HUDUBAR JUMA'A NA MASALLACIN ANNABI NA SHEIKH ALIYU ABDURRAHMAN
ALHUZAIFI 17 RAJAB 1438 AH
Dukkan yabo da godiya
sun tabbata ga Allah Masanin gaibi, mai juya zukata, Mai yawan gafarar zunubai,
ina yabon Ubangijina da godiya a gare shi bisa ni'imominsa da ba mai iya
kididdige su sai shi, Na shaida ba abin bauta wa da gaskiya sai Allah shi kadai
ya ke ba shi da abokin tarayya, mulki da kyakyawan yabo na shi ne, kuma shi ne
mai iko ga dukkan komai,
Na shaida Annabinmu
kuma shugabanmu Muhammad bawansa ne, kuma Manzonsa ne, Mai albishir kuma Mai
gargadi, ya Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka bisa ga bawanka kuma
Manzonka Muhammad da iyalansa da
sahabbansa wadanda Allah ya jibince su,
to madallah da majibinci kuma madalla da mai taimako,
Bayan haka ku ji tsoron
Allah Mai tsarki, a sirracenku da a bayyanenku, don ya jibinci al'amuranku ya
kuma gyara halayenku, domin takawa hanya ce ta mutanen kwarai da masu rabauta,
rashin takawa shi ne bayyanannen hasara,
ya ku bayin Allah ku kasance daga cikin ma'abota lura da imani, ku bi tafarkin
masu hankula da kyautatawa, ma'abuta lura su ne masu lafiyayyen hankali
mikakke, kuma masu lafiyayyen fidira,
kuma suke amfana da wahayi, suna
fahimtar ma'anonin abin da Allah ya saukar bisa manufar Allah da Manzonsa, tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi, suna aiki da maganar Allah don fatan ladarsa da tsoron ukubarsa, Allah
Madaukakin Sarki ya ce : (kuma wadanda suka nisanci shaidanu ga bauta musu,
kuma suka maida al'amari ga Allah, suna da bushara ,to, ka bayar da bushara ga
bayi na . wadanda ke sauraron magana sa'annan su bi mafi kyaunta . wadancan
sune Allah ya shiryar da su , kuma
wadancan su ne masu hankali)
Lura na daga ayukan masu hankali mai
haskakawa kuma yana daga cikin ayyukan masu basira masu
gogewa lura yana shiryarwa zuwa ga
rabauta da tsira daga ayuka masu halakarwa, kuma yana datar da ma'abocin shi
zuwa ga ayuka na kworai , kuma ya shiryar da shi zuwa ga hanyar mutanen kirki
masu neman kawo gyara
kuma karshen shi yana zamewa zuwa ga alheri , wanda ya rasa lura tunatarwa bazai mishi amfani ba zai fada cikin halaka kuma zai bi sha'awe-sha'awen
rayuka, kuma ya bi ta hanyar mabarnata sai ya zame cikin masu nadama , lura shi ne kaura daga wani hali da ya
shude ma'abocin ukuba da azaba zuwa ga kyakkyawan yanayi ta hanyar nisantar
sabuban ukuba da azaba ko kuma kaura
daga tarihin mutanen kworai da abinda
Allah ya karrama su da shi , zuwa da aiki da ayukan su da bin sawun su , ko
kuma tunani cikin abin halittu da sanin tsirrin da suka kunsa da sifofin su da
hikimar samar da su don bautawa mahaliccin su
da kebance shi da tauhidi da biyayya
albarka da daukaka ya tabbata agare shi
.
Hakika Allah mabuwayi
da daukaka ya halicci halittu kuma ya sanyawa
duniya hanyoyin da suke tafiya a kai sai ya sanya da'a sababi ne na dukkan
alheri a duniya da lahira ya sanya sabo sababi ne na dukkan sharri a
duniya da lahira shin akwai wanda ya
taba zama shakiyyi sabo da biyayya ga Allah?
Ko kuma akwai wanda ya rabauta
sabo da sabawa Allah? Hakika Allah mai tsarki ya bamu kissa a littafinsa
haka ma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bamu
kissoshi da wasu halaye na Annabawa da Manzanni da muminai wanda a
cikin shi akwai abin lura da kuma abu na
koyi ga wanda ke bayan su , da abinda akwai tsira daga ukubobi a cikin shi da kuma rabauta da alheri , da
abinda akwai kyakkyawan karshe tare da shi da daga darajoji Allah madaukakin sarki ya ce: (Lallai ne
hakika abin kula ya kasance ne acikin kissoshin su , ga masu hankali. Bai kasance kirkirarren
labari ba, kuma amma shi gaskatawa ne ga abin da yake a gaba gare shi, da
rarrabewar dukkan abubuwa , da shiriya da rahama ga mutane wadanda suka yi imani)
Allah madaukakin sarki ya ce :( Sa'annan kuma muna kubutar da
manzanninmu da wadanda suka yi imani ,
kamar wannanne, tabbatacce ne a gare mu mu kubutar da masu imani ) Allah mai tsarki ya ce game da masu karyatawa
:( Kuma suka kulla makirci, kuma muka kulla sakamakon makirci alhali su ba
su sani ba . ka duba yadda akibar makircin su ta kasance lallai mu mun darkake su da mutanen su gaba
daya . wadancan gidajen su ne wofintattu
sabo da zalunci da suka yi lallai ne a
wancan akwai aya ga mutane da suke
sani).Muka tsirar da wadanda suka yi imani , kuma sun kasance suna takawa).
Yayin da Allah ya
ambaci dewa daga cikin kissoshin Annabawa tsira da amincin Allah su tabbata a
gare su a cikin suratul Shu'ara'I ya ciken kissan da fadin sa madaukakin sarki , bayan tsiran
Manzannin sa da muminai tare da su :( Hakika
lallai akwai aya a cikin
wancannanka, yawancin su ba su kasance muminai ba . Hakika Ubangijinka lallai
shi ne mabuwayi mai jinkai )
Ibn kasir Allah ya
mishi rahama ya ce: Hakika lallai akwai aya a cikin wancannanka.
Ai a wannan kissan da
abunda ke cikinta na ban al'ajabi da taimako da karfafa ga bayin Allah muminai akwai nuni da hujja na
yanke da hikima na kololuwa ( lallai
Ubangijinka shi ne mabuwayi ) wato wanda ya buwayi dukkan komai kuma yayi galaba a kansa kuma ya fi karfinsa
mai jinkai da halittunsa baya gaggawa ga wanda ya saba mishi sai dai ma yana
sarara mishi kuma ya jinkirta mishi , sa'annan ya damke shi damka irin na
mabuwayi mai iko, Sa'id Dan Jubair Allah ya kara mishi rahama ya ce mai jinkai ga duk wanda ya tuba zuwa gare shi
, maganan ta tike a fadin Allah
madaukakin sarki a kissan mutanen Ludu
amincin Allah ya tabbata a gare shi
lallai a cikin hakan a kwai ayoyi ga masu lura katada yake cewa ga masu lura Bagawi ya ambaci haka a cikin
tafsirin sa mafi amfana da abubuwan da
suke faruwa na tarihi , da hikimomi na yanayi ,sai masu lura masu tunani
wadanda suke koyi da mutane na
kwarai masu neman gyara , kuma sukan bar ma'abota
barna da fasadi amma shi wanda baya lura baya wa'azantuwa ! baya wa kanshi hisabi baya aiki don lahiransa
addinin shi baya hanashi aikata komai , ko hankalin shi baya hana shi aikata
munanan aiyuka da laifuka wannan kamar
fa dabba ne Allah madaukakin sarki ya ce:
( ko kana zaton cewa , mafi yawansu suna ji , ko kuwa suna hankali
? su ba su zama ba face dabbobin gida suke . A'a, su ne mafi bacewa ga hanya.)
A cikin Hadisi daga
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gashi : (Lallai ne idan mumini
yayi rashin lafiya sai cutar ta buge shi har ya mutu ,to zai zama kaffara ne ga
zunubansa da suka shude, idan Allah ya sauwaka mishi to zai zama kankara
ne ga zunubansa da suka shude, kuma wazi ne ga lokaci mai fiskantowa. Idan kuma
munafuki ya yi rashin lafiya, sannan ya samu sauki to zai zama kaman rakumi ne
da masu shi suka daure shi sannan suka sake shi, to bai san don me aka daure
shi ba kuma don me aka sake shi ba.) Nasa'I ne bya rawaito
Allah bai ambaci tarihin Annabawa ba da
Manzanni da cikamakin su Annabinmu tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi face don ayi izina da tarihin su a yi kuma koyi da shiryarwar su da halayen su mku bi tafarkin su hakika Allah ya umarci Annabinsa Muhammada
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
da yayi koyi da su sai mai tsarki
ya ce :( Wadancanne Allah ya shiryar
sabo da haka ka yi koyi da shiryarwar su
. ) Allah madaukakin sarki ya ce :( Sabo
da haka ka yi hakuri kamar yadda masu karfin niyya daga Manzannai suka yi
hakuri).
Allah madaukakin sarki ya ce game da muminin yasin
:( Ya mutane na ku bi Manzannin nan ,
ku bi wadanda ba su tambayarku
wata ijara , kuma su shiryayyu ne ). Cikamakin su Annabin mu Muhammad tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi wanda
Allah ya goge sauran shari'u da shi
kuma ya aiko shi da shari'a mafi
kamala da addini , Allah ya dauki nauyi ga duk wanda
ya yi riko da shi zai shiryar da shi ya bashi
kyakkyawar rayuwa a duniya da
lahira ya shigar tare da shi mafificin halitta gidan aminci Allah madaukakin sarki ya ce : (Kuma
wadannan da suka yi da'a ga Allah da Manzon sa , to wadannan suna tare da
wadanda Allah ya yi ni'ima a kansu , daga Annabawa da masu yawan gaskatawa , da
masu shahada da saliha kuma wadannan nan
sun kyautatu da zama abokan tafiya )
To wani girmamawa ne ya
fi wannan , to wani daukakane ya ke kusa da wannan matsayi?, kamar yanda Allah ya kissanta mana kissoshin Annabawa amincin Allah ya tabbata a
gare su da wadanda suka yi imani da su don muyi
koyi da su kuma mu bi tafarkin
tsira tare da su muyi lura da tarihinsu
mu kuma san halayen su ,Allah ya kuma
bamu kissan labaran masu karyata su kuma masu
musu da gaskiya kuma masu girman
kai daga binsu wanda suka fifita rayuwan duniya akan na
lahira masu bin sha'awe – sha'awen su da
jin dadi , don fa mu yi izina da ukubar su, kuma mu wa'azantu da abinda ya faru
da su na walakacin duniya da azabar
lahira kuma mu gargadu daga tsinuwan da aka tabbatar a gare su .
Allah madaukakin sarki
ya ce :(Da Adawa da Samudawa , alhali
kuwa lallai alamun azaba sun bayyana a gare su , daga gidajen su kuma sahidan ya kawata musu ayukan su . sabo
da haka ya kange su daga hanyar Allah
kuma sun kasance masu basira .
Kuma Karuna da
Fir'auna da Hamana . kuma lallai Musa ya zo musu da hujjoji, sai suka yi girman
kai acikin kasa kuma ba su kasance masu tserewa ba , sabo da haka ko wannan su
mun kama shi da laifinsa: wato daga
cikin su akwai wanda muka aika iskar tsakuwa a kansa , kuma daga cikin su akwai wanda tsawa ta kama
, kuma daga cikin su akwai wanda muka birkice kasa da shi , kuma daga cikin su
akwai wanda muka nutsar, ba ya yiwuwa ga Allah ya zalunce su , amma sun kasance
kansu suke zalunta .
Allah madaukakin sarki
ya ce :( ko wannan su ya karyata Manzanni
sai narko ya tabbata a gare su )
Allah madaukakin sarki ya ce a kissan Banu ndir :( To ku lura fa ya
masu basirori,) tarihin manzanni
tsra da amincin Allah su tabbata a gare su tare da masu karyatawa na daga masu
sabawa Allah da Manzanni mutane sun san su zamani bayan zamani , na
karshe ya karba a gun na farko , wannan na daga cikin manyan hujjojin Allah
akan bayinsa wurin karfafan gaskiya da sanin tauhidi da taimakawa masu kadaita Allah a cikin bata da shirka da gargadi daga
gare shi
amma lura da dabi'un halittu da
gano hikimanta da siffofinta da tunani
akan kirkiran da Allah ya mata da tunani
cikin aikin Ubangiji gayarsa da kuma fa'idansa shi ne
kadaita Allah madaukakin sarki mabuwayi da daukaka da kuma bauta masa da mishi
da'a , to wanda ya kebanta da halitta shi ne abin bautawa bisa cancanci . Allah
madaukakin sarki ya ce : ( Kuma
lallai ne da abin lura a cikin dabbobin ni'ima; muna shayar da ku daga abinda yake a cikin cikunansu daga tsakanin tukar tumbi da jini, nono
tsantsan mai saukin hadiya ga masu sha ) Aallah madaukakin sarki ya ce :(
Allah yana juyar da dare da yini , lallai ne a cikin wannan akwai abin kula
da ma'abota gannai)
"ka ce ku yi dubi me ke cikin sammai da
kasa, kuma ayoyi da gargadi ba za su yi amfani ba ga mutanen da basu ba da
gaskiya da Allah ba "
To shi tuntuntuni cikin
halittu ibada ne ga musulmi, amma daukan izina cikin wadannan halittu yana kara
wa musulmi imani, kuma yana kara mishi zurfi cikin yakini, Allah Madaukakin
sarki ya ke cewa :( Lalle ne a cikin sammai da kasa akwai ayoyi ga masu imani)
Tunani da lura na
tabbatar da mai shakku, yana kuma raya zukata, yana haskaka gannai, yana mikar
da halaye, shi kuma kauda kai daga tunani da lura yana kekasar da zukata, yana
haifar da gafala,yana ja zuwa ga nadama, yana kuma jefa mutum cikin sabo An karbo daga Abu Huraira Allah kara yarda
a gare shi ya ce : ( Lalle Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi ya ce a isra'I : yayin da na sauko zuwa sama ta duniya sai na dubi
kasa ta, to sai ga wata iska da kara da hayaki, sai na ce : me ye wannan ya kai
Jibrilu? Sai yace : wadannan shaidanu ne ake kona su a gaban dan Adan basu
tunani ga mulkin sammai da kasa ba don haka ba da sun ga abin mamaki) Ahmad ne
ya rawaito
Aallah madaukakin sarki
ya ce :( Lalle ne wadanda suka yi takawa idan wani tashin hankali daga
shaidan ya shafe su, sai su tuna (Allah) sai ga su sun zama masu basira. Kuma
'yan uwansu (shaidanu ) suna taimakon su a cikin bata sa'anan kuma ba su takaitawa).
Allah sanya albarka a
gare ni da gare ku cikin Alkur'ani.
Huduba ta biyu :
Dukkan yabo da godiya
sun tabbata ga Allah wanda ya haskaka zukatan masoyansa da Alkur'ani, ya
haskaka gannansu da imani, ya kawata ayyukansu da kyautatawa,
Ina kyautata yabo ga
Ubangiji na kuma ina gode mishi, bisa ga ni'imominsa da ba mai iyakance su koma
bayansa,
Na shaida ba abin bauta
wa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, mulki da
yabo duka na shi ne, Mai rahama mai jinkai.
Na shaida cewa
Annabinmu kuma shugabanmu bawansa ne kuma manzonsa ne, wanda aka kebantar da shi
da dunkulallun kalmomi masu kamalar ma'ana da cikan bayani, Ya Allah ka yi
salati da aminci da albarka bisa ga bawanka kuma manzonka Muhammad da iyalansa da sahabbansa, da
wadanda suka bi su da kyautatawa
Bayan haka. Ku ji
tsoron Allah Madaukaki zai gafarta muku,zai tattaro muku dukkan alheri a
rayuwanku da bayan mutuwarku,
Ya ku bayin Allah ! Ku
yi wa kan ku hisabi kafin a yi muku hisabi, kowannen ku ya duba game da karshen
al'amari, da karewar ajali, to wanda ya yawaita lura to kurakuransa za su karanta,
wanda duk ya kiyaye sabawa Allah da zunubai to zai rayu cikin aminci, kuma a
datar da shi zuwa ga kyakkyawan karshe, mai samun sa'ada shi ne wanda ya
waazantu da waninsa, mai hasara kuwa shi ne wanda waninsa ya waazantu da shi.
Hakika Allah ya yi zambo ga masu bin son rai wadanda basu yi
lura ba suka wa'azantu da abin da Allah ya basu na labarai, Allah Madaukakin
sarki ya ce :( Kuma suka karyata kuma suka bi son zuciyarsu, alhali kuwa
kowane al'amari (wanda suke son su tare daga Annabi ) an tabbatar da shi. Kuma lalle abin da yake akwai tsawatarwa a cikinsa na labarai ya zo
musu.)
Ku saurara Allah
Madaukakin sarki na da wasu hanyoyin da ya saba bada lada da alhaki akan su to
duk wanda ya ci karo da sunnar Allah to za ta tambadar da shi ta tarwatsa shi
ya fado ya kaskanta, Allah Madaukaki ya ce : (A kan hanyar Allah (ta gyaran
jama'a) a cikin wadanda suka shude gabaninka , kuma ba za ka sami musanya wa ba
ga hanyar Allah.)
Ya zo a hadisi (ku
yawaita ambaton mai katse jin dadi mutuwa)
Ya ku bayin Allah
: Lalle Allah da Mala'iku na salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi
salati a gare shi kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi.
vv
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق