Hudubar
Masallacin Annabi na shaikh Aliyu Abdurrahman Alhuzaifi 3/7/1438 Ah
Da sunan Allah
mai rahma mai jin kai
Dukkan yabo da
godiya sun tabbata ga Allah Mai rahma Mai jin kai masani mai hikima ma'boci mai
falala may girma ina keawtata yabo da ubangijina kuma ina gode mishi ina tuba
zuwa gare shi ina neman gafararsa, na
shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin
tarayya ma'aboci al'arshi mai girma. na shaida Annabinmu kuma shugabanmu Muhammad bawansa ne kuma
manzonsane ma'abocin halaye masu girma,
ya Allah ka yi dadin tsira da aminci ga bawanka kuma manzonka Muhammad da iyalansa da sahabbansa masu
da'awa(kira zuwa ga Allah)Masu shiryarwa zuwa ga tafarki mikakke, bayan haka,
Ku ji tsoron
Allah da aiki don neman yardarsa da kauracewa abin da ya haramta don ku rabauta
da yardarsa da ni'imar aljannarsa kuma ku tsira daga fushinsa da ukubarsa,
Ya ku
musulmai! Lalle ubangijinmu Allah mai girma da daukaka ya yawaita kofofin
alheri, da hanyoyin ayyuka na da'a da falala da rahama da kyauta da karamci
daga Ubangiji Mabuwayi da daukaka, don musulmi ya shiga daga kowane kofa na
alheri, kuma ya bi kowane tafarki na da'a, don Allah ya gyara masa duniyarsa
kuma ya daga darajarsa a lahirarsa, don Majibinci Mai daukaka ya karrama shi da daddadar rayuwa, da walwala
a rayuwarsa kuma ya samu ni'ima zaunanniya, da yardar Ubangiji bayan mutuwarsa.
Allah Madaukakin sarki ya ce :(sai ku yi tsere zuwa ga ayyukan alheri, inda
kuka kasance duka Allah zai zo da ku gaba daya, Lalle ne Allah akan kome mai ikon
yi ne.)
Allah
Madaukakin sarki yace game da Annabawa wadan da su abin koyi ne ga mutane tsira da amincin Allah su tabbata a
gare su gaba daya : (Sun kasance suna gudun tsere zuwa ga ayyukan alheri.
Kuma suna kiran mu akan kwadayi da fargaba. Sun kasance masu saunar (aikata
sabo) gare mu.
Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da Mu'az : ( Ase ba zan
nusar da kai ga kofofin alheri ba, Azumi garkuwa ne, sadaka na tunkude
kusakurai, kamar yadda ruwa ke kashe wuta,da
sallar mutum cikin dare, sai ya karanta : ( Sasanninsu na nisanta daga
wuraren kwanciya, suna kiran Ubangijinsu bisa ga tsoro da tsammani kuma suna
ciyarwa daga abin da muka azurta su.Sabo da haka wani rai bai san abin da aka
boye musu ba na sanyin idanu, domin sakamako ga abin da suka kasance suna
aikatawa).sannan yace ase ba zan baka labari ba ga tushen al'amura da
ginshikinsa, da kololuwar tozonsa? Sai na ce : E, a bani labari ya Manzon
Allah.sai ya ce : Tushen al'amari shine musulunci, ginshikinsa shine salla
kololuwar tozonsa shi ne Jahadi a tafarkin Allah ) Tirmizi ne ya rawaito ya
kuma inganta shi.
Na daga cikin
kofofi na alheri da hanyoyi na ayyukan kwarai da da'a da sabuba na kankare
munanan zunubbai akwai neman gafara
(Istigfari), Istigfari sunna ne na Annabawa da Manzanni tsira da amincin Allah su tabbata a gare su,
Allah Madaukakin sarki yace game da
mahaifa biyu na mutum amincin Allah da
rahamarsa da albarkarsa ya tabbata a
gare su, :
(suka ce ya Ubangijinmu
! Mun zalunci kanmu. Kuma idan ba ka gafarta mana ba, kuma ka yi mana rahama,
hakika muna kasancewa daga masu hasara)
Nuhu amincin
Allah ya tabbata a gare shi ya ce : (ya ubangiji na ka yi mini gafara (ni)
da mahaifa na biyu, da wanda ya shiga gida na yana muminai maza da mata).
Allah mabuwayi
da daukaka yace game da Ibrahim amincin Allah ya tabbata a gare shi, : (ya
Ubangijinmu ! ka yi gafara gare ni, kuma ga mahaifana, kuma da muminai, a ranar
da hisabi ya ke tsayawa).
Allah
madaukaki yace game da Musa amincin Allah ya tabbata a gare shi :(Yace : Ya
Ubangiji na ka gafarta mini ni da dan'u wa na , kuma ka shigar da mu a cikin
rahamarka alhali kuwa kai ne mafi rahamar masu rahama.!)
Allah madaukai
yace : Kuma Dawuda ya tabbata cewa mun fitine shi sabo da haka ya nemi
Ubangijinsa gafara kuma ya fadi yana mai sujada, kuma yana maida al'amari ga
Allah.)
Allah
Madaukakin sarki yace yana mai umarni ga Annabinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,
(saboda haka ka sani cewa babu abin bautawa face Allah kuma ka nemi gafara
ga zunubinka, kuma sabo da muminai maza da muminai mata).
Na daga cikin
koyarwar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yawan istigfari,
tare da cewa Allah ya gafarta masa abin da yan gabata na daga zunuban shi da
abin da ya jinkirta, an karbo daga Abdullahi dan umar رضي الله عنهما (ya ce:
mun kasance muna kirga wa annabi صلى الله عليه وسلم a
majlisi daya fadinsa ya ubangiji ka gafarta mini ka karbi tubana domin kai mai
yawan karban tuba ne har so dari ) Abu
Dawuda ne ya rawaito da Tirmizi kuma yace hadisi ne hasan kuma ingantacce,
kuma an
karbo daga A'isha رضي الله عنها ta ce (Annabi ya kasance yana yawaita cewa subhanallahi wa bi hamdihi astagfirullaha wa atubu ilaihi" kafin mutuwarsa ) Buhari da Muslim ne suka rawaito, kuma an karbo dagaAbu Huraira رضي الله عنه yace : (Ban ga wanda yafi manzon Allah صلى الله عليه وسلم yawaita fadin cewa Astagfirullaha wa atubu ilaih ba ) Nasa'i ne yarawaito
(mai tsira da amincin Allah sutabbata a
gareshi ya kasance yana cewa bayan sallama daga salla: Astagfirullah sau uku) Muslim ne ya rawaito daga hadisin Sauban
Allah ya kara yarda a gare shi.
Sa'annan
daga bisani sai ya fadi zikirorin da aka shar'anta fadinsu a bayan sallolin
farilla.
Kuma
lallai NEMAN GAFARA Dabi'ar salihai ne, kuma aiki ne na mutane
masu biyayya, da takawa, kuma alama ce ta muminan mutane,
Allah (تعالى) yana cewa:
"Ya
Ubangijinmu! Ka gafarta mana zunubanmu, kuma ka kankare mana munanan aiyukanmu,
kuma ka dauki rayukanmu tare da masu yin biyayya" [Ali-imrana: 193].
Kuma Allah (تعالى) yana cewa:
"Wadanda
suke cewa: Ya Ubangijinmu! Lallai mu mun yi Imani; sai ka gafarta mana
zunubanmu, kuma ka katange mu daga azabar wuta * Masu
hakuri, da masu gaskiya, da masu kankan da kai, da masu ciyarwa, da masu yin
istigfari a lokutan asuba" [Ali-imrana: 16-17].
Alhasan yace: Sun
yi ta sallah har zuwa lokacin sahur, sannan suka fiskanci ibadar neman gafara.
Kuma Allah (تعالى) yana cewa:
"Sune
kuma Wadanda, idan suka aikata wata alfasha, ko suka zalunci kayukansu su kan
tuna Allah; sai su nemi gafarar zunubansu, Kuma wanene zai gafarta zunubai idan
ba Allah ba, kuma basa dogewa akan abinda suke aikatawa, alhalin suna sane"
[Ali-imrana: 135].
Ibnu-rajab yace:
((Shi kuma neman gafara daga zunubai shine: Neman lullube
su. kuma lallai bawa yana da matukar bukata zuwa ga hakan;
saboda ko-yaushe ya kan yi kuskure cikin dare da rana. Kuma lallai ambaton TUBA
DA NEMAN GAFARA ya maimaitu a cikin alkur'ani, da kuma yin umurni da su, da kwadaitarwa
zuwa gare su)). … Maganarsa ta kare.
Kuma lallai NEMAN GAFARA DAGA Ubangiji mabuwayi da daukaka Allah ta'alah yayi
alkawari da cewa zai amsa, kuma zai yi gafara.
Kuma lallai an shar'anta cewa Bawa ya rika neman gafara a kan zunubi aiyananne,
sananne; saboda fadin Annabi (صلى الله عليه وسلم):
"Lallai
bawana ya aikata wani zunubi, Sannan yace: Ya Ubangijina, lallai ni na aikata
wani zunubi; sai ka gafarta mini shi, Sai Allah yace: Bawana lallai ya san
cewa yana da Ubangijin da yake gafarta zunubai, ya kuma tafiyar da
shi, to lallai na gafarta wa Bawana", Bukhariy da Muslim suka ruwaito
shi daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه).
Kamar yadda shari'a ta zo da cewa: Bawa ya rika neman gafara, a sake ba kaidi;
sai yace: Ya Ubangijina! ka gafarta min, kuma kayi mini rahama. Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma ka
ce: Ya Ubangijina! Ka yi gafara kuma ka yi rahama, domin kai ne mafi alherin
masu rahama" [Mu'uminuna: 118].
Kuma lallai
Annabi (صلى الله عليه وسلم)
ya kasance yana sanar da mutumin da ya musulunta da cewa ya rika yin addu'a da
wadannan kalmomin :
"Ya Allah
ka yi gafara a gare ni, ka yi mini rahama, ka shiryar da ni, ka bani lafiya, ka
azurta ni", Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Darik dan Ashyam (Allah
ya kara yarda a gare shi).
Kamar yadda aka shar'anta: Bawa ya rika nema daga Ubangijinsa cewa ya gafarta
masa zunubansa gabadayansu; wadanda ya san su da wadanda bai sansu ba; wannan
kuma saboda zunubai dayawa babu wanda ya sansu sai Allah, kuma lallai bawa za a
kama shi akansu; Ya zo daga Abu-Musa al'ash'ariy (رضي الله عنه)
daga Annabi(صلى الله عليه وسلم)
lallai shi ya kasance yana yin addu'a da wannan addu'ar:
"Ya
Allah! Ka gafarta min kurakuraina da jahilcina, da ketare iyakana cikin lamari,
da abinda kai ne ka fini saninsa. Ya Allah! Ka gafarta mini gaskena da wasana,
da kuskurena da gangancina, kuma dukkan haka, akwai shi a wurina. Ya Allah! Ka
gafarta mini abinda na gabatar da wanda na jinkirta, da abinda na boye da
abinda na bayyanar, da abinda kai ne ka fi ni saninsa, kai ne Mai gabatarwa,
kuma kai ne Mai jinkirtarwa, kuma lallai kai akan kowani abu mai iko ne",
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Da kuma saboda fadin
Annabi (صلى الله عليه وسلم):
"Shirka a
cikin wannan al'ummar tafi buya fiye da tafiyar tururuwa, Sai Abubakar
(رضي الله عنه)
yace: To ta yaya za a kubuta daga gare ta, ya Manzon Allah? Sai
yace: Ka rika cewa: Ya Allah ina neman ka tsare ni kan yin shirka a
gare ka alhalin ina sane, Ina kuma neman gafararka daga zunubin da ban sani ba",
Ibnu-Hibbana ya ruwaito shi, daga hadisin Abubakar, Da kuma Ahmad, daga hadisin
Abu Musa.
An ruwaito daga
Abu-hurairah (رضي الله عنه),
daga Annabi (صلى الله عليه وسلم)
lallai shi ya kasance yana yin addu'a:
"Ya
Allah! Ka gafarta min zunubaina dukkansu; kananansu da manyansu, na kuskurensu
dana gangancinsu, na sirrinsu dana bayyanansu, na farkonsu da na karshensu", Muslim ya ruwaito shi, da Abu-dawud.
Idan bawa ya rokiUbangijinSa gafarar
zunubansa; wadanda ya sani daga cikinsu da wadanda bai sani ba, to lallai an
datar da shi; dace mai girma.
Kuma bawa ya roki Ubangijinsa gafarar zunubai cikin ikhlasi da naci da roko mai
tattare da kankan-da kai yana kunsan TUBA DAGA ZUNUBAN, Shi kuma ROKON A DATAR
DA MUTUM ZUWA GA TUBAN yana kunsan NEMAN GAFARAR; saboda haka, kowanne daga
cikin ISTIGFAAR da TUBA idan aka ambace shi ba tare da dayanba to yana kunsan
ma'anan dayan. Idan kuma ambatonsu ya hadu a cikin nassoshin Kur'ani ko
hadisi to Ma'anan: ISTIGFAARI sai ya zama: Neman shafe zunubi da gusar da
alamarsa ko gurbin da ya bari, tare da bada kariya kan sharrin da ya gabata na
zunubin, da kuma suturce shi. Ita kuma TUBA sai ma'ananta ya zama: Komawa zuwa
ga Allah; ta hanyar barin aikata zunubai, da kuma kare bawa daga abinda ya ke
tsoro; na munanan aiyukansa a rayuwar da yake fiskanta, tare da yin azama ko
niyyar ba zai sake aikata zunubin ba.
Kuma lallai
AyarAllah ta ambaci ISTIGFAARI da TUBA a hade, a inda Allah yake cewa:
"Kuma ku
nemi gafarar Ubangijinku, sa'annan ku tuba zuwa gare shi, zai jiyar da ku dadi
jiyarwa mai kyau, zuwa ga wani lokaci ambatacce, kuma ya baiwa dukkan ma'abocin
girma girmansa, Idan kuma kuka juya to lallai ni ina tsoron azabar yini mai
girma akanku" [Hud: 3].
Da wassu ayoyin
wadanda ba wannan ba.
Kuma lallai
Annabi (صلى الله عليه وسلم)
yace:
"Ya ku
mutane! Ku tuba zuwa ga Ubangijinku, kuma ku nemi gafararSa; saboda Ni na kan
tuba zuwa gare shi, ina kuma neman gafararSa; a kowani yini sau dari",
Annasa'iy ne ya ruwaito shi, daga hadisin Al'agarri Almuzaniy (رضي الله عنه).
Kuma lallai bawa yana da matsananciyar bukatar YIN ISTIGFAARI, a
ko-da-yaushe, musamman kuma a wannan zamanin
saboda yawaitan ZUNUBAI da FITINTINU, wannan kuma domin Allah
ya datar da shi a rayuwarsa, da kuma bayan mutuwarsa, ya kuma gyara masa
sha'aninsa. Saboda yin istigfaari ya kan bude kofofin
alherori, ya kuma tunkude sharrori da ukubobi.
Kuma lallai itama al'ummar musulmai tana da matsananciyar bukata zuwa ga
dawwama kan neman gafara; domin Allah ya yaye mata ukubobi da suka sauka a gare
ta, ya kuma tunkude mata ukobobin da za su sake sauka a gare ta.
Kuma babu wanda zai yi sakaci KAN NEMAN GAFARA sai wanda ya jahilci amfanoninsa
da albarkokinsa, saboda falolinsa sun zo dayawa a cikin
ALKUR'ANI da SUNNAH; Allah (تعالى) yana cewa dangane da annabi Salihu (عليه السلام):
"Ya ku
mutanena! Don me kuke gaggawan aikata mummuna gabanin kyakkyawa, Da dai kun
nemi gafarar Allah; da tsammanin za a yi rahama a gare ku" [Naml:
46]. Saboda da yin istigfaari ne ake yin rahama ga al'ummah.
Kuma Allah (تعالى) yana fada dangane da annabi Nuhu (عليه السلام):
"Sai
nace: KU NEMI GAFARAR UBANGIJINKU lallai shi ya kasance mai yawan
gafara * Zai saki ruwan sama akanku;
mamako * kuma ya karfafe ku da wata dukiya,
da 'ya'ya, kuma ya sanya muku gonakai, kuma ya sanya muku koguna"
[Nuh:10-12].
Kuma Allah (تعالى) yake fadi dangane da annabi Hudu (عليه السلام):
"Kuma, ya
mutanena! Ku nemi gafarar Ubangijinku, sa'annan ku tuba zuwa gare shi; sai ya
saki ruwan sama akanku, ya kuma kara muku wani karfi akan karfinku, Kuma kada
ku juya baya kuna masu laifi" [Hudu: 52].
Allah (تعالى) yace:
"Allah
bai kasance zai azabta su ba alhalin kana cikinsu, kuma Allah bai kasance mai
azabta su ba; matukar suna neman gafara" [Anfaal: 33].
Abu-Musa yake
cewa (رضي الله عنه):
((Lallai wannan
al'ummah a cikinku akwai abubuwan samun aminci guda biyu; Amma
dangane da wannan annabin –صلى الله عليه وسلم-
to shi kam ya shude, Yayin da shi kuma NEMAN GAFARA zai ci gaba da wanzuwa a
cikinku har zuwa tashin kiyama)).
Don haka; Wannan al'ummar; Idan ta yawaita istigfaari = zai dauke mata musibun
da suka sauka ko suka auku, sannan ya tunkude mata wadanda za su sauka a
gaba; saboda bala'i baya sauka sai idan an yi
ZUNUBI, kuma ba a yaye shi sai da yin TUBA da
ISTIGFAARI, An ruwaito daga Abdullahi dan Abbas (رضي الله عنهما)
yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم)
yace:
"Duk
wanda ya lazimci yin istigfaari Allah zai sanya masa mafita daga kowani kunci,
da kuma yayewa daga kowani bakin ciki, ya kuma azurta shi ta yadda baya
tsammani", Abu-dawud ya ruwaito shi.
Kuma lallai KALMOMI DA AKA KIYAYE SU MASU ALBARKA na ISTIGFAARI sun zo daga
Annabi (صلى الله عليه وسلم),
kuma lallai cikin fadin wadannan kalmomin akwai lada mai yawa;
Yana
daga cikinsu:
Fadinsa (صلى الله عليه وسلم):
"Duk
wanda ya fadI: ASTAGFIRUL LAHAL ALZIY LA ILAHA ILLA HUWAL HAYYAL KAYYUMA, WA
ATUBU ILAIHI, Duk wanda ya fadi haka to an gafarta zunubansa,
koda kuwa ya gudu a wurin yaki". Abu-dawud da Tirmiziy suka ruwaito
shi, da Hakim, kuma yace: hadisi ne ingantacce, akan sharadin Bukhariy da
Muslim.
An ruwaito daga
Abu-Sa'id alkhudriy, daga Annabi (صلى الله عليه وسلم),
lallai yace:
"Duk
wanda ya fada a lokacin da ya tafo zuwa ga shumfudinsa: ASTAGFIRUL LAHA ALLAZIY
LA ILAHA ILLA HUWAL HAYYUL KAYYUMU, WA ATUBU ILAIHI, sau uku, to
Allah zai gafarta zunubansa, koda sun kai kumfan teku", Tirmiziy ne ya
ruwaito shi.
An ruwaito daga
Ubadah dan As-samit (رضي الله عنه)
yace: Annabi (صلى الله عليه وسلم)
yace:
"Duk
wanda ya tashi daga barcinsa, a cikin dare' Sa'annan yace: LA ILAHA ILLAL LAHU,
WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN KADIR,
SUBHANAL LAHI, WALHAMDU LILLAHI, WA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR, ALLAHUMMAG
FIR LIY, Sai yayi addu'a to an amsa masa, idan kuma ya tashi yayi sallah to an
karbi sallarsa", Bukhariy ne ya ruwaito shi.
Ya zo cikin wani
hadisin cewa:
"Duk
wanda a gabanin ketowar alfijir din juma'a yace: ASTAGFIRUL LAHAL ALZIY LA
ILAHA ILLA HUWAL HAYYAL KAYYUMA, WA ATUBU ILAIHI, sau uku, an
gafarta zunubansa koda sun kasance misalin kumfar teku ne".
Kuma an ruwaito
daga Shaddad dau Aus (رضي الله عنه)
daga Annabi (صلى الله عليه وسلم)
yace:
"Jagoran
laffuzan neman gafara shine bawa yace: ALLAHUMMA ANTA RABBIY LA ILAHA ILLA
ANTA; KHALAKTANIY, WA ANA ABDUKA, WA ANA ALA AHDIKA WA WA'ADIKA MASTADA'ATU,
A'UZU BIKA MIN SHARRI MA SANA'ATU, ABU'U LAKA BI NI'IMATIKA ALAYYA, WA ABU'U BI
ZANBIY; FAGFIR LIY; FA INNAHU LA YAGFIRUZ ZUNUBA ILLA ANTA, Duk wanda ya fadi
kalmomin nan cikin yini yana mai samun yakini akansu sai ya mutu a wannan yinin
nasa, gabanin yayi yammaci ya shiga aljannah. Wanda kuma ya fade su cikin dare,
alhalin yana da yakini akansu sai ya mutu gabanin yayi yammaci to yana cikin
'yan aljannah", Bukhariy ya ruwaito shi.
An ruwaito daga
Anas (رضي الله عنه)
yace: Na ji Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم)
yana cewa: Allah (تعالى) yana cewa:
"Ya kai dan
Adam! Da zunubanka za su cika sashen sama gabadaya, sannan sai ka nemi gafarata
sai in gafarta maka, ba zan damu ba!", Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma
yace: hadisi ne mai kyau.
Kamar yadda kuma ake shar'anta neman GAFARAR ALLAH a lokacin yin wata
ibada ko bayan kammala ta; wannan kuma domin ta magance abinda ya kasance a
cikin ibadar na tawaya ko nakasa, tare da nisantar da mutum daga ji-da kai, ko
riya; Allah (تعالى)
yana cewa:
"Sa'annan
ku tafo ta wurin da mutane suke gangarowa, kuma ku nemi gafarar Allah, lallai
Allah Mai gafara ne Mai rahama" [Bakarah: 199].
Kuma Allah (سبحانه) yana cewa:
"Kuma ku
tsayar da sallah, kuma ku bada zakka, ku bada rance wa Allah rance mai
kyau, kuma duk abinda kuka gabatar ga kayukanku na alkhairi
za ku same shi a wurin Allah, zai kasance mafifici kuma zai fi girma ga
sakamako, Kuma ku roki Allah gafara; lallai Allah Mai gafara ne Mai rahama"
[Muzammil: 20].
Sai Allah yayi
umurnin a nemi gafararSa a lokacin da ake yin wadannan aiyukan da'an, da kuma
bayan kammala su.
Haka kuma an shar'anta musulmi ya rika neman gafara ga 'yan'uwansa muminai;
maza da mata, da musulmai maza da msulmai mata, rayayyu daga cikinsu da wadanda
suka mutu, wannan kuma a matsayin kyautatawarsa ne a gare su,
da bayyanar da soyayya, da lafiyar zuciya, tare da amfanar da musulmai, da kuma
(tsoma baki) don neman cetonsu a wurin Allah; Allah (تعالى) yana cewa:
"Da kuma
wadanda suka zo a bayansu, suna cewa: Ya Ubangijinmu ka yi mana gafara, tare da
'yan'uwanmu da suka rigaye mu da Imani, kuma kada ka sanya wani kulli a cikin
zukatanmu dangane da wadanda suka yi imani, Ya Ubangijinmu lallai kai Mai
tausayi ne, Mai rahama" [Hahsri: 10].
An ruwaito daga
Ubadah dan Assamit (رضي الله عنه)
daga Annabi (صلى الله عليه وسلم)
lallai shi yace:
"Duk
wanda ya nemi gafara ga muminai maza da muminai mata to lallai Allah zai rubuta
masa lada a madadin kowani mumini namiji da mumina mace", Alhaisamiy
yace: Isnadin wannan hadisin yana da kyau (jayyid).
Wannan kuma kamar
nema musu gafara kenan a lokacin yin sallar janaza a gare su, da kuma nema musu
gafara a makabartai idan musulmi ya ziyarce su.
Hakan kuma koyi
ne da Mala'ikun da suke dauke da al'arshi, da kuma sauran Mala'iku
makusanta, Allah yana cewa:
"Wadanda
suke rike da al'arshi, da wadanda suke kewayensa suna yin tasbihi da gode wa
Ubangijinsu, kuma suna yin imani da shi, suna kuma neman gafarar Allah ga wadanda
suka yi imani (suna cewa) Ya Ubangijinmu! Lallai ka yalwaci kowani abu da
rahama da kuma ilimi; sai ka yi gafara ga wadanda suka tuba, suka kuma bi
hanyarka, kuma ka kare su daga azabar wutar jahim" [Gafir: 7].
Yin haka kuma
yana daga cikin manyan hakkokin muminai!
Ya ku bayin Allah… !
Ku amsawa umurnin
Ubangijinku, Allah yana cewa a cikin hadisin kudusiy:
"Ya ku
bayina ! lallai ku, kuna yin laifi dare da rana, Ni kuma ina gafarta zunubai
gabadaya; sai ku nemi gafarata; zan gafarta muku", Muslim ya ruwaito
shi daga hadisin Abi-zarrin.
Sai
ku fiskanci Ubangijinku da neman gafararSa, za ku ga karamcinSa da kyautarSa da
falalarSa, da albarkokinSa, kuma za ku sami shafe aiyukanku munana, da daukaka
darajoji, Hadisi y azo daga Abu-hurairah (رضي الله عنه)
yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم)
yace:
"Na
rantse da wanda raina yake hannunsa! Da ace bakwa yin zunubi to da Allah
ta'alah ya tafiyar da ku, kuma da ya zo da wassu mutanen wadanda suke yin
zunubi; sai suna neman gafarar Allah ta'alah sai ya gafarta musu",
Muslim ya ruwaito shi.
Kuma saboda
kasancewarsa Allah madaukaki Mai yalwar gafara ne, mai baiwa da kyauta da
karamci, yana son a rika neman gafararSa, ana rokonSa Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma duk
wanda ya aikata mummunan aiki, ko ya zalunci kansa, sa'annan sai ya nemi
gafarar Allah, to lallai zai sami Allah Mai yawan gafara Mai rahama"
[Nisa'i: 110].
Allah yayi mini albarka Ni da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da
mu da abinda ke cikinsa na ayoyi da tunatarwa mai
hikima, kuma ya amfanar da mu da shiriyar
shugaban manzanni, da kuma maganganunsa mikakku, Ina fadar
maganata wannan, kuma ina neman gafarar Allah Mai girma Mai daraja wa Ni da Ku,
da kuma sauran musulmai da muminai, Ku nemi gafararSa;
lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da
godiya sun tabbata Allah Mai gafara abin godiya, Ga Ubangiji na na da sunaye
kyawawa da sifofi madaukaka, ina godewa Ubangiji na bisa ga ni'imominsa masu
girma, kuma na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba
shi da abokin tarayya, kuma na shaida shugabanmu kuma Annabinmu Muhammad
bawansa ne kuma Manzonsa ne, zababbe, ya Allah ka yi salati da aminci ga
bawanka kuma Manzonka Muhammad da iyalansa da Iyalansa da sahabbansa masu
tsoron Allah, bayan haka,
Ku ji tsoron
Allah Madaukaki, ta hanyar neman
yardarsa da aiki da biyayyarsa da nesatan abin da ya haramta, hakika Ubangijimu
ya baku iko na aiki na kwarai ya kuma sanya wannan duniya gida ne na aiki,
lahira kuma gidan sakayya, Hakika masu aiki da ikhlasi a wannan gida da
kyautatawa sun rabauta, masu barna wadanda suka bijire sun yi hasara, kai kace
ka ajali ya zo muku, ga buri ya juya baya, kuna da abin lura daga wadanda suka
shude, kuma game da labarunsu da tarihinsu kuna da izina a ciki, na cikin kabari dayansu na fatan ya dawo duniya don ya
yi salla raka'a biyu,kuma ya nemi gafara da yawa, sai dai faufau da a amsa
masa, Allah madaukakin sarki ya ce : ( Har idan mutuwa ta je wa dayansu sai
yace : ya Ubangiji na ku mayar da ni (duniya)* Tsammani na in aikata aiki na
kwarai cikin abin da na bari, kayya lalle ne ita kalma ce shi ne mafadinta
alhali kuwa a baya gare su akwai wani shamaki har ranar da zaa tayar da su.)
Kar ka rena
kadan na daga alheri ko kadan na sharri, ya zo a hadisi : (Na hore ku rena kananan
zunubai, don suna taruwa ga mutum har su halka shi,
Ya zo a hadisi
( kar ku rena wani abu na aikin alheri,
Ya ku bayin
Allah : Lalle Allah da Mala'iku na salti ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani
ku yi salati a gare shi kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi.
Mimi Tamara Johnson kwa jin. Ninaishi Marekani, kati ya hii Nataka Kutum ili kuwaonya washauri Wote sana wa mkopo Kuwait Makin sababu kuna kashfa Kwa Kila Mahal. Nimeshambuliwa på wakopaji kadhaa mtandaoni. Nilikuwa nimepoteza Tumaini Kwa Hadi RAFIKI yangu alipokuwa akanipeleka wakopaji sana wa kuaminika aitwaye Collins Williams Loan Company Ambay alinipa mkopo usio wa Salama ya Chini 75.000 Dola tabel 24 Shida yoyote bold. Ikiwa en Haja Aina ya ya yoyote mkopo du wasiliana Naye sasa kupitia Barua pepe: hii Nitumia bigloan15@gmail.com kati ili kuwaonya Kwa Wote wanaotafuta mkopo sababu ya ya Jahannamu niliyopita katika mikono wakopaji bandia.Mimi vi Tamara Johnson Kwa Jina. Ninaishi Marekani, kati ya hii Nataka Kutum ili kuwaonya washauri Wote sana wa mkopo Kuwait Makin sababu kuna kashfa Kwa Kila Mahal. Nimeshambuliwa ikke wakopaji kadhaa mtandaoni. Nilikuwa nimepoteza Tumaini Kwa Hadi RAFIKI yangu alipokuwa akanipeleka wakopaji sana wa kuaminika aitwaye Collins Williams Loan Company Ambay alinipa mkopo usio wa Salama ya Chini 75.000 Dola tabel 24 Shida yoyote bold. Ikiwa en Haja Aina ya ya yoyote mkopo du wasiliana Naye sasa kupitia Barua pepe: hii Nitumia bigloan15@gmail.com kati ili kuwaonya Kwa Wote wanaotafuta mkopo sababu ya Jahannamu niliyopita katika wakopaji Mika Band.
ردحذفTreba li vam kredit? Ovo je registrovana, garantovana i sertifikovana kreditna kompanija, odobravamo kredite pojedincima, kompanijama, ustanovama, poslovnim organizacijama i ljudima svih vrsta širom sveta. Da li vam je potreban kredit za bilo koju svrhu? Da li ste u finansijskom problemu, da li vam trebaju finansijski asistenti, firma Fred Larry je rešenje svih vaših finansijskih problema, naši krediti su laki, jeftini i brzi. Kontaktirajte nas danas za taj kredit koji vam je potreban, možemo dogovoriti bilo koji zajam koji odgovara Vašem budžetu sa samo 2% kamate. zainteresirani podnositelji zahtjeva trebaju nas kontaktirati putem e-pošte: (petercolmanloancompany@gmail.com) ili Call / Whatsapp: +2347053278874
ردحذف