Da sunan Allah Mai rahama
Mai jinkai.
Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun
tabbata ga Allah Mabuwayi Masani, wanda ya halicci mutum cikin mafi kyan tsari,
wanda ya tausayawa mukallafai da saukar musu wannan littafi mai daraja, wanda
ya yi baiwa ga halittu da ni'imomin da basu gidayuwa na daga falalarsa mai
girma, ina kyautata yabo ga Ubangiji na kuma ina gode mishi bisa ni'imominsa da
baiwarsa da alherunsa da muka sani da wadanda bamu sani ba, ba abin bauta wa da
gaskiya sai shi, Ma'abocin kyautatawan da bai katsewa da
kyautayinsa dadadde, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi
kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, Mai rahama Mai jinkai, na kuma shaida
Annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne kuma ManzonSa ne, mai shiryarwa
zuwa ga tafarki mikakke, ya Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka ga
bawanka kuma Manzonka Muhammad da iyalansa da sahabbansa wadanda suka rabauta
da daukaka na duniya, a lahira kuma suka rabauta da ni'ima na har abada.
Bayan haka, ku ji tsoron
Allah wanda ya halicce ku ya baku duk abin da kuke kauna ya tunkude muku abin
da kuka tsana, ya ku mutane! Ina tunatar da ku da ni kai na da ni'ima da ta fi
kowacce, dukkaninta Allah ya ni'imta mutum da su, muddin ya kiyaye ta ya bata
matsayinta cancancin matsayinta, ya kiyaye ta ya mutu a kanta to hakika ya samu
sa'ida a rayuwarsa da bayan mutuwarsa sa'idar da bai zai taba tsiyacewa ba da
ita har abada ya kuma rabauta da alhairu,
kuma ya tsira daga sharri da abubuwa masu halakarwa, Allah zai gyara dukkan
lamuransa baki daya a rayuwarsa, kuma ya jikansa bayan mutuwarsa, kuma wannan
shine babban rabo, idan mutum ya sauya wannan ni'ima mai girma ta hanyar
kafurcewa ko munafunci ko da wani aiki da ke kishiyantar wannan ni'imar ya
sarayar da ita da rashin kiyaye ta to hakika ya yi hasara mabayyaniyar hasara,
ko da an hada mishi abubuwan jin dadin duniya da kyalakyalanta, to ba wani abu
bane ita sai inuwa mai gushewa, kuma jindadi ne mai kaucewa, kuma ni'ima ce mai
karewa jindadinta na tafiya ta bar hasara. Allah Madaukakin sarki yace (Rayuwar duniya ba wata aba ba ce face jindadi mai rudi) Allah
Madaukakin sarki yace (ya ku mutane lalle
alkawarin Allah gaskiya ne kada rayuwar duniya ta rude ku, kada wani mai rudi
ya rude ku daga Allah.)
Ya ku bayin Allah! Ko kun san wannan ni'ima
mafi girma wanda Allah ya yi ga mutum ya kuma mutunta shi da ita? Lalle ita ce
ni'ima ta fidira, to menene hakikanin fidira, ana nufi da fidira halin da
Allah ya halicci mutum a kai, mai iya karbar kadaita Allah shi kadai ba
Ubangiji koma bayanSa, kuma ba abin bauta bayan shi, mai kaunar Alheri mai kin
sharri mai karkata zuwa ga biyayya, mai gano munin abubuwan da aka haramta, mai
sanin gaskiya a dunkule, kuma masanin bata a dunkule, da ace wannan fidirar da
Allah ya halicci mutum a kai ta kubuta daga shaidanun mutane da aljanu da
abubuwa masu tasiri da ke iya sanja ta to da ta zabi tauhidi da musulunci, sai
dai wannan fidira bata iya wadata da kanta wurin sanin gaskiya daki- daki daya -bayan
daya kuma ta yi aiki da shi haka ma sanin sharri da bata daya bayan daya da
nesatansu, to don haka ne Allah Mai tsarki ya turo manzanni, kuma na karshen su
shine Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi don su
kiyaye fidira kuma su koyar da
ita sharia su taimake ta da haske na wahayi a matsayin manhaji na rayuwa, na
daga cikin dalili da ke nuni cewa fidira ita ce halin da Allah ya halicci mutum
a kai da lafiyayyar dabi'a mai iya amsar addini mai son musulunci akwai fadin
Allah Madaukakin sarki ( ka tsayar da mafiskantar
ka ga addini kana mai totar izuwa gare shi kirar Allah ce wacce ya kera mutune
a kanta, babu musanyawa ga addinin Allah) Ibnu kasir Allah ya masa rahama
yace a cikin tafsirisa : ( ma'anarsa Allah
Madaukaki ya daidaita halittunsa gaba dayansu a kan fidira bisa dabia mikakkiya
da ba a haifan kowa face a kan haka, ba fifiko tsakanin mutane cikin haka) ta
tike.
An
karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : Dukkan abin haihuwa ana
haifansa ne akan musulunci to iyayensa ne ke yahudantar da shi ko kiristantar
da shi ko majusantar da shi, kamar yadda dabba lafiyayya kan haifi lafiyaya
babu wani abu da ku ke gani na gutsurarren hanci ko kunne.) Buhari da Muslim ne
suka rawaito.
An karbo
daga Iyad dan Himar Allah ya kara yarda
a gare shi, yace watarana Annabi ya yi huduba sai ya fada a cikin hudubar tasa
: lalle Ubangiji na ya umarce ni da na sanar da ku abin da baku sani ba. dukkan
dukiyan da na bawa bayi na na halal , lalle na halicci bayi na akan addini
hanifiya gabadayansu sai shaidanu suka zo musu suka batar da su daga addinin
su. suka haramta musu abin da aka halatta musu suka umarce su da su yi shirka da abin da ban saukar da
shi ba na hujja) Muslim ne ya rawaito
Imamul Bagawi
Allah ya mishi rahama ya ce a cikin
tafsirinsa: "Ance ma'nansa dukkan wani abin
haifa ana haifansa ne a farkon halittansa bisa fidra wato dabi'u masu lafiya da
halaye da suke a shirye don karban addini da zai tafi ne bisa lazimtar ta sabo da
wannan addinin kyanshi na nan cikin hankali sai dai kawai zai kauce ne daga
wannan zuwa wanin shi sabo da wata musiba da ta faru na daban kamar koyi ko
kwaikwayo, da mutun zai kubuta daga wannan musibun to ba zai kudurta wani abu
ba sai addini) . maganar ta kare.
wato fidra ana nufi da ita mahalli na imani
wanda shi ne dabia'n da mutun ya tafi a kan shi wanda aka halicce shi akanta a halinsa na dan adam kuma zuciyarsa a shirye
ta ke don karban ilimi mai amfani da aiki na kwarai, ma'ana na biyu a tafsirin fidra shi ne hasken
wahayi da ilimin sharia.
Ibnu abbas
Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : "Babu
canji ga halittan Allah ai ga addinin Allah"
Imamul Buhari
ya ce : "fadinsa la tabdila li kalkillah
ma'ana babu canji ga halittan Allah lidinillahi wato dabiyun mutanen farko shi
ne addinin mutanen farko addini da fidra kuma shi ne al islam .
maganan ya
tike.
To sai ya bayyana cewa fidra ita ce mahalli ko
bigire na imani da addini shi ne abin da aka haifi mutun akai na daga halitta
mikakkiya ko dabi'a mikakkiya wanda ana nufin da fidra shi ne halin da ya ke
cikinta na asali shi ne na shari'a da
imani.
Zan koro
misalai na wadannan ma'anoni biyu, kamar misalin fidira da aka haifi mutum a kai,
kamar misalin fitila ne na wutan lantarki wanda aka sana'anta aka yi shi ya
rika karbar wutar lantarki, shi wutan
lantarki kamar ilimi ne da wahayi da ke cikin zuciya idan aka hada kwan
lantarki da wayan lantarki mai wuta sai ya yi haske ya haskaka ya bada launi,
idan ba a hada su ba to ba dayansu da zai amfanar shi kadan shi wurin haskakawa,
to haka nan ma fidira ba za ta amfanar da ma'abocinta ba sai da ilimi
mai amfani da aiki na kwarai.
Fidira
ita ce abin da Allah ya karrama mutum da ita ya fifita shi da wannan fidira wacce
da ita ne ya ke sanin ma'arufi ya ki abu na munkari ya siffanta abu mai kyau da kyau ya munanta
abu mara kyau, idan fidira ta juya
ta rushe to kuwa mutum ya zama mamaci ko da yana tafiya a doron kasa, Allah Madaukakin sarki ya ce :( shin kuma wanda ya kasance matacce, sa'annan muka rayar
da shi, kuma muka sanya wani haske dominsa yana tafiya da shi, yana zama kamar
wanda misalinsa yana cikin duffai, shi kuma ba mai fita ba daga gare su.)
Fidirar mutum
ba ta samun kiyayewa ta karu da haske da sheki ta cika a karfi da rayuwa face
da ilimi mai amfani da aiki na kwarai, da imani da aiki na da'a, domin da'a ke
ciyar da ita ta sanya ta ta yi karfi, kuma nesatan abubuwan da aka haramta na
kare ta daga abubuwa masu darkakewa, duk
wani umarni na wajibi ko mustahabbi na kiyaye Fidira ya raya ta Allah Madaukakin sarki ya ce :( ya ku wadanda suka yi imani ku amsa wa Allah kuma ku
amsa wa Manzo idan ya kiraye ku zuwa ga
abin da yake rayar da ku).
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
ya ce :( Abubuwa goma suna cikin fidira : rage gashin baki da barin gemu da yin
aswaki da shaka ruwa da yanke kumba da wanke matattara da ke tsakanin yatsu,da
cire gashin hamata, da tsarki da ruwa, wato istinja'i) Muslim ne ya rawaito.
Idan
wadannan ta'adodin na cikin Fidira to
wasunsu na daga farillu sun fi dace wa su shigo ciki,
An karbo daga Bara'u dan Azib Allah ya kara yarda a gare
shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da
ni :idan kazo kwanciya to ka yi alwala, alwala irin na salla, ka kishingida a
baryarka na dama, ka ce : ya Allah na mika rayi na a gare ka na fiskantar da
fiska ta a gare ka, na fawwala al'amari na zuwa gare ka, na komar da baya ta
zuwa gare ka, halin kwadayi da tsoro
gare ka, ba mafaka da matsirata daga gare ka sai izuwa gare ka, na yi
imani da littafinka da ka saukar, da Annabinka da ka turo, to idan ka mutu to
zaka mutu ne a kan fidira ka sanya su karshen abin da za ka fadi.)Buhari
da Muslim ne suka rawaito.
Idan
fidira ta kasance ita ce sa'adar mutum ta hanyar gyaruwarta to lalacewarta kuwa
ita ce daidaicewar mutum da walakantarsa da hasararsa to ya wajaba mutum ya
nesaci abin da zai sanja ta ya lalata ta, kuma mafi hadarin aiki da zai sanja
ta ya lalata ta shine shirka, wato hada Allah da wani a bauta, ko sifanta Allah
da abin da ya tsarkaka daga shi, na daga da ko aboki, kamar fadin mushrikan
larabawa kafin turo Manzo na cewa : Mala'iku 'ya'ya mata ne na Allah, da wanda
ya yi irin wannan zance,
An karbo daga
Abdullahi dan Abbas Allah ya kara yarda a gare su daga Annabi tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi yace : Allah Madaukakin sarki ya ce :Dan Adam ya
karyata Ni , kuma bai dace ya yi hakan ba, Dan Adam ya zage Ni kuma bai dace ya
yi hakan ba, Amma karya ta Ni da yayi ita ce zaton sa da ya yi na cewa ba zan
iya maida shi kamar yadda ya ke ba, amma zagi Na da ya yi shi ne cewa da ya yi
ina da da, tsarki ya tabbata a gare Ni da na riki da,) Buhari ne ya rawaito. A
hadisin Abu Huraira :Amma zaginsa gare Ni cewarsa : Allah ya riki da Alhali kuwa Nine Allah tilo Assamad bai haifa
ba kuma ba a haife shi ba, bai da wanda yake kininSa,
Wannan yayi
nuni da fadinsu ya fi muni a kan masu bautan gumaka. shirka Allah ba ya gafarta
shi sai da tuba Allah Madaukakin sarki ya ce :( lalle wanda ya ke hada Allah da wani to hakika Allah ya
haramta Aljanna a gare shi kuma babu wasu mataimaka ga azzalumai )
Na daga cikin
abin da ya ke sauya fidra kuma ya bata ta akwai zunubai da aikata sabo Allah
bai halaka alumman da su ka gabace mu ba face sabo da lalacewan fidransu da
kuma ketare iyakansu daga umarnin Allah mabuwayi da daukaka Allah bai tsiratar
da muminai ba da su ke tare da su face da gyaruwan fidrarsu Allah madaukakin sarki
ya ce (sai muka tsiratar da wadanda suka yi
imani sun kasance kuma suna jin tsoron Allah) ga wannan aya akwai
abin lura cikin halaka mutanen ludu gaba dayansu ba wanda ya tsira daga cikin
su ko da mutun daya saboda lalacewan fidran su da kuma juyawanta suna aikata
alfahasha mai mummuna ba wanda ya tsira sai ludu amincin Allah su tabbata a
gare shi da 'ya'yansa mata biyu
Sabo yana
lalata fidra ta fiskan abin lura shi ne ko wani Annabi da Allah ya halaka
alummarsa wasu sashi sun yi imani da shi sai Allah ya tsiratar da su daga shi
amma mutanen ludu hakika sabo ya lalata musu fidrar su sai aka yi musu mafi
tsananin ukuba a doron kasa
Na daga cikin
abin da ya ke lalata fidra akwai yin zina domin yana da tasiri wurin kazanta
zuciya, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (mai zina ba zai yi zina ba a yayin da ya ke zina a
halin yana mumini, Barawo ba zai yi sata ba a yayin da ya ke sata a halin yana
mumini mai shan giya ba zai sha giya ba
ayayin da ya ke shan giya a halin yana mumini ) Buhari da Muslim ne
suka rawaito daga Abi Huraira
Ibnu mas'ud Alla ya kara yarda a gare shi ya
ce: "An hada zina tare da shirka"
yana nufin fadin Allah Madaukakin sarki (mazinaci
ba zai aura ba face mazinaciya ko mushrika )
To fa giya
ita ce ummul kaba'isi wato uwar kazanta Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce : (ku nisaci ummul
kaba'isi) Ibnu Hibban ne ya rawaito da baihaki daga hadisin usman
Allah ya kara yarda a gare shi manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi ya ce : (giya matattara ce ta laifi) saboda tana rusa fidra ta lalata gudanarwa da
hankali, kayan maye da miyagun kwayoyi su suka fi tsananin lalata fidra da
hankali kuma su suka fi hatsari ga alumma, to giya illan ta kan iya zame wa
kebabbiya ga mai shanta, kuma yana katangewa daga jin alkura'ani wanda shi ne
sababin dukkan alheri, kuma yana kai ma'abocin shi zuwa ga ukuba.
Na daga cikin abin da ya ke lalata fidra akwai
zaluncin bayi ga junan su, rushewar duniya na ga zaluntar bayi sashin su ga
sashe, Allah madaukakin satrki ya ce (kuma wadancan alkaryu mun halaka su a lokacin da suka yi
zalunci kuma muka sanya lokacin alkawarin ga halaka su)
Ya kai mutum
rabautar ka da gyaruwarka da farincikinka da daidaituwan al'amuranka gaba
dayansu da gadanka ga Aljanna mai ni'ima da tsirar ka daga azaban jahima na ga kiyaye
daidaitacciyar fidira ta hanyar riko da wannan sharia ta musulunci mikakkiya, Allah
Madaukakin satrki ya ce (kuma lalle wannan ne
tafarki na yana madaidaici sai ku bi shi kuma kada ku bi wasu hanyoyi su
rarraba ku daga barin hanya ta, wannan ne Allah ya muku wasiyya da shi ko za ku
ji tsoron Allah)
Allah ya sanya mini albarka ni da ku a
Alkur'ani mai girma ya kuma amfane ni da ku da abin da ke cikinsa na ayoyi da
ambato mai hikima.
Huduba ta
biyu
Dukkan yabo
da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai Mai karfi, Majibincin masu
tsoron Allah, ina kyautata yabo ga Ubangiji na kuma ina gode masa bisa ga
ni'imominSa da ba mai iya kididdige su sai shi, muna gode masa irin godiyar
masu shukura, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke
bashi da abokin tarayya, Allan mutanen
farko da na karshe, kuma na shaida Annabinmu kuma shugabammu Muhammdu bawansa
ne kuma ManzonSa ne mai gaskiya amintacce Allah ka yi dadin tsira da aminci da
albarka bisa ga bawanka kuma Manzon ka muhammad da iyalansa da sahabbansa da
wanda suka bi su da kyautatawa zuwa ranan sakayya, bayan haka ku ji soron Allah
madaukaki cancancin soron shi ku kiyaye saba wa shari'arsa ba wanda zai rabauta
cikin wanda su ka saba mishi.
Ya ku bayin
Allah ku kyautatawa kanku ta hanyar daidaituwa kan tafarki, hakika Allah ya
kyautata muku da shiriya da nau'ka na karama ya kai mutun : ka tsarkake ranka
daga kazantaccen abubuwa ka tsarkaketa ta hanyan amsa kira da karban abinda Ubangijinka
ke kiran ka zuwa gare shi Allah Madukakin sarki ya ce (ku amsa wa Ubangijinku tun gabanin wani yini ya zo ba bu
makawa gare shi daga Allah ba ku da wata mafaka a ranan nan kuma ba ku iya yin
wani musu )
Idan ka amsa
ya kai mutun ga umarni to za ka tashi da shi idan ka amsa kira ga hani kuma to
za ka nesace shi, to hakika matsayinka zai daukaka a wurin Ubangijinka kuma ka
karrama kanka ka gode wa ni'man fidra
wacce ta ke ita ce mafi girman ni'ma. Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce : (Lalle Allah na daga
darajan wasu mutane da wannan Alkur'ani, kuma ya kan yi kasa da wasu dalilin
shi)
da kuma abin da
al ummu su ka canja wanda ta wofanta daga fidrar Allah ba su amsa kiran Manzanninsu
ba sai su ka walakanta a wurin Allah kuma za su auka cikin tozarci da kuma
hasara ) Allah madaukakin sarki ya ce:( saboda
haka ko wannen su mun kama shi da laifinsa daga cikin su akwai wanda muka aika
iskar tsakuwa akan sa kuma daga cikin su akwai wanda tsawa ta kama kuma daga
cikin su akwai wanda muka birkice kasa da shi , kuma daga cikinsu akwai wanda
muka nutsar, baya yiwuwa ga Allah ya zalunce su , amma sun kasan ce kan su su
ke zalunta )
Ya ku bayin
Allah! lallai Allah da mala'ikunsa suna salati ga Annabi, ya ku wadanda su ka
yi imani ku yi salati gare shi da aminci tabbatacce .
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق