
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana yawaita fadinsa.: ya mai juya zukata da basira tabbatar da zuciya ta bisa addininka).
Idan mumini ya san shaidan  na dakonsa ne, to ya yi kokari don yayi  yaki da fizgarsa, ya tunkude waswasinsa, ya toshe kofofin yaudarasa, kada ya mika wuya, kada ya samu karayar zuci, yana mai neman agaji daga Ubangijinsa, Allah Madaukakin sarki ya ce: ((To idan ka zo karanta kur'ani to ka nemi tsarin Allah daga shaidan abin jefe wa. Lalle shi bai da iko a kan wadanda suka yi imani, kuma suna  dogaro ne ga Ubangijinsa)
Mafi alherin guzuri ga wanda ya ke neman guzuri, kuma mafi alherin abokin tafiya a hanyar tabbatuwa bisa tafarki shine riko da littafin Allah da aiki da shi, wanda ya yi riko da shi Allah zai kare shi, wanda ya bi shi kuma Allah zai kubutar da shi.
Musulmi fadakakke yana yin kokari don ya ga ya fita daga yanayi na gafala, da sharri na rauni da gajiyawa, sabo da zai ji farinciki ne idan ya yi biyayya ga Allah, yana mai neman yardar Ubangijinsa, wani mutum ya tambayi Manzon Allah menene imani? Sai Manzon Allah ya ce :( idan kyawawan ayyukanka suka burge ka munanan ayyukanka suka bata maka rai to kai mumini ne).
  Ta yaya zai gafala daga Allah ya gajiya daga ibada wanda zuciyarsa akwai haske na Alkur'ani! Yana dandana halawar imani kuma ya san cewa yana da Ubangiji mai tausayi wanda ke yafe kusakuran masu tuba kuma yana gafarta zunubai, Allah Madaukakin sarki ya ce : (kuma wanda ya aikata mummuna ko ya zalunci kan shi sannan ya nemi gafarar Allah to zai samu Allah Mai gafara ne Mai jinkai)
Ambaton Allah da tunani cikin ayoyinSa yana farkar da zuciya kuma yana kara imani kuma yana tsarkake zuciya; Allah Madaukakin sarki ya ce : (Abin sani kawai, muminai sune wadanda suke idan an ambaci Allah zukatansu su firgita, kuma idan an karanta musu ayoyinsa sai su kara musu imani, kuma ga Ubangijinsu suke dogara.)
Ya dace ga musulmi ya dawo da ransa in ya gafala, da gabbansa idan sun yi rauni ko gajiya a ibada, domin tsoron fushin Allah da ukubarSa, na daga cikin Adu'ar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, (Ya Allah ina neman tsarinka daga gushewar ni'imarka da juyawar afiyarka da azaba bagtatan da dukkan abin da zai fusata ka,)
Zuciya kan karkata zuwa ga duniya a wasu lokuta tana ta neman abin duniya ido rufe wasu lokuta, sabo da haka ne Allah ya umarce mu da yawaita ambato, don a samu daidaito,  a gare mu tsakanin neman abin duniya da sauke nauyin wajibi na addini, : (ya ku wadanda suka yi imani ku ambaci Allah ambato mai yawa ku yi tasbihi safiya da maraice).
 Kamar yadda zurfafawa cikin abubuwan da aka halatta da barna da wuce gona da iri cikin al'adu yana haifar da gajiya Allah Madaukakin sarki ya ce : (ya 'yan adam ku riki adonku a gun dukkan masallaci ku ci ku sha kada ku yi barna, lalle shi bai son mabarnata.)
Ba ya boyu wa ga masu hankali cewa abota da masu raunin himma da marasa  manufa kan haifar da gajiya wa da gafala.
Idan musulmi bai ankara ba daga gafala da ya ke ciki ya gaza tunkude gaza wa da yake da shi da rauni to sai sifa ta tsauri da kekashewar zuciya ta yi galaba a kan shi da rauni da nauyi wajen sauke nauyin ibada,  da'a ta yi mishi wahala zuciya ta yi tsatsa ya dushe hasken imani
Allah Madaukakin sarki ya ce : (Bone ya tabbata ga wanda zukatarsu suka kekashe daga ambaton Allah wadancan suna cikin wata bata bayyananna).
 Idan musulmi bai magance zuciyarsa ba to zai dangana da halin nan da Allah  Mai tsarki ya bada labari game da ita, a fadinsa (sa'annan kuma zukatanku suka kekashe daga bayan wancan, sabo da haka suka zama kamar duwatsu, ko mafi tsanani  ga kekashewa, kuma lalle ne daga duwatsu hakika akwai abin da maremari suke bubbuga daga gare shi, kuma lalle ne daga gare su hakika akwai abin da ya ke tsatsagewa har ruwa ya fita daga gare su, hakika, akwai abin da ya ke fadowa domin tsoron Allah, kuma Allah bai zama gafili ba daga abin da ku ke aikatawa.)
Allah ya sa mana albaka ni da ku cikin Alkur'ani Mai girma kuma ya amfanar da ni da ku da abin da ke ciki na ayoyi da ambato mai hikima. Iya abin da ya sawwaka kenan cikin abin da zan fada tare da neman gafarar Allah, kuma ku nemi gafararSa domin shi Mai gafara ne Mai jinkai.
  
    HUDUBA TA BIYU
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya amsa kiran wanda ya roke shi, musulmi na gode masa a sirrinsa da ganawarsa, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya ba wani Ubangiji koma bayanSa, na shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne kuma  zababbenSa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa wadanda suka rabauta da kaunarSa kuma da yardarSa.  
Bayan haka :To ina muku wasiyya da ni kai na da jin tsoron Allah.
 Duk wani abu da ya samu musulmi na gafala kuma alama na gazawa ta afka mishi kafa ta zame, to lalle kofar tuba a bude take, hanyoyin alheri birjik su ke, Allah na son masu yawan tuba da komawa gare shi, kuma yana cewa a hadisul kudsi : (ya ku bayi na lalle ku masu yin kuskure ne cikin dare da wuni, ni kuma mai gafarta zunubai ne baki daya, ku nemi gafara ta zan gafarta muku).  
Ku yi salati ga Annabin shiriya. Hakika Allah ya umarce ku da hakan a littafinSa sai ya ce :(Lalle Allah da mala'ikunSa suna salati ga Annabi, ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce.)  

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق