Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun
tabbata ga Allah, muna gode masa kuma muna neman taimakonsa muna neman
gafararsa
Muna neman tsarin Allah daga
sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu,
duk wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, wanda ya batar kuma babu mai
shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke
ba shi da abokin tarayya, yana halitta abin da ya so kuma ya zabi abin
da ya so, wanda ya kagi sammai da kasa, komai a kaddare ya ke a gare shi, na
shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne amintacce, cikamakin
Annabawa da manzanni, ya isar da sako, ya sauke amana ya kuma yi nasiha ga al'uma, ya yi jahadi don
Allah cancancin jahadi har mutuwa ta zo mishi, Tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbansa baki daya.
Bayan haka,
Mafi alherin zance shine maganar Allah, mafi alherin shiriya shi ne
koyarwar Annabi Muhammad, mafi sharrin al'amura shine fararrunsu, kuma dukkan
bid'ah bata ce, kuma dukkan bata na wuta.
Ya ku bayin Allah ku ji
tsoron Allah cikin umarninsa ku hanu daga abin da ya yi hani a kai ya kuma
tsawatar. Ku sani duk wani babba da karami abu ne rubutacce a littafi (ya ku wadanda suka
yi imani ku ji tsoron Allah kuma rayi ya yi dubi ga abin da ya gabatar don
gobe, ku ji tsoron Allah lalle Allah Masani ne ga abin da ku ke aikatawa)
Ya ku jama'ar musulmai!
Allah kan zabawa fifiko
mahalli da wuri kamar yadda ya ke zaba mishi lokaci da zamani, da ahali, da
mataimaka, hakika Allah ya fifita awasu sassa a doron kasa sai suka zama sune
mafi daukakan garuruwa kamar yadda ya sanya makka masaukar wahayi, kuma alkibla
ga musulmai, kuma ya sanya ta uwar alkaryu kuma gari mai aminci da masallaci
mai alfarma, gurin da zukatan mumunai ke karkata zuwa gare shi.
Garin Madina ya samu daukaka
ne sabo da hijiran Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a
nan ne musulunci ya yadu, ana ce da shi Daiba
Zama ya yi
dadi a cikinshi tsakanin duwatsun shi biyu harami ne kuma shi ne masulala na I'mani
da mafakarsa da masaukinsa kuma da makoncinsa da mabinnansa
Ya ku bayin
Allah :
Hakika Allah
ya daukaka garin madina ya fifitashi kuma ya umarci annabinsa tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi da ya yi hijira zuwa gare shi ya haramta abinda ke
tsakanin duwatsun shi biyu ya tsine wa duk wanda ya yi barna a cikin shi kuma
kokuma ya bada mafaka ga mabarnaci a
cikin shi to ku bawa garin hakkin shi kuma ku ji alhurman da ya ke tattare da
shi an karbo daga Anas Allah ya kara
yarda a gare shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce
: (Madina harami ne daga kaza zuwa kaza ba a'a yanke
itaciyansa ba a'a farsar da barna a cikinsa to duk wanda ya farar da barna a
cikinsa to tsinuwan Allah ta tabbata a gare shi da mala'iku da mutane baki daya)
Buhari ne ya rawaito
An karbo daga
A'mir dan Sa'ad daga baban shi ya ce :Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce : (lallai ni na haramta
tsakanin duwatsun garin madina guda biyu da atsinke kayansa ko a kashe abin
farautansa ) Muslim ne ya rawaito
Kuma an karbo
daga Aliyu Allah ya kara yarda a gare shi lallai Annabi tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi ya ce: (garin Madina haram
ne daga A'ir zuwa kaza duk wanda
ya farar da barna a cikinsa to tsinuwan Allah ta tabbata a gare shi da Mala'iku
da mutane baki daya ba za a karba mishi nafila ko farilla ba ) Buhari
ne ya rawaito
Ya jama'ar
musulmai
Madina masulala
ne na i'mani Allah ya ambace shi da gida da kuma i'mani, a cikinsa ne
alkura'ani ya yi ta sauka mai dumbin yawa, a ciki ne aka shar'anta hukunce
hukunce, rukunnai suka kafu, zaman lafiya ta tabbatu,
Daga nan ne tutocin musulunci suka taso a ka
bude garuruwa, Allah ya daukaka addininSa ya taimaki bawanSa ya rusa makiyanSa,
Daga Abu
Huraira Allah ya kara yarda a gare shi daga Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce : ( Lalle imani na sulalewa
zuwa Madina kamar yadda maciji ke sulalewa zuwa raminsa.) Muslim ne
ya rawaito.
Madina sulke ne
mai bada kariya, kuma garkuwa ne mai tsawo, ya kore kazantarsa yana tsarkake
mai dadinsa, mala'iku na tsaronsa daga kofofinsa, firgicin Masih-Addujjal ba
zai shige shi ba, ko annoba, daga Anas dan Malik, Allah ya kara yarda a gare
shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Ba wani gari face dujjal zai taka shi face Makkah da Madina,
ba wani kofa daga cikin kofofinta face Mala'iku na jere cikin sahu suna kare
su, sannan Madina zai kada da mutanen cikinsa girgizawa uku, sai Allah ya fitar
da duk wani kafiri da munafuki,) Buhari ne ya rawaito.
Daga Abu
Huraira Allah ya kara yarda a gare shi daga Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce : (A kofofin Madina
akwai Mala'iku annoba ko dujjal ba zai shiga garin ba) Muslim ne ya rawaito.
Ya ku bayin Allah ! ma'abocin
Kazanta ko kaidi bai da mazauni a garin Madina, amincin Allah ya tabbata a gare
shi,
Daga
Aisha diyar Sa'ad ta ce na ji Sa'ad Allah kara yarda a gare shi ya na cewa, na
ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya na cewa :Ba
wanda zai yi wa mutanen madina kaidi face ya narke kamar yadda gishiri ke
narkewa a ruwa,) Buhari ne ya rawaito.
An
karbo daga Jabir Allah kara yarda a gare su ya ce Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi yace : Madina tamkar zuga zugi ne ya kore
kazantarsa ya tace mai tsarkinsa.) Muslim ne ya rawaito.
Lalle Ibarahim ya haramta Makkah ya mar adu'a
da albarka, kuma lalle Annabi ya haramta Madina ya yi mar adu'a da ribin abin
da Annabi Ibrahim ya roka wa mutanen Makka
An karbo daga Abdullahi bin zaid Bin Asim cewa Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce :( Lalle
Ibrahim ya sanya alfarma ga Makka ya yi adu'a ga mutanenta, lalle ni kuma na
sanya alfarma ga Madina kamar yadda Ibrahim ya sanya wa Makka, ni kuma na roki
Allah game da sa'in madina da mudunsa da ribin abin da Ibrahim ya roka wa mutanen
makka) Muslim
ne ya rawaito.
Daga
Anas -Allah ya kara yarda a gare shi- daga Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce : (Ya Allah ka sanya
albarka ga Madina ribin abin da ka sanya a makka). Buhari ne ya rawaito.
Ya ku bayin Allah!
Lallai Madina ya kasance mafi
soyuwan gari ga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya
kasance yana nuna masa kauna da wafa'i kuma yana bayyana hakan karara An karbo daga
A'isha Allah ya kara yarda a gare ta tace : Manzon Allah tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi ya ce : (ya Allah ka sanya
mana kaunar Madina kamar yadda ka sa mana kaunar Makka ko ma sama da haka. Ya Allah
ka sa albarka ga sa'inmu da mudunmu ka inganta mana shi, ka kaurar da Annoban zazzabinsa
zuwa juhfa) Buhari ne ya
rawaito.
Daga Anas -Allah ya kara yarda a gare shi- idan Annabi
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya dawo daga tafiya ya hangi gine –ginen
Madina sai ya saki dabbarsa in yana kan dabbarsa ne sai ya kada ta sabo da
kaunar Madina.) . Buhari ne ya rawaito.
Ya kasance idan ya fiskanto Madina
sai ya kara sauri idan dutsen Uhud ya bayyana gare shi sai yace : wannan dutse
ne da ya ke sonmu mu ma muna son shi,
An
karbo daga Abu Humaid yace mun fita tare da Manzon Allah a yakin tabuka ya koro
hadisin sannan ya ce : sai muka fiskanto har muka zo wadil kura sai Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :( Lalle ni zan kara
sauri wanda ya ke so cikin ku to ya yi sauri tare da ni wanda ya so kuma ya
zauna, sai muka fita har muka kusanto Madina sai yace : Wannan Daba ne
wannan dutsen Uhudu ne shi dutse ne da yana son mu muna son shi). Muslim
ne ya rawaito.
Hakika zukatan
masu ziyara ta ta'allaku da Madina kuma ya bar wasu abubuwa na tarihi a zukatansu
na tsananin kauna sai zukatansu ta
tausasa zuwa ga garin suna masu tsanani shauki , ya Allah ka sanya mu daga
cikin masu son sa (garin ke nan)
Ya jama'ar
musulmai :
Madina shi ya
fi muku alheri kar ku ki shi Allah ya zabe shi ga Annabin ku to ku zabi abinda ya zaba ku ladabtu da
kusanci ku san hakkin makobci an karbo daga abi Zuhair Allah ya kara yarda da a gare shi ya
ce na ji Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi yana cewa (za a bude
garin yaman wasu mutane za su zo suna kora dabbobinsu suna daukan iyalansu da
ma wadanda suka biye musu, Madina yafi alheri agare su da sun sani za abude Sham
sai wasu mutane su zo suna kora dabbobinsu sai su dibi iyalansu da ma wadanda
suka musu da'a alhali Madina yafi alheri a gare su da sun kasance suna sani
kuma za a bude garin Iraki sai wasu mutane su zo suna kora
dabbobinsu sai su dibi iyalansu da ma wadanda suka musu da'a alhali Madina yafi
alheri a gare su da sun kasance suna sani) Bukari ne ya rawaito
An karbo daga ibnu Umar Allah ya
kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi ya ce (Duk wanda zai mutu a Madina to
ya mutu a cikinsa lallai ni zan yi ceto ga wanda ya mutu a cikin shi )
Tirmizi ne ya rawaitoshi kuma ya inganta shi
An karbo daga A'mir dan Sa'd daga
babansa Allah ya kara yarda a gare su ya ce : Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Madina ya
fi alheri a gare su da sun kasance suna sani duk wanda ya bar garin halin ya
tsani garin to Allah zai sanja shi da wani wanda ya fi alheri ba wani da zai
tabbata a ciki ya yi hakuri da wahala da
tsanani irin nashi face na kasance mai ceto a gare shi ko mai shaida a gare shi
ranar alkiyama) Muslim ne ya rawaito ,Allah ya samini albarka ni da
ku a cikin alkur'ani mai girma
Huduba ta biyu
Ya ku bayin Allah
lallai
Madina na da daukaka da falala to ku nemeshi da alhurma da kima da wasu laduba
da ya ya wajaba a yi ladabi a iyakoki na harami dama masallacin Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi haka nan kuma da wurinda Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke lallai adabi tare da
shi yana raye kamar yimishi ladabi ne a bayan ya rasu hakika Allah ya umarci a
yi ladabi gaba gare shi a kuma yi kasa da murya , Allah madaukakin sarki ya ce
: (ya ku wadanda suka yi imani kada ku sha gaban
Allah da Manzonsa ku ji tsoron Allah lallai Allah mai ji ne masani )(ya ku wadanda su ka yi I'mani kar ku daga sautukanku sama da sautin Annabi
kada kuma ku bayyana zance a gare shi kamar yanda sashinku ke daga murya ga
sashi don kada ayyukanku su rushe a halin baku sani ba)( lallai wadanda su ke
kankan da sauti gaba daManzon Allah wadan nan su ne wadanda Allah ya jarabi
zukatansu da takawa suna da wata gafara da lada mai girma )(lallai wadanda su
ke kiranka a bayan dakuna mafiya yawansu basu da hankali ) (da a ce sun yi
hakuri har ka fito zuwa gare su da ya kasance mafi alheri a gare su Allah mai
gafara ne mai jin kai )
ku ladabtu ya ku bayin Allah a gaba
gare shi da kyakyawan laduba an karbo daga Sa'ib
da yazid ya ce : na kasance ina tsaye a masallaci sai wani ya jefeni da tsakuwa
sai na duba sai naga Umar dan kaddabi ne sai ya ce je ka taho min da wadancan mutane guda biyu sai na taho
mishi da shi sai ya ce : ku waye ? ko kuma daga ina ku ke sai suka ce : daga
garin Dayif sai ya ce : da kun kasance mutanen garin Madina ne da na jiyar da
ku a jikinku (da na azabtar da ku) kuna daga muryan ku a masallacin Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ? ) Buhari ne ya
rawaito .
Allah ka daukaka musulunci da
musulmai .
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق