HUDUBAR JUMA'A NA
MASALLACIN ANNABI 18/6/1438 AH, NA SHEIK
HUSAINI BIN ABDUL'AZIZ AL- ASSHAIKH
A irin wannan zamani da
ke cike da fitintinu ga musibu sun yawaita, makiya na mulkan al'umar musulmai wanda hakan
ke haifar da radadi da bakinciki mai yawa kuma daban- daban, to lalle bukatuwa
na tsananta zuwa ga tunatar da musulmai game da mafita na dahir daga dukkan
kowane bakinciki, da sabuba na hakika da zaa kubuta daga dukkan bacin rai da
wahalhalu.
Ya ku Musulmai!
Wannan rayuwa mai kare wa cike take da musibu
da gajiyarwa (Wahala) Allah ya ce: (Hakika Mun halitta mutum cikin wahala)
Lalle tushe mai girma
na fita daga wadannan musibu a wannan rayuwa ta duniya da kuma kubuta daga
damuwowinta yana kasance wa ne cikin tabbatar da tsoron Allah a boye da kuma
bayyane, da komawa gare shi da dawowa
zuwa ga kusancinsa dare da wuni , da bada lokaci na gabadaya don girmarsa cikin
sauki da tsanani, Allah madaukakin sarki
ya ce ( Duk wanda ya ji tsoron Allah
zai sanya masa mafita.Kuma ya azurta shi daga inda ba ya zato, kuma wanda ya
dogara ga Allah to Allah ne Mai ishinsa.) Allah Mai girma da daukaka ya ce
:(To wanda ya ji tsoron Allah zai sanya masa wani sauki daga al'amarinsa).
Na daga cikin naui na
rusunawa da kankan da kai da mika wuya ga Allah mai girma da daukaka akwai abin
da Annabi ya shiryar da wasu sahabbai kuma ya musu wasiya da shi ciki da waje
fadi da aiki da hali da dabia hakika ya shiryar da Abu Musa Allah ya yarda da shi
da fadinsa a gare shi: ( kace la
haula wala kuwwata illa billahi domin ita taska ce daga cikin taskokin
aljannah)Bukhari da Muslim ne suka
rawaito
Abu zarri Allah ya kara
yarda a gare shi yace:(masoyina tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
ya min wasiya kan na yawaita fadin la haula wala kuwwata illah billahi
Lallai ita din nan
wasiya ce madaukakiya mai girma da babbar
ambato, kalmomin ta dan kadanne amma ma'anoninta
na da girma, zikiri wanda harshe ke furta shi zuciya ya sakankance da shi lallai shaanin shine babu mai taimako game da
tabbatar da maslahohin duniya da lahira face Allah mabuwayi da daukaka to duk
wanda Allah ya taimaka shine abin taimako wanda kuma ya tabar shine tababbe.
Zikiri ne wanda bawa zai sakankance da shi cewa bashi da dabara shi ko
wanin shi na ya fita daga wani halin zuwa wani halin haka nan bai da karfi bisa
ga wani sha'ani daga cikin sha'anunnukansa ko tabbatar da manufa daga cikin
manufofinsa face da tsoron ALLah mai karfi madaukaki mai girma.
Zikiri ne da bawa zai bayyana hakikanin talaucinsa da kankan dakai da
kai ga ubangijinsa kuma yana cikin larura da bukatuwa zuwa ga mahaliccinsa
mabuwayi mai rinjayi.
Zikiri ne da yake fita daga harshen bawa zuciyan shi na kadaita tilo mai
girman shaani daga gunshi ake nemo nasara da galaba da yayewa da mafita ALLah mai
tsarki da daukaka yace :(Allah zai sanya sauki abayan tsanani )zikiri
dashi ake samun rabauta da nasara da mafita da kubuta Allah madaukakin sarki
yace : (yaku wadanda sukayi imani idan kun hadu da wata kungiyar yaki to ku
tabbata kuma ku ambaci ALLah da yawa ko kuna cin nasara )
Lallai zikiri ne da ya dace da ko wani musulmi da ya furta shi da
harshen magana da aiki, tun da sirri ne na tauhidi, wanda ke hukunta rusuna wa
mahalicci,da tare wa gare shi da kubuta daga dabara ko karfi sai daga gare shi,
Mabuwayi da daukaka.
Ibnul kayyim Allah ya yi mishi rahama yace ;( Wannan kalmar tana da
tasiri na ban mamaki wurin tafiyar da abubuwa masu tsanani, da dauke wahala da
shiga ga masu mulki da ake tsoro, da dauke manyan wahalhalu).
Ya ku bayin Allah:
ku
saurara ga wannan kissa mai girma wanda hujja ce mai haske bisa ga karfin
tauhidi wanda ke warware bakin ciki duk yanda ya girmama, kuma ke tafiyar da
wahalhalu duk yanda ta tsananta .
Wata kissa ce da da yawa daga cikin malaman
tafsiri sun ambata ta, ta zo ta fiskoki daban –dabam, mafi karancin darajanta a
ce hassan , ita ce Auf dan Malik al-ashja'I yana da da wanda ake cewa Salim
mushirikai sun kama shi cikin fursunonin yaki sai ya zo wurin Annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi, sai ya ce da shi ya Manzon Allah : lallai
abokan gaba sun kama da na ( cikin kaman mun yaki) ya kuma koka mishi talauci ,
sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: ( Ba
abin da ya wuni a wurin iyalan Muhammadu sai mudu to ka ji tsoron Allah ka yi hakuri ka yawaita
fadin lahaula wala kuwwata illa billahi0)
A wata
ruwaya kuma ya zo cewa ya umarce shi
ne kuma ya umarci uwan dan da haka, sai
mutumin ya akaita hakan , yayin da yake cikin gidan shi, sai ga dan shi ya zo
mishi a halin makiya din sun gafala daga gare shi sai yasamo rakuma ya zo da su
zuwa ga baban shi, da ma baban matalauci ne baban sai ya zo gun Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi sai ya ba shi labarin Auf da labarin rakuma
, sai Manzon Allah ya ce da shi: ( ka
aikata abin da ka so da su ka yi abinda ka saba yi da rakumar ka da su ).
Fadin
Allah:( ( Duk
wanda ya ji tsoron Allah zai sanya masa
mafita.Kuma ya azurta shi daga inda ba ya zato, kuma wanda ya dogara ga Allah
to Allah ne Mai ishinsa.) Allah Mai girma da
daukaka ya ce :(To wanda ya ji tsoron Allah zai sanya masa wani sauki daga
al'amarinsa). Daga nanne sahabbai suka tafi akan wannan wasiyyar din cikin
fadi kuma da aikatawa.
Ibnu
Abiddunya ya rawaito cewa Abu Ubaida da aka katange shi sai Umar ya rubuta zuwa gare shi: duk abin da ya
sauka zuwa ga mutum na tsanani Allah zai
yaye bayan haka, kuma hakika tsanani
daya ba zai ci galaba akan sauki biyu ba , kuma yana ce mishi : ( ku yi
hakuri kuma ku yi dauriya kuma ku yi
zaman dako, kuma ku yi takawa ko za ku
ci nasara).
Lallai
ta'alluki da Allah da dogaro gare shi da
ambaton sa a harshe , na daga cikin abin
da yake tafiyar da bakin ciki duk yanda ya tsananta makomanta zai zama yayewa
ne da mafita .
Fudail ya ce : wallahi da mutum zai yanke
tsammani daga halittu ka ji ba ka bukatar komai daga gare su , to da majibincin
ya baka du abin da kaake so.
Na daga cikin sabuba wanda yake yaye bakin
ciki ya tafiyar da bacin rai shi ne dan Adam a duk lokacin da yayewa ya yi jinkiri har ma ya yanke tsammani
daga gare shi bayan ya yawaita rokon sa da kankan da kai zuwa gare shi kuma bai
ga wani alama na amsa aduwar ba a gare shi, to ya wajaba ya koma ya zargi kan
shi ya sake sabon tuba ya yi tuba na gaskiya ya dukufa zuwa ga Allah yana mai tsarkake
niya yana mai rusunawa majibinci kuma ya
yi ikirari da cewa yana cikin wadanda
suka cancanci jarabawa ya sauka a gare su kuma ba ya cikin wadanda suke ahlin amsar
adu'a sai dai yana fatar rahamar Ubangijin sa
kuma yana neman afuwar sa, to
anan ne fa amsar adu'arsa za ta zo da yayewar bakin cikin shi sabo da Allah
madaukaki yana tare da duk wadanda zukatan su suka rusuna zuwa gare shi don shi kamar yadda
Malaman magabata suka tabbatar.
Ya ku Musulmai!
Ku kiyaye irin wannan zikiri mai girma a
kowani lokaci da yanayi,don alherin sa nau'uka ne daban daban , falalolinsa na
da yawa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ba
wani mutum a doron kasa da zai ce : La'ilaha illalah Wallahu Akbar wa
subhanallah wala haula wala kuwwata illa billa, face an kankare masa
kusakuran shi, ko da sun fi yawan tarukucen saman teku ne.) Ahmad ya rawaito,
Tirmizi ya ce Hasan ne Hakim kuma ya inganta shi kuma zahabi ya mar muwafaka.
An karbo daga Ubada dan samit Allah ya yarda
da da shi ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
ya ce :(Wanda ya tashi cikin dare sai yace : La'ilaha illallahu Wahdahu la
sharika lahu lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa ala kulli shai'in kadir,
Alhamdu lillahi wa subhanallahi wa lailaha illallahu wallahu Akbar wala haula
wala kuwwata illa billah, sai yace ya Allah ka gafarta mini, ko ya yi adua
zaa amsa masa, kuma in ya yi alwala ya
yi sallah za a karbi sallar sa) Buhari ne ya rawaito.
Lalle adua ne na alheri ga bawa kuma kariya
ne da katange wa ne ga maslahohinsa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce: (wanda ya ce- idan ya fita daga gidan shi -
Bismillah na dogara gare shi ba dabara ko karfi sai gare shi, za a ce da shi
:An isanmaka an baka kariya kuma shaidan zai yi nesa da shi).Abu Dauda da Tirmizi
ne suka rawaito.
Sabo da wannan zikiri ne da ke hukunta mika
wuya ga Allah da maida al'amari a gare shi, da yarda da rusuna wa gare
shi,tsarki ya tabbata a gare shi, kuma ba mai maida al'amarinsa, kuma bawa bai
mallaki komai ba na al'amarinsa,ragamar al'amura na hanun Allah madaukaki,
al'amuran bayi na jawuwa ne bisa hukuncinsa da kaddararsa, ba mai maida
al'amarinsa ko bin kadun hukuncinsa.
To kai musulmi ka kasance mai natsuwar zuciya mai kwanciyan hankali mai
sakankance wa da yaye wan bakinciki da samun mafita, duk abin da ke duniya na
karkashin iko ne na Allah.
Duk abin da ke wannan duniya ko yaya karfinsa
ya kai, ko tsananin ya kai to hakika tana karkashin karfin Allah ne da
umarninsa, da hukuncinsa da kaddararsa, to duk wani mai karfi mai rauni ne a
gun Allah mai girma da daukaka,ya kai bawan Allah ka shagaltar da kanka da
sauran ayyukan da'a da nau'uka na alheri, ka lazimci ambatonsa da nau'uka na
zikiri daban daban a yanayi na sauki da cuta ko tsanani da yelwa. Na daga cikin
abin da ya inganta daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi cewa:(Duk wanda yake son Allah ya amsa mishi adu'a yayin tsanani da
bakin ciki to ya yawaita adu'a lokacin yalwa ).
Aikata
aiki na alheri mai yawa da falala mai
girma, duniya ba za ta yi dadi ba sai da ambaton Allah , lahira kuma ba za ta
yi dadi ba sai da afuwar sa, aljanna kuma ba za ta yi dadi ba sai da ganinsa, ka kasance mai yawan ambaton lahaula wala
kuwwata illa billahi don tana taimakawa wajen dauke abubuwa masu nauyi kuma
tana tunkude abubuwa na ban tsoro da tsanani,
da ita ake samun daukaka a dukkan yanayi Allah ne wanda ake neman taimako a gare shi ,
kuma a gare shi ake dogaro, babu dabara ko karfi sai ga Allah mai girma .
HUDUBA
NA BIYU :
Ya
ku Musulmai
mumini
mai kadaita Allah mai kiyaye dokokin Allah , mai lazimtar biyayyar
sa da kuma biyayyar Manzonsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Allah
na tare da shi da kiyayewar sa na
musamman Allah madaukakin sarki ya ce :( Allah yana tare da wadanda suka yi takawa da kuma wadanda suke su masu kyautatawa ne ).
Wanda Allah ya kasance tare da shi to lallai
yana tare da bangaren da ba a yin galaba akansu, kuma da mai kiyayewanda ba
ya yin bacci da mai shiryarwan da ba ya bacewa , kamar yanda katada ya ce: ( lallai ita mai taimakawa ne tana hukunta samun
nasara da karfafa da kiyayewa da taimako da
fita daga zaure na bakin ciki da wahalhalu masu tsanani.
Duk
wanda ya kiyaye Allah ya kuma kiyaye hakkokin sa zai same shi gaba gare shi a duk halin da yake ciki wanda ya nemi sanin Allah a lokacin yalwa to
Allah zai kawo mi shi dauki a yayin tsanani,
sai ya tsiratar da shi a yayin tsanani ya kubutar da shi daga musibu, wanda ya yi mu'amala da Allah da takawa da biyayya , cikin yardan sa to Allah zai masa mu'amala
da tausasa wa da taimaka wa a yayin fadawarsa cikin tsanani,
ya zo a Hadisil kudusi : (Bawa
na ba zai gushe ba yana kusanta na da
nafilfilu har na so shi idan na so shi
sai na kasance jin sa da ya ke ji da shi, da kuma ganin sa da yake gani da shi da
hanunsa da yake damka da shi , da kafarsa
da yake tafiya da ita, kuma idan ya roke ni zan ba shi , kuma idan ya nemi
tsari na zan bashi) Buhari ne ya rawaito.
Sannan ku sani mafi tsarkin abin da rayuwarmu
za ta mike da shi shagaltuwa da salati
da aminci ga Annabi mai girma, ya
Allah ka yi dadin tsira da aminci da
albarka ga bawanka kuma manzon ka
Annabinmu Muhammad , ya Allah ka yarda
da Al-kulafa'ur rashidun
Abubakar daUmar da Usman da Aliyu ya Allah
ka gyara halayenmu da halayen musulmai, ya
Allah ka yaye bakin ciki ka gusar da
bacin rai , ya Allah ka tsiratar da bayin ka musulmai daga dukkan wata jarabawa
da fitina , ya Allah ka yi maganin makiya musulmai domin su ba za su gagare ka
ba ya mai girma , ya Allah ka kiyaye 'yan uwan mu musulmai a ko ina ya
Allah ka kasan ce mai taimakon su da ba su nasara ya
mabuwayi ya mai karfi, ya Allah
ka datar da kadimul haramaini
ash-sharifaini cikin abin da ka ke
so kuma ka yarda da shi ya Allah ka taimaki addini da shi ka daukaka kalmar
musulmai da shi, ya Allah ka gafartawa
musulmai maza da musulmai mata rayayyu daga cikin su da matattu ya Allah ka
bamu kyakkyawa anan duniya da kyakkyawa a lahira kuma ka kare mu daga azabar wuta .
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق