Hudubar Juma'a
na Masallacin Annabi 17/10/1437 tare da
sheikh Abdulmuhsin Alkasim.
Hudubar farko.
Dukkan yabo da godiya
sun tabbata ga Allah muna gode masa kuma muna neman taimakonsa da gafararsa,
muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da munanan ayyukanmu, duk wanda
Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi, kuma duk wanda ya batar babu mai
shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah,shi kadai yake
ba shi da abokin tarayya, na kuma shaida Annabinmu Muhammad bawansa ne kuma
manzonsa ne, tsira da amincin Allah su tabbata gare shi da iyalansa da
sahabbansa da aminci tabbatacciya mai yawa.
Bayan haka, ku ji
tsoron Allah yadda ya dace a ji tsoron shi – ya ku bayin Allah- ku yi
murakabarsa a boye da bayyane,
Ya ku musulmai:
Abu mafi kyau da mutum
zai sadaukar da rai don shi, shine tunani a ayoyin Allah da abubuwan ban mamaki
na aikinsa, da kaura zuwa taallakan zuciya da himmatuwa da Allah ba wani abu
cikin halittansa ba,
Ayoyin ubangiji sune dalilai da hujjojin da bayi zasu
san Ubangijinsu da su da sunayensa da
siffofinsa da ayyukansa, da kadaita shi,
Kuma Tunani a halittun Allah ibada ne, kuma
shiriya ne, kuma shine mafarin alheri da
mabudinsa, da shi ne bawa zai girmama Ubangijinsa, kuma ya kara imani da
sakankancewa, kuma ya bude basira ta zuci, ya fadakar da shi daga gafalarsa, ya
gadar mishi da rayuwa da lura da kauna ga Allah da tunani.
Tunani a ayoyin Allah na daga cikin abu mafi daraja daga cikin ayyukan zuci kuma mafi amfani, yana kira ga aiki kuma ya sanya ma'abocinsa
mika - wuya,
Sufyan dan Uyaina Allah jikansa yace:
"Tunani mabudi ne na rahama, ase ba ka gani mutum kan yi tunani ya
tuba"
Shi ne abu mafi Alherin
abin da zaa yi wa'azi ga bayi da shi. Allah madaukakin sarki yace : ka ce ni
kawai ina yi muku gargadi da kalma guda wato ku tsayu domin Allah, bibbiyu da dai dai, sa'an nan ku yi tunani )Saba'I 46
Idan mutum na
tunani to a komai zai zama yana da abin
lura, Alkur'ani mai girma na cike da kiran halittu zuwa ga tunani bisa ayoyin
Allah, da dubi ga halittunsa, Allah madaukakin sarki ya ce: ( shin basu yi dubi ba a cikin mulkin
sammai da kasa da kuma abin da Allah ya halitta daga komai). Araf 185
A cikin halittun Allah
akwai abin lura da wa'azi Allah ya yi umarni da tunani game da su, sai
yace: "ka ce ku yi dubi me ke cikin sammai da kasa" yunus 101
Shekul Islam Allah ya mishi rahama ya ce : ''
kuma dubi zuwa ga halittun sama da na
kasa don yin tunani da lura abu ne da
aka yi umarni da shi kuma mustahabbi ne''
Hankula cikakku masu wayo su ke gane abubuwa
bisa hakikanin yadda suke, Allah ya yabi
masu tunani cikin halittunsakuma lalle suna cikin masu zurfin hankali,Allah
madaukakin sarki yace : ( Lalle ne a cikin halittar sammai da kasa da
sabawar dare da yini akwai ayoyi ga ma'abuta hankali. Wadanda suke ambaton
Allah a tsaye kuma a zaune a bisa sasaninsu, suna tunani akan halittar sammai
da kasa, ya Ubangiji baka halitta wannan a kan banza ba, Tsarkin ka sabo da
haka ka tsare mu daga azabar wuta. ) Ali Imran 190-191.
Allah ya yi zambo ga
masu kauda kai daga tunani sai yace : (kuma
da yawa wata aya a cikin sammai da kasa suna shudewa a kanta kuma su suna
bijirewa daga gare ta.) yusuf 105
Na daga cikin
ukubobin Allah karkatar da ayoyin shi
daga masu girman kai, sai ya ce:
:( za ni
karkatar da wadanda suke yin girman kai a cikin kasa ba da wani hakki ba daga
ayoyi na kuma idan sun ga dukkan aya ba za su yi imani da ita ba).A'araf 146
Hasanul Basri yace :( Abin da ya
hana su tunani a ciknta.)
Rana na cikin manyan
ayoyin Allah na yau da kullum, Allah madaukakin sarki ya ce:( kuma
akwai daga ayoyinsa dare da wuni da rana da wata,) Fussilat 37
Allah ya sanya ta ga duniya haske a sama kuma fitila mai tsananin haske.
tana gudu ba tare da sauti ba duk da girman gangan jikinta, tana tafiya
bisa kididdiga mai zurfi cikin
yalwataccen falaki, zuwa ajali abin ambato, (Rana ba ya kamata a gare ta ta
riski wata kuma dare ba ya kamata a gare shi ya zama mai tsere wa yini, kuma dukkansu a cikin sarari guda
suke yin iyo) yasin 40
Allah ya hore ta ga
bayin sa, to hudowarta da faduwarta ke
bada tsayuwar dare da yini, ba don
samuwarta ba da al'amuran wannan duniya ya rikirkice, a cikinta akwai hikimomi
da maslahohin da halittu ba za su iya iyakance su ba, Allah ya kafa hujja da
shi bisa kadaicinsa da uluhiyyarsa sai ya ce : (kuma lalle Idan ka tambaye su wane ne ya halitta sammai da kasa,kuma ya hore rana da
wata ? lalle suna cewa ; Allah ne.) Ankabut 61
Kuma ya sanya ta aya ga
mutane masu hankali, Allah madaukakin sarki ya ce :
(kuma ya hore muku dare da wuni, da rana da
wata,kuma taurari horarru ne da umarninsa, lalle ne a cikin wancan, hakika
akwai, ayoyi ga mutane wadanda suke hankalta.)Nahli 12
Ya kuma kirayi bayi
zuwa ga dubi ga horewarta da yayi na ban
al'ajabi.sai ya ce : ( Ashe ba ku ga lalle Allah, yana shigar da dare a
cikin rana ba, kuma yana shigar da rana a cikin dare, kuma ya hore rana da wata.)
lukman :29
Kuma da su ne halittu
ke kidanya lokutansu, kuma su san manyan
alamomi na al'amuransu na yau da kullum (kuma ya sanya dare mai nitsuwa, da
rana da wata bisa lissafi) An'am 96
Kuma Allah yahalicci inuwa, ya kuma sanya rana ta
zama mai nuni a gare ta.
Imamul Baghawi - Allah mishi rahama ya ce : " Ma'anar
nuni a gare shi shi ne cewa : Ba don
rana ba da ba a san inuwa ba, kuma ba don haske ba da ba a san duhu ba, abubuwa
ana gane su ne da kishiyoyinsu." Allah ya ta'allaka tafiyarta a matsayin alama na da yawa daga cikin ibadoji kamar
sallah sai yace : ka tsayar da sallah a karkatar rana zuwa ga duhun dare)
Isra 78
Game da mafificin
lokuta na Ambaton Allah yace : ( Kuma ka yi tasbihi game da gode wa
Ubangijinka a gabanin fitowar rana da gabanin bacewarta) K 39
A azumi kuma mai azumi zai yi buda baki idan
ta bace.., na daga cikin alamomin lailatulkadri (Rana tana bullowa wayan garin daren lailatul kadri tana halin bata
haske mai karfi, a wannan wunin nata.)Muslim ne ya rawaito.
A ranakun (Ayyamuttashrik)
Alhaji zai yi jifa ne na jamara bayan zawali.
Lokaci
na datsewar ibada na tuba na na fara wa ne da bullowar rana daga yamma
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Allah na
shimfida hannayensa da dare don mai laifin wuni ya tuba, kuma yana shimfida
hannunsa da rana don mai laifin dare ya tuba har zuwa rana ta fito daga yamma) Muslim ne ya rawaito,
Lalle Allah na
shimfida hannayensa da dare don mai
laifin rana ya tuba, kuma yana shimfida hanunsa da rana don mai laifin dare ya
tuba, har rana ta fito daga mafadanta,
Muslim ne ya rawaito,
Da salla kafin hudowar
rana da kafin faduwarta Allah ya sanya lada
gare ta mai yawa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi yace : (lalle za ku ga ubangijinku kamar yadda ku ke ganin wannnan wata.ba ku tumurmusa, a wajen ganinsa, idan za ku iya kar sallah ta kubce
muku, kafin hudowar rana (Asuba) da faduwarta(sallar la'asar) to ku aikata
hakan). Buhari ne ya rawaito.
Kisfewarta
tsoratarwa ne na Allah ga bayinsa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi yace :( Lalle rana da wata ba su kisfewa sakamakon mutuwar wani ko rayuwarsa, sai dai
suna cikin ayoyin Allah ne. Allah na tsoratar da bayinsa da su, idan kun ga
kusufi ku ambaci Allah har sai ya yaye).Muslim ne ya rawaito
Sabo da girman halittarta da yawan amfaninta Allah ya rantse da ita sai yace: ( Ina
rantsuwa da rana da hantsinta). Shams
1
Tare da wannan girma
kuma Allah ne ke tafiyar da ita, ita tana tasbihi gare shi, Allah madaukakin
sarki yace :(Ashe baka gani ba lalle Allah wanda ya ke acikin sammai da
wanda ya ke a cikin kasa yana yin sujjada a gare shi da kuma rana da wata da
taurari,da duwatsu da itace da dabbobi da kuma masu yawa daga mutane.) Hajj 18
A kowani rana tana
sujada ga Allah bayan faduwarta, Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce ; ya Abu zarri! Ko
ka san a ina rana ke faduwa? Sai nace : Allah da Manzonsa ne suka fi sani, sai
yace : lalle Tafiya ta ke yi har ta yi sujada a karkashin Al'arshi) wannan
shine fadin Allah madaukaki. (Kuma rana tana gudana zuwa ga wani matabbaci
nata, wannan kaddarawar mabuwayi masani.) Yasin 38
Buhari ne ya rawaito.
Kuma Baiwa ce ga Allah ba'a bauta mata, na daga
cikin shirka a yi mata sujada Allah ya
ce yace:( kar ku yi sujada ga rana ko wata
ku yi sujada ga Allah in kun kasance shi kadai ku ke bautawa)Fussilat
37.
Faduwarta salo ne
daga cikin salon da Annabawa suka rika na kira zuwa ga tafarkin Allah.
Annabi ibrahim
Amincin Allah su tabbata a gare shi ya kafa hujja bisa uluhiyyar Allah
da rushewar bauta mata da faduwanta. Allah
madaukakin sarki yace:( sa'annan a lokacin da ya ga rana tana bayyana
yace ; Wannan shine ubangiji na, wannan ne mafi girma) sa'annan a lokacin
da ta fadi yace : ya mutane na lalle ne
ni barrantace nake daga abinda kuke yi na shirka) Lalle ne na fuskantar da fuskata ga
wanda ya kaga hallitar sammai da kasa ina mai karkata zuwa ga
gaskiya kuma ba ni cikin masu shirka ) Al
An'am 78-79
An fitini da yawa da ga
cikin halittu sai suka bauta mata koma
bayan Allah, Huda huda tace da Annabi sulaiman, tana mai hakaitowa, game da
sarauniyar saba'I da mutanenta, (Na
same ta ita da mutanenta suna yin sujada
ga rana baicin Allah, Kuma shaidan ya kawata musu ayyukansu saboda haka sai ya
karkatar da su daga hanya sa'anan su
basu shiryuwa) Annaml 24.
Musulmi bai kirdadan
faduwan rana ko hudowarta da sallar sa, a wannan lokacin ne wasu kafurai ke mata
sujada, a dalilin sujadan wasu mutane gare ta sai shaidan ya kafa bauta gare ta
yayin bullowarta da yayin faduwarta, yana nuna shi suke yi wa sujada, sabo da
toshe kofar bauta mata aka hana musulmi
da ya kirdadi sallah kafin fitowar rana ko faduwarta, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi yace: (kar ku kirdadi fitowar rana ko faduwarta da sallarku domin
tana hudowa ne a kahon shaidan) Muslim ne ya rawaito.
A yayin zawali na rana
a kowani wuni akwai wa'azi ga mumini,
domin ana zuga wuta a ruruta(ana kunna ta a cika ta) to sai aka hana sallah a
wannan lokaci, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :
A wannan lokaci ne ake zuga jahannama) Muslim ne ya rawaito.
Fitowar rana daga ta inda ba ta nan ta saba
fitowa ba alama ne na kusancin Tashin Alkiyama. Kuma umarni ne daga Allah da
rushewar duniya. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya
ce :(Alkiyama ba za ta tsaya ba har sai rana ta fito da mafadarta, ida ta
fito mutane suka ganta duk sai su yi imani,
wannan shine lokaci da imani ba zai amfanar da rayi ba.) Bukhari da
muslim ne suka rawaito.
Kuma farkon ayoyi da zai fito, fitowan rana daga yammacinta
da fitawar dabba ga mutane da hantsi, kuma duk wanda ta riga dayanta fita to
dayan ma na biye a kusa .
kuma a matattara Allah yana hada mutanen farko da na karshe a farfajiya guda,
mai kira
na jiyar da su, kowa na ganin kowa, rana zata matsa kusa da halittu har
ta kai tsakaninta da su kwatankwacin (Mel). Sulaim dan Amir Allah mishi rahama ya ce:
"To wallahi ban san wanne yake nufi ba da mel na na auna kasa,ko tsinken kwallin da ake sawa a ido ?"
Manzon Allah tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Mutane za su kasance cikin
zufa kowa gwargwadon aikinsa, akwai wanda zai kai zuwa idon sawunsa, wani kuma
zuwa guiwarsa, wani kuma zuwa kwankwasonsa, akwai wanda zai nuta cikin zufa,
gumi ya kai har zuwa bakinsa, ) Muslim
ne ya rawaito,
Mutane bakwai Allah zai musu inuwa a
ranar da ba inuwa sai inuwarsa, son Allah ne da girmama shi ya hada su, sai
Ubangiji ya yi yekuwa ya na cewa :(Duk wanda ya kasance yana bautawa wani
abu to ya bi wannan abin, masu bautan rana sai su bi rana,sai a jefa su cikin
jahannama, a wannan lokaci ne rana za ta dunkule haskenta ya tafi,kuma a jefa
ta cikin jahima)
Allah madaukakin sarki
ya ce: (Kuma idan aka shafe hasken rana)Takwir 1
Ibnu kasir –Allah mishi
rahama- ya ce : "Abin da ake nufi da (kuwwirat):an tattaro sashenta
aka hade da sashen sa'annan sai a nade ta a wurga ta, to idan an yi hakan da
ita sai haskenta ya tafi.
Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Rana da Wata za'a shafe
haskensu ranar alkiyama,) Bukhari ne ya rawaito.
A cikin Aljanna babu
rana ko jaura, don ana haska ta ne da hasken Allah. Mafi girman ni'ima ga 'yan
Aljanna ita ce ganin Allah, za su gan
shi -Tsarki ya tabbata a gare shi- kamar yadda mutane a duniya suke kallon rana
a tsakiyar wuni ba tare da girgije ba.
Sahabbai sun ce ga
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: shin ko za mu ga
Ubangijinmu ranar alkiyama? Sai ya ce: ( shin kuna cutuwa ga (Kallon) rana
yayin da babu gajimare? Sai suka ce : aa ya manzon Allah. Sai ya ce : ( To
kamar hakan zaku gan shi)Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Bayan haka .. ya ku
musulmai!
Dukkan halittu tun daga
kwayar zarra har ya kai ga Al'arshi suna nuni ne akwai Allah,Duniya kuma na
furuci ne da kadaitakarsa. Kallo mai
amfani shine wanda aka yi da idon basira ba da
tsurar ido kawai ba. Musulmi na aiki da hankalin sa da tunaninsa don ya
yi wa kansa hisabi ya kuma gyara zuciyarsa.
Ku ambaci Allah ku
girmama shi, ku fiskance shi da biyayya ku kadaita shi. Ku kiyaye daga gafala
da bijirewa ku yi tasbihi a gare shi.
Ina neman tsarin Allah
daga shaidan abin jefewa, (Wannan shi ne halittar Allah. To ku nuna mini ,
"Mene ne wadanda ba shi ba suka halitta? Aa, azzalumai suna cikin bata
bayyananna") Lukman 11
Allah
sa mini albarka ni da ku cikin Alkur'ani mai girma, Allah ya amfane ni da ku da abin da ke cikinsa na
ayoyi, da ambato mai hikima, iya abin da zan fadi ina neman gafarar Allah ga ni
da ku da dukkan musulmai daga dukkan zunubai, ku nemi gafararsa shi mai gafara
ne kuma mai jinkai.
Huduba ta Biyu
Dukkan yabo ya tabbata ga Allah bisa kyautatawarsa, godiya a
gare shi bisa datarwarsa da baiwarsa, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai
Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya sha'aninsa abin girmamawa ne. Na shaida Annabinmu Muhammad bawansa ne
kuma Manzonsa ne,tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da
sahabbansa da aminci tabbatacce mai
kari.
Ya ku Musulmai:
Hikimar Allah ta
hukunta ya sanyawa rana daguwa da sauka wanda ke haifar da zafi da kuma sanyi,
ya a zafin bazara akwai wa'azi ga muminai, tsananin zafin shi daga tururin
jahannama ne, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Wuta
ta koka wa Ubangijinta sai tace: sashi na na cin sashe, sai ya mata izini da
numfasawa biyu, Numfasawa a cikin hunturu numfasawa a lokacin bazara, shine
tsananin zafi da kuke ji a bazara da tsananin sanyi da kuke ji na jaura.)
Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Duniya na gauraye ne da
radadi da ni'ima, radadinta zai tuna mana radadin wuta kamar yadda ni'imarta
zai tuna mana da jin dadi na aljanna. Jujjuyawarta daga sanyi zuwa zafi da kuma
daga dare zuwa wuni dalili ne na karewarta da gushewarta.
Mumini wani abu ba zai
raba shi da Allah ba, to zafi ba zai hana shi sallah ko azumi ba da biyayya da
alheri, Allah ya zargi masu cewa :(kar ku fita a lokacin zafi) ya amsa
da narko na azaba,(ka ce wutar jahannama ta fi tsananin zafi da sun kasance
suna fahimta) Tauba 81
Abin mamaki ga mutumin
da ya ke kare kansa daga zafin wutan duniya amma kuma bai karewa daga wutar
Jahima?
Sannan ku sani Allah ya
muku umarni da salati da aminci ga Annabinsa sai yace: a cikin Muhkamin
littafinsa da ya saukar :(Lalle Allah da Malaikunsa suna salati ga Annabi.
Ya ku wadanda suka yi imani ! ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin
amintarwa a gare shi).Ahzab 56.
Ya Allah ka yi dadin
tsira da aminci da albarka ga Annabinmu Muhammad,ya Allah ka yarda da khalifofinsa shiryayyu, wadanda
suka yi hukunci da gaskiya, kuma da shi suke adalci: Abubakar da Umar da Usman
da Aliyu, da sauran sahabbai baki daya.mu ma ka yarda da mu tare da su da
kyautarka da karamcinka, ya mafi karamcin masu karamci.
Ya Allah ka daukaka
Musulunci da musulmai, ka kaskantar da shirka da mushrikai, ka ruguza makiya
addini, ya Allah ka sanya aminci ga wannan gari da kwanciyar hankali da yalwa
da sauran garuruwa na musulmai.
Ya Allah duk wanda ya
nufe mu ko ya nufi gidajen musulunci da musulmai da mugun nufi, to ka shagaltar
da shi da kan shi, ka maida mishi makircinsa cikin halakarsa, ka jefa tsoro
cikin zukatansu, ya mai karfi mabuwayi.
(Ya ubangijika ka
bamu mai kyau cikin duniya,da kuma mai kyau a cikin lahira, kuma ka tsare mana
azabar wuta.) Bakara 201.
Ya Allah ka gyara
halayen musulmai a ko ina, ya Allah ka sanya gidajensu gida ne na Aminci da
yalwa, ya ma'aboci daukaka da karramawa.
(Ya Ubangijinmu! Mun
zalunci kanmu, kuma idan ba ka gafarta mana ba, kuma ka yi mana rahama, hakika
muna kasancewa cikin masu hasara.)Araf 23.
Ya Allah ka datar da
jagoranmu da shiryarwarka,ka sanya aikin shi cikin yardarka.
Ka datar da dukkan
jagorori na musulmai da aiki da littafinka, da yin hukunci da shariarka Ya
Ubangijin talikai.
Ya Allah ka amintar da
iyakokinmu, ka sanya gidajenmu gidaje ne na imani da karfi da tauhidi ya
ma'aboci daraja da daukaka. Ya Allah ka taimaki sojojinmu ka hada zukatarsu ka
tabbatar da diga digansu, ka taimake su a kan makiya ya Mai karfi Mai buwaya.
Ya ku bayin Allah:
(Lalle Allah na yin
umarni da adalci da kyautatawa da baiwa ma'abocin zumunta, kuma yana hani da
alfahasha da abin da aka ki, da zalunci, yana muku gargadi ko za ku na tunawa.)
Nahli 90.
Ku ambaci Allah Mai
girma da daukaka zai ambace ku,ku gode mishi bisa ni'imominsa zai kara muku.
Ambaton Allah shi ya fi komai, Allah ya san Abin da ku ke aikatawa.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق