الأحد، 24 نوفمبر 2019

FALALAR SALLAMA DA LADUBARTA A MUSULUNCI


Hudubar Masllacin Annabi na SheikhAbdulmuhsin Bin Muhammad Alkasim  25-3-1441AH 22-11-2019 A
Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna gode masa kuma muna neman taimakonsa
Muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu  da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, wanda ya batar kuma babu mai shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya,kuma na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa. Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa.
Bayan haka, ku ji tsoron Allah -ya ku bayin Allah- cancancin tsoronSa, duk wanda ya ji tsoron Ubangijinsa zai daukaka da darajoji, makomansa zai dadada bayan mutuwa.
Ya ku musulmai :
Allah ya yi wa bayinSa ni'ima da addini mai girma wanda ya tattaro dukkan abubuwa masu kyau, kuma da shi ne halittu zasu gyaru, kuma da shi ne zasu samu sa'idarsu,  ya kuma karramasu da littafi mai haske mai shiriya mai waraka ya zaba wa wannan alumma mafificin manzonSa bai bar wani kofa na alheri ba face ya nusar da mu zuwa gare shi babu kofa na sharri kuma face ya gargade mu game da shi tare da cikan  nasiharsa da fasaharsa da rahamarsa. A addinin musulunci akwai laduba mafi daidaituwa da tsarkakuwa cikin al'amuran duniya da addini musulmi ya samu kamala a addininsa da halayyarsa da kuma ibadarsa da dabiunsa sai ya hada kyautata alaka a tsakaninsa da ubangijinsa    kuma da halittunsa na daga cikin manyan alamomi na wannan addini da kuma ladubansa akwai gaisuwa irin na aminci ta hanyan ambaton sunan Allah Madaukaki Assalamu da kuma neman kubuta da neman salama daga gare shi da kuma neman aminci daga gare shi tare da cikakken alkawari na aminci da cewa wanda ake yiwa sallama sharri ba zai riske shi ba ko wata cuta daga mai yin sallamar sabo da daukakar matsayi na sallama.
Allah ya yi gaisuwa da shi ga wanda matsayinsa ya daukaka a addini, Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :(Jibrilu ya zo ga  Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai yace ya Manzon Allah ga kadija nan tana zuwa maka da kwano cikinsa da abinci ko abin sha to ka isar mata da gaisuwa daga Ubangijinta, kuma ka mata albishir da gida na lu'ulu'u ba hayaniya a ciki ko wahala.) Buhari ne ya rawaito.
Na daga  cikin mafi alherin ni'ima a Aljanna Gaisuwar Allah  da aminci ga 'yan Aljanna, Allah Madaukakin sarki yace : (Aminci da magana daga Ubangiji Mai jinkai). Imamul Bagawi Allah ya mishi rahama yace : (wato Allah zai musu sallama ta hanyar magana)
Hakan kuma na sabunta a duk lokacin da suka hadu da shi, (Gaisuwarsu a yayin da suka hadu da shi ita ce Aminci)
 Jibrilu ya yi gaisuwa ga wacce ta tashi da hakkin Manzon musulunci tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, . Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da A'isha -Allah ya kara yarda a gare ta- Lalle jibrilu na gaisuwa a gare ki na aminci, sai tace, nace  :Amincin Allah ya tabbata a gare shi da rahamar Allah ) Muslim ne ya rawaito.
Idan an bude kofofin Aljanna farkon maganan da 'yan Aljanna zasu ji daga Mala'iku gaisuwa ce ta aminci gare su, (har zuwa lokacin da suka je a gare ta  aka bude kofofinta masu tsaronta su ce da su  : Aminci  ya tabbata a gare ku kun ji dadi ku shige ta kuna madawwama (a cikinta).)
A cikin lafuzan sallama akwai natsuwa da girmamawa da ni'ima,sabo da haka Allah ya umarci Mala'iku da su yi gaisuwa da ita ga 'yan Aljanna, a lokacin da suka shige ta don karin girmama wa a gare su, ta hanyar sauraron lafuza na aminci da taya murna,ta dukkan kofofi na Aljanna Allah Madaukakin sarki ya ce : (kuma mala'iku na shiga a gare su ta kowani kofa Amincin Allah su tabbata a gare ku to madalla da akibar gida.)
Sabo da matsayin sallama  da daukakar kimansa sai Allah ya zabe shi ga Adam da zuriyarsa, a farkon lokacin da Allah ya halicci Adam sai ya ce da shi, je ka yi sallama ga wadancan - tawaga na mala'iku – da ke zaune ka ji da me zasu gaishe ka da shi,to wannan ita ce gaisuwarka da zuriyarka,sai yace :"Amincin Allah ya tabbata a gare ku" sai suka ce Amincin Allah ya tabbata a gare ka da rahama sai suka kara da rahama.) Buhari da muslim ne suka rawaito.
Sai Allah ya kebanci shi a matsayin gaisuwa ne na musulmai a tsakaninsu, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:Ba abin da yahudu suke yi muku hasada game da shi kamar Gaisuwa da cewa Amin)Ibnu Maja ne ya rawaito.
Kuma ya hana su fara gaida wani da ba musulmi ba da shi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:( kada ku fara sallama ga yahudu da nasara) Muslim ne ya rawaito.
Haka kuma idan suka fara ba zaa maida musu da shi ba idan Ahlul kitabi suka muku sallama sai ku ce: kuma  a gare ku) Buhari da muslim ne suka rawaito.
Ba su rabuwa da sallama a cikin Aljanna kuma suna jin dadi da sun ji shi, (Ba su ji wata yasasshiyar magana a cikinta ko wani abu na laifi sai dai fadi na aminci aminci) ita  ce gaisuwa ga 'yan Aljanna a tsakaninsu, Allah Mabuwayi da daukaka ya ce : (suna masu dawwama a cikinta da izinin Ubangijinsu gaisuwarsu cikinta ita ce aminci).
A na samun alheri da albarka a cikin sallama, Allah Madaukakin sarki ya ce : (To ku yi sallama ga junanku gaisuwa daga Allah mai albarka ,tsarkakka.)
Na daga cikin albarkanta ma'abotanta na kusa da Ubangiji Allah, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:(Lalle mafi cancancin mutane kusantar Allah shine wanda ya fara sallama) Abu Dauda ne ya rawaito, Imam Addibi Allahya masa rahama  ya ce : " wato wanda ya fi kusancin rahamar Allah cikin mutane da suka gamu shi ne wanda ya fara sallama".
Matsayin sallama a musulunci na da girma, farkon abin da Annabi ya fara magana da shi da ya shigo garin Madina shine ya yi umarni da a yada sallama, Abdullahi dan salam ya ce :A yayin da Annabi ya zo garin Madina mutane sun yi cacarindo zuwa gare shi, ana cewa Manzon Allah ya iso Manzon Allah ya iso. Sai na shigo cikin mutane don na gan shi, a yayin da na samu ganin fiskar shi sai na tabbatar wannan fiskar ba na makaryaci ba ne,farkon maganar da ya fara da ita ya ce ne : (ya ku mutane ku yada sallama ku ciyar da abinci, ku sada zumunci, ku yi salla a halin mutane suna barci za ku shiga Aljannar Ubangijinku da aminci).Tirmizi ne ya rawaito, Imam Annawawi Allah ya masa rahama yace : A cikin yada sallama akwai haduwar zukantan musulmai sashinsu ga sashi, da kuma bayyana daya daga cikin manyan alamomi da ke rarrabe su da mabiya wasu addinai, wadanda ba su ba.
Annabi ya umarci sahabbansa da al'umarsa da ita (sallama) Albara'u dan Azib Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :( Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya umarce mu da abubuwa guda bakwai daga ciki akwai :" ku yada sallama").
Imam Annawawi Allah ya masa rahama yace: "yada sallama shine a yayata ta a yawaita a isar da ita ga kowani musulmi"
. sallama na daya daga cikin mafi alherin ta'ada na musulunci, kuma mafi darajan rassansa, Wani mutum ya tambayi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi:wani abu ne yafi a musulunci, sai yace : (ka ciyar da abinci, ka yada sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba,) Buhari da muslim ne suka rawaito. Imam Alkhaddabi Allah ya masa rahama yace: "ya sanya mafi alherin magana a da'a da karramawa shine yada sallama, wanda ke gamewa ba ya kebantarwa har ya zame don Allah kadai babu rabon rai da ko karya, domin wani alami ne na musulunci ya zama ruwan dare ne ga kowane musulmi".
sallama na kara imani, Ammar dan yasir Allah ya kara yarda da shi yace; "Abu uku idan mutum ya hada su to ya hada imani; Adalci a kanka, da yada salama ga duniya, da ciyar a halin talauci" Buhari ya rawaito.
Don yin biyayya ga Allah  da kaunar Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da girmama shi ya sa ake yin sallama  a gare shi, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Lalle Allah da mala'ikunsa suna salati ga Annabi, ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce"
Kuma Sallama a gare shi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a tahiyar salla rukuni ne daga cikin rukunnanta
Fara sallama da amsata na daga cikin hakki musulmi a kan musulmi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( hakkin musulmi a kan musulmi shida ne daga ciki idan ya hadu da shi ya yi sallama a gare shi) muslim ne ya rawaito .
A riwayar bukari da muslim (amsa sallama) kamar yanda sallama rayayye na amfana da ita haka nan ma matattu na da rabo a cikinta  annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya  kasance idan ya zo makabarta yana cewa (Aminci ya tabbata a gare ku ma'abota gidaje na daga muminai da musulmai ) muslim ne ya rawaito
Da sallama ne kauna da dunkulewa tsakanin musulmai ke dasuwa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce  (Na rantse da wanda raina ya ke hanunSa  ba za ku shiga Aljanna ba har sai kun yi imani, kuma ba za ku yi imani ba har sai kun so juna, ase ba zan nusar da ku zuwa ga abin da in kun yi shi za ku so junan ku ba ? ku yada sallama a tsakaninku ) muslim ne ya rawaito .(umar dan kaddab Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : abu uku za su tace ma kaunar dan uwanka ka mar sallama idan ka hadu da shi kuma ka yalwata mishi a majlasi kuma ka kira shi da sunan da yafi soyuwa a gare shi ) . 
sallama wata sifa ce ta karamci  Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi  ya ce : (mafi rowan mutane shi ne wanda ya yi rowan sallama  ) Ibnu Hibban ne ya rawaito. kuma shi dalili ne na alheri kuma shi ne mafi alherin magani ga wadanda su ka kaurace wa juna manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce  (ba ya halatta ga musulmi ya kauraci dan uwan shi sama da dare uku za su hadu su biyu amma wan nan ya juya baya wancan  ma ya juya baya mafi alheri a cikinsu shi ne wanda ya fara sallama ) bukari da muslim ne suka rawaito
Da sallama ne ake samun aminci da albarka  manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce(ku yada sallama za ku samu aminci tare da tabbatar da tauhidi da ingan cin imani sallama kan wajabta  aljanna ga ma'botnsa wani mutumi ya ce ga annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bani labari wani abu da zai wajabta min Aljanna sai ya ce ka kyautata zance kuma ka yada sallama ) ibnu hibban ne ya rawaito
Hasali ma sallama ya na kai darajoji na kololuwa a aljanna .
Lallai a cikin aljanna akwai wasu dakuna da ana ganin wajensu daga cikinsu kuma ana ganin cikinsu daga wajensu sai wani balaraben kauye ya tashi ya ce na waye ne su ya manzon Allah sai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( na wanda ya dadada zance kuyma ya yada sallama ya ciyar da abinci kuma ya yi salla da daddare mutane na bacci  )ibnu hibban ne ya rawito . saboda muhimmancin sallama da falalarta da girman fayidodinta aka shar'anta ga ko wani musulmi a ko wani hali duk wanda ya shiga gida zai yi sallama ga mutanen gidan Allah Madaukakin sarki ya ce : (To idan kun shiga gidaje ku yi sallama ga junanku gaisuwa daga Allah mai albarka ,tsarkakka.) kada wani ya shiga gidan waninsa sai bayan ya yi sallama kuma ya nemi izini Allah Madaukakin sarki ya ce : (ya ku wadanda su ka yi imani kada ku shiga gidaje wadanda ba gidajenku ba sai kun sami izini kuma kun yi sallama akan ma'abotansu wan nan ne mafi alheri a gare ku tsammanin ku za ku tuna ) wanda ya konkosa kofan waninsa don neman izini to ya fara da yin sallama sannan magana ta biyota  , wani mutumi ya zo ga annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a halin yana  gida sai ya ce in shigo ? sai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce ga mai mishi hidima (fita zuwa ga wan nan ka koya mishi yanda ake neman izini ka ce da shi: ka ce :assalamu alaikum in shigo ? sai mutumin ya ji shi sai ya ce assalamu alaikun na shigo ?sai annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi mishi izini   ) abu dauda ne ya rawaito kuma an sharanta haka a majlisai yayin shigansu ko fitansu manzon aAllah tsira da amincin Allah su tabbat a gare shi ya ce : (idan dayanku ya zo ga majlisi to ya yi sallama to haka ma idan zai tashi daga majlisin ma to ya yi sallama domin sallamar farkon ba ta fi na karshen ba ) abu dauda ne ya rawaito zai maimaita shi a duk masallatan shi har a masallatayya kamar yanda ya zo a hadisin mai bata  sallarsa .
 Sallama na daga cikin hakki ne na hanya ga wanda ya zauna a kanta manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (na horeku da zama a kan hanyoyi sai suka ce ya manzon Allah ba mu da mwuraren zamam mu muna tadi a cikinta sai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : idan kjun ki , dole sai kun zauna to ku bawa hanya hakkinta sa suka ce : to menene hakkin hanya ya manzon Allah sai ya ce runtsa gani  da kame cutarwa da amsa sallama da umarni da kyakkyawa da hani da mummuna ) buhari da muslim ne suka rawaito
To kaman yanda manya su ke da hakki na gaisuwa to haka yara ma suna da hakki, kuma a kan wannan ne sahabban Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi suka tafi, anas Allah ya kara yarda a gare shi ya wuce wasu yara sai ya yi sallama a garesu sai ya ce: annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance  yana aikata haka ) Buhari da muslim ne suka rawaito  manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana ziyartan lansarawa sai ya yi sallama ga yaransu  ) Bukari da Muslim ne suka rawaito
Sabo da muhimmancin sallama ga al'uma da daidaiku Allah bai sanya masa wani lokaci ba, sai dai kawai a duk lokacin da ya ga musulmi ko da bai san shi ba, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Duk wanda ya  hadu da dan'uwansa ya mishi sallama.)Buhari ne ya rawaito a Adabul Mufrad.
 (Idan dayanku ya hadu da dan'uwansa to ya mishi sallama.idan wata itaciya ta yi shamaki a tsakaninsu ko kango ko dutse sannan ya hadu da shi to ya mishi sallama)Abu Dauda ne ya rawaito.
Na daga cikin sifa na sallama akwai yada ta da yawaita ta  da yin ta ga kowani musulmi ba tare da banbantawa ba da wanda ka sani.
Ya ku Musulmai!
Musuunci Addini ne na alheri da aminci yana kira ga wanke zuciya da yada natsuwa da kwanciyar hankali ga al'uma, kuma yana kwadaitarwa wurin yada hadan kai da kauna tsakanin halittu, kuma yana sanya rahama a gare su da duk wani abu da zai iya tabbatar da hakan na daga sallama waninta, to musulunci na umarni da shi bisa wajabci ko mustahabbanci.
Ina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan abin jefewa.
(Idan an gaishe ku da gaisuwa to ku mayar da wacce ta fi ta ko ku maida irin ta lalle Allah ga dukkan komi mai kididdiga ne.)
Allah ya sa mini Albarka ni da ku cikin Alkur'ani Maigirma.


Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa kyautatawarsa, godiya ta tabbata a gare shi bisa datarwarsa da baiwarsa, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, ina mai girmama sha'aninSa, na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa. Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa.
 Ya ku musulmai! Farawa da sallama sunna ce da aka kwadaitar a kanta maida ta kuma wajibi ne. kari kuma wurin amsawa mustahabbi ne, maida irinta kuma farilla ne, na daga cikin laduban sallama karami ya gaida babba, mahayi ya gaida matafiyi a kafa, na tafe ya gaida na zaune, 'yan kadan su gaida masu yawa.idan na farkon ya bar sunna to na karshen mustahabbi ne ya gagauta aikata ta, an shar'anta maimaita sallama yayin bukata, kamar a taro mai yawa, ko zaton rashin isan sautin, Anas Allah kara yarda a gare shi ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan ya yi sallama ya kan maimaita sau uku.) Bukari ya rawaito.
Mustahabbi ne daga sauti yayin sallama, a farawa ne ko amsawa, don wannan abin da yada sallama ke hukuntawa kenan, Ibnu Umar Allah ya kara yarda a gare shi ya ce ;"idan ka yi sallama to ka jiyar, haka ma idan ka amsa to ka jiyar"
To jiyarwa kuma na kasancewa ne ba tare da cutar da wani ba,kamar mai barci da makamancinsa,hakika na daga cikin koyarwarsa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kan zo da dare ya yi sallama wanda bai tada mai barci kuma ya cjiyar da wanda ya ke fadake) Muslim ya rawaito.
Ba abin da ke hana sallama ko amsa shi sai hudubar juma'a, sabo da wajabcin sauraronta, haka kuma lokacin biyan bukata, don ba lwuri ne na gaisuwa ko zikiri ba, mustahabbi ne maida sallama ga wanda ya turo da wanda ya isar da ita :(Jibrilu yazo gurin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a halin yana tare da khadija, Allah ya kara yarda a gare ta.sai ya ce Allah na sallama ga khadija.sai tace lalle Allah shine Assalamu to amincin Allah ya tabbata ga jibrilu kai ma amincin Allah ya tabbata a gare ka da rahamarsa da albarkarsa )Nasa'I ne ya rawaito.
To ku sani Allah ya umarce ku da salati da aminci ga AnnabinSa.

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق