السبت، 4 مارس 2017

FALALAR MADINA DA LADUBAN MASALLACIN ANNABI NA SHEIKH SUDAIS

Hudubar Juma'a na Masallacin Annabi  4/6/1438 AH Tare da sheikh Abdurrahman Bin Abdul'Aziz Assudais
  Da sunan Allah mai rahama mai jin kai
 FALALAR   MADINA DA LADUBBAN MASALLACIN ANNABI  
Huduban farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah , muna gode maka , Ubangijina  muna neman taimakonka, muna neman gafararka muna tuba zuwa gare ka, kuma muna sake  kyautata dukkan yabo a gare ka  . To dukkan yabo ga Allah   ba yankewa ga zamanin shi*  iya adadin  abinda ya bada na ni'ima a halin godiya ya gajerta .
Ina yabo gare shi  bisa ga ni'imominsa masu yawa kuma ina gode mishi bisa falalolinsa masu yawa tsarki ya tabbbata a gare shi shi ne ma'abocin baiwa da kadartawa,  wanda ya kebanta da halittawa da zabi wanda ya fada a cikin littafinsa mafi hikima ,  kuma Ubangijinka yana halitta abin da yake so kuma yake zabi  Alqasas 68.
 Kuma na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya mabuwayi mai yawan gafara tsarki ya tabbata a gare shi shi ne Allah guda daya mai yawan rinjayi, na shaida Annabin mu Muhammad bawan Allah ne kuma Manzonsa ne  zababbe mafi alherin wanda yayi taku a kasar Daba ( Madina) gidajen ansarawa gurin hijiran sahabbai zababbu, Allah ya yi salati da aminci da albarka a gare shi da iyalansa tsarkaka, da sahabbansa masu biyayya da tabi'ai da wanda suka bisu da kyautatawa,  muddin dare da wuni na bibiyan juna.
BAYAN HAKA:
 Ya ku Musulmai: Daga mimbarin masallacin mafi alherin halittu , ina muku wasiyya da ni kai na da wasiyya mafi alheri, ku ji tsoron Allah mabuwayi da daukaka domin shi ne matattaran dukkan alheri kuma mabubbugan dukkan albarkatu, kuma shi ne aminci daga dukkan musibu, kuma kariya ne daga dukkan wasu bala'I (ya ku wadanda kuka yi imani ku ji tsoron Allah hakikanin tsoronsa  kada ku mutu face kuna musulmai)
Tsoron Allah shi ne tushen al'amari to ka sanya *** tsoron sa tattali don gyara al'amarinka
Kuma ka gaggauta himmatuwa zuwa ga mishi da'a ***domin fa baka sani ba yaushe ne za a tafiyar da rayuwarka
Bayin Allah , lallai mai lura a yanayi na wannan duniya   zai samu mafi girman dalili na kadaituwan Allah, da kuma mafi girman shaida bisa ga rububiyyarsa da cikan hikimarsa da iliminsa da kudurarsa kasantuan shi mabuwayi da daukaka  yana zaban abinda ya so na daga mutane da wurare  yakan kuma kebance abinda yaso na daga abubuwa da zamani sabo da wasu manufofi masu girma  da wasu manyan hadafi  wanda maslahohi na bayi ke dore akansu   bashi da abokin tarayya tsarki ya tabbata a gare shi yana zaba kamar irin zabinsa , kuma yana gudanarwa kamar irin gudanarwarsa    ( kuma Ubangijinka yana halitta abin da yake so kuma yake zabi  Alqasas 68).
Lallai na daga cikin mafi bayyana na wannan zabin, zabin sa da yayi tsarki ya tabbata a gare shi na daibataddaiba Madina garin Annabi don ta kasance garin hijira na Manzonsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi , ita take biye wa Makkah mafi alherin bigire  kuma mafi daukakan guri   da doron kasa  mai biye mata wurin alfarma da girmamawa,  da daukakawa da mutuntawa gari mafi kima ,  da sanyin idon garuruwa da adon kasashe  da hasken birane  lallai ita ce gari na masoyi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  matsira na itaciya mai yabanya daular farko na musulunci,   a cikin  ta ne ka'idodin addini ya cika  a kasanta ne mai tsarki a ka dabbaka hukunce-hukunce na musulunci da sha'anoninsa  , muna karantawa a tarihinta  tarihin al'umma, wacce aka haifa tare da bullowan alfijir rananta ta haska  tare da wanzuwansa tarihinsa ya haska , sai ga shi nan tattare da shi akwai tarihi na daula wanda ke cike da dukkan ma'anoni da siffofi masu kyau na imani  da akida , da raya kasa, da ilimi, da ci gaba, lallai ita ne Almadinatul munauwara bata gushe ba da alheru da albarkatu da suke kewaye da ita Daiba masoyiya , kuma daba mai hankali . 
Allah ya sanya ta mafarin sakon Musulunci   madauwami  kuma wurin saukan wahayinsa  kuma mashinfidi na da'awar Annabinsa , kuma  wani kango ne na daga kangoyen shiriya , kuma dutse ne madaukaki , kifiyoyin makiya  na faduwa a gabansa , ita ce manara na musulunci kuma makwancin imani, kuma wurin renon akida , kuma matattaran  ci gaba , kuma daga inda jagoranci ya tashi  da jan ragama  na duniyan musulunci  bisa  haske  na manhajin tsakatsakiya da daidaito nesa daga  fandarewa da ketare iyaka, da kuma ta'addanci da bangaranci da tsoratarwa ,  da kuma tabbatar da bin littafin Allah da sunna kamar yanda Allah madaukakin sarki ya ce : (  ku yi riko da igiyan Allah gaba daya kar ku rarraba ).
  Daga nan ne ci gaba na musulunci ya taso  ya busa alheri , da aminci da rahama  da adalci da rangwami da salama ,  (  Ba mu turo ka ba sai rahama ga talikai)  bisa ga tushen tauhidi da tsarkake addini a gare shi da tabbatar da akida ingantacciya  da lafiyayyen kuduri , da manhaja mikakkiya  da kuma  samun daukaka na alamomi na addini ,  aka daga tuta na sunna da lazimtar manhaja na magabata na korai wanda  wannan kasa mai albarka ta tafi a kai .
  A Daiba akwai zane na Annabi da kuma  Ma'ahad ***
 mai haskakawa hakika zanen kan goge asake shimfida shi  amma ayoyin ba sa goguwa daga gida mai alhurma***
 a gare ta akwai mimbari   na shiriya wanda ya kasance yakan haura  da ayoyi bayyanannu da sauran manya-manyan wurar***da guri na shi da yake salla da sujjada
Akwai dakna wanda yakasance  a tsakiyar su yake sauka *** wani haske daga Allah da ake haskakawa da shi kuma a kunna
Wasu manyan alamomi bisa tsawon zamani ba a shafe alamomin su ba  *** lalacewa ya zo musu amma an asake sabunta alamomin na su
Ya ku jama'ar musulmi :
 Lallai itane Madina da ake cewa Daibatuddaiba garin hijira  kasar sunna  wanda ya ziyarce ta  don neman kusanci da lada  da kuma kauna na wadannan guraren  Allah zai saka mishi ya kuma bashi lada, ase ba ita ce masulalan imani ba  garin hijiran shugaban dan  adnan  amincin Allah da salati su tabbata a a gare shi mafi cika da kamala Buhari da Muslim sun fitar a hadisin (Abu Huraira Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce lallai imani na sulalewa zuwa ga Madina kamar yanda macijiya ke sulalewa zuwa raminta  )
Wannan gaba gare kiu Daiba ne da gidajenta *** hakika ansa albarka wa gidajen a cikin talikai 
Wannan Madina hakika  an dora mata kambu samanta   wanda aka sanya mata shiriya
Ita ce masulala na imani a zamanin da yake koka tsagewan gini na ababan mutunci
Ya ku 'yan uwa na na imani: na daga cikin falalanta Allah ya dada  kiwata ku , lallai Allah wanda sunan shi ya daukaka yabon  shi ya girmama  hakika  ya kara imani akanta inada ya ce: ( da wadanda suka zaunar da gidajen su (ga musuiunci)  kuma (suka zabi) imani , a gabanin zuwansu  suna son wanda yayi hijira suwa gare su  kuma basa tunanin wata bukata a cikin kirazansu daga abinda aka baiwa muhajirina , kuma suna fifita wadansu akan kawunansu kuma  koda suna da wata lalura. Wanda ya sabawa rowar ransa  , to wadannan sune masu babban rabo ) Alhashr aya na 9
Imamu Malik Allah ya mishi rahama yana cewa: a cikin  siyakin ambaton sa na falalan madina  akan watanta na daga sassan duniya( lallai Madina ambata  masauki na imani da hijira  , amma watanta na daga alkaryu an bude su ne da takuba) .
Kuma na daga cikin falalarsa lallai Allah ya  umarci Annabin shi da hijira zuwa gare shi an karbo daga Abi Musa   ya rawaito daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :  (Ya gaci cikin bacci y a ce lallai ni zanyi hijira daga garin makka  zuwa wata kasa  wanda ke da itatuwan dabino , sai tunani na ya tafi kan  Yamama ko Hajar ase ita ce garin Madina Yasriba ) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
 'Yan uawa Musulmai:
 Ya masoya shugaban halittu- Allah ya kara haske fiskokin ku ,  ku saurara na daga cikin mafi daukakan falaloli na madina :- an gina masallaci na Annabi a cikinta , wanda an assasashi ne akan tsoron Allah,  Allah madaukakin sarki ya ce : (Kada ka tsaya a cikinsa har abada. Lalle ne Masallaci wanda aka yi harsashinsa akan takawa tun farkon yini , shi ne mafi cancantar ka tsaya a cikinsa. A cikinsa akwai wadansu maza suna son su tsarkaka. Kuma Allah yana son masu neman tsarkakuwa) Tauba :108
Muslim ya fitar a sahihinsa na daga hadisin Abu sa'id Alkhudri yace : ( Na shiga wa manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a halin yana dakin wasu shashi na daga matayensa : sai na ce ya manzon Allah wani masallaci ne cikin masallatayya biyu  aka yi harsashinsa  a kan takawa? ya ce : sai ya dauki cikin tafi na tsakuwoyi  ya buga su ga kasa, sannan yace : wannan masallacin naku ne," ga masallacin Madina .
Na daga cikin falala na wannan masallacin mai albarka shi ne daya daga cikin masllatayya uku da ba ya halatta a nika gari sai zuwa gare su. An karbo da Abu Sa'id Alkudri Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : na ji manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : Kada ku nika gari sai zuwa ga masallatayya guda uku: Masallacin Makka da wannan Masallacin nawa da Masallacin Aksa) Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Na daga cikin falalarsa kuma ana ribanya ladan sallah a cikinsa na farilla ne ko na nafila, cikin zance mafi inganci na malamai, An karbo daga Abu Huraira Allah kara yarda agare shi ya ce  :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : Sallah a Masallaci na ya fi sallah dubu a wani masallaci sai dai Masallacin Makkah) Bukhari da muslim ne suka rawaito
Kuma masallaci na ya kasance kai bai ma gushe ba abin buri ****
Zukatan da suka bata hanya  na rarrafawa zuwa gare shi.
Akwai miliyoyi da ke kwana bisa kauna ta su wayi gari ****
Cikin tunani na da haukan kauna ta idan sun yi tafiya.
  A cikin sa akwai bigire wanda Dausayi ne daga cikin dausayi ne Aljanna, An karbo daga Abu Huraira Allah kara yarda a gare shi, yace : Tsakanin gida na da minbari na dausayi ne daga cikin dausayin Aljanna. Kuma minbari na na kan tabki na,) Bukhari da muslim ne ya rawaito.  Kuma a riwayar Ahmad : Minbari na wannan na  kan tabki daga cikin tabkunan Aljanna, a riwayar Nasa'i, kuma lalle kafafun Minbari na matabbata ne a Aljanna.
 Ya jama'ar musulmi  hakika Allah ya sanya wannan gari mai daukaka  harami amintacce ba a zubar da jini a cikinta ba a daukan makami  don yaki, Muslim ya fitar a cikin Sahih nasa daga hadisin sahlu dan Hanif Allah ya kara yarda a gare shi yace : Manzon Allah ya sunkuyo da hanun shi zuwa ga Madina sai ya ce :(Ita  Harami ne amintacce)  
Madina na da Alhurma tun daga tsakanin duwatsunta biyu da konannun duwatsunta biyu da Manyan duwatsunta da hanyoyi tsakanin duwatsun. Daga Aliyu Allah kara yarda a gare shi yace : ( Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:  Madina harami ne tun daga dutsen Air zuwa saur) Bukhari da Muslim ne suka rawaito
Ba a koran abin farautar ta, baa kama tsuntsunta ko abin farautar, ba a yanke kayarta, ba a tsinke itaciyarta, ba a cire ciyayinta, ba a cire danyen itacenta ba a cire wata bishiya deaga ita sai dai idan mutum zai yi ciyayi wa rakumin ba a tsintan tsintuwa a cikinta sai ga mai shelantawa  ba wan da zai yi makida ga mutanen garin  Madina ko ya nufe su da mummunan abu ko  sharri face  ya narke kamar yadda gishiri ke narke wa a ruwa Manzon shiriya tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake cewa: ( duk wanda ya tsorata da mutanen Madina bisa zalunci   mabuwa yi da daukaka Allah zai tsorata shi kuma tsinuwan Allah ya tabbata a gare shi da Mala'iku da mutane baki daya , Allah ba zai karbi daga gare shi ba ranar alkiyama , aiki na farilla ko na nafila ).  Imamu Ahmad ne ya rawaito shi
 YA KU MUSULMAI:
Wanda ya bayyana a Madina wata bidi'a  ya fari wata barna ko ya bada  mafaka  ga mabarnaci to ya kai kan shi ga halaka mai tsanani, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa : (  Madina harami ne   tsakanin  dutsen air zuwa dutsen saur duk wanda  ya farar da  abu a cikinta  na fitina ko ya bada mafaka wa mabarnaci to  to tsinuwan Allah ya tabbata a gare shi da Mala
Ikunsa da Mutane baki daya ba za a karba daga gare shi ba  aikin farilla ko na nafila)  Buhari da Muslim ne suka rawaito .
 YA KU BAYIN ALLAH:
Na daga cikin falalan Madina  ita ce masoyiyar masoyi  masoyiyar abin kauna  tsira  da amincicin Allah su tabbata a gare shi  wanda ya kasace yana cewa : ( Ya Allah ka sanya son garin Madina zuwa gare mu kamar yanda kamar yanda muke son garin Makka ko ma sama da haka  ) Buhari da Muslim ne suka rawaito .
 Ita ce gidan shi wurin hijiran shi a nan ne ya kafa mihrabinsa kuma ya  daga mimbarinsa  a ciki ne kuma makoncinsa yake kuma a nan ne za atada shi .
 Wurin hijiranMusdafa mai shiryarwa kuma makwancinsa*** wanda yake abin komawa ga jarumai idan tsanani ya tsananta
Abin komawa ga zakuna idan yaki yayi tsamari***
Gari ne na masoyi gari ne abin kauna ga mazauna daiba wurin masauki  zamewa a cikinta tare da imani daukaka ne kuma da yalwa zamewa dan garin tare da tsoron Allah daukaka ne kuma da kaiwa kololuwa
Ya jin dadin wanda suka zauna a cikinta***ya walwalan mazauna cikinta *** Ya rabautan wanda ya jibinci zama acikinta har mutuwa ta zo mishi a kasanta
 An karbo daga Abdullahi dan Umar Allah ya kara mishi yarda shi da mahaifinshi  ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( duk mutumin da zai iya ya mutu a garin Madina to ya aikata haka  domin ni zan yi ceto ga duk wanda ya mutu acikinta) Imamu Ahmad ya fito da shi.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan ya dawo daga tafiya yakan dubi kangonnin Madina  da kuma manya-manyan itatuwanta   da kuma darajojinta  sai ya kafe abun hawarsa sai ya kada dabbarsa sai ya ingizata  ya sata ta kara sauri don kaunan wannan gari na  Madina idan ya fiskantota sa ya ce : ( wannan garin Daba ne sai ya ce wannan kuma Uhudu ne dutse ne da yana son mu , muna son shi  ).
Na daga cikin falalansa cewa tsoro na Dajjal ba zai shigo mata ba ko firgici ba zai zo gare ta ba  kafansa shi Dujjal ba zai taka zuwa gare ta ba Mala'iku suna kofofinta  suna bakin garin da kofofinta da hanyoyinta da mashiganta suna gadinta suna bada kariya a gare ta an karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce  :( A bakin kofofin Madina akwai Mala'iku wanda annoba ba zai shige ta ba ko kuma dajjal ) Buhari da Muslim ne suka rawaito.
Ya ku Musulmai:
 Zama a cikinta akwai albarka wanda zai sa a dauki watanta ba komai ba a wurin yalwa na rayuwa da rafahiyya ,  an karbo daga Abu Huraira  Allah ya kara yarda a gare shi ya ce  Manzon Allah tsira da Amincin  Allah su tabbata a gare shi  ya ce :(   Wani lokaci zai zowa mutane mutum zai kira dan baffansa da makusancin shi , taho zuwa ga yalwa , taho zuwa ga yalwa , kuma Madina ne tafi alheri a gare su da sun kasance sun sani . ) Muslim ne ya rawaito shi
  Ya ku mazauna cikin Daiba    ya ishe ku *** daga tafiya zuwa neman daukaka kusantan Ahmadu
To duk mai neman wanin ta  zuwa wani gari ko da ta daukaka*** game da wani a bin duniya to bazai  samu shiryuwa ba.
 'yan uwa na imani:
  Madina na da albarka a sa'in sa da mudun ta da kilonta  da dabinon ta  da kadan nata da mai yawanta  Annabi ya masa addu'a ya ce: (  Ya Allah ka sanya a madina  ribi biyu na abinda kasanya a Makka na albarka) Buhari da Muslim ne suka rawaito
YA JAMA'AR MUSULMI :
Wannan ita ce Daba  garin shugaban halittu : Falalolinta basa kirguwa, albarkatunta basa kididdiguwa  , ya zauna a tsawon tarihi a shudewan karnoni  gini ne na kololuwa ta zamana wuri ne katangange na imani da 'yan uwantaka   da kuma makoma ne na akida kuma masdari ne na da'awa  .
 Allah mai girma!  a Daiba akwai kamsasan  abubuwa na tunawa , na dindindin  akwai kuma kamsasan abubuwa na gwarzanta na daukaka.
YA KU MUSULMAI:
Lallai bada kulawa ga Madina madaukakiya  ya doru a kanmu , da kuma bada kulawa ga girman alfarmarta ga dukkan alheri da ta kunsan  kuma hanyar yada darajar ta abu ne mai kawo ceto,  falalanta gami da   tattaro wurarenta na daukaka  ta dace da wuraren da aka raya su da wahayi da saukarwa  Jibrilu da Mika'ilu sun yi kai koma a cikinta    mala'iku sun haura da Mala'ika Jibrilu  dan a girmama farfajiyarta a shaki kamshin iskarta  a ribaci lokutan cikinta a kuma yawaita ayuka na kwarai a cikinta .
Ya gidan mafi alherin Manzanni da wanda ke tare da shi*** an shiryar da mutane  kuma an kebe shi da ayoyi
Ina da tsananin kauna a gare ki  da matukar  so ***  da kuma  shauki mai kunna  garwashi.
   Ya jama'a makusanta abin misali ,  ya dace ga duk wanda ya nufi kusantar Madina ya zamana yana da saukin hali  da tausasawa mai kiyaye alhurmar wurin nata  tare da la'akari da mazaunanta , ya yi tarayya da su a majalisain su ba a kalacen su ba  ya yi cunkoso tare da su a lokutan su ba a abincin su ba , ya kuma ribaci halayensu ba arzikinsu ba  ya tsinkaya daga biyayyansu ba daga alkamarsu ba , kuma ya kwadaici kaunarsu ba kwayarsu ba .
Ya tawagan maziyarta zababbu :- ga ku kuna gabatowa zuwa garin Musdafa Al-mukhta'; na bada fasan mahaifina da mahaifiya ta a gare shi tsira da   amincin Allah su tabbata a gafre shi – ku tuna wajabcin bin sunnarsa  da taku kan tafarkin sa, da sha a koshi daga tarihin sa Allah madaukakin sarki ya ce : (  in kun kasance kuna son Allah to ku bini Allah zai so ku kuma ya gafarta muku zunuban ku) Ali Imran 31
  Abinda da'ansa da kaunar sa ke hukuntawa  shi ne neman sanin laduban ziyarar masallacin sa da laduban yin sallama a gare shi da abokan shi biyu- yardan Allah ya tabbata a gare su – da kuma laduban zama a garin sa  Madina na Annabi abin haskakawa  , bata gushe ba tana  albarkatu     na kewaye da ita a katanganta  da kuma  kadaita Annabi wurin  bin shi, a halayen sa irin na Muhammad  , da kuma dabi'unsa na zababbe da kuma rashin shan gabansa ko da ga sauti a wurinsa.
 Ya ku wadanda suka yi imani kada  ku daukaka sautunttukanku bisa sautin Annabi , sama  kuma kada ku  bayyana sauti gare  shi  a magana kamar bayyanawar sashinku ga sashi , domin kada ayyukan ku su baci alhali kuwa ku baku sani ba ).
AL'UMAR MUSULMI:  Lallai wajibi ne a gare mu gaba daya da mukula da laduba game da wannan gari na Madina mai tsarki sai dai-Allah abin neman taimako!- Shin na daga ladabi bawa ya aikata acikinta abinda zai sabawa akida ingantacce   da sunna mikakkiya , ko kuma ya kirkiri wata bidi'a ko wani abu na sabawa?! 
 Ku ji tsoron Allah Ubangijinku-ya ku musulmai- ku kyautata ladabi tare da garin shugaban halittu  ku lazamci dukkan laduba na Musulunci a masallacin mafi alherin halittu, lallai wajibi ne a gare mu gaba daya da mu yabi Allah mu gode mi shi bisa abinda ya bamu  na ni'ima a wannan bigire mai albarka , kuma mu kula da ladabi a cikinta da zaman lafiya da bin tsari a gidaddajenta   da kuma  tsakanin maziyartanta  kuma maziyartanta  su kimtsa don  ziyara , kada su shagaltu da barin ibada ta hanyar amfani da wayan tafi da gidanka ko daukan hotuna ko makamantan su su nisanci cunkokso da cutar da 'yan uwansu, kuma mace idan ta halarci wannan masallacin mai daraja ya da ce ta siffantu da hijabi da kame kai kuma rashin cakudaidainiya da maza .
muna rokon Allah da ya azurta mu da ladabtuwa da   laduba na musulunci kuma ya azurtamu da binsunnan shugaban halittu da baiwansa da karamcin sa  kuma ya azurta Musulmai da ladabi na kusanci da kyautata zama  a kusa da shugaban halittu mafi girman salati da  mafi tsarkin aminci a gare shi   kuma bisa  ga iyalansa da sahabbansa masu karamci .
 Ina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan abin jefewa
 (Lallai abin koyi mai kyau ya kasance gare ku daga manzon Allah ga wanda ya kasance yana fatan rahamar Allah da ranar lahira  kuma ya ambaci Allah da yawa )
Allah ya sa mini albarka ni da ku  a wahayi biyu kuma ya amfane ni da ku da shiryarwan  shugaban haliyttu   (aljanu da mutane)  ina fadi na wannan kuma ina neman gafaran Allah da ni da ku da kuma dukkan Musulmai , ku nemi gafaransa domin shi mnai yawan gafara ne mai jin kai.
HUDUBA TA BIYU:
Dukkan yabo sun tabbata ga Allah mai wadatarwa da ni'ima da baiwa na shaida ba bu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya  ya korara mana daga ni'imomin shi masu yawa   cikin aminci da imani, kuma ya yalwata a gare mu na daga karamcin ludufinsa,  na baiwa da kyautata  na shaida cewa Annabinmu Muhammadu bawan Allah ne kuma Manzon sa ne Allah ya yi dadin tsirada aminci da albarka a gare shi da ilansa da sahabbansa  , da tabi'ai dawanda  suka bisu da kyautatawa zuwa ranar sakayya
 BAYAN HAKA:
Ku ji tsoron Allah- bayin Allah- ku gode mishi bisa abinda yayi na baiwa a gare ku game da wadannan wurare masu  tsarki da bigire madaukaka.
 'Yan uwa na musulunci ku saurara : na daga cikin falalan Allah madaukakin sarki   wannan gari na Musdafa ya rabauta da karin kulawa   daga jagorori na wannan gari mai albarka  tunda a ka kafa har zuwa yau . Mafi hasken hujjoji dake furta  haka da dalilai masu nuna  hakan    :  wannan fadadawa na gini na tarihi mai bankaye  mai jan hankali wanda ake kidanya shi cikin abin alfahari ga duk wani Musulmi kuma haske ne mai haskakawa a fiskan tarihi ta yanda zai bada daman  tattaro adadin mafi girma na masu nufo wannan masallaci na Annabi  da kuma masu ziyarar sa daga sassan duniya  don hidima ga  masallacin Musdafa amincin Allah ya tabbata a gare shi  da neman hutu ga maziyartan shi  da masu nufo shi da basu dama don yin ibadansu da biyayyan su cikin tsari na hidima na musamman ,  acikin wani yanayi wanda  ke kunshe da sauki da natsuwa ,  hakika a maganan gaskiya ta dace a nada mata kambu na  hedkwata  na har abada  na wurin shakatawa da kuma wayewa na musulunci  .
 Ya 'yar uwar makka a sama ki yi haske***  ki yi alfahari cikin dimuwa kina ma adontawa dai haskakawa   Allah ya sakawa jagororin wannan gari mai albarka- garin tauhidi da sunnu- mafi alherin sakayya ya sakawa kadimul haramaini da alheri bisa ga wannan kokari madaidaici wurin hidimawa  harami biyu masu daraja  da masu fiskantosu, da kuma abinda ya gabatar kuma yake gabatarwa ga musulunci da musulmai Allah ya sanya shi a mizanin ayyukan shi na kwarai.
Wannan kenan ku yi salati da aminci-Allah ya muku rahama- bisa ga mai shiryarwa mai albishir kuma fitila mai haskakawa  kamar yanda mai tausayi gwani ya umarce ku da   sai ya ce : ( Lallai Allah da Mala'ikunsa suna salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce )
Ya ku masu fatan ceto mafi alheri *** daga Ahmadu ku yi salati a gare shi da aminci
Ma'aboci daukaka yayi salati a gare shi da aminci muddin mai talbiya na talbiya ko   mai ihrami na tahalluli .
 ya Allah ka yi dadin tsira da aminci ga wannan rahama da ka bamu shi, da kuma ni' ima da ka bamu kyautansa  : Annabinmu Muhammad dan Abdullahi , ya Allah ka yarda da kalifofinsa masu shiryarwa Abubakar da Umar da Usman da Ali da sauran sahabbai da tabi'ai da wanda ya bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakayya     kuma ka game rahamarka da mu tare da su  ya mafi tausayin masu tausayi.
 Ya Allah ka daukaka musulunci da Musulmai, ya Allah ka daukaka musulunci da musulmai ,  ka bada aminci ga masu umura da ziyara ka sanya wannan gari cikin aminci da kwanciyar  hankali cikin kyauta da yalwa  da sauran garuruwan musulmai  ya Allah  ka bamu aminci  a garuruwan mu kuma ka gyara kuma ka datar kuma ka kiyaye jagororinmu da shuwagabanninmu, ka karfafi shugaban mu  da gaskiya kuma jagoran al'amuran mu , ya Allah ka datar da shi da mataimakan shi biyu da 'yanuwansa zuwa ga abinda akwai daukaka na musulunci da gyaruwa  na musulmai .
Allah ka datar da dukkan jagororin musulmai don su yi hukunci da shari'anka da bin littafinka da sunnan Annabin ka  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Ya Allah ka sanya su rahama bisa ga bayin ka muminai.
 Ya Allah ka gyara halayen musulmai a ko ina ,  Ya Allah ka gyara halayen musulmai a ko ina , Allah ka kare jinannakin su, Allah ka kare jinannakin su ya Ubangijin talikai ya Allah ka bamu kyakkyawa anan duniya da kuma kyakkyawa a lahira ka kre mu daga azabar wuta .
( Ya Ubangiji ka karba daga gare mu domin kai mai ji ne masani  kuma ka karbi tubanmu  don kai mai  karban tuba ne kuma mai jiin kai . karshen adu ar mu shi ne dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin talikai  tsira da amincin Allah su tabbata ga  shugabanmu Muhammadu da iyalansa da sahabbansa baki daya.       





   
     

    

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق