Hudubar farko
Sakamako mai dacewa
Dukkan yabo da godiya sun
tabbata ga Allah, muna gode masa kuma muna neman taimakonsa
Muna neman tsarin Allah daga
sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu,
duk wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, wanda ya batar kuma babu mai
shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke
ba shi da abokin tarayya,kuma na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma
ManzonSa. Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da
sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa.
Bayan haka, ku ji tsoron Allah
-ya ku bayin Allah- cancancin tsoronSa, ku yi murakabarSa a halin sirri da
ganawa,
Ya ku musulmai!
Allah ya kagi halittar halitu sai ya kyautata
abin da ya sana'anta, tsarki ya tabbata a gare shi ya kuma kyautata addininSa
da abin da ya shar'anta, Mai hikima ne kuma Masani, Adili ne Mai jinkai, cikin
halittarsa da umarninSa akwai sunnoni da basu sabawa ko sauyawa game da
halittunSa, daga ciki akwai sakawa bayi
daidai da ayyukan da suka yi, in na alheri to da alheri in na sharri to
da sharri, (Sakamako mai dacewa)
da
kaddara da sharia duk sun yi taron dangi bisa hakan, Allah Madaukakin
sarki yace : (To wanda ya aikata wani aiki gwargwado nauyin zarra na alheri to zai gan
shi. To wanda ya aikata wani aiki gwargwado nauyin zarra na
sharri to zai gan shi).
Allah
ya gandaya ladaddaki masu yawa ga ayyukan alheri wanda yake irin su kuma daidai
da su, sakayyar kan kasance daga jinsin da'ar , shehun musulunci Ibnu Taimiyya Allah ya masa rahama ya ce: (sakayya a ko yaushe daga na kasancewa daga jinsin aikin
da mutum ya yi ne).kuma babu
wata sakayya ga wanda ya kyautata sai kyautatawa Allah Madaukakin sarki
yace : (shin kyautatawa na da wani sakamako face
kyautatawa).
Wanda ya kiyaye dokokin Allah
da hakkokinSa to Allah ma zai kiyaye shi a duniya da lahira, Manzon Allah tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: (ka
kiyaye Allah sai Allah ya kiyaye ka) Tirmizi ne ya rawaito
Idan bawa ya nemi shiriya da
gaskiya sai Allah ya shiryar da shi Allah Madaukakin sarki yace : (Wadanda suka bi shiriya sai Allah ya kara musu shiriya).
Cika alkawarin Allah na daga
cikin imani da shi da kuma da abin da ManzonSa tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya zo da shi, sakayyarsa shine Allah na saka wa ma'abocinsa
da aljanna. Allah Madaukakin sarki yace : (kuma ku
cika alkawari na zan cika muku naku alkawarin)
Wanda ya gaskata Allah sai
Allah ya karrama shi da abin da ya ke so da kuma kari Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi yace: (muddin
ka yi wa Allah gaskiya to zai gaskata ka.) Nasa'i ne ya rawaito. Ibnu kayyim Allah ya masa rahama ya ce: (Bawa bai da wani abu da ya fi amfani kamar gaskiyarsa ga
Ubangijinsa, duk wanda ya mu'amalanci Allah da gaskiya cikin dukkan al'amuransa
sai Allah ya mishi abin da ya fi abin da ya ke yi wa waninsa na kyautatawa).
Iya gwargwadon kusantar bawa
ga Ubangijinsa ta hanyar da'a da ibada iya kusancin Allah gare shi, Allah Madaukakin
sarki ya ce a hadisul kudusi : : (muddin bawa na
ya kusance ni da taki to zan kusance shi da zira'i, idan ya kusance ni da
zira'i zan kusance shi da ba'i) Buhari ne ya rawaito.
Bawa na da
abinda ya zata daga ubangijin sa in alkairi ne to zai samu alheri in kuma ya
munana zato to zai samu kwatankwacin haka manzon Allah tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi ya ce : (ina inda bawa na
ya zace ni) bukari ne ya rawaito
Kuma tauhidi
shi ne tushen alheri da sa'ada duk wanda ya hadu da Allah da shi to zai rabauta
da aljanna Aa farkon lamari ko karshen sa Manzon Allah tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi ya ce : Allah madaukakiun sarki ya ce (ya dan adam da za ka zo mini da cikin kasa na kusakwarai
sannan ka hadu da ni ba ka hadani da wani to da zan
zo maka da cikin kasa na gafara )tirmizi
ne ya rawaito
Duk wanda ya
kyautata a wan nan duniya da imani da tauhidi to a lahira yana da aljanna da
ganin ubangiji mai daukaka Allah Madaukakin sarki ya ce : (ga wadanda su ka
kyautata suna da kyakkyawa da klari ) sallah na da kofa a cikin aljanna
da za a rika kiran masu yinta daga gare shi saboda sheki na gabban alwala da tsarki za a gane wannan alumma ranar
alkiyama da shi Mnzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya
ce(lallai aluamma ta za a kira su ranar alkiyama suna masu hasken goshi da
kafafuwa sakamakon gurbin alola ) bukari da muslim ne suka rawaito
(kayan ado da
bawa ya ke sawa yana isa ga mumini har
inda alolan sa ya isa ) muslim ne ya rawaito
Mai kiran
sallah ya na daga muryanshi da shelantawa na sallah sai sakayyarsa ya zama daga jinsin Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi (mai kiran sallan shi ne mafi tsawon wuya a
mutane ranar alkiyama ) muslim ne ya
rawaito (ba wanda zai ji iya sautin mai kiran sallah aljani ne ko mutun ko itaciya ko dutse face ya yi mishi shaida ranar alkiyama ) bukari ne ya rawaito Allah ya yi izini a
daukaka masallatayya a ambaci ku sunan shi a cikin su duk wanda ya gina
wa Allah masallaci alhlin yana nemar
yardan Allah to Allah zai gina mishi kwatan kwacin shi a alja) bukari da muslim na su ka
rawaito
Kuma
sadaka dalili ne na imani kuma rance ne abin ribanyawa a wurin Allah duk wanda ya ciyar da wani abu to Allah zai
maye mishi da abinda ya fii shi na alheri
Manzon Allah
tsira da amincin Allaah su tabbata a gare shi ya ce :(Allah
madakakin sarki ya ce : ya kai dan adam ka ciyar zan ciyar da kai )
bukari da muslim ne suka rawaito
(ba wata rana da bayi za su wayi gari a cikin shi face
malayiku biyu sun sauka dayansu sai ya ce ya allah duk mai ciyarwa ka maye
mishi daya kuma ya ce : ya allah duk mutumin da ke kame hanu to ka bashi
lalatacce ) Bukari da muslim ne
su ka rawaito
(ku ci ku sha ababan
farin ciki sakamakon abin da ku ka gabatar a ranakun da su ka shude )
Mujahid Allah ya mishi rahama yace : (Ta sauka ne akan
masu azumi). Za a kirayesu ne ta kofan rayyan kuma warin baskin mai
azumi ya fi kamshin turaren almiski a wurin Allah
Duk wanda ya mutu yana halin ihrami to za a
tashi yana mai talbiya,
Ambaton Allah
na raya zukata kuma yana sa karfin jiki, ma'abotansa basu da sakayya da ya fi
Allah ya ambace su, Allah Madaukakin sarki ya ce : (ku
ambace ni zan ambace ku) Duk wanda ya ambaci Allah a wani hali
to Allah zai ambace shi a hali mafi kyau Allah Madaukakin sarki ya ce a hadisin
kudsi (Ni ina tare da shi idan ya ambace ni,
idan ya ambace ni a zuciyarsa sai na ambace shi a zuciya ta, idan kuma ya
ambace ni cikin jama'a ne to sai na ambace shi a jama'ar da suka fi alheri a
kan su.) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Majalisai na
zikiri dausayi ne na aljanna, bawa na da abin da ya ke so a cikinta gun
Ubangijinsa, wasu mutane uku suka fiskanto Manzon Allah tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi, dayansu sai ya ga wani wuri a majlisin sai ya zauna a
wurin amma dayan sai ya zauna a bayansu, amma na ukun sai ya juya baya ya tafi
sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :Ase ba zan
baku labari game da mutanen nan uku ba? Shi na farkon su ya nemi mafaka a gurin
Allah sai Allah ya ba shi, shi dayan kuma sai ya ya ji kunya sai Allah ma ya ji
kunyarsa, amma dayan sai ya juya baya sai Allah ma ya juya masa baya. Buhari da
Muslim ne suka rawaito.
Addini
daukaka ne ga ma'abotansa, to duk wanda ya taimaki addinin Allah to shi wanda
zaa taimaka wa ne Allah Madaukakin sarki
ya ce :(Lalle Allah zai taimakawa wanda ya taimaki
addininSa)
Wanda ya
nusar ga alheri to yana da lada kwatankwacin ladan wanda ya yi aikin, kuma
wanda ya sunnanta wata sunna kyakkyawa to yana da ladanta da ladan wanda ya yi
aiki da ita har zuwa ranar alkiyama.
Kuma jarabawa
sunnar Allah ce a halittunSa, kuma girma sakayya na ga girman jarabawar, duk
wanda ya rungumi kaddara ya yarda to yana da yardar Allah, wanda ya yi fushi
kuma zai hadu da fushin Allah.
Hakuri wajibi
ne a umarni da hani da kuanyar shiga Aljannama kaddara, duk wanda ya jure ya yi
hakuri to Allah zai bashi juriya da hakuri, duk wanda ya nemi sanin Allah a
halin sauki to Allah zai kawo mishi
dauki yayin tsanani.
Gyaruwan
al'uma na ga ilimi, :(wanda ya bi wata hanya
yana mai neman ilimi to Allah zi saukake mishi da shi hanyar zuwa
aljanna.)Muslim ne ya rawaito shi.
Dukkan
dan Adam mai kuskure ne kuma mafi alherin masu kuskure sune masu tuba).
Wanda Allah
ya datar da shi zuwa ga tuba sai ya fiskanci Allah yana mai tuba to Allah zai
karbi tubansa kuma ya bashi lada Allah
Madaukakin sarki ya ce : (wanda ya tuba bayan
zalunci da ya yi ya kuma gyara to Allah zai karbi tubarsa.
Mumini idan
mutuwa ta zo mishi sai a mishi albishir da yardar Allah da karamarSa, to sai ya
zama ba wani abu da ya fi soyuwa a gare shi sama da abin da ke gaba gare shi
sai ya kaunaci gamuwa da Allah sai Allah ma ya so haduwa da shi, duk wanda ya muamalanci halittu da alheri sai
Allah ya muamalance shi da kwatankwacinsa a duniya da lahira. Kuma mafi
karamcin halittu shine Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi, duk wanda ya mishi salati guda to Allah zai mishi guda goma, Ansarawa
(sahaban Annabi na madina) ba mai son su sai mumuni, wanda ya so su Allah zai
so shi.
Kuma Allah na
tausayawa masu tausayi ne cikin bayinSa, duk wanda ba ya tausayawa mutane to
Allah ma ba zai tausaya mishi ba, Manzo Allah tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi ya ce : (wanda bai tausayi to ba zaa
tausaya mishi ba) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Wata mace
mazinaciya ta tausaya wa kare sai Allah ya mata rahama ya gafarta mata.
Wadanda suka
fi dacewa da kyautatawa sune 'yan uwa makusanta, wanda ya sada zumuncinsa sai
Allah ma ya sada masa.
Akwai aminci
cikin sallama wa mutane, Manzo Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi ya ce : (ku yada sallama za ku samu aminci)
Ibnu Hibban ne ya rawaito.
Wadanda ya
kankan da kai sabo da Allah to zai daukaka shi, Allah bai karawa bawa wani abu
sabo da yafiya face buwaya, Allah Madaukakin sarki ya ce : (su yi rangwami su yi afuwa shin ba ku son Allah ya muku
gafara ne).
Ibnu kasir Allah ya mishi rahama yace : (To lalle sakayya
na daga jinsin irin wannan aiki to kamar yadda zaka yafe wa wanda ya ma laifi
kai ma za a yafe maka haka nan kamar yadda ka yi rangwami kai ma za a ma
rangwami ).
Duk wanda ya
kaunaci wani bawa don Allah to Allah zai kaunace shi, haka duk wanda ya yi wa
dan'uwansa adu'a a bayan idonsa to sai mala'ikan da aka wakilta da shi ya ce
:amin kai ma Allah ya baka kwatankwacinsa.
Kuma buda wa
wani a majlisai sakayyarsa na daga
jinsinsa, Allah
Madaukakin sarki ya ce : (ya ku wadanda suka yi
imani da Allah idan an ce da ku ku buda a majlisai to ku buda Allah zai buda
muku).
Duk wanda ya
yafe wa musulmi to Allah ma zai yafe masa kurakuransa ranar alkiyama.
Allah na
kasance wa tare da mutum kamar yadda mutum ke tsayawa dan'uwansa musulmi,
Manzon Allah tsira da amincin Allaah su tabbata a gare
shi ya ce :(Duk wanda ya tsaya wurin biya wa dan uwansa bukata to Allah ma zai
kasance cikin biya masa bukata, duk wanda ya yaye wa musulmi wani bakinciki to
Allah ma zai yaye masa bakinciki daga bakincikin ranar alkiyama, duk wanda ya
rufa asirin wani musulmi to Allah ma zai rufa asirinsa ranar alkiyama)Buhari da
muslim ne suka rawaito.
(duk wanda ya yassara wa mara galihu to shi ma Allah zai
yassara mishi duniya da lahira. Allah na taimakon bawa muddin bawa na taimakon
dan'uwansa) Muslim ne ya rawaito.
Duk wanda ya
yafe wa halittu shi ma Allah zai yafe
masa, duk wanda ya 'yanta bawa, Allah zai 'yanta shi daga wuta gaba a madadin
gaba. Duk wanda ya ci bashin dukiyar mutane yana nufin ya biya to Allah zai
biya mishi, duk wanda ya wadatu da Allah da kuma abin da ya bashi to, to Allah
zai wadata shi kuma ya isan mishi, Manzon Allah
tsira da amincin Allaah su tabbata a gare shi ya ce :(Duk wanda ya nemi wadatar
Allah to Allah zai wadata shi) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Idan mutum ya
kame kai daga haram da rokon mutane to Allah zai sanya shi ya zama mai kame wa,
Manzon Allah tsira da amincin Allaah su tabbata
a gare shi ya ce :(Lalle ne duk wanda ya nemi ya zama mai kamun kai to Allah
zai maida shi mai kamewa.) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Ba wani bawa
da zai tausayawa wani bawa face shi ma Allah ya tausaya masa, Manzon Allah tsira da amincin Allaah su tabbata a gare
shi ya ce :(Ya Allah duk wanda ya jibinci wani abu na jagoranci a cikin
al'umata ya kuma tausaya musu to ya Allah ka tausaya masa.) Muslim
ne ya rawaito.
Alheri na
zuwa da alheri ne, ta daya hanun kuma shi ma sharri na zuwa da sharri ne, to
sakayyar mummuna ita ce mummuna kwatankwaciyarta. (Kuma
ba a saka muku face da abin da ku ka kasance kuna aikatawa.)
Wanda
zuciyarsa ta makance daga ganin gaskiya sai Allah ya makantar da ganinsa a
Matattara, (Kuma wanda ya kasance a nan makaho to a
lahira yana makaho kuma mafi bace wa bisa tafarki).
Duk wanda ya
kaucewa gaskiya bayan ya santa to Allah zai karkatar da zuciyarsa daga shiriya
ya jefa mishi shakku da tabewa. (Kuma a yayin da suka karkace sai Allah ya karkatar da
zukatansu).
Bijirewa
alheri da addini karshensa tube rigar imani ne,
Allah
Madaukakin sarki ya ce : (kuma hakika idan aka
saukar da wata sura sai sashinsu ya yi dubi zuwa ga sashi(su ce), shin wani
mutum yana ganinku? Sa'anan kuma sai su juya. Allah ya juyar da zukatansu,
domin hakika su mutane ne da ba su fahimta.)
Duk wanda ya
bar da'a ya shakala yinta da gangan to
Allah zai tabar da shi ya mantar da shi kansa ya bar shi cikin azaba, Allah
Madaukakin sarki ya ce : (sun mance Allah sai ya manta da su)
Lalacewar badini
akibar ta kara lalacewar, Allah Madaukakin sarki ya ce : (A cikin zukatansu akwai wata cuta sai Allah ya kara musu
wata cuta.)
Duk wanda ya
yi shamaki wa basirarsa daga addini to Allah zai masa shamaki daga ganinsa
ranar sakayya, Allah Madaukakin sarki ya ce : (A a
ha lalle ne su a wannan ranar abin shamakacewa ne daga Ubangijinsu).
Shirka shine
mafi girman zunubi to duk wanda ya
ta'allaka zuciyarsa da wani abu ba Allah ba sai a kyale shi da shi, duk wanda
ya nufi riya ko sum'a neman a ji da
aikinsa sai a saka mishi da irin aikin
shi, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce : (Duk wanda ya yi sum'a(neman aji) to sai Allah ya sa a ji
shi wanda ya yi riya sai Allah ya mai da
shi mai riya) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Mai bauta wa
wanin Allah tababbe ne a duniya da lahira,
Allah Madaukakin sarki ya ce : (kuma suka riki gumaka baicin Allah domin su kasance
mataimaka a gare su. A aha za su kafirta da ibadar su kuma su kasance
makiyansu.)
Wanda ya yi
wani aiki ya hada Allah da wani a cikinsa sai Allah ya bar shi da shirkansa,
wanda ya kasance yana bautawa wani abu baicin Allah to zai bi shi cikin wutar
jahannama, duk wanda ya rantse da wani addini bisa karya koma bayan musulunci
to ya koma kamar yadda ya ambata, duk wanda ya suranta sura zaa azabtar da shi
da ita ranar alkiyama, kuma a kallafa masa da ya busa masa rai, kuma ba zai iya
busawa ba, duk wanda ya nemi yardan mutane wajen fusata Allah, to Allah zai yi
fushi da shi kuma ya sanya mutane ma su yi fushi da shi, duk wanda ya tsani
haduwa da Allah da Allah to Allah ma ya tsani haduwa da shi, duk wanda ya nufi
ya yi kaidi da yaudara da makirci da hila ga addini to Allah zai mishi daurin
talala kuma in ya tashi ya mishi kamun ba zata, Allah Madaukakin sarki ya ce : (su ka yi makirci kuma Allah ya shirya musu sakamakon
makircinsu Allah shi ne ya fi makirai sakamakon makirci ) kuma ya ce
: (suna
yaudaran Allah shi kuma ya na maida musu yaudaran su )
Wanda ya
jinkirta salla Allah zai jinkirta shi
Manzon Allsah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (wasu mutane ba za su gushe ba suna yin jinkiri har sai
Allah ya jinkirta su ) muslim ne ya rawaito duk wanda ya ki yin sujjada a duniya sai a
hana shi yinta ranar alkiyama Allah
Madaukakin sarki ya ce (ranar da ake yayewa ga makengema kuma a kira su zuwa ga
sujjada ba za su samu daama ba )(gannansu
ta na wulakance saboda wulakanci tana lullube su ana kiransu a duniya zuwa
sujjada alhalin sauna masu lafiya ) girman kai shi ne dagun kai a
kan gaskiya ga halittu sai a tada ma'botan shi kamar kwayan zarra mutane na
taka su duk wanda ya yi karya guda daya da ta yadu to lallai Allah ranar
alkiyama zai juya muka mukinsa zuwa keyasa mazinata wani harshen wuta zai rika
zuwa musu tun diga kasansu Allah ya na debe albarkan riba maciyinshi kuma za a rika wurwurishi da
duwatsu a cikin bakin shi ranar alkiyama
duk wanda ya boye ilimi Allah zai sanya mishi linzami irin linzami na wuta
ranar alkiyama duk wanda ya ci gululi zai zo da abinda ya ci na gululi ranar
alkiyama duk wanda ya hana saurar ruwa Allah zai ce da shi ranar alkiyama a yau
zan hana ka falalata kamar yanda ka hana abinda ba hanunka ne ya aikatashi ba
duk wanda ya sha giya a duniya san nan bai tuba ba to an haramta mishi ita
ranar alkiyama wanda ya sanya alhariri daga cikin maza a duniya to ba zai sanya
ta ba a lahira wanda kuma ya yi da'awa irin da'wa na karya domin ya kara dukiya
ba abinda zai kara mishi a wurin Allah sai talauci butulcewa ni'ma yana
shelanta gushewanta Allah ba ya canja wani abu na ni'ma tare da mutane da jin
dadi na rayuwa har sai sun canja daga kawunan su da zalunci da sabo izgilanci
da addini da ma'botan addini sakayyansa na daga jinsinsa wanda ya yi izgilanci
ga bayin Allah Allah ma zai mar izgili alaman munafiki shi ne kin mutanen
madina na daga nasarawa wanda kuma ya ki su Allah zai ki shi duk wanda ya kashe
rayi tare da wani abu to za a rika azabtar da shi da wannan abun har ranar
alkiyama , mai sata na miji ya shinpida hanunshi ne akan barna saboda haka ta
cancanci a yanketa ,duk wanda ya yi kazafi wa kuyangansa ko kuma bawansa alhali
kuma shi ya barranta daga wannan to za amishi bulala ranar alkiyama za a
kafawa mahayinci tuta wanda za a sanshi
da shi a ranar alkiyama duk wanda ya la'anci wani abu wanda wannan abun bai
cancanci hakan ba to la'nan zata dawo kanshi Allah ya tsine wa wanda ya tsine
wa iyayenshi zalunci duhhai ne ranar alkiyama duk wanda ya yi zalunci gorgodon
kaidi na taki Allah zai nadeshi daga kassai guda bakwai
Yanke zumunci
na makusanta yafi muni akan waninsa Allah yana cewa ga mahaifa (ba ki yarda na sadar da wanda ya sadaki ba na yanke wanda
ya yankeki ba ) bukari da muslim ne suka rawaito Allah ya yi
alkawarin narkon azaba ga wadanda suke azabtar da mutane ba tare da hakki ba
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (lallai Allah yana azabtar da wadanda suke azabtar da
mutane a duniya ) muslim ne ya rawaito riskar da cutarwa da
wahalarwa ga halittu karshensa baya haifar da da mai ido Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (duk
wanda ya cutar to Allah ma ya cutar da shi duk wanda ya wahalar to shi ma Allah
ya wahalar da shi) tirmizi ne ya rawaito , duk wanda aka bawa wani
abu na jagoranci na musulmai sai ya kuntata musu ko kuma ya shamaki tsakaninshi
da su gameda bukatunsu to Allah ma sai ya yi shamaki tsakaninshi da shi duk
wanda ya bibiyi al'auran mutane to Allah ma zai bibiyi al'aurarsa har sai ya
kunyatashi a gidansa mai cin nama yana kekketa mutuncin mutane da harshensa zai
zo ranar alkiyama yanada farata daga karafunan nuhas bagwanja yana pippige
fiskansa da su wanda ya ji zancen wasu mutane wanda suke suna kin hakan za a
kwararamishi a kunnenshi harsashi na narkakken dalma ranar alkiyama garin
manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi amintacce ne duk
wanda ya bada tsoro ga mutanenta Allah ma zai tsorata shi wanda ya kasance
yanada mata biyu ya karkata zuwa ga dayansu zai zo ranar alkiyama tsaginshi a
karkace idan bawa ya bude kofan roko to Allah zai bude mishi kofan talauci rowa
da kamkame hanu yana goge albarka kuma yana wajabta tsananin hisabi Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (kada ka kididdige Allah ma sai ya kididdige maka)
bukari da muslim ne suka rawaito
Bayan haka ya
ku musulmai :
Allah mai
dubi ne ga bayinsa kuma yana dakonsu a madakata kuma zai sakanya wa kowa abunda
ya aikata sakayya na daga jinsin aikin wanda ya yi daidai da shi a alheri ne ko
na sharri kamar yanda ka ke hisabi kaima za amaka hisabi duk wanda ya nufi ya
san makomansa a wurin Ubangijinsa to ya duba abinda ya ke da shi a wurin Allah
domin Allah yana saukar da bawa ne inda bawa ya saukar da kansa
Ina neman
tsarin Allah daga shaidan abin jifa
Duk wanda ya
yi aiki na kwarai to don kansa wanda kuma ya munana to don kansa Ubangijinka
bai zama mai zalunci ba ga bayi Allah sa mini albarka ni da ku a cikin
alkur'ani mai girma
Huduba ta biyu
dukkan yabo
da godiya sun tabbata ga Allah bisa kyautatawansa dukkan godiya bisa ga
datarwansa da kuma baiwansa , na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah
shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya ina mai girmama sha'ninsa na shaida
cewa annabin mu Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi da iyalanshi da aminci tabbatacce mai kari
ya ku musulmai
duniya gida
ne na aiki lahira kuma gida ne na sakayya Allah ya kan gaggauto wa bawansa da
wani sakayya a nan duniya shi ni'man da ke hade da godiya ga ma'bota da'a
albishir ne , su kuma musibu tare da
hakuri daukaka ne ko kankaran zunubai , amma mai sabo wanda ya juya baya to
idan an jarrabeshi to wannan ukuba ce da gaggawa abinda ya ke gurin Allah shi
ya fi tsanani idan kuma an jinkirta ukubarsa to jinkirin da Allah ya misahi
kamar daurin talala ne
sannan ku
sani Allah yana umurtan ku da salati da aminci ga annabin sa.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق