HUDUBAR JUMA'A A
MASALLACIN ANNABI 13/05/1438AH, NA
SHAIKH SALAH BIN MUHAMMAD AL-BUDAIR.
HUDUBAR FARKO:
Ya ku Musulmai:
Hakkoki tsakanin
ma'aurata biyu ya ta'allaka ne da Kulla aure, wanda kuma ke lazimta kyakkyawar
muamala da juna, kada ya jinkirta bashi hakkin shi ko ya ki bada abin da ke kan shi. Kyautata muamalarsa
ga abokin zamansa da tausaya masa da juriya bisa ga cutarwarsa sabo da fadin
Allah (su matayen suna da hakki akan maza irin wanda mazan suke da shi
akansu, da abin sani.)
Ita kyakkyawar mu'amala
da kyakkyawan zama ya fi kawo sanyin ido, da kwanciyan hankali da daddadan
rayuwa, Allah madaukakin sarki ya ce :- ( ku yi mu'amala da su da kyakkyawa)
ma'ana ku yi cakudedeniya da abota
da su, da bishara da kuma sakin fiska , da bada hakkoki da aka farlanta, kamar
na daga sadaki da ciyarwa da raba kwana, da barin cutar da ita da kakkausar
magana , da bijire mata, da karkata zuwa
ga watanta, da rashin hada mata fiska,
da turmuke mata ba tare da wani laifi ba , sa'annan Allah na ladabtar da bayinsa
da fadin sa ( sa'annan kuma idan kun
ki su , to, akwai tsammanin ku ki wani abu, alhali kuwa Allah ya sanya wani alheri a cikinsa mai
yawa) a cikin ayan kwai kwadaitarwa
bisa rike su da kyautata zamantakewa da su, ko da mijin ya tsani wani abu daga
cikin halayen su, domin rai ya ki abu ba ya nuni da kore alheri da wannan abu,
ta iya yuwuwa abinda rai taki ya zama
shi ya fi maslaha a addini, kuma ya fi zamewa abun godiya a karshe , so da yawa
abin ki kan komawa abin yabo, kuma abin yabo kan koma wa abin zargi, miji kan tsani mata sabo da wata sifa daga cikin sifofinta, amma
kuma a rike ta din akwai wani alheri da yawa da bai sani ba, kuma ba zai gane hakan ba, Abdullahi dan
Abbas Allah ya yarda da shi da mahaifin
shi ya ce: ta iya yiwuwa Allah zai azurta
shi da Da daga gare ta , sai Allah ya sanya alheri mai yawa acikinsa .
Ya ku musulmai:
Lallai mutum yana da
wahala ya samu wanda ya ke kauna wanda
bai da wani abu da ya ki tare da shi ,
to yayi hakuri da abin da ya ki sabo da abin da ya ke so, yana da wahala ka samu mutane biyu suna mu'amala ko wannensu ya yarda da dukkan
dabi'un junansu, ba wasu mutane biyu da za su yi mu'amala da junan su fa ce daya na kawaici dan uwansa
an karbo daga Abu huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:- ( Kada mumini ya tsani mumina, idan yaki
wani hali na ta idan ya ki wani hali na ta to zai so wani hali nata Muslim ne
ya rawaito) .
Wato kada mutum ya ki matar sa ki na gaba daya wanda
zai sanya shi ya rabu da ita ya sake ta ya warware kullin aure, to idan ya
tsani wani hali nata mara kyau to kuwa zai samu wani hali nata abin yarda.
To ya ku mazaje
ku riki matayenku kar ku yi gaggawan kosawa da sa'insa kar ku yi
gaggawan rabuwa kada ku yi gaggawa zuwa
ga cika , kar ku kambama abu wurin nuna tsana da kiyayya so dewa mutum rauni na hankali yaka yi galaba a kanshi fushi ya rinjaye shi sai ya yi aiki na wauta ya yi gaggawa ya yi cika sannan daga baya kuma ya dawo yana
nadama a halin kuma wato kome ya tsere mishi
ya wuyata a gare shi, ta koma
gare ta daga cikin wadanda suka saki matan su
sannan rayin kuma tabi ta shiga damuwa akwai Qais Dan zarih in da yayi
waka yana mai nuna hasara cewa:-
Wayyo zuciyata da ta
saki ginina £ Rabuwa da abin ginina
kamar wani yaudara ne
Masu kai komo a
tsakani su suka kewaye ni su suka ruda ni £ kaito da mutanen da za su yiwa masu
shiga tsakani biyayya £ ga shi na wayi gari cikin zargin zuciya ta ga wani al'amarin da
ba ni da kuma yanda zan yi ba yanda na iya £
Kamar mutumin
da abu ya boyu a gare shi yana cizon
yatsa £ kamar mutumin da ya yi faduwa
yayi asara yana ciza yaza £ sa annan kuma sai bayan ya riga ya saida abinne sai ya gane ase faduwa
yayi.
Ya ke mata mumina , kar
ki zama cikin masu ci don tarawa, kuma ki zama kina yawaita zargi, mai yawan
hayaniya da saurin fushi, wacce bata bin umarnin mijinta , kuma in ya yi
rantsuwa bata biye mishi , ki kyautatawa
mijinki , ki kasance kusa da kaunarsa, mai taimaka masa yayin bukatarsa mai amsa kiransa, mai sauka zuwa ga bukatarsa mai tuna falalarsa da kyautatawansa, kar ki zama mai munana mishi
mu'amala , kar ki yi musu da shi yayin
fushin shi da fusatan shi, kar ki
tsauwala mishi yayin da ya cije ko ya
harzuka , Mu'awiya Allah ya kara mishi yarda ya ce da Sa'asa'atu dan sauhan
cikin mata wacce tafi soyuwa a gareka ? sai ya ce :- mai biyewa abinda kake so, waccece kuma ka fi ki
acikinsu ? wacce tafi nesa da abinda kake so , sai Mu'awiya ya ce :- wannan cin
gyara na duniya kenan, sai Sa'a'sa'atu
ya ce:-Da ma'auni na adalci .
An karbo daga abu Uzaina Assadafi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi ya ce:- ( masu tsananin
kauna masu yawan haihuwa , mai aikta (abinda ka ke so) , muddin suka ji tsoron
Allah , mafi sharrin matayen ku kuma sune masu bayyana tsiraici , masu alfahari
sune munafukai, ba wanda zai shiga aljanna a cikin su, face kamar bakin
hankaka. Nasa'I ne ya fito da shi
An karbo daga Abdullahi Dan Mihsan daga wata gogon shi cewa ta shiga wurin Manzon Allah sai
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata
agare shi sai ya tashi don wata
bukata , sai ya biya mata bukatar tata ,
sai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce mata ko ke kina
da miji ? sai ta ce e, sai ya ce
yaya kike da shi sai ta ce bana gajartawa ( a hakkinsa) sai abinda ya
gagareni sai Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:- to, ki duba matsayinki a gunshi domin shi ne
aljannan ki kuma wutanki) . Nasa'I
ne ya rawaito shi
Idan rayuwa ta kasance
ana rayatacike da kyawawan halaye ba kiyayya ba gaba, to ya
haramta akan mace ta nemi cika , ko kuma ta nemi kul'i a daya daga cikin
zantuttuka mafi inganci a magan ganun malamai an karbo daga saubana Allah ya
kara mishi yarda ya ce:- Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a
gareshi ya ce ( Dukkan matan da ta tambayi mijinta saki ba
tare da wani laifi ba to, kamshin aljanna ya haramta a gare ta ) Ahmad ne
ya rawaito.
An karbo daga Ukubata
dan Amir Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :-( Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:- lallai mataye wadanda suke wofantattu , masu
yin khil'I masu warware auren su sune muna fukai ) Dabarani ne ya
rawaito shi Ibnu kudama ya ce :-
wannan yana nuni cewa haramunne yin
khul'I ba tare da bukata ba sabo da akwai cutarwa ga ita da kuma mijin nata
, da kuma gusar da maslahohin aure ba tare da bukata
ba , sabo da haka aka haramta.
Mustahabbi ne a sulhu tsakanin ma'aurata biyu wanda suke rikici da junansu an karbo
daga Abdullahi dan Abbas Allah ya kara yarda a gare su shi da mahaifinshi cewa mijin
barira ya kasance bawa ana ce da shi
Mugithu kai kai ka ce ina kallo
zuwa gare shi ina dubi yanda yake shawagi a bayanta yana kuka hawaye na zuba a gemun sa
sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce ga Abbas :- ( Ya
Abbas baka mamaki irin kaunar da mugithu yake yiwa barira da kuma irin kin da
barira take yiwa shi Mugith sai ya ce da ita da kin koma mishi sai ta ce ya
Manzon Allah umarni ne ka ke min sai ya
ce a'a sai dai kawai ina nema mishi
shawara sai ta ce bani da bukata zuwa
gare shi ).Buhari ne ya fito da shi.
…
Yana nuni cewa idan
mace ta ki miji bai kasancewa ga waliyinta da ya tilasta mata kan zama da shi.
Idan ta so shi kuma bai kasance wa ga waliyinta da ya raba su, Allah ya amfanar
da mu da Alkur'ani da sunna da abin da ke cikin su na daga ayoyi da shiriya
bayyanannu da wazi da hikima .
Ina neman gafaran Allah
ku nemi gafararsa shi Ubangiji na mai gafara ne Mai kauna.
HUDUBA TA BIYU
Ya ku Musulmai ! Allah
ya sanya shika da warware igiyar da aka kulla tsakanin ma'aurata biyu a hanun
miji, sai dai ya haramta ya munana
amfani da hakkin nasa cikin sakin da rikon sa wata hanya don ribatar ita matar
da firgita ta, ya sanya shi kamar wata bulala ce a fiskar ta don ya bautar da
ita da tsorata ta, da walakanta ta, Allah madaukakin sarki ya ce : ( To
ku rike su da kyautata wa ko ku sake su da kyautata wa.) An karbo daga
ASSUDI kan fadinsa (ko a sake su da kyautata wa) Da ya bata
cikakken hakkinta kada ya cutar da ita, ko ya zage ta, wanda ya katange matarsa
bai sake ba bai kuma barta ta yi aure ba idan iddarta ya kare, ya cutar da ita
da duka, da kuntata mata, ko ya hana ta hakkokinta na daga ciyarwa da kason
kwana, da makamancinsau don ta fanshi kanta daga gare ta sai ta yi to khulin ya
baci kuma zaa maida mata abin da ta bada don fansan.
(ba ya halatta a
gare ku ku gaji mata a kan tilas kuma kada ku hanasu aure domin ku tafi da
sashen abin da kuka basu ).
Idan ta zo da alfahasha
sai ya hana ta aure don ta fanshi kanta daga gare shi sai ta yi hakan to
khul'in ya inganta. Sabo da fadin Allah Madaukaki: (kuma kada ku hana su
aure domin ku tafi da sashin abin da ku ka ba su, face idan suka zo da wata
alfahasha bayyananniya.)
Ba ya dace wa rike
wacce ba ta kamun kai, sabo da tawaya ne ga mijin a addinin shi da dabiunsa da
bata sunansa da zubar da mutuncinsa, bai da amincin kada ta bata mishi
shimfidinsa da jingina mishi wani da da ba nashi ba, kuma mace mai sakaci da
hakkokin Allah na wajibi kamar sallah da makamancinta, wacce ba ta jin nasiha Mustahabbi ne a sake ta.
Kuma rantsuwar shika na
cikin rantsuwa na fasikai, wadanda ke rikan ayoyin Allah da izgilanci, Ibnul
Arabi yace a cikin Ahkamul Kur'an : (Na daga cikin rikan ayoyin Allah da
izgilanci abin da aka rawaito daga Abdullahi dan Abbas kan cewa an tambaye shi
game da mutumin da yace da matarsa : Ke sakakkiya ce sau dari, sai yace : Ukun
ya isan maka a gare ta, sauran casain da bakwai ka riki ayoyin Allah da su bisa
izgili ).
Daga cikin mazaje akwai
wanda ya sanya furta shika da yawaita
shi abin ambato a bakinsa kuma abin sabon shi da al'adan shi,da abu mafi soyuwa
a gare shi a abu mai kima da mara kima da babba da karami da mai girma da abin
da bai taka kara ya karya ba,sai yace : In kiyi magana da wane to mata ta ta
saku,ko saku ya tabbata a gare ni idan na ci abincin wane. Ko shika ya
tabbata a gare ni muddin kika tafiya da
wane, ko shika ta tabbata a gare ni muddin mata ta ta shiga gidan wane, ko yace
wa bako: Shika ta tabbata a gare ni muddin baka ci abincin rana a gu na ba, wannan
dare , ko kuma in gobe baka ci abincin dare a guna ba, amma ba shikan yake nufi
ba, ko rabuwa ba, sai dai ya yi hakan ne kamar rantsuwa, don yana nufin
kwadaitarwa ko hanawa,ko tilastawa, wadannan lafuza ne haramtattu da ayyuka ne
na laifi, da walakanta rayuwan zamantakewa da rena hakkokin mace da yara da
wasa da shika da hukunce – hukuncenta.
Ya wajaba ga miji ya
kiyaye harshensa daga yawaita furucin shika, da tsoratarwa da ita da jirwaye da
kamar ruwa game da aukar da shi.
Ku ji tsoron Allah ya
ku Musulmai kada ku riki ayoyin Allah abin izgili kar ku ketare iyakokin Allah
madaukaki duk wanda ke ketare dokokin Allah to ya zalunci kansa, kuma dun wanda
ke katare dokokin Allah to wannan yana cikin azzalumai.
Ya kare.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق