Hudubar Farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah,
tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah… bayan haka.
(Sharri Ya kai sharri ga mutum ya
rena dan'uwansa musulmi, Haramun ne
jinin musulmi ga dan'uwan shi musulmi, da dukiyarsa da mutuncinsa)
Musulmi wani rayayye ne da ke da karama da kima,
wani halitta ne da sharia ta kare matsayinsa,ta mutunta abubuwansa kebabbu da
suka shafe shi shi kadai to ka kiyaye
masa abubuwa da su ka shafe shi shi kadai, da basu kariya daga cutarwar duk
wani mai dakon sharri ko yaranta da neman laifukan wani, Allah Madaukakin sarki
ya ce :( ya ku wadanda suka bada gaskiya kada ku
tambayi abubuwan da in an bayyana muku su ranku zai baci)
Abin nufi
tambayar da bata shafe ka ba na daga yanayi da hali na mutane, ta yadda
hakan na iya kaiwa ga tona asirin su. Da tsinkayar sirrin su ko munanan halin
su.
Nassoshi na shari'a sun karfafa game da toshe
kofofin da zasu kai ga bankado asirin mutum musulmi, Allah Madaukakin sarki ya ce :( kada ku leko asiri) kar ku bayyana abin da
Allah ya suturce ta hanyar bincikowa game da laifukan mutane da bibiyan
al'aurarsu da musu tonon silili.
To dukkan musulmi yana da alhurma a kansa da
gidarsa da sum'arsa da dukiyarsa da maslahohinsa,wannan kyakkyawar dabia da
ladabi kan daga darajar musulmi ya nesatar da shi daga kaskantattun halaye,na
bibiyan sirrin mutane don kowa ya rayu cikin aminci da kwanciyar hankali a
kansa da gidansa da sirrinsa da al'auransa. Abin da yake na bayyane shi zamu yi
la'akari da shi,ba ya halatta mu binciko abin da yake na badini, Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Ni ba a umarce ni da na tono abin da ke zukatan mutane ba,ko na
zakulo abin da ke cikinsu ba).
Tajassus shine mutum ya rika bibiyar dan'uwansa musulmi
don ya gano sirrinsa, ko da kuwa ta kowani irin fiska ne na leken asiri, to a
cikin haka akwai cutarwa da hadari mai girma ga daidaiku da al'uma, sau da dama
ya haifar da bala'i ya raba zumunci ya dasa gaba da kiyayya a tskani.ya rusa
gida ya raba tsakanin dangi Allah Madaukakin
sarki ya ce :(Da wadanda ke cutar da muminai
maza da muminai mata ba tare da wani abu da suka aikata ba to hakika sun riki
kage da laifi bayyananne.).
A yayin da ka yi lura da fadin Allah Madaukakin
sarki (kada ku yi tajassus)
zai bayyana maka
gamewa da ya tabo kowane bangare na rayuwa, zaka ga yana magana da uba uwa yana
musu gargadi da kada su fada tarkon Tajassus da aukawa cikin keta
hurumin wanda suke bawa tarbiya ba tare da izininsu ba da ketare iyaka ba da
masaniyarsu ba, shi aikin tarbiya da gina al'uma da bada amana da sauke nauyi
ba ya hukunta leken abin da ya halatta ka leka, da kete alfarma da shiga
zarafin wani da kutawa cikin khususiyyar wani, Manzon Allah ya hana mutum ya kwankwasawa iyalansa
cikin dare, (yana neman sanin ha'incinsu
ko neman laifinsu,) kuma ya
ce: (Lalle idan ka bibiyi al'auran mutane zaka
lalata su ko kuma kana kusa da ka bata su)
Leken asirin juna tsakanin ma'aurata a gidansu
na aure ba tare da samuwar wani abu na hakika
da zai sa a yi hakan ba, ta hanyar binciken wasiku, maganganu, da
sakonni, a waya dabia ce da ke rusa aminta da ke akwai a tskani, ya tafiyar da
walwala ya gurbata alaka ya jefa shakku da juna.
Domin bada kariya ga khususiyya a rayuwa ta iyali musulunci ya dasa kyakkyawan
dabia na neman izini a zukatan yara maza da mata.
Na daga cikin abu tabbatacce karfafaffe fadin
Allah Madaukakin sarki :( kada ku leko
asiri) ya hada har da masu shiga kafafen sada zumunta,da su kame
daga keta hurumin musulmi da shige masa gona da iri cikin shaninnsa.sabo da
abin da wannan dabi'a ta kumsa na matsanancin cutarwa da mummunar illa.wanda da
shi ko ta hanyarsa ake jefa firgici da taaddanci da barna.
Kamar yadda mummunar zato ga dan'uwansa musulmi
kan jefa shi cikin duhun leken asiri(Tajassus), mummunan zato bai gushe
wa da ma'abocin shi har ya sa shi ya fadi abin da bai bayyana ba kuma ya aikata
abin da bai dace ba. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
ya ce :(Na hore ku da mummunar zato domin zato
shine mafi karyar zance, kuma kada ku yi Tajassus.)
Mutun kan fada ga tajassusi da gabbansa ya keta
alfarmar musulmi dalilin rashin abin yi da zurfafawa da tambaya game da rayuwan
mutane daki daki sai ya rika bibiyan abinda baida ilimi game da shi kokoma ya
yi sauraro zuwa ga wani abu ko ya yi dubi zuwa ga alauran da baida hakkin ya yi
kallo zuwa gareta Allah madaukin sarki ya ce: (kada
ka bibiyi abin da baka da ilimi game da shi lalle ne ji da gani da zuciya
dukkan wadannan Allah zai tambayi mai su me ya aikata da su)
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata
agare shi ya ce (na daga cikin kyautatuwan
musuluncin mutum barinsa abin da bai shafe shi ba )
Masifar tajassus na yaduwa cikin mutanen
da fahimtarsu ta gajarta, ginshikan addininsu ya bace sakamakon maida hankali
kan jita jita da yada shi ta hanyar tonon silili, Abin da ya ke wajibi a kan
musulmi shine ya lazimci zaman lafiya ta hanyar nesatan
Tajassus (neman laifin mutane) ya shagaltu da gyara laifukansa,domin
kuwa lalle wanda ya shagaltu da laifukansa daga laifukan waninsa to ya hutar da
gangan jikinsa kuma bai gajiyar da zuciyarsa ba, to amma wanda ya shagaltu da
laifukan mutane ya manta da laifukansa sai zuciyarsa ta makance jikinsa kuma ya
wahalta, kuma ya kasa barin laifinsa.
Imanin Musulmi na kare shi daga wannan cuta,ta
hanyar tafiya bisa manhajin Annabi da ya tsara mana, tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi,a fadinSa (Allah ya karhanta
muku abubuwa uku, jita –jita, da sarayar da dukiya, da yawan tambaya)
Ya tawagar wadanda suka yi imani da
halshensu,imani bai kai ga zuciya ba,kada ku ci naman
musulmi kada ku bibiyi al'auransu, to duk wanda ya bibiyi al'auran nusulmi,
Allah ma zai bibiyi al'auransa, duk wanda Allah ya bibiyi al'auransa to zai
kunyata shi ko acikin abin hawarsa ne).
Magani mafi dacewa ga cutar Tajassusi da
bin al'aurar mutane da kai komo wajen bankado kuskuren mutane,: shine musulmai
su tashi da abin da yake na wajibinsu wurin gyara laifin 'yan 'uwansu da
suturce al'auransu da nasiha, idan musulmi ya bar tajassusi a dabiunsa ya yi
nesa da shi daga bibiyan sirrin dan'uwansa ya dauke kai zuwa suturce musu, sai
Allah ya saka masa da kyautatawa mafi girma , Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce :Duk wanda ya suturce
musulmi Allah zai suturta shi a duniya da lahira). Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(wanda
ya yafe wani kuskureAllah zai yafe masa kuskurensa ranar alkiyama)
Huduba
ta biyu
Ya wajaba ga musulmi ya sani cewa Alhurma da
Allah ya kiyaye mishi ya bashi kariya tana hukunta kada ya keta alhurman
Allah,a halin kadaitarsa, domin Allah ya san sirrinsa da ganawarsa, ba abin da
ke boyuwa a gare shi,ya san sirri da aka boye wanda zuciya ta boye shi, An
karbo daga sauban daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace
: (na san wasu mutane cikin Al'umata zasu zo
ranar Alkiyama da lada masu yawa kamar dutsen tihama fari fat sai Allah
Mabuwayi da daukaka ya maishe shi kura tarwatsatsse, sauban ya ce : ya Manzon
Allah! Sifanta mana su bayyana mana su don kada mu kasance cikinsu a halin bamu
sani ba! Sai yace:Ai su din 'yan uwanku ne daga irin fatanku kuma suna tsayuwan
dare kamar yadda kuke yi, sai dai su mutane ne da idan sun kadaita da abin da
Allah ya haramta sai su keta ta).
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق