Na daga cikin ginshiki na
yanke a wannan addini namu akwai haramcin cin kazantacciyar dukiya, na daga
cikin mafi munin dukiya na haram ribatar da wasu ke yi a ma'aikata ko watanta
na yin awun gaba da dukiyar al'uma (sata) ko yi ma dukiyar ta'annuti, ta kowace
fiska a ka yi ta ko ta wace hanya aka bijiro da ita. Allah Madaukakin sarki ya
ce (ya ku wadanda suka yi imani kada ku ci
dukiyarku a tsakanin ku bisa bata sai
dai ta hanyar kasuwanci bisa yarjejeniya daga gare ku.)
To dukiyar kasa asalinta tana
da alhurma sabo da mallakan al'uma ne baki daya, ana sarrafa ta ne wajen
amfanin kowa da kowa, da maslahohin da ake tarayya a kanta.
To duk wanda ya riki wani
aiki, kowani irin aiki ne to shi abin tambaya ne gaba ga Allah na dukkan nauyin
da aka dora masa, to ba ya halatta ya yi gaban kansa a ciki face abin da ya zo
daidai da koyarwar shariar Allah a kankanin abu ne ko babba, sawa'un cikin abu
mai kima ne ko mara kima, da kuma abin da tsari ya shirya don cinma maslahohi
na gabadaya da amfani iri iri na kowa da kowa.
Lalle sakaci cikin shanin
kowane dukiya yana komawa ne ga bangaren wanda ya yi sakacin ko da wani
ma'aikaci ne kuwa wannan laifi ne a mahanga na sharia tsarkakakkiya, haka ma
yin rufa-rufa ga wani sabo da dangantaka ko abokantaka ko don neman wani
anfanin kai, to duka sun shigo cikin satan dukiyar al'uma, kuma yana cikin
barna a doron kasa da ha'intar shugaban kasa jagoran musulmai da kuma ha'intar
al'uma, sakamakon abin da wannan ha'inci ya kumsa na hadura da ke barazana ga
zaman lafiyar al'uma da tattalin arzikinta da habakanta da ci gabanta da
yalwanta. Allah Madaukakin sarki ya ce (Duk wanda ya
ci gululi zai zo da abin da ya ci na gululi ranar alkiyama sa'annan a cika wa kowane
rai sakamakon abin da ya aikata kuma ba
za a zalunce su ba).
Ana cewa gallar rajulu fa huwa yagullu wato mutum ya yi gululi idan ya
yi ha'inci, Al'aghlal : shine cin amanar wani nauyi da aka dorawa mutum wanda
ya hada dukkan nau'ukanta, kuma ana fassara ta da satan dukiyar al'uma ta
dukkan fiskokin sata, sabo da haka ne a ke cewa ga mahauci ya yi gululi idan ya
saci wani abu na nama bayan ya dauki fata.
Allah Madaukakin sarki ya ce (kada ku yi barna a ban kasa bayan an gyara ta.)
Al'uma ba zata ta ba gyaruwa
ta yi kyau ba sai kowa ya tashi da nauyin da ke kan shi na amana bisa yanayi
mafi kyau, a yi taimakekeniya gurin kiyaye dukiyar al'uma, ta kowace hanya da
ta sawwaka, Allah Madaukakin sarki ya ce game da AnnabinSa yusuf (ka sanya ni a kan taskokin kasa, lalle ne ni,
mai tsarewa ne, kuma masani.)
Haka kuma a kissar musa game da
yaran mata biyu na shuaibu ( ya Baba ka bashi aikin
kodago, lalle ne mafi alherin wanda ka bawa aikin kodago shi ne mai karfi
amintacce.)
Lalle ribatar dama na aiki ko
waninsa don a yi awun gaba da dukiyar al'uma ba bisa halacci ba na daga cikin
manyan laifuka na zunubai da kuma munanan al'amura, Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Lalle
wasu mutane na kutsawa cikin dukiyar Allah ba tare da hakki ba,to wuta ta
tabbata a gare su ranar alkiyama) Buhari ne ya rawaito.
Ibnu Hajar Allah ya masa
rahama yace : ( wato suna barna a dukiyar musulmai).
Lalle kalmar malaman fikihun
musulunci ta nassatan cewa dukiyar al'uma kamar dukiyar maraya ne wurin
wajabcin kiyaye ta, da haramcin dauka daga gare ta, da matsanancin kwadayin
tafiyar da ita a gurarenta da suka dace ba tare da yin sakaci ba ko tawace
fiska.
Ya 'Yan uwa a Musulunci
Na daga cikin
abubuwa na bayyane da ke faruwa daga wasu ma'aikata na gabatar da wasu a
matsayi da fifita su a kan wasu ba tare da cancanci ba, tare da fakewa da wata
doka da ta fito daga shugaban kasa, don tabbatar da maslahar kowa da kowa na
daga 'yan kasa, sai wannan ma'aikacin ya riki wannan kamar wata garabasa yana
zaton tamkar dukiyarsa ne na aljihunsa, sai ya gabatar da wanda bai cancanta ba
bisa wanda ya cancanta. Na daga cikin irin wannan akwai sakaci da wasu ke yi
wajen bada kwangila ba bisa ka'ida ba, ko don maslahar kai, da wuce gona da iri
wajen sanya farashin aikin, wanda in da na kan shi ne bai zai yarda da haka ba.
Yana daga cikin sakaci na rashin kulawa da
dukiyar al'uma kamar lambuna da asibitoci da wuraren shakatawa da hanyoyi da makamantarsu.
Yana daga
ciki amfani da abin da yake mallakar hukuma ne wurin bukatun kai ba tare da
izini da ke bisa tsari ba daga shugaban kasa.
Na daga cikin
sakaci da wasu ke yi akwai tafiyar da magani na kasa da makamantarsa da raba shi ba ga
bigerin shi da ya dace ba,na daga ciki akwai kasuwantar da daukan aiki da cin
riba a cikinsa, ko srayar da lokacin aiki ko jinkirta abin da aka dorawa mutum
na aiki ta fiskar da ba haka ya dace ba, wadannan da makamantarsu na cikin
nau'uka na barna, kuma ha'intar jagoran al'umar musulmi ne da ita kanta al'umar
sabo da abin da ke ciki na barna mai
girma da sharri mai fadi wanda zai haifar da cutarwarsa mai tsanani, kuma zai
kawo cikas ga ci gaban kasa da habakarta da ma mutanenta Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi ya ce : (Lalle sau da yawa wani na
kutsawa cikin dukiyar Allah da manzonSa cikin
abin da ransa ya so ranar alkiyama bai da wani abu sai wuta.) Tirmizi ne ya
rawaito kuma yace Hadisi ne Hasan sahih, kuma Ibnu Hibban ma ya rawaito shi a
littafinsa Sahih da sanadi ingantacce.
Ya ku bayin
Allah
Lalle abin da
yak e wajibi ga duk wanda ya biye wa ransa abin da ya raya masa har ya yi gaba
da fadi da dukiyar al'uma ta ko wace irin hanya ce daga cikin hanyoyi da ya
koma ga Ubangijinsa ya tuba ga Mahaliccinsa ya rabu da wannan kudin haramun ta
hanyar maida shi ga taskar kasa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi yace : : (Yana kan mutuum abin da ya
sata har sai ya mayar da shi).Ahmad da Abu Dauda da Tirmizi ne suka rawaito
kuma Tirmizi ya ce Hadisi ne ingantacce.
Malaman fikihu
sun yi tarayya kan cewa duk wanda ya lalata wani abu na dukiyar al'uma to dole
ne ya biya haka kuma in ya dauki wani abu daga ciki ba tare da hakki ba to ya
dawo da shi ga taskar kasa wato Baitul mali na musulmai.
Hakika Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kafa mana wata ka'ida ga duk wanda ya rike wata amana na musulmai
da kada ya ribaci wani abu na aikin hukuma da makamancinsa ya yi amfani da shi
cikin maslahar kansa, wannan shi ake cewa ilimin tsarin gudanarwa Tushe da bada kariya ga dukiyar al'uma, sai
yace ga wanda ya je tattaro dukiyar zakka bayan yace wannan naku ne wannan kuma
an bani kyauta ne : (To me ya sa
dayanku ba zai zauna a gidan iyayensa ba ya ga ko za a kawo masa kyauta ko aa,
na rantse da wanda rai na ke hanunSa dayanku ba zai dauki wani abu ba face ya
zo da shi ranar alkiyama yana dauke da shi a wuyarsa.) Buhari da Muslim ne suka
rawaito.
Ku ji tsoron Allah
yak u bayin Allah ku yi taimakekeniya dukkanku wurin kiyaye dukiyar al'uma ta
dukkan hanyoyi da za ku iya yin hakan ku kiyaye kada ku yi sakaci da hakan
Allah Madaukakin sarki yace : (ku yi taimakon juna bias
da'a da takawa kada ku yi taimakekeniya a kan laifi da gaba)
Duk wanda ya
biye wa ransa wurin sabo ko wani irin sabo ne da ya sani in ya faku daga idon
mutane to fa Allah na tsinkayar sirrinsa
da bayyanensa ku tuna fadin Allah Madaukakin sarki :
(ku sani lalle Allah yana sanin abin da ke cikin zukatanku to lalle ku kiyaye
shi) da fadinSa : (ya san maha'intar
idanuwa da abin da zukata ke boyewa.)
Na daga cikin
nusarwar Manzon Allah : (Duk namar da ta tsiro
daga haram to wuta ce ta fi dace wa da ita). Kada ka gabatar da
duniya mai karewa a kan lahira mai wanzuwa, kada ka shigar da wani abu ga kanka
da iyalanka sai halal mai tsarki da dukiya tsarkakakkiya.
Ya zo cikin kissar
yaron da mashi da ba a san daga ina ba ya kashe shi a yakin khaibar mutane na
cewa barkan shi da samun Aljanna sai Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (A'a ahir, na
rantse da wanda rai na ke hanunSa lalle bargon da ya dauka a ranan khaibar
kafin a raba ganima na babbaka da wuta a kan shi). Buhari da Muslim ne suka
rawaito.
An rawaito
daga Abubakar :"Duk wanda ya nemi arziki ta
hanyar haram to zai rasa albarkan, ba za ka ga wani gurbi na kwarai ba a dukiyarsa
idan ya ciyar da dukiyarsa gurin abincinsa to zai hadu da ukubarsa a lahira, idan ya ciyar da iyalansa da shi to
hakika ya ha'ince su bai kyauta musu ba, kuma ba abin mamaki ba ne in dansa ya zama
mara biyayya a gare shi. Halayen wadanda yake daukan nauyi ya lalace, suka zama
kwatankwacinsa kuma ya hadu da alhakin abin da ya aikata a rayuwarsa ta duniya
kuma azabar lahira ta fi tsanani."
Huduba ta
biyu
Ya tabbata daga
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi : (Kafafuwan bawa ba za su gusa ba a ranar alkiyama har sai
an tambaye shi game da rayuwarsa yadda ya tafiyar daita, da iliminsa cikin abin
da ya tafiyar da shi da dukiyarsa ta wacce hanya ya same ta kuma ta yaya ya kasha
ta, da jikinsa ta yaya ya tsofatar da shi).
Ku tsarkakar
da hanyar ku ta neman abinci ku nesanci kazantattun hanyoyi za ku tsarkaka ku
rabauta, za ku yi nasara kuma ku ji dadi.
Ibnu Taimiyya
Allah ya masa rahama yace: "Abinci na
hadewa ne ya cakudu da jiki ya tsiro da
shi sai ya zama kamar sinadari ne nasa, idan abincin ya zaman a kazanta ne sai
jikin ma ya kazance sai wuta ta wajaba a gare shi, sabo da haka ne Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi y ace : (Duk namar da ta tsiro daga haram to wuta ce ta fi dace
wa da ita). Aljanna tsarkakakkiya ce bam
ai shiganta sai mai tsarki."
Abin da ake
nufi da ci ya kunshi da wani abu da ya ke amfana da shi a kan saya a ji dadi a
wannan rayuwa.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق