بسم الله الرحمن الرحيم
Godiya ta tabbata ga Allah; Ubangijin qasa da sama, Mai amsa
addu'a, Wanda yake faran bayi da ni'imomi, Kuma yake yaye mummuna da bala'i,
Ina yabon Ubangijina kuma ina godiya a gare shi, Ina tuba zuwa gare shi, ina
neman gafararSa, Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai
yake bashi da abokan tarayya, Ma'abucin buwaya da girma.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu
bawansa ne manzonsa ne wanda aka turo shi da shrai'a cikakkiya, mai haske.
Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da albarka ga bawanka
kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa masu
rigaye zuwa ga aiyukan biyayya ababen godiya.
Bayan haka:
Ku kiyaye dokokin Allah da taqawa, iyakar kiyayewa, saboda
duk wanda yayi riqo da taqawa to sai Allah ya haxa masa alkhairi a duniyarsa da
lahirarsa. Wanda kuma ya nisanci taqawa to sai ya tave a qarshen lamuransa, ko
da kuwa duniyarsa ta fiskance shi.
Ya ku Musulmai!!
Lallai Allah ya qaddara sabbuban alkhairori, da samun rabo a
duniya da lahira, Kuma ya qaddara sabbuban sharrukan duniya da lahira, saboda
haka; Duk wanda ya yi riqo da sabbuban alkhairi da rabauta to sai Allah ya
lamunce masa samun gyaruwan rayuwarsa ta duniya, A lahira kuma zai kasance yana
da kyakkyawan makoma, yana mai dawwama cikin aljannonin ni'imah, tare da
rabauta da samun yardar Ubangiji Mai rahama. Allah (تعالى) yana cewa:
"Ba komai ba
ne sakamakon kyautatawa face kyautatawa" [Suratur Rahman: 60].
Wanda kuma yayi aiki da sabbuban sharri, to sai ya girbe sakamakon aikinsa, a
rayuwarsa ta duniya, da kuma bayan mutuwa. Allah yana cewa:
"Wanda ya
aikata mummunan aiki za a saka masa da shi, Kuma ba zai sami wani masoyi ba,
baicin Allah, kuma ba zai sami mataimaki ba" [Suratun Nisa'i: 123].
Ku
saurara!
[Yin addu'a]
Lallai yana daga cikin sabbuban gyaruwa da kawo gyara, da rabauta, da yawaitar
samuwan alkhairori, da tunkuxe fitintinun da suke sauka, da uqubobi, da xauke
musibun da ake cikinsu, da baqin ciki: YIN ADDU'Ada ikhlasi, da
zuciya da take halarce, tare da yin naci, Saboda Ubangiji Mabuwayi da xaukaka
yana son a riqa yin addu'a, kuma yayi umurni da shi. Shi kuma addu'a yana yin
amfani akan abinda ya sauka, da wanda bai sauka ba (na musibobi), Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma Ubangijinku
ya ce: Ku roqe ni zan amsa muku, Lallai waxannan da suke kangarewa daga bauta
mini, za su shiga jahannama qasqantattu" [Ghafir: 60].
Kuma addu'a shine Bauta, kamar yadda ya zo a cikin hadisin Annu'uman xan Bashir
(رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), Ya ce:
"Addu'a
shine bauta (ibada)",
Abu-dawud ya ruwaito shi da Attirmiziy, kuma yace: Hadisi ne mai kyau
ingantacce.
Kuma
an ruwaito daga Abu-hurairah (رضي
الله عنه), yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Babu
wani abu wanda yafi matsayi a wurin Allah fiye da addu'a", Attirmiziy ya
ruwaito shi, da Ibnu-Hibbana a cikin sahihinsa, da Alhakim, kuma yace:
Isnadinsa ingantacce ne.
Kuma Addu'a abun kwaxaitarwa ne akansa a kowani lokaci, kuma ibada ne wanda Allah
ya ke bada sakayya akansa da mafi girman sakamako, Kuma addu'a yana tabbatar da
ababen nema gabaxayansu; kevantattu, da waxanda suka game, na addini, da na
duniya, a cikin wannan rayuwar da bayan mutuwa.
Kuma saboda amfanin da addu'a yake da su masu girma Allah
ta'alah ya shar'anta yinsa a cikin ibadodin da aka farlanta, a matsayin wajibi
ko mustahabbi, saboda rahamar Ubangijinmu da karramawa da yin baiwa, domin bayi
muyi aiki da wannan sababin; da Allah ya sanar da mu Shi. Kuma lallai da Allah
bai sanar da mu yin addu'a ba, to da kwakwalenmu basu shiryu izuwa gare shi ba,
Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma aka
ilmantar da ku, abinda Ku da ubanninku baku sani ba" [Suratul
An'am: 91].
Don
haka; Yabo da godiya na Allah ne, yabo mai yawa, mai daxi, mai albarka, kamar
yadda Ubangijinmu yake so, kuma kamar yadda Ubangiji ya yarda.
Kuma buqatar yin addu'a a ko-da-yaushe ta kan yi tsanani, Musamman a wannan
zamanin, Wanda fitintinu suka bayyana, kuma suka yawaita, tare da saukar
bala'oi da annoba masu halakarwa, da kuma saukar ababen baqanta rai, ga
Musulmai, da bayyanar qungiyoyin bidi'a; waxannan da suke rarrabe kan Musulmai,
kuma suke halatta zubar da katangaggen jini da kwasar dukiya ta haramaun, suke
kuma kyamar ilimi da ma'abutansa, kuma suke yin fatawa da jahilci, da kuma
vata. A lokacin da maqiyan Musulunci suke taruwa don murqushe shi, suke kuma
shisshirya makirce-makirce akan masu Imani, su kuma Musulman suke tavar da
junansu, suke rarrabewa, suke savani, a tsakaninsu. A kuma lokacin da dangogin
cutuwa suka riski kowanne daga cikin xaixaikun Musulman da aka fitar da su,
daga gidajensu, da zalunci, kuma cutuka suka shafe su, buqatunsu suka zama da
wahala, Lallai a irin waxannan halaye masu tsanani; waxanda Musulmai suke quna
da wutansu a garurrukan da fitintinu suka kunnuBuqatuwar yin addu'a tana
yawaita.
Kuma lallai haqiqa Allah yayi yabo akan waxanda suke roqonSa, suke kuma
qanqan-da kai izuwa gare shi Mabuwayi da xaukaka; IDAN har manyan lamura
ko tsanani suka sauka akansu, Allah (تعالى) yana cewa dangane da iyayenMu guda biyu (Adamu da
Hauwa'u عليهما
السلام):
"Su biyun,
suka ce: Ya Ubangijinmu! lallai ne Mu mun zalunci kayukanmu, idan har baka
gafarta mana kayi rahama a gare mu ba, zamu kasance daga cikin masu hasara" [Suratul
A'araf: 23]. Kuma Allah (تعالى) yace:
"Kuma tabbas
zamu jarrabe ku da wani abu na tsoro da yunwa da tawaya cikin dukiya da rayuka
da 'ya'yan itatuwa, Kuma ka yi bishara ga masu haquri * Waxannan da idan musiba
ta same su, sai su ce: Lallai Mu daga Allah muke, kuma lallai Mu zuwa gare shi
masu komawa ne * Waxannan akansu akwai albarku daga Ubangijinsu, da wata
rahama, Kuma waxannan sune shiryayyu" [Suratul Baqarah: 155].kuma
Allah mabuwayi da xaukaka ya faxa dangane da annabi Yunus s(عليه السلام):
"Kuma annabi
Yunus sa'ad da ya tafi yana mai fushi, sai yayi zaton cewa ba za mu quntata
masa ba, sai yayi kira a cikin duffai, cewa: babu abin bautawa face kai, tsarki
ya tabbata a gare ka, lallai Ni kasance daga azzalumai" [Suratul
Anbiya'i: 87].
Hadisi
ya zo daga Sa'ad xan Abiy-Waqqas (رضي الله عنه) yace, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Addu'ar
annabi Yunus wanda kifi ya haxiye, a lokacin da ya roqi Allah alhalin yana
cikin kifi, babu wani Mutum Musulmai da zai yi roqo da shi, face Allah ya amsa
masa addu'ah",
Ahmad ya ruwaito shi, da Attirmiziy, da Alhakim, kuma yace: Isnadinsa
ingantacce ne.
Kuma a yayin da Annabi (صلى
الله عليه وسلم) ya kirayi qabilar Saqifu zuwa ga Musulunci, sai suka qi karvar
da'awarsa, sannan suka jefe shi da duwatsu, sai ya roqi Ubangijinsa yana mai
cewa:
"Ya Allah ina koka raunin qarfina zuwa gare ka, da
qarancin dabarata, da qasqancin da nake da shi a wurin Mutane, Ya mafi rahamar
masu rahama; izuwa ga Wa; zaka jivintar da Ni; zuwa ga maqiyin da yake xaure
min fiska, ko kuma izuwa ga wani maqiyin da ka mallaka masa lamarina, Idan baka
yi fushi da ni, ba; to bani da damuwa, Saidai kuma lafiyarka ita tafi
yalwa a gare ni. Ina neman tsari da hasken fiskarka wanda ya haskaka duffai,
kuma lamarin duniya da lahira suka gyaru da shi, kada fushinka ya sauka akaina,
Komawa naka ne, har sai ka yarda, Babu dabara babu qarfi face daga wurinka".
Da yin addu'oi ne, ake fiskantar tsanani da ababen vacin rai, na abubuwan da
Mutum ba zai iya tunkuxe maka su ba; saboda Yazo daga Sauban (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Babu abinda ke tunkuxe qaddara sai addu'a, kuma babu
abinda yake qara tsawon rai sai xa'a ga iyaye da sada zumunci, Kuma lallai
mutum ana haramta masa arziqi saboda wani zunubin da ya aikata",
Ibnu-Hibbana ya rawaito shi a cikin sahihinsa, da Alhakim, kuma yace: Isnadinsa
ingantacce ne.
An
ruwaito daga Abdullahi xan Umar (رضي الله عنهما), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), yace:
"Lallai addu'a yana amfani daga abinda ya sauka, da kuma wanda
bai sauka ba, Ya ku bayin Allah; Sai ku lazimci yin addu'a",
Attirmiziy ya ruwaito shi, da Alhakim.
An
ruwaito daga Abu-Hurairata (رضي
الله عنه) yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: Lallai Allah (تعالى) yana cewa:
"Ni, Ina yadda bawana ke zatona, kuma Ni ina tare da shi
idan ya roqe ne", Bukhariy ya ruwaito shi, da Muslim.
Kuma
lallai wannan lada da falala ya kai yadda ya kai (A ce, Allah yana tare da
bawansa; idan ya roqe shi!).
Kamar yadda Allah yayi zargi ga waxanda suke barin roqon Allah ko addu'a
a lokacin da uqubobi suka sauka, ko bayyanar fitintinu; Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma haqiqa
mun kama su, da azaba, saidai basu qanqan da kai ga Ubangijinsu ba, kuma ba sa
yin tawali'u"
[Suratul Muminuna: 76]. Kuma Allah mabuwayi da xaukaka yace:
"Kuma lallai
mun aika zuwa ga al'ummai daga gabaninka, sai muka kama su da tsanani da cuta,
tsammaninsu za su qanqan da kai * To, don me lokacin da tsananinmu ya je musu
basu yi tawali'u ba, Sai zukatansu suka qaiqashe, kuma Shexan ya qawata musu
abinda suka kasance suke aikatawa" [Suratul An'am: 42-43]. Kuma
Allah (تعالى) yace:
"Kuma ba mu
aika wani annabi a cikin wata alqarya (sai suka qaryata shi) ba, face mun kama
mutanenta da azaba, da cuta, tsammaninsu za su qasqantar da kai" [Suratul
A'araf: 94].
Kuma lallai qin yin addu'a, a lokacin tsanani dogewa ne, akan zunubai, da kuma
raina lamarin kamu ko damqar Ubangiji mai tsanani, Allah (سبحانه) yana cewa:
"Lallai
damqar Ubangijinka mai tsanani ce" [Suratul Buruj: 12].
Kuma lallai shi addu'a sababi ne mai girma na sauqar alkhairori da albarkoki,
da tunkuxe sharri, ko xauke shi, daga mai yin addu'ar.
Kuma yin addu'a shine sababin da ya fi qarfi domin fita daga sharrin da ya
auku, da mummunan yanayin da ake ciki, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma da
Ayyuba a lokacin da ya kirayi Ubangijinsa lallai ne Ni, cuta ta shafe ni, kuma
kai ne mafi rahamar masu tausayi * Sai muka
amsa masa, sa'annan muka kwaranye abinda ke a tare da shi na cuta, Kuma muka
kawo masa iyalansa da kwatankwacinsu tare da su, saboda rahama daga gare mu, da
tunatarwa ga masu ibada" [Suratul Anbiya'i: 83-84]. Kuma Allah (تعالى) yace:
"Ko, Wane ne
ya ke amsawa mai buqata, idan ya roqe shi, kuma ya kwaranye mummuna" [Suratun
Naqml: 62]. Ai, Babu wani da yake aikata hakan, sai Allah (تعالى).
Kuma
Allah (سبحانه) yace:
"Ka ce Wane
ne yake tsirar da ku daga duffan tudu da ruwa, kuna roqonsa bisa ga qanqan da
kai, kuma a voye; Lallai ne idan ka tsiratar da mu daga wannan (masifa), zamu
kasance masu godiya * Ka ce: Allah ne, yake tseratar da ku daga gare ta, da
kuma dukan baqin ciki, Sa'annan sai ku kuma ku ci-gaba da yin shirka" [Suratul
An'am: 62-63].
Shi Musulmi wajibi ne akansa ya riqa addu'a da kwaxayin Allah (تعالى) ya gyara masa sha'anoninsa, gabaxaya,
yana mai xaga buqatunsa zuwa ga UbangijinSa gabaxayansu, ya riqa roqonSa kowani
abu. Kuma mafi girman abin nema shine aljannah, da kuvuta daga aukawa wuta,
Allah (تعالى) yana faxa a
cikin hadisin Qudusiy:
"Ya ku bayina! dukkaniku vatattu ne, sai wanda na shiryar
da shi; ku nemi shiryarwata; in shiryar da ku. Ya ku bayina! dukkaninku
mayunwata ne sai wanda na ciyar da shi; sai ku nemi ciyarwata; in ciyar da ku.
Ya ku bayina! kowanenku tsirara ya ke; babu tufafi sai wanda na tufatar da shi;
sai ku nemi tufatarwata, in tufatar da ku. Ya ku bayina ! lallai kuna yin laifi
dare da rana, ni kuma ina gafarta zunubai gabaxaya; sai ku nemi gafarata; in yi
muku gafara", Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Abu-zarri (رضي الله عنه). Ma'anar hadisin kuma shine: Ku roqe ni
shiriya, da ciyarwa, da tufatarwa da gafara.
Kuma
y azo a cikin hadisi cewa:
"Xayanku
ya riqa roqon UbangijinSa koda akan igiyar takalminsa ne (da ya tsinke), da
gishirin abincinsa".
Kuma dayawa, addu'a
ta kan canza abinda yake gudana a tarihi daga sharri zuwa ga alheri, ko kuma
daga abu mai kyau zuwa wanda yafi shi kyau, Allah (تعالى) yana cewa dangane da Babanmu annabi
Ibrahim (عليه
الصلاة والسلام):
"Ya
Ubangijinmu! Ka aiko a cikinsu, wani manzo, daga gare su, yana karanta musu
ayoyinka, kuma yana karantar da su wannan littafin da hikima, kuma yana
tsarkake su, lallai ne kai, kai ne Mabuwayi Mai hikima" [Suratul
Baqara: 129]. Kuma an ruwaito daga Abu-Umamah (رضي الله عنه), yace: Na ce: Ya ma'aikin Allah! Menene farkon lamarinka? Sai
yace: Ni addu'ar babana ne annabi Ibrahim, kuma busharar annabi Isah,
Sai mamata ta gani a mafarki cewa wani haske ya fita daga gare ta, wanda har ya
haskaka benayen qasar Sham", Ahmad ya ruwaito shi.
Kuma
saboda wannan addu'ar ta annabi Ibrahima; Musulmai suka kasance cikin alheri
madawwami, kai, dukkan dumiya itama wannan addu'ar ta shafe su.
Haka, addu'ar da annabi Nuhu (عليه
الصلاة والسلام) itama ta kasance alheri ga muminai masu tauhidi, sharri ga
mushirkai.
Haka addu'ar da annabi Isah (صلى
الله عليه وسلم) zai yi; shi da sahabbansa waxanda za a killace su a jikin
dutsen AXXUR, a qarshen zamani itama zata kasance nasara ce ga muminai,
sa'annan halaka ga YAJUJU da MAJUJU, waxanda suke kamar farar da za ta game dukkan
qasa (duniya), Mafi sharrin halitta, masu tsananin varna da qetare iyaka da
qirman kai, saboda Ya zo cikin hadisin Annawas xan Sam'an (رضي الله عنه) bayan annabi Isa ya kashe MASIHU
AD-DAJJAL:
"Sai
Allah (تعالى) yayi wahayi ga annabi Isah (صلى الله عليه وسلم) cewa: Lallai ni na fitar da wassu bayi, waxanda wani bashi da
ikon yaqarsu, Sai ka killace bayina a wajen dutsen Ax-xur. Sai Allah ya tayar
da Ya'ajuju da ma'ajuju alhalin suna gaggawa daga kowani tudun qasa; Sai na
farkonsu su shige ta jikin wani qaramin teku na xabariya, sai su shanye dukkan ruwan da ke cikinsa, Sai na
qarshensu su zo shigewa sai su ce: Lallai wannan, da akwai ruwa a cikinsa, To,
sai a killace annabin Allah Isah (صلى الله عليه وسلم)shi da sahabbansa;
har sai ya kasance kan Saniya yafi alheri ga xayansu, fiye da dinari xari ga
xayanku a yau, to daga nan, sai annabin Allah; Isah ya bayyanar da kwaxayinsa
shida sahabbansa (رضي الله عنهم) wa Ubangijinsu maxaukaki; ta hanyar
roqonsa, Sai Allah (تعالى) ya saukar da tsutsotsi a wuyan Ya'ajuju
da Ma'ajuju, sai su wayi gari sun mutu, kamar mutuwar rai guda xaya. Sa'annan
sai annabin Allah; Isah da sahabbansa su sauka kan qasa, saidai kuma ba za su
sami daidai da taqi xaya ba, a doron qasa face gawar Ja'ajuju da ma'ajuju da
warinsu ya cike shi; Sai annabin Allah; Isah ya bayyanar da kwaxayinsa shida
sahabbansa (رضي الله عنهم) wa Ubangijinsu maxaukaki; ta hanyar
roqonsa, Sai Allah (تعالى) ya turo da wassu tsuntsaye, waxanda suke
kama da wuyan raqumi, sai su tattare su; su kai su, su jefa, a wurin da Allah (تعالى) ya nufa", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma addu'ar da annabi (صلى
الله عليه وسلم) shugaban halitta, yayi; shi da sahabbansa, a yaqin
badar, itama ta kasance wata nasara ce ga Musulunci, har abada, kuma tavewa ce,
ga kafirci har abada; Allah (تعالى) yana cewa:
"A lokacin
da kuke neman agajin Ubangijiku sai ya amsa muku; da cewa: lallai ne Ni zan
taimaka muku da dubu daga cikin Mala'iku, a jere" [Suratul
Anfal: 9]. Sai Annabi (صلى
الله عليه وسلم) yayi ta yin addu'a, kuma ya nace, wajen yin addu'ar, har sai
da mayafinsa ya faxi, A nan ne, Abubakar (رضي الله عنه) ya rungume shi, sa'annan ya ce: Yadda kake yin magiya wa
Ubangijinka, ya isa, ya ma'aikin Allah! Kuma lallai Allah zai cika maka abinda
ya yi maka alkawari.
Kuma lallai yin addu'ar taimakon gaskiya, da ruguje varna, yana daga nasiha ga
Allah da littafinSa, da ManzonSa, da jagororin Musulmai, da kuma sauran
Mutanensu.
Kuma babu wanda zai guje wa yin addu'a, yana mai qaurace masa face wanda ya tozarta
rabonsa a duniya da lahira, sa'annan ya tozarta abinda ya wajaba akansa na
haqqin Musulunci da Musulmai. Ya zo a cikin hadisi cewa:
"Duk wanda bai himmatu da lamarin Musulmai ba to baya
cikinsu".
Kuma da a ce, za mu yi ta bibiyar fa'idodin addu'a da albarkokinsa, da
alherorinsa, da natijojinsa, daxaxa, kuma ababen mamaki, to da, ambaton hakan
yayi tsayi. Saidai abinda muka riga muka yi ishara, a baya, ya isar.
Kuma lallai addu'a yana da SHARRUXA, DA LADDUBA;
Kuma yana daga cikin sharruxan addu'a: Cin
abinci na halal, da sanya tufar halal, Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace wasahabinsa
Sa'ad xan Abiy-Waqqas (رضي
الله عنه):
"Ka
kyautata abincinka; sai a amsa maka addu'arka".
Kuma yana daga cikin sharruxansa: Riqo da Sunnah, da
kuma amsawa Allah (تعالى)
; ta
hanyar aikata abubuwan da ya yi umurni, da nisantar abubuwan da yayi hani,
Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma idan
bayina suka tambaye ka dangane da ni, ka ce: Lallai ni, a kusa nake, ina amsa
addu'ar mai addu'a idan ya roqe ni, Sai su nemi amsawata, kuma su yi Imani da
ni, tsammaninsu za su shiryu" [Suratul Baqara:186]. Kuma Allah
(تعالى) yace:
"Kuma yana
amsawa wadannan da suka yi imani, suka kuma aikata aiyukan kwarai, kuma
yana qara musu sakamako daga falalarsa" [Suratush Shurah: 26]. Mutumin
da aka zalunce shi, shi kuma ana amsa masa, idan yayi addu'a; koda kuwa kafiri
ne, ko xan bidi'a.
Kuma yana daga cikin sharruxansa: Yin ikhlasi da halarto da zuciya, da
yin naci, wa Allah, da yin gaskiya cikin neman mafaka, daga Ubangiji (تعالى), Allah ta'alah yana cewa:
"Sai ku roqi
Allah kuna masu tsarkake addini a gare shi, ko da kuwa kafirai sun qi" [Suratul
gafir: 15].
Ya
zo cikin hadisi cewa, "Allah baya karvar addu'a daga zuciya
rafkananniya mai wargi".
Kuma yana daga cikin sharruxansa: Kada ya yi, addu'a da savo, ko yanke
zumunta, kuma kada ya qetare iyaka, cikin addu'a.
Kuma yana daga cikin
sabbuban amsa addu'a: Yin yabo wa Allah (تعالى) da sunayensa mafiya kyau, da sifofinsa
maxaukaka, tare da yin salati wa annabi (صلى الله عليه وسلم); Ya zo cikin wani hadisi cewa; Lallai annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ji wani Mutum
yana cewa:
"Ya
Allah, lallai ne Ni ina roqonka , da shaidawata cewa babu abin bautawa da
gaskiya sai kai, Makaxaici, Wanda ake nufi da biyan buqata, wanda bai haifu ba,
kuma ba a haife shi ba, kuma bashi da wani wanda yake daidai da shi, Sai yace:
Lallai ne, ka roqi Allah da sunanSa da yafi girma; wanda idan aka roqe shi da
shi ya kan bayar, idan kuma aka yi addu'a da shi, ya kan amsa", Abu-dawud ya
ruwaito shi, da Attirmiziy, kuma yace: Hadisi ne mai kyau (hasan).
Da
kuma Ibnu-Majah da Ibnu-Hibbana, da Alhakim, daga hadisin Buraidah (رضي الله عنه).
An
kuma ruwaito daga Fadalah (رضي
الله عنه), yace: Wata-rana Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana zaune, sai
wani Mutum ya shigo yayi sallah, Sa'annan ya ce:
"Ya
Allah, ka gafarta mini, ka yi mini rahama, Sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace: Ka yi gaggawa ya kai mai sallah, Idan ka zo sallah; sai
ka zauna, to ka yi godiya wa Allah da abinda ya cancance shi, San'annan sai ka
yi min salati, Sa'annan sai ka roqi Allah", Ahmad ya ruwaito shi, da
Abu-dawud, da Attirmiziy, kuma yace: Hadisi ne hasan.
A
cikin wani hadisin kuma:
"Lallai
addu'a yana rataye tsakanin sama da qasa har sai ya yi salati wa Annabi (صلى الله عليه وسلم)".
Kuma yana daga cikin ladduban addu'a da sharruxan karvarsa: Kada ya yi
gaggawar amsawa, A'a yayi haquri, Ya zo a cikin hadisi cewa:
"Za a
amsa wa xayanku matuqar bai yi gaggawa ba; yace: Na roqa, na roqa, amma ba a
amsa mini ba",
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi, daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه).
Kuma lallai, dawwama kan addu'a (da yawaita yinsa), a tare da shi akwai amsawa,
Ya zo cikin hadisi cewa:
"Babu
wani Musulmi a bayan qasa, wanda zai roqi Allah da wata addu'ar face, Allah ya
bashi ita, ko kuma ya tunkuxe masa wani mummunan kwatankwacinta, matuqar bai
roqi sabo, ko yanke zumunta ba. Sai wani Mutum yace: To, lallai za mu yawaita!
Sai yace: Allah zai fi ku yawaitawa", Attirmiziy ya ruwaito shi, kuma
yace: Hadisi ne, hasan sahih, kuma Alhakim ya ruwaito shi daga riwayar
Abiy-Sa'id, sa'annan ya yi qari a cikinsa: Ko
kuma, a ijiye masa kwatankwacin addu'arsa.
Kuma ya dace, Musulmi ya yi kirdadon lokutan amsa addu'a, An ce wa Manzon Allah
(صلى الله عليه وسلم):
Wace
addu'a ce, aka fi amsawa? Sai yace: "Ta qarshe dare, da bayan
sallolin farilla",
Attirmiziy ya ruwaito shi, yace: Hadisi ne, hasan, daga hadisin Abiy-Umamah.
Kuma ya zo cikin wani hadisin cewa:
"Ubangijinmu
yana sauka zuwa ga saman duniya, a cikin xaya bisu ukun dare na qarshe; Sai ya
ce: Wa zai yi roqo sai na amsa masa, Wa zai tambaye ni sai na bashi, Wa zai
nemi gafarata sai na gafarta masa", Bukhariy ya ruwaito shi, da
Muslim daga hadisin Abu-hurairah.
Da
kuma tsakanin kiran sallah da yin iqamah, Nan ma ba a mayar da addu'a: Ya
zo cikin hadisi cewa:
"Lokacin
da bawa yafi kasancewa kusa da UbangijinSa shine a lokacin sujjada; Sai ku
yawaita addu'a",
Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Abu-hurairah.
Da kuma lokacin ganin ka'abah, da lokacin saukan ruwa, da hali na
buqatuwa, da bayan khatamar alqur'ani gabadaya, da bayan yin sadaka.
Ka yi mamakin girman
rabauta, da nasara, da samun ladan Mutumin da ya killace zuciyarsa, ga Allah (تعالى); yana roqonSa, yana fatanSa, yana kuma
dogara akanSa, yana neman taimakonSa.
Da kuma tavewa, da girman shirka ko kafircin wanda yake roqon kabari, ko yake
neman agaji daga Annabawa (عليهم
الصلاة والسلام), da waliyyai, ko yake roqonsu koma bayan Allah (تعالى), ko yake xaga buqatunsa zuwa ga wani
mala'ika makusanci, ko wani annabi mursali; saboda Annabawan Allah (عليهم الصلاة والسلام) sun zo ne, don
kiran Mutane, cewa su keve Allah (تعالى) da yin roqo a gare shi, sa'annan su kaxaita shi da bauta shi
kaxai. Su kuma waliyyai an umurce mu da mu riqa yin aiki irin nasu, sa'annan mu
so, su, kuma aka hane mu, kan roqonsu, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma lallai
masallatai na Allah ne, kada ku roqi wani tare da Allah"[suratul Jinn:
18]. Kuma Allah (تعالى) ya ce:
"Kuma ka ce:
Kawai ni, ina roqon Ubangijina ne, kuma ba zan tara kowa da shi ba" [Jinn:
20].
Kuma
wanda baya halarce, da matattu babu wani daga cikinsu da yake amsa addu'a;
saboda addu'a babu mai amsa shi idan ba Allah Mabuwayi da daukaka ba, Allah (سبحانه) yana cewa:
"Kiran
gaskiya nasa ne, Wadanda kuma suke roqon waninshi basa amsa musu da komai, face
kamar mai shumfuda tafukansa zuwa ga ruwa domin ya kai ga bakinsa, kuma shi ba
mai kaiwa gare shi ba ne, Kuma kiran kafirai (ga wanin Allah) bai zama ba, face
a cikin bata"
[Suratur Ra'ad: 14]. Kuma Allah (تعالى) yace:
"Babu wanda
ya fi bata fiye da wanda ke roqon wanin Allah, wanda ba zai amsa masa ba, har
ranar qiyama, alhalin (wadanda ake roqan) sun gafala da kiran masu kiran * Kuma
idan aka tattara mutane, za su kasance abokan gaba a gare su, kuma za su
kasance masu kafircewa ga bautan da suka yi a gare su" [Ahqaf: 5-6].
Kuma
Allah (تعالى) yace, alhalin
yana bada labarin aiyukanSa:
"Yana shigar
da dare a cikin yini, kuma yana shigar da yini cikin dare, kuma ya hore wata da
rana; kowannensu yana gudana zuwa ga ajali ambatacce. Wannan shine Allah
Ubangijinku, mulki nasa ne, kuma waxanda kuke roqa waninSa basa mallakar ko da
fatar kwallon dabino * Idan kuka roqe su, to ba za su ji kiranku ba, koda sun
ji to ba za su amsa muku ba, kuma a ranar qiyama za su kafirce wa shirkarku,
kuma babu mai baka labari, kamar wanda ya sani", [Fadir:
13-14].
Kuma lallai Allah bai yi izinin a roqi waninSa ba, duk irin kusancin da yake da
shi, Allah (تعالى) yana cewa:
"Almasihu ya
ce: Ya ku 'ya'yan Isra'ila, Ku bauta wa Allah; Ubangijina, kuma Ubangijinku;
lallai ne duk wanda ya yi shirka da Allah to, lallai Allah ya haramta masa
aljanna, kuma makomarsa itace wuta, kuma babu wassu mataimaka ga azzalumai" [Ma'idah: 72]. Kuma
me tsarki da daukaka (Allah) ya ce ''kuma baya umurninku da ku
riki mala'iku da annabawa iyayengiji . shin ze umarceku da kafirci ne bayan kun
riga kun zama masu sallamawa (musulmi)
Ya
zo cikin hadisi cewa: "Wanda ya mutu alhalin yana roqon wani koma
bayan Allah ya shiga wuta", Bukhariy ya ruwaito shi daga hadisin Abdullahi dan
Mas'ud (رضي
الله عنه).
Ya
kai Musulmi!!
Wannan shine littafin
Allah, da hadisan ManzonSa (صلى
الله عليه وسلم) suna bayyana maka cewa, lallai ADDU'A shine BAUTA, kuma lallai
Allah mabuwayi da xaukaka shine kawai ya kevanta da addu'a, ba a yinsa sai ga
Allah maxaukaki, kuma duk wanda ya haxa wani da Allah a cikin addu'a to wannan
mushirki ne mai babbar shirka.
Kuma kada wani ya yi koyi da wani cikin vata da shirka;
saboda shirka da kafirci basu auku a cikin 'ya'yan Adam ba face, da sababin
taqalidanci, da bin mutane vatattu, Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma shin
wancan, shine mafi zama alheri ga liyafa, ko kuma itaciyar zaqummi * Lallai Mu
mun sanya ta fitina ga azzalumai * Lallai ita wata bishiya ce, wadda take fita
daga asalin wutar jahima * Fudarta, kai kace kayukan shexanu ne * Lallai su
haqiqa masu ci ne daga gare ta, sa'annan masu cika cikinsu ne daga gare ta *
Sa'annan suna da wani gauraye a kanta, daga ruwan zafi * Sa'annan lallai
makomarsu izuwa ga wutar jahimu take * Lallai su, sun iske Ubanninsu suna datattu
* Sai suka kasance akan gurabansu suke ta yin gaggawa" [As-safat:
62-70].
Kuma
Allah (ta'alah) yana cewa:
"Kuma ku
roqi Ubangijinku da qanqan da kai, da kuma a boye, Lallai ne shi, baya son masu
qetare iyaka kuma kada kuyi barna a cikin kasa bayan gyaranta kuma ku kirayeshi
saboda tsoro da tsammani : lallai ne rahamar Allah makusanciya ce daga masu
kyautatawa"
[A'araf: 55].
ALLAH YAYI MINI ALBARKA, NI DA KU A CIKIN ALQUR'ANI MAI GIRMA.
HUXUBA
TA BIYU
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai rahama, Mai jin qai, Mabuwayi Mai
hikima, Ma'abucin sunaye da suka fi kyau, da sifofi maxaukaka.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi
kaxai yake bashi da abokin tarayya, Maxaukakin da Yafi xaukaka.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu
bawansa ne manzonsa ne Zavavve.
Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da albarka, ga
bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa Masu taqawa.
Bayan haka:
Ku kiyaye dokokin Allah, sai ya gyara muku aikyukanku,
sa'annan ya sanya ku daga cikin masu rabauta a yanzu, da kuma bayan komawa
izuwa ga makoma.
Ya ku Bayin Allah!
Ku kasance, masu bayyanar da kwaxayi zuwa ga Allah, masu dawwamar da yin roqo a
gare shi (da yawaitawa); saboda Duk wanda ya roqi Allah baya tavewa, wanda kuma
ya yi fatan samun Allah ba a hana shi.
Umar Allah kara yarda a gare shi yace : Lalle
ni ba na dorawa kai na damuwar amsa adua sai dai na kan damu da yin aduar, in
har an min dacen yin adua to Allah ya lamunce amsa aduar.
Kuma kowani Mutum yana da buqatun da suke
sabuntuwa, da ababen nema a kowani lokaci masu yawa; Don haka; Sai kowa ya roqi
UbangijinSa, duk abinda ya san alheri ne. kuma ya yi wa Musulmai da aka zalunta
a addini adu'a, ya kuma nemi tsarin Allah daga duk abinda ya san sharri ne.
Kuma mafi girman abin roqo shine neman samun
yardar Allah, da kuma aljannah.
Shi kuma mafi girman abinda ake neman tsari
daga gare shi, shine wuta da sabubanta.
Kuma Mutum Musulmi ya yi naciyar roqon abinda
ya dame shi, daga wajen Ubangijinsa; saboda Allah Mawadaci ne, Mai karimci,
Abun godiya, Mai yawan baiwa, Mai girma, Mai iko, Allah maxaukaki yana cewa:
"Ya ku bayina! Da, na-farkonku da na-qarshenku, da
mutanenku da aljanunku zasu tsaya a bigire xaya, sai kowanne ya roqe ni, sai in
bada kowanne xaya abinda ya roqa; to ba zai rage komai daga cikin abinda ke
wurina ba sai kamar gwargwadon abinda allura ta rage; idan aka tsoma ta a cikin
ruwan teku", Muslim ya ruwaito shi/ ya zo a hadisi :Wanda
bai roki Allah ba zai yi fushi da shi,
Kuma mustahabbi ne, Musulmi ya riqi addu'oi masu gamewa, waxanda suka zo daga
Annabi (صلى الله عليه وسلم), kamar faxinsa maxaukakin sarki:
"Ya Ubangijinmu ka bamu mai kyau a Duniya, a lahira ma mai kyau, ka
kare mu daga azabar wuta" [Baqara: 201].
Da kuma misalin
"Ya Allah, lallai ne Ni ina roqonka aljanna da abinda ya kusantar
zuwa gare ta na zance ko aiki, Kuma ina neman tsarinka daga wuta da kuma abinda
ya kusantar zuwa gare ta na zance, ko aiki".
Ya
ku bayin Allah!
"Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku
waxanda suka yi imani ku yi salati a gare shi domin amintarwa"
[Ahzab: 56].
Addu'a ….
……………….
……………….
……………….
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق