Hudubar farko
Allah yana fadi a cikin littafinSa mai girma,
kuma shi ne mafi gaskiyar masu magana. (Ina
rantsuwa da zamani. Lalle mutum na cikin hasara. Face wadanda suka yi imani kuma
suka yi aiki na kwarai kuma suka yi wasiyya ga juna da gaskiya kuma suka yi
wasiyya da hakuri.)
Allah ya yi rantsuwa da Asr wato zamani
ko kuma wani yanki na shi, wato lokacin yammaci, shi aka yi rantsuwa da shi kan
cewa lalle jinsi na mutum na cikin hasara, to kowa duk wanda ya kasance haka to
makomarsa gidan halaka tir da matabbata, sai Allah ya toge daga cikin
hasararrun wadanda suka siffatu da sifofin nan guda hudu da ayoyi bayyanannu
suka nuna:
Sifa ta farko ita ce a fadinSa: "Face
wadanda suka yi imani" Imani kuma asalin shi da kamalarsa bai
samuwa sai da ilimi.
Sifa ta biyu ita ce a fadinSa:"
kuma suka yi aiki na kwarai" shi aiki na kwarai shi ne wanda
aka yi shi don Allah kuma bisa koyarwar Manzon Allah.
Sifa ta
uku ita ce a fadinSa Madaukakin ambato :" : "kuma suka yi wasiyya ga juna da
gaskiya" Hakikaninta kira zuwa ga Allah.
Sifa ta hudu ita ce a fadinSa Tabaraka wata'ala : " kuma suka yi wasiyya da hakuri." Wato
suka Siffatu da wannan sifa mai kubutarwa daga
hasara.
Duk wanda ya yarda da Allah a matsayin
Ubangiji, kuma ya yarda musulunci shine addini, kuma ya yarda Muhammad a matsayin Annabi kuma Manzo, ya san abin da
Allah ya ke kauna, ya fahimci manufa na wahayin Allah, ya yi aiki na kwarai don
Allah, ya tsarkake shi daga shirka, da bidia abin munantarwa, ya maida kansa
kamili ta hanyar ilimi mai amfani da aiki na kwarai, sannan ya yi kokari wurin
maida waninsa ma kamili ta hanyar kiransa zuwa ga gaskiyan da ya samu, ya yi
wasiyya kuma ya nemi a mar nasiha da abin da zaa tambayi kowa a kabarinsa na
sanin Allah da sanin Manzonsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da
sanin addinin musulunci, sani da ke tare da dalilanta na daga littafin Allah da sunnan Manzonsa tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi, da kuma abin da aka karbo daga sahabbai da limamai na
addini masu shiryarwa. Kuma ya yi hakuri
bisa imani da aiki na kwarai, da kuma kira zuwa ga Allah Mabuwayi da daukaka
yana yin shi a aikace da neman sani da ilmantarwa, da kuma hakuri bisa abin da
ke faruwa na cutarwa ga duk wanda ya riki
tafarkin Annabawa, to hakika wallahi ya tsira da hasara na rantse da Ubangijin
zamani.
Sabo da cika na wannan sura mai girma tare da
gajarcinta wajen bayanin abin da zaa umarci mutane don su tsira su rabauta Abu
Abdullahi Imam Al shafi'i Allah ya jikan shi ya ke cewa: "Wannan sura da Allah bai saukar da wata hujja ba ga
bayinSa sai ita to ta ishe su."
Ai da ta ishe su wajen tsaida musu hujja sabo
da wajabcin riko da umarnin Allah na sharia, ta hanyar gaskata wahayi na Allah,
da bin umarninSa da nesatan haninSa,da kudurta abin da Allah Mai tsarki ya halatta.
Allah sa min Albarka ni da ku.
Huduba ta biyu
Allah Madaukakin sarki yana cewa (ka sani cewa ba
abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma ka nemi gafarar zunubinka da na muminai
maza da muminai mata Allah ya sa majuyarku da mazauninku).
Sufyan Bin
Uyaina Allah ya masa rahama ya ce : "sai ya fara da ilimi kafi fadi da aiki," dukkan shiriya na cikin sanin ba abin bautawa
da gaskiya sai Allah, Addinin gaskiya gabadayansa ya kunshi neman gafara ne
gurin Allah da tuba zuwa gare shi furuci da aiki,
Allah Mabuwayi da Dauka yana cewa (Suna so su bice
hasken Allah da bakunansu alhali kuwa Allah Mai kammala haskenSa ne ko da
kafurai sun ki.shi ne wanda ya turo ManzonSa da shiriya da Addinin gaskiya don
ya daukaka shi akan dukkan addinai ko da mushrikai sun ki)
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق