الجمعة، 24 يناير 2020

LOKACIN HUNTURU GA MUSULMI


Hudubar Masllacin Annabi na Sheikh Salah Bin Muhammad Albudair  22-5-1441AH 17-1-2020 AC
Hudubar farko
Ya ku musulmai
Hunturu ya sauka gare ku bayan shudewar bazara mai tururi, busa irin na jaura ya kada muku bayan hurawan garji, tsananin sanyi ya zo muku bayan gushewar yanayin zafi.
(Allah yana juyar da dare da yini, lalle ne a cikin wannan akwai abin lura ga masu basira.)
To ku yi lura da ido na basira cikin shanin girman Allah da ikonSa da halittarSa, ku yi tunani game da hunturu da gajimare da ruwan sama, ku yi lura ga yayyafi da mamakon ruwa, ku dubi yadda yankin  gajimare ke saukowa ga girgije mai girma, ku yi dubi zuwa ga duwatsu masu sanyi da garuruwa masu kankara, da birane da sanyi ya mamaye su da fari fari, ku yi tasbihi ga Allah Mahalicci Masani Mai girma,Wanda ya kirkiri duniya ya samar da ita, kuma ku ba komi ba ne face wani yanki dan kadan daga halittanSa na ban mamaki mai ban tsoro, to ku girmama Allah cancancin girmamawanSa ku ji tsoron tsananinSa da azabanSa ku kame daga saba masa da rena shanin hakkinSa .
Ya ku musulmai
Hakika hunturu ya zo da karfinsa da tsananinsa da kuma tsaurinsa, to ku kiyaye daga sanyi domin yana kankarar da gine-gine kuma yana rusa jiki yana tsofatar da tsoffi , Rabi'u Bin Dabi'u ya ce : (Idan hunturu ya zo to ku dundumani domin tsoho hunturu na lalata sha'nin sa)
 wani kuma ya ce : (Hunturu ya zo ga shi ba ni da rigan sanyi, *** tsananin  sanyi kuma abokin jayayya ne  ba a maida shi  sai dai ana mishi garkuwa).
An rawaito cewa Umar Allah ya kara mishi yarda ya ce : (lallai hunturu ya zo kuma shi makiyi ne to ku kimtsa masa kimtsawa na daga fata da huffofi da safanni, ku riki fatu ya zama rigan waje da 'yar ciki, domin lallai sanyi makiyi ne mai saurin shiga jiki mai wuyan fita).
Ya ku iyaye da kuma majibinta al'amura  : ku tausaya wa 'yan yaran ku da jariranku  ku tufatar da su ku musu rahama, to ita rahama ba a a cire ta  sai daga zuciyan shakiyyi, kuma sau dayawa akan samu baba da ya kaurace wa 'yayansa ya daina ciyar da su, sabo da sabaninsa da matarsa ko wacce ya sake ta, baya tufatar da su alokacin bazara ko hunturu ko idi baya basu ciyarwa ko ya kyautata musu sai wasu bare sun musu sadaka da makusanta, to wani irin kekashewar zuciya ce wannan wani irin tsauri ne wannan wani irin hankali ne wannan wani irin tunani ne  ya sa wannan baba azzalumi ja'iri ne wanda ya wofantar da yaransa ya kyale su ya yada su ya barsu su ka daidaice!?  wani maula ( Bawa) ya ce ga Abdullahi dan Amr Allah ya kara yarda a gare shi : (lallai ni ina so na zauna wata guda a wannan gari na baitul-makdis sai ya ce da shi : shin ka barwa iyalanka abin da zai ciyar da su na wannan wata ?  sai ya ce: a'a , sai ya ce : to koma zuwa ga iyalanka ka bar musu abincin su,Lallai ni na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa : (ya isa laifi ga mutun ya wofantar da wanda ya ke ciyarwa ) Ahmad ne ya rawaito da Abu Dauda , a wurin muslim kuma : (ya isa laifi ga mutun da ya buya daga wanda ya ke mallakan ciyarwansa)
Ya ku musulmai !
Ba abin da ya fi tsanani kamar gagaran daukan nauyin hunturu da kuma ta'azzara a gare ka na tufatarwa a halin kuma kana da laruran haka kana bukatan shi, mutun nawa ne cikin talakawa suka gagara rigan sanyi da za su sa ko mayafi ko abun lullubuwa ko kuma abun karyawa ko kuma magani ya gagare su ko na yaransu ba za su iya samun kudinsa ba, an ce da wasu mai ka tanadar wa sanyi sai ya ce : (tsawon karkarwa da kadawan jiki da kekasawa).
 To ku tuna masu rauni da talakawa da miskinai da wadanda mazajensu suka rasu suka barsu na daga mata da marayu da kuma mabukata, ku tuna 'yan gudun hijira da wadanda suke yasassu da kuma wadanda aka kora daga garuruwansu wanda sanyin hunturu ya bugesu kankara ya lullubesu, iska mai tsanani ya kakkashe su, talaka yana kuka mai rauni yana neman taimako wanda yake halin kaka ni kayi yana ta kururuwa hanunsa ya kuntata (baida abinda zai ci) kokawansa ya yi girma tsananin sanyi na hunturu ya sauka gidan sa dattijo ya kwana yana sandare, Mumunai su ne makukusantan mutane da rahama da shafaka da tausayawa da kyautatawa su suka fi tausayawa ga talakawa kuma da yatimai da miskinai su suka fi bada kulawa ga wadanda mazajensu suka mutu suka barsu da ku wadanda aka sake su da kuma masu rauni sune suka fi tausayawa wadanda suke masu tsananin bukata kuma suka fi amfanar da wadanda suke cikin kunci da bakin ciki ba wani abu da suke da shi da zai ishe su ba mafaka da za su fake to ku bibiyesu ku bincikesu ku taimaka musu ku lullubesu da mayafai da fatu ku agaza musu da hanyoyi na jin dumi .
Tausayawa da kyautatawa daga musulmi ga dan uwan shi musulmi shi ne abu mafi girma na dumamawa ga wanda ba yi da abin dumi .
An karbo daga Abu sa'id Alkudri Allah ya kara yarda a gare shi ya ce yayin da muna cikin halin yanayi na tafiya tare da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi sai wani mutumi ya zo akan abar hawansa sai ya rinka juya ganinsa yana kallo dama da hagu sai Manzon  Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke cewa: (To duk wanda ya kasance yana da wani sauran abin hawa to ya taimaka da shi ga wanda bai da abin hawa, wanda ya ke da wani saura na  guzuri to ya taimaka ga wanda bai da guzuri) sai ya ambata nau'uka daban daban na dukiya abin da ya  ambata har muka ga cewa wani bai da wani hakki a cikinmu akan wani abin da ya karu kan bukatu a dukiyansa, muslim ne ya rawaitoshi
Ya ku musulmai !
Karamci a lokacin hunturu da tsanani da ciyarwa da kyautatawa idan har an samu karanci na guzuri da abinci da yawan fari abu ne mai daraja kuma  abun girmamawa ba masu siffantuwa da shi sai mutane masu yawan kyauta da tausayawa Allah Mabuwayi ya ce  :(ko  kuwa ciyarwa, a cikin yini ma'abucin yunwa, ga maraya ma'abucin zumunta, ko kuwa wani matalauci ma'abucin turbaya).
      Ibrahim Annakha'i yake cewa : a irin ranakun da abinci yana da wahala a wannan ranan .
Muhammad dan Abdus bamalike ya yi sadaka a wani daren hunturu da kiman amfanin gonansa gaba daya alhali kuma kimansu ya kai dinari dari na zinari ya ce ban yi bacci ba a daren saboda bakinciki game da talakawan al'umman Muhammad,
 Darfat binul Abd yake cewa : mu a lokacin hunturu muna kira ne ( kowa da kowa) tawaga tawaga *** ba a gani mai gayyatan abinci  a cikinmu yana kiran daidaiku  .
Kansa' ta ce Allah ya kara yarda a gare ta a lokacin da take wakan juyayi ga dan uwanta sakhr : lallai sakhr din nan shi ne mai kula da mu kuma shi ne shugaban mu lallai sakra din nan a lokacin da aka yi hunturu mai yawan soke dabba ne.
Aus binu hajar yake cewa : masu suka ne a wurin yaki sa'annan kuma masu ciyarwa ne ga baki*** idan sararin samaniya ya yi fatsi fatsi saboda tsananin sanyi
Shi kuma kars : shi ne tsananin sanyi mai ratsa jiki
Wani yake cewa : dan uwan hunturu bakonsa ya san cewa abin da ke tukunyarsa  *** zai yawaita kuma zai yi dadi
Wani kuma yake cewa : dan uwan hunturu tukunyansa ba ya gushewa  *** yana zuba a cikinsa sannan kuma yana fita.
Ku yi kyauta, ku yi sadaka, ku ciyar da mayunwaci da wanda ke cikin talauci  mayunwaci, ku shayar da wanda ya fada cikin tsananin kishi da mai jin kishi kuma ku tufata da mukamukinsa ke karkadawa jijiyoyin wuyansa ke girgizuwa saboda tsanani sanyi ku bibiyi makobtanku da  wanda suke muku hidima da ma'aikata da makusanta da talakawa da masu rauni da masu kiwo a sahara ba mumini ba ne mutuminda zai koshi makobcinsa na cikin yunwa ku toshe yunwan miskini da bukatansa da talaucinsa  , an karbo daga a'yisha Allah ya kara yarda a gare ta ta ce  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (lallai Allah yana renon dabinon dayanku da lomansa kamar yanda dayanku yake rainon irinsa har ya zame kaman dutsen uhudu) Ahmad ne ya rawaito
Ina fadin abinda kuke ji ina neman gafaran Allah kuma ku nemi gafaranshi domin shi lallai mai yawan  karban tuba ne kuma mai gafara .
Huduba ta biyu
Ya ku musulmai
A lokacin hunturu ne mutane ke neman jin dumi daga sanyi da wuta suna jin dadin shi kuma suna kewaye shi kuma su kunnashi a gidajensu da gonakinsu da kuma shemominsu kamar shi ne iyayan itacensu , abincinsu kuma abinda ke hadasu
Wuta ita ce 'ya'yan itace da ake ki lokacin hunturu duk wanda ya ke son cin 'ya'yan itace na hunturu to ya ji dumi Allah mabuwayi da daukaka yake cewa (wannan wuta din mun sanyata a matsayin tunatarwa ne da kuma jin dadi ga mutane da suke matafiya) duk wanda ya ruruta wutansa ya kunnata ya yi dafu da ita ya dafa masa ya ji dumi ya rike shi kaman abin hira ya amfana da ita to kar ya bar gaushi  ko wuta a makamashin ko abin sanya gaushin face ya kashe ta a dare ne ko wuni tsoron gobara ko shakewa (da hayakinta) domin wuta fa makiyi ne da ba a sa mar linzami tartsatsinsa kan fire baa kuma amintuwa da harshensa,
  
Daga ibnu Umar Allah ya kara yarda a gare su daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce : kar ku bar wuta a gidajenku yayin barci) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Daga Abu Musa Al'Ash'ari Allah ya kara yarda a gare shi  yace an yi gobara a wani gida ya kone da mutanen gidan a garin Madina cikin dare a yayin da a ka labartawa Manzon Allah tsira da amincin Allah su game da shaninsu sai yace : ( Lalle ita wuta makiyiya ce a gare kum to idan kun zo barci to ku kashe ta ) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Haka ma na'urorin jin dumi na wutan lantarki  in an tsoraci zafin wutan nata ko tururin nata to an shar'anta da a kashe ta bayan kammala bukata da ita, a yi nesa da wayoyinta  daga shinfidi da tufafi da fefofi da yara don gujewa hatsura da aukuwan mummunar abin da ba a zata ba.
Ku yi salati da aminci ga Ahmad mai shiryarwa mai ceton bayi kaffataninsu.


ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق