السبت، 4 مارس 2017

HAKKOKIN MA'AURATA NA SHEIKH BUDAIR

HUDUBAR JUMA'A A MASALLACIN ANNABI  13/05/1438AH, NA SHAIKH SALAH BIN MUHAMMAD AL-BUDAIR.
HUDUBAR FARKO:
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, wanda falalolinsa sun game a wurin yalwa, ni'imominsa kuma sun kasu iri iri a rabe ko a tare, Na shaida ba abin bauta wa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, wanda ya ce :Duk wanda ya kusanc ni da kwatankwacin taki to zan kusance shi da zira'I, na shaida Annabinmu  kuma shugabanmu Muhammad  bawansa ne kuma Manzonsa ne, falalarsa  na da yawa tamkar girgije,kimarsa ya fi karan hanci,kyawawan halayensa ya fi cikakken wata  haske, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da iyalansa da sahabbansa da suke tsinkaya daga haskensa, da kuma bin sawunsa, salati na har abada mudin sama na haskakuwa da wata kasa na kawatuwa da ruwa.
Bayan haka , Ya ku Musulmai:
Ku ji tsoron Allah  don shine abu mafi daraja da zaka samu, biyayya gare shi ke kai wa kololuwa. (Ya ku wadanda suka bada gaskiya ku ji tsoron Allah hakkin tsoronsa kar ku mutu face kuna musulmai) Al-Imran 102
Ya ku musulmai :
Hakkoki tsakanin ma'aurata biyu ya ta'allaka ne da Kulla aure, wanda kuma ke lazimta kyakkyawar muamala  da juna, kada  daya ya jinkirta bawa daya  hakkin shi, ko ya ki  bada abin da ke kan shi. Kyautata muamalarsa ga abokin zamansa da tausaya masa da juriya bisa ga cutarwarsa sabo da fadin Allah (su matayen suna da hakki akan maza irin wanda mazan suke da shi akansu, da abin sani.)
Ita kyakkyawar mu'amala da kyakkyawan zama ta fi kawo sanyin ido, da kwanciyan hankali da daddadan rayuwa, Allah madaukakin sarki ya ce :- ( ku yi mu'amala da su da kyakkyawa)  ma'ana ku yi cakudedeniya da abota da su, da bishara da kuma sakin fiska , da bada hakkoki da aka farlanta, kamar na daga sadaki da ciyarwa da raba kwana, da barin cutar da ita da kakkausar magana , da bijire mata,  da karkata zuwa ga watanta,  da rashin hada mata fiska, da turmuke mata ba tare da wani laifi ba , sa'annan Allah na ladabtar da bayinsa da fadin sa (  sa'annan kuma idan kun ki su , to, akwai tsammanin ku ki wani abu, alhali kuwa  Allah ya sanya wani alheri a cikinsa mai yawa)  a cikin ayan akwai kwadaitarwa bisa rike su da kyautata zamantakewa da su, ko da mazajen sun tsani wani abu daga cikin halayen su, domin rai ya ki abu ba ya nuni da kore alheri ga wannan abu, ta iya yuwuwa  abinda rai ya ki ya zama shi ya fi amfani a addini, kuma ya fi zamewa abin godiya a karshe , sau da yawa abin ki kan komawa abin yabo, kuma abin yabo kan koma wa abin zargi, Hakika  miji kan tsani mata  sabo da wata sifa daga cikin sifofinta, amma kuma a rike ta din akwai wani alheri da yawa da bai sani ba,   kuma ba zai gane hakan ba, Abdullahi dan Abbas  Allah ya yarda da shi da mahaifin shi ya ce: "Ta iya yiwuwa Allah  zai azurta shi da Da daga gare ta , sai Allah ya sanya alheri mai yawa acikinsa."
Ya ku musulmai:
Lallai mutum yana da wahala ya samu wanda ya ke kauna  wanda bai da wani abu da ya ki tare da shi  ,  to yayi hakuri da abin  da ya ki sabo da abin da ya ke so,  yana da wahala ka samu mutane biyu  suna mu'amala ko wannensu ya yarda da dukkan dabi'un junansu, ba wasu mutane biyu da za su yi mu'amala  da junan su fa ce daya na kawaici ga dan uwansa, An karbo daga Abu huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:-  ( Kada mumini ya tsani mumina, idan ya ki wani hali na ta to zai so wani hali nata ) Muslim ne ya rawaito .
Wato kada  mutum ya ki matar sa ki na gaba daya wanda zai sanya shi ya rabu da ita ya sake ta ya warware kullin aure, to idan ya tsani wani hali nata mara kyau to kuwa zai samu wani hali nata abin yarda.
To  ya ku mazaje :
  ku riki matayenku kar ku yi gaggawan kosawa ko fada, kar ku yi gaggawan rabuwa   kada ku yi gaggawa zuwa ga shika , kar ku kambama abu wurin nuna tsana da kiyayya  sau da yawa rauni na hankali  yakan yi galaba a kan mutum,  fushi ya rinjaye shi  sai ya yi aiki na wauta da shirme  ya yi gaggawa  ya yi shika sannan daga baya kuma ya dawo yana nadama a halin kuma wato komai  ya tsere mishi  ya wuyata  ta koma  gare shi.
Ya ke mata mumina:
 kar ki zama cikin masu ci don tarawa, kuma ki zama kina yawaita zargi, mai yawan hayaniya da saurin fushi, wacce bata bin umarnin mijinta , kuma in ya yi rantsuwa bata biye mishi  , ki kyautatawa mijinki , ki kasance kusa da kaunarsa, mai taimaka masa yayin bukatarsa  mai amsa kiransa,  mai sauka zuwa ga bukatarsa  mai ambaton  falalarsa da   kyautatawarsa, kar ki zama mai munana mishi mu'amala  , kar ki yi musu da shi yayin fushin sa da fusatan shi,  kar ki tsawwala mishi  yayin da ya cije ko ya harzuka .
 Mu'awiya Allah ya kara mishi yarda ya ce da Akil dan Abu talib : " A cikin mata wacce tafi soyuwa a gareka ? sai ya ce :- mai biyewa  abin da mu ke so, sai yace " To waccece kuma ka fi ki acikinsu ?sai ya ce :" wacce tafi nesa da abin da kake so ", sai Mu'awiya ya ce :- wannan suka  na duniya kenan, sai ya ce:-Da  ma'auni na  adalci .
 An karbo daga abu Uzaina Assadafi    Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:- (Mafi alherin matanku sune,  masu tsananin kauna masu  yawan haihuwa , mai aikta  (abin da ka ke so)  mai share ma hawaye, muddin suka ji tsoron Allah , mafi sharrin matayen ku kuma sune masu bayyana tsiraici , masu alfahari sune munafukai, ba wanda zai shiga aljanna a cikin su, face kamar farin hankaka.)  Baihaki ne ya fito da shi, Farin hankaka  wato mai farin fiffike da kafafuwa: yana nufin karancin masu shiga aljanna a cikinsu, don samun wannan sifa na da wahala a cikin hankaki.
 An karbo daga Husain dan  Mihsan daga wata gogon  shi cewa ta shiga wurin Manzon Allah sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata  agare shi ,  sai ya biya mata bukatar tata , sai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce mata ( ko ke  kina  da miji ? sai  ta  ce e,  sai ya ce   yaya kike a gun shi? sai ta ce bana gajartawa ( a hakkinsa) sai abinda ya gagareni,  sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:- to,  ki duba matsayinki a gunshi domin shi ne aljannan ki kuma wutanki)  . Nasa'I ne ya rawaito shi
Idan rayuwa ta kasance ana rayata cike  da  kyawawan halaye ba kiyayya ba gaba, to ya haramta akan mace ta nemi shika , ko kuma ta nemi kul'i, a daya daga cikin zantuka mafi inganci a maganganun malamai,
An karbo daga saubana Allah ya kara mishi yarda ya ce:- Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi  ya ce  ( Dukkan matan da ta tambayi mijinta saki ba tare da wani laifi ba to, kamshin aljanna ya haramta a gare ta ) Abu Dauda da Tirmizi ne suka  rawaito.
An karbo daga Ukubata dan Amir Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :-( Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:-  lallai mataye wadanda suke neman fansa,  da masu neman  warware auren su sune munafukai ) Dabarani ne ya rawaito shi    Ibnu kudama ya ce :- wannan yana nuni cewa haramun ne  yin khul'I ba tare da bukata ba sabo da akwai cutarwa ga ita da kuma mijin nata ,  da kuma  gusar da maslahohin aure ba tare da bukata ba,  sabo da haka ya haramta.
Mustahabbi ne  a sulhunta  tsakanin ma'aurata  biyu wadanda suke rikici da junansu
An karbo daga Abdullahi dan Abbas Allah ya kara yarda a gare su shi da mahaifinsa  cewa mijin  barira ya kasance bawa ana ce da shi  Mugisu, kai  ka ce ina kallo zuwa gare shi yana  shawagi a bayanta yana kuka  hawaye na zuba  a gemun sa,  sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce ga Abbas :-  (  Ya Abbas baka mamaki irin kaunar da mugisu yake yi wa barira da kuma irin kin da barira take yiwa shi Mugisu?  sai ya ce da ita da kin koma mishi, sai ta ce ya Manzon Allah umarni ne ka ke min?  sai ya ce: a'a  sai dai kawai ina nema mishi alfarma ne, sai ta ce bani da bukata  zuwa gare shi  ).Buhari ne ya fito da shi.       
Ibnu Hajar –Allah ya rahimce shi - yace : " wannan Yana nuni cewa idan mace ta ki miji bai kasance wa ga waliyinta da ya tilasta mata kan zama da shi. Idan ta so shi kuma bai kasance wa ga waliyinta da ya raba su,
 Allah ya amfanar da mu da Alkur'ani da sunna da abin da ke cikin su na daga ayoyi da shiriya bayyanannu da wazi da hikima.
Ina neman gafaran Allah ku nemi gafararsar sa, Ubangiji na Makusanci ne Mai amsawa.
 HUDUBA TA BIYU
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai shiryar da wanda ya nemi shiriyarsa, Mai bada kariya ga wanda ya nemi kariyarsa, Mai isarwa ga wanda ya kirdadi yardarsa, na shaida ba abin bauta wa da gaskiya sai Allah ba wanda ya cancanci a bauta wa da gaskiya koma bayan shi, Kuma na shaida Annabinmu   kuma shugabanmu  Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne, Allah ya yi dadin tsira a gare shi da iyalansa da sahabbansa da wanda ya bi sunnarsa  ya nemi shiriya da shiryarwarsa.
Bayan haka Ya ku Musulmai !
Allah ya sanya shika da warware igiyar da aka kulla tsakanin ma'aurata biyu a hanun miji, sai dai  ya haramta ya munana amfani da hakkin nasa cikin sakin da rikon sa wata hanya don ribatar ita matar da firgita ta, ya sanya shi kamar wata bulala ce a fiskar ta don ya bautar da ita da tsorata ta, da walakanta ta, Allah madaukakin sarki ya ce : ( To ku rike su da kyautata wa ko ku sake su da kyautata wa.) An karbo daga ASSUDI  kan fadinsa  (ko a sake su da kyautata wa) " Da ya bata cikakken hakkinta kada ya cutar da ita, ko ya zage ta, "
Wanda ya katange matarsa bai sake ba bai kuma barta ta yi aure ba idan iddarta ya kare, ya cutar da ita da duka, da kuntata mata, ko ya hana ta hakkokinta na daga ciyarwa da kason kwana, da makamancinsu don ta fanshi kanta daga gare shi, sai ta yi, to khulin ya baci kuma zaa maida mata abin da ta bada don fansan.  
 Allah madaukaki ya ce: ( Kuma kada ku hana su aure domin ku tafi da sashen  abin  da kuka basu ).
Idan ta zo da alfahasha sai ya hana ta aure don ta fanshi kanta daga gare shi sai ta yi hakan to khul'in ya inganta. Sabo da fadin Allah Madaukaki: (kuma kada ku hana su aure domin ku tafi da sashin abin da ku ka ba su, face idan suka zo da wata alfahasha bayyananniya.)
Ba ya dace wa rike wacce ba ta kamun kai, sabo da tawaya ne ga mijin a addinin shi da dabiunsa da bata sunansa da zubar da mutuncinsa, bai da amincin kada ta bata mishi shimfidinsa da jingina mishi wani da da ba nashi ba, kuma mace mai sakaci da hakkokin Allah na wajibi kamar sallah da makamancinta, wacce ba ta jin nasiha  Mustahabbi ne a sake ta.
Ya ku Musulmai :
Daga cikin mazaje akwai wanda  ya sanya furta shika da yawaita shi abin ambato a bakinsa kuma abin sabon shi da al'adan shi,da abu mafi soyuwa a gare shi a abu mai kima da mara kima da babba da karami da mai girma da abin da bai taka kara ya karya ba.
Na daga cikin al'adu mara kyau akwai  rantsuwar shika
kamar yace : In kiyi magana da wane to mata ta ta saku,ko saku ya tabbata a gare ni idan na ci abincin wane. Ko shika ya tabbata  a gare ni muddin kika yi  tafiya da wane, ko shika ta tabbata a gare ni muddin mata ta ta shiga gidan wane, ko yace wa bako: Shika ta tabbata a gare ni muddin baka ci abinci a gu na ba, wannan dare , ko kuma in gobe baka ci abincin dare a guna ba, amma ba shikan yake nufi ba, ko rabuwa ba, sai dai ya yi hakan ne kamar rantsuwa, don yana nufin kwadaitarwa ko hanawa,ko tilastawa.
Wadannan lafuza ne haramtattu da ayyuka ne na laifi, da walakanta rayuwan zamantakewa da rena hakkokin mace da yara da wasa da shika  da hukunce – hukuncenta.
Ya wajaba ga miji ya kiyaye harshensa daga yawaita furucin shika, da tsoratarwa da ita da jirwaye da kamar ruwa game da  aukar da ita.
Ibnul Arabi yace a cikin Ahkamul Kur'an : (Na daga cikin rikan ayoyin Allah da izgilanci abin da aka rawaito daga Abdullahi dan Abbas kan cewa an tambaye shi game da mutumin da yace da matarsa : Ke sakakkiya ce sau dari, sai yace : Ukun ya isan maka a gare ta, sauran casa'in da bakwai ka riki ayoyin Allah da su bisa izgili ).

Ku ji tsoron Allah ya ku Musulmai kada ku riki ayoyin Allah abin izgili kar ku ketare iyakokin Allah madaukaki,(Duk wanda ke ketare dokokin Allah to ya zalunci kansa) ,( kuma duk wanda ke katare dokokin Allah to wannan yana cikin azzalumai.)
Ku yi salati da sallama ga Ahmad Alhadi mai ceton talikai gaba daya to duk wanda yayi salati guda agare shi Allah zai mishi salati goma.
Ya Allah ka yi salati da aminci ga bawanka kuma manzon ka Muhammad da kuma dukkan Iyalai da sahabbai ka yarda da mu tare da su da baiwanka da karamcinka ya Mai karamci Ya Mai yawan kyauta.
Ya Allah ka daukaka musulunci da musulmai,ka kaskantar da shirka da mushrikai,ka ruguza makiya addini, ka sanya wannan gari cikin aminci da natsuwa, da wadata da yalwa da sauran kasashen musulmai.
Ya Allah ka datar da jagoranmu shugabanmu cikin abin da ka ke so kuma ka yarda da shi, ka riki makwarkwadan shi zuwa ga biyayya da takawa, ka datar da dukkan jagororin musulmai cikin yin hukunci  da shariarka, da bin sunnar Annabinka Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Ya Allah ka sanya arzikinmu cikin yelwa, kar ka sa wani ya mana dariyan keta, kar ka bawa wani azzalumi karfi akanmu.
Ya Allah ka warkar da marasa lafiyanmu, ka bada waraka ga wanda aka jarabta a cikinmu, ka jikan matattunmu, ka kwance kamammunmu, ka taimake mu a kan wanda ya yi gaba da mu, ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka dayyaba mu don haduwa da kai, ya Allah ka dayyaba mu don haduwa da kai, ka azurta mu da yarda da hukuncinka,ka sa mu wadatu da kyautarka, ka sa mu wadatu da halal naka akan haram naka.mu wadatu da falalarka akan waninka.
Ya mai girman afuwa, ya mai girman afuwa, ya mai yalwan gafara ya mai yalwan gafara, ya makusancin  rahama, ka gafarta mana baki daya, ka gafarta mana baki daya, ka sa mu walwala da takawarka, ka sanya mu ji tsoronka kamar muna ganinka.
Ya Allah ka bamu ruwa, ya Allah ka bamu ruwa, ya Allah ka bamu ruwa, ya Allah ka saukar mana da  ruwa kar ka sanya mu cikin masu yanke kauna.ya Allah ka sanya aduar mu karbabbiya ce, kiran mu daukakakkiya ce.
Karshen aduarmu  shi ne dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai.  


ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق