الجمعة، 15 نوفمبر 2019

Gulma a musulunci


Hudubar Masllacin Annabi na Sheikh Husaini Alusshaikh  18-3-1441AH 15-11-2019 A

Hudubar Farko
Na daga cikin tushen na zaman lafiya da ka'idoji na tsira akwai kiyaye harshe daga sharrace -sharrace da laifuka da shaidan zur da karya da kage Allah Madaukakin Sarki yace :(Ba ya lafazi da wata magana   face tare da shi akwai mai tsaro halartacce)  Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (wanda ya kasance yana imani da Allah da ranan duk lahira to ya fadi alheri ko ya yi shuru) anyi ittafaki bisa ingancinsa.
kuma manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare  shi yace (wa zai lamunce mini harshensa da farjinsa sai na lamunce masa Aljannah) Bukhari ne ya rawaito.
Ma'abota ilimi suka ce: "Ba ya dace wa yayi magana sai idan akwai alheri a maganar, wato ita ce wacce maslahar yinta ta bayyana duk wanda yayi shakku bisa maslaharta to yayi shuru".

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :(lallai bawa zai yi magana da kalma ba zai bayyana mishi (hadarinta) ba, zai zame cikin wuta a dalilinta fiye da nisan mahudan rana da mafadanta) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
A riwayar Buhari kuma :(lallai bawa zai yi magana da kalma na daga fushin Allah Madaukaki wanda ba zai kula da ita ba zai fada a cikin jahannama adalilinta )
Ya ku bayi Allah ku saurara!
Na daga cikin abubuwa mafi girma da suke halakarwa kuma mafi munin laifin akwai (giba) yi da wani shine mutum ya ambaci dan uwansa musulmi abayansa da wani abu dake tare dashi wanda bazai soba ,wan nan abin sawa,u ya kasance game da jikinsa ne ko Addininsa ko duniyarsa ko kuma halinsa ko halittarsa ko dukiyarsa ko dansa ko mahaifinsa,
Duka daya ne wurin haramcin giba  da lafazi ne ko a rubuce ko da wata alama ko wani nuni.
Allah madaukakin sarki yace "kada wasu sashinku suci naman wasu" Hakika Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fassara da fadinSa (ko kun san menene gibah sai suka ce Allah da ManzonSa ne suka fi sani, sai yace shine :Ambaton dan'uwanka da abin da ba zai so ba, sai aka ce to idan ga dan'uwan nawa akwai abin da nake fadi tattare da shi, yace : idan har akwai tare da shi abin da kake fadi to hakika ka ci namansa, to idan babu tare da shi abin da ka ke fadi to ka mar kage) Muslim ne ya rawaito.
To ka ji tsoron Allah ya kai musulmi! Ka sani cewa mutuncin musulmi abin karewa a musulunci, ka kiyaye kada ka yi da wani a bayansa da abin da ba zai so a ambace shi da shi ba na daga abin da zai musguna masa ko aibata shi,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Lallai jinannakinku da dukiyoyinku da mutuncinku haramun ne ga junanku kaman haramcin wannan rana naku a wannan gari naku a wannan watan naku) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
To ya kai wanda ka saki wa harshensa linzami cikin cin mutuncin musulmi ka tuna abin da Annabi ya fada wa Aisha masoyiyarsa diyar masoyinsa Allah ya kara yarda a gare ta tace na ce da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,:(Ya ishe ka ga safiya sifanta na kaza da kaza,) wasu marawaita suka ce tana nufin gajeruwa. Sai Annabi ya ce: Hakika kin fadi wata kalmar da da zaa surka ta da ruwan kogi da ta jirkita ta. Sai tace sai na hakaito mishi wani mutum,sai yace ban so a ce kin kwaikwayi wani ba, kawai da kin ce ina da kaza da kaza)   Tirmizi ne ya rawito  kuma ya ce Hadisi ne Hasan kuma sahihi.
Imam Annawawi yace : Wannan hadisi na cikin hadisai mafi tsawatarwa game da yi da wani ko ma shi ne mafi girmansu, kai ni ban san wani hadisi da ya kai kololuwa na aibata gulma ba kamar wannan hadisi!
Ya 'yan Uwa musulmi! Lalle giba na kai mutum ga halaka, an yi alkawarin ukuba mai girma ga mai yinta da sakayya mai radadi Allah Madaukakin Sarki ya ce : (Da wadanda ke cutar da muminai maza da muminai mata ba tare da wani abu da suka aikata ba to hakika sun riki kage da laifi bayyananne.).
 Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (A yayi da aka Mi'iraji da ni zuwa sama na hadu da wasu mutane suna da faratu na karfe suna yagunan fiskokinsu da kirazansu, sai nace su wanene wadannan ya Jibrilu  sai yace : wadannan su ke cin naman mutane suna taba mutuncinsu"Abu Dawuda ya rawaito, ibnu Hajar da waninsa suka ce hadisi ne Hasan, Ibnu Muflih ya ce : Isnadinsa ingantacce ne.
Ya ku musulmai!
Ya haramta ga musulmi da ya bada dama a yi gulman wani a gaban shi ko ya saurari hakan ko ya karanta, sai dai ma ya zama wajibi a gare shi ya yi hani ga mai gulman, kamar yadda ka'idoji na sharia ya gandaya.
Allah Madaukakin Sarki ya ce : (kuma idan kaga wadanda suke kutsawa a cikin ayoyinMU  to ka bijire daga gare su har sai sun kutsa a cikin wani labari da ba shi ba, kuma lallai imma shaidan ya mantar da kai to kada ka zauna a bayan tunawa tare da mutane azzalumai).
 Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Duk wanda ya kare mutuncin dan'uwansa musulmi to Allah ma zai kare fiskarsa daga wuta ranar Alkiyama) Tirmizi ne ya rawito ya ce hadisi ne hasan Ibnu Hajar shi ma ya ce Hadisi ne Hasan.

Ya 'yan Uwa Musulmai!
Giba na halatta ne kawai da manufa ingantacciya ta sharia, wanda ba zaa iya kaiwa gare ta ba sai ta hanyar hakan, misali mutumin da aka zalunta yana neman a masa adalci a karba masa hakkinsa daga wanda ya zalunce shi. Haka ma a halin yin nasiha ga wanda ya nemi shawara game da tarayya da wani da muamala da shi ko aurar mishi.

Huduba ta biyu
Ka gaggauta tuba zuwa ga Allah daga dukkan wani laifi da kusakurai ya dan'uwa na musulmi, ka sani lalle tuba daga yi da mutum na bukatar ka nemi yafiyarsa idan yana da masaniya, to amma idan ya kasance bai sani ba ko kuma neman yafiyar zai janyo wata fitina da barna daga wanda aka ci namarsa, to sai a nema masa gafara a yi masa adu'a, kuma ka ambaci alherinsa da kyawawan halayensa da ka sani a wuraren da ka kasance ka ci namarsa, wannan shine zancen mafi yawan malamai, kuma wannan zancen shine zabin  shaihun malamin musulunci Ibnu Taimiyya da almajirinsa babban malami Ibnul kayyim Allah ya jikansu da rahama.
Duk wanda Allah ya san gaskiyar niyyarsa da ikhlasinsa cikin tuban to Allah zai saukake masa sabubanta sabo da falala irin nashi(Allah) da karamci da kyautatawa.  

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق