السبت، 28 يناير 2017

ALFAHARI NA SHAIK ABDUL BARI ASSUBAITI (HUDUBAR 9 ZUL KIDA 1437 AH

Hudubar Juma'a daga Masallacin Annabi 9/11/1437 Tare da Sheikh Abdulbari Al subaiti
Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya  sun tabbata ga Allah, Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, godiya mai yawa da tsarkaka da albarka a cikinta,dukkan godiya da falala tasa ce, kamar yadda ya tsarkake zukatan bayinsa da tausayawa juna, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, wanda ya sanya tunkudedeniya sunna ta rayuwa,na shaida shugabanmu kuma Annabinmu Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa ne, ya gargadi da jifan juna da kauracewa da alfahari, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa, wadanda babban sifa ta 'yan uwantakarsu akwai kawaici da yafiya ga juna,    
Bayan haka:
Ina muku nasiha da ni kai na da tsoron Allah, Allah madaukakin sarki ya ce :(ya ku wadanda suka bada gaskiya! Ku ji tsoron Allah ku kasance cikin masu gaskiya) Tauba 119
Yayin da muka yi lura da koyarwar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da rayuwarsa za mu samu ya yi nesa da dorawa kai nauyi da wuce gona da iri a maganganunsa da ayyukansa da abincinsa. kuma musulunci ya koyar da mu : cewa duk yadda ayyuka suka daukaka suka yi kyau to ba zai dace a yi alfahari da shi ba muddin ya rasa imani, Allah madaukakin sarki ya ce (: Shin kun sanya shayar da mahajjata da rayar da masallaci mai alfarma kamar wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, kuma ya yi jihadi a cikin hanyar Allah, ba su daidaita a wurin Allah) Tauba :19
Amma yin alfahari da kai da ambaton  kyawawan halaye da matsayi na kabila ko dangi da tinkaho da ta'adodi da ji da kai da bayyana niimomi da sunan isa, to sifofi ne ababan zarga, kuma naui ne na rauni irin na dan adam, kuma  dalili ne na raunin mutum da rashin cikan hankalinsa, Allah madaukakin sarki ya ce : ( Lalle Allah bai son dukkan mai takama mai alfahari) Lukman :18
Mafi hadarin sura na alfahari da ke  barazana ga akidar musulmi shi ne Riya, wanda Annabi ya siffanta shi da karamar shirka, shi ne mutum ya tashi ya na sallah sai ya kawata sallarsa sabo da sanin wani mutum na kallonsa,  )
Na daga cikin sifofi na alfahari akwai bayyana sabo, wanda zai haifar da mummunar karshe ga maabocinsa.
Alfahari da jiji da kai  ya bata sunan maana mai kyau da kararamci ke dauke da shi, ta hanyar sanya israfi da almubazzaranci har ya kai shi ga wauta da musu da kafurcewa niima, da almubazzaranci da musulunci ya hana.
Alfahari da isa ya hada da dagun kai da tinkaho,  wanda ya ginu akan ji da kai da riya da girman kai , Allah madaukakin sarki ya ce :(Alfahari da yawan dukiya da dangi ya shagaltar da ku,*Har kuka ziyarci kaburbura) Takasur 1-2.
Masu alfahari sun ta'allaka ne da abubuwa na zahiri, sakamakon juyawan maauni, da fadawa cikin wahamin cewa  karfi na ga abubuwan shigowa na kayan masarufi na rayuwan duniya mai juyawa da gushewa.
Ba ya boyuwa ga mai hankali cewa : dukiya da lafiya da kyau da matsayi kyauta ne na ubangiji Mabuwayi da daukaka, kuma suna juyawa, to ya wajaba ga mutum ya fiskance su da kankan da kai ba da tinkaho da alfahari ba.
Kur'ani ya bayyana  halin wadanda su ke alfahari da dukiyansu da 'ya'yansu sai ya ce :(Mu muka fi yawan dukiya da 'ya'ya kuma mu ba abin azabtarwa ba ne.) saba'I 35. sai Allah mabuwayi da daukaka  ya maida martani a gare su :(dukiyoyinsu da 'ya'yansu ba za su wadatar musu da komai ba daga Allah.) Ali Imran :10
Shuhura cuta ce mai tsanani, masu nemanta da kauna sune masu gudu bayan kawawainiya, basu damu ba ko da kuwa zai kai ga sabawa addini da kyawawan halaye, mai neman shahara na rayuwa ne a daure a gaban idunuwan wadanda zai burge, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Duk wanda ya sanya tufafi na shuhura ta Allah zai sanya mishi tufafi na kaskanci ranar alkiyama).
Na daga cikin gurbi mafi hadari da alfahari ke haifarwa akwai lalatawa musulmi  addini : domin addini na iya lalacewa sakamakon kwadayin daukaka na duniya. Musamman idan mutum ya nufi riya ko neman a san shi ko a ji shi. Wannan dabiar na haifar da kaskanci da walakanci da tozarci Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( Duk wanda ya nemi a ji shi to Allah zai sa a ji shi kuma  wanda yayi riya da aikinsa Allah zai sa aga aikin nasa )   Bukhari ne ya rawaito
Kamar yanda alfahari a cikin ibada na tafiyar da albarkan aikin ya kuma lalatashi Allah madaukakin sarki ya ce (shin dayanku na son cewa wani lambu ya kasancewa a gareshi na dabinai da inabi koramu tana kwarara a cikinta yana da dukkan ya‘yan itaciya acikinta alhali tsufa ya riskeshi kuma yana da zuri'a rawnana kuma guguwa ta sameta da wuta take cikinta ta kone kurmus ) Bakara 266.
To wannan aiki na gari asalinshi  kamar gona ne me girma me yawan ya'yan itace, shi kuma bayyana aiki da nufin alfahari da riya kamar iska ne mai wuta aciki da ya afka ma gona zai gama da ita gamawa sai ya tafiyar da duk albarkatunta ya lalata ta.
Mutun ya kan zame a gidansa da kewayen iyalansa da wani abu na alfahari da isa ta hanyan bijiro da wasu abubuwa na zamantakewa da barna a shimfidi da kayayyakin gida da sura ko mutum mutumi, wanda haka ya kunshi  ketare iyaka a wurin sadaki da bukukuwan aure.
Alfahari yana zamar da  mutum ya fada  zuwa ga mantuwan  godewa mai ni'ima da yaba wa falalansa  Allah madaukakin sarki ya ce ( idan tsanani ya samu mutum sai  ya roki ubangijinsa  yana komar da alamarinsa zuwa gare shi sannan ida ya bashi ni'ima daga gareshi sai ya mance abinda ya kasance yana kira zuwa gareshi gabannin haka )Zumar 8.   wato zai rika takama da alfahari da ni'ima sai  ya manta da ubangijinsa da ya kasance yana bauta masa yana kankan da kai zuwa gare shi.
Alfahari : abu ne me tunkudawa zuwa ga rena wasu, kamar yadda haka ya bayyana a halin iblis cikin Fadinsa (ni na fishi alheri ka halicceni daga wuta kuma ka halicce shi da tabo)A'araf 12,  to sai  ya jingina zalunci zuwa ga ubangijinsa a nashi zaton cewa shi ne mafifici.
Dauka wa kai alfahari da tinkaho yana lalata tunanin musulmi game da sako na cigaba da raya kasa  :  gudu bayan da'awar banza da kuma abubuwa na zahiri wanda akwai yaudara a cikinsu  yana jefa  mutun musulmi ne zuwa ga sha'awe sha'awen rayuka da kuma nitso  cikin abin da bai da amfani na daga ayyuka.
Na daga cikin illolin alfahari yana rusa al'umma,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi  ya ce (kawai Allah yana taimakon wannan alumman ne saboda masu rawninta, kuma da adduoinsu da kuma sallolinsu da kuma tsarkake niyyarsu ) nasa'I ne ya rawaito
 Wannan yana bayyana cewa riya da kwadayin abubuwa na zahiri sababi ne na galaba akan al'umma.
A cikin alfahari da tinkaho da aikin alkhairi akwai  tunzura zuciyan musulmai  daga marasa galihu cikinsu wanda suke cikin kunci na rayuwa sakamakon rashin abin hanu, na daga cikin illoli na alfahari da tinkaho yaduwar hasada yayin da mutum yake magana akan ni'imomin da Allah yayi a gareshi  ta hanyan takama da alfahari da ruduwa, ko ta hanyan janyo hassadar mahassada.
   saboda haka kuma da waninsa  musulunci ya gandaya  ukuba mai tsanani akan yin alfahari da takama,da tinkaho da duk surorin shi da nau'ukanshi,  har a tafiya   Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce : (yayin da wani mutumi  yana alfahari yana tafiya a cikin tufafinsa kansa  na burge shi Allah sai ya nitsar da shi a kasa  yana nitso a cikinta har rana kiyama )  muslim ne ya rawaito shi
Allah sa mini albarka ni da ku ya amfane ni da ku da abin da ke cikinsa na ayoyi, da ambato mai hikima, iya abin da zan fadi ina neman gafarar Allah mai girma ga ni da ku da sauran musulmai daga dukkan zunubai, ku nemi gafararsa shi mai gafara ne kuma mai jinkai.



Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah da ya yi halitta ya daidaita, wanda ya kaddara kuma ya shiryar, ina gode masa – tsarki ya tabbata a gare shi- ina godiya a gare shi bisa ni'imominsa da ba za su kidanyu  ko akididdige su ba, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, Madaukaki kuma Mafi daukaka.Na shaida shugabanmu kuma Annabinmu Muhammad bawansa ne, kuma Manzonsa ne, wanda aka turo shi da haske a shiriya, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,da iyalansa da sahabbansa, wadanda suka biyo sawunsa.
Bayan haka:
Ina muku wasiyya da ni kai na da jin tsoron Allah – Mabuwayi da Madaukaki.
idan ni'imomi suka bayyana a tattare da mutum ba tare da nufin ya bayyana su  ba ko yayi dagun kai ga wasu ba  to wannan ba laifi  Allah ya ce : ( kace wanene ya haramta adon ubangiji wanda ya fitar da shi saboda bayi da dada'da na arziki) A'araf 32
An umurci musulmi da ya ambaci ni'imomin da Allah ya yi masa kamar yadda Ubangijinmu yake so ya ga alamar  ni'imarsa ga bawansa ta hanyan godiya a gareshi – Mai tsarki da daukaka - da kyakyawan yabo ba wai ta fiskan alfahari ba  Allah ya ce : (kuma amma ni'imomin ubangijinka sai ka fada (domin godiya) Adduha 11
babu laifi a shari'ance a boye ni'ima, kai shi ne ma asali idan har ma'abocinta  yana tsoron hasada da kambun ido,  Allah ya ce game da Annabi ya'akub (yace ya kai dan yaro na kada ka labarta mafarkinka ga yan uwanka kada su maka kaidi, kaidi hakika shaidan ga mutum makiyi ne bayyanenne )Yusuf 5
  kuma Manzon Allah tsira da amincin Alla su tabbata a gare shi ya ce (ku nemi cimma bukatunku ta hanyar boyewa domin duk wani ma'abocin ni'ima abin abin a yi mar hasada ne ).
Ku saura! Ku yi salati – ya ku bayin Allah-  ga Manzon Shiriya, hakika Allah ya umarce ku da hakan a cikin littafinsa sai ya ce: ( Lalle Allah da Mala'ikunsa suna salati ga Annabi, ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da sallama tabbatacciya.) Ahzab 56.
Ya Allah ka yi salati ga Muhammad da matayensa da zuriyarsa, kamar yadda ka yi salati Ibrahim da Alayensa, ka sa albaka ga Muhammad da matayensa da zuriyarsa, kamar yadda ka sa albarka ga Ibrahim da iyalansa.
Ya Allah ka yarda da khalifofi guda hudu shiryayyu: Abubakar da Umar da Usman da Aliyu da Iyalai kuma da sahabbai masu daraja, ka game  mu tare da su, a afuwarka  da karamcinka da kyautatawanka, Ya Mafi jinkan masu jinkai,
Ya Allah ka daukaka musulunci da musulmai, Ya  Allah ka daukaka musulunci da musulmai, ka kaskantar da kafurci da kafurai, Ya Allah ka rusa makiyanka kuma makiya addini, Ya Allah ka sanyawa wannan garin aminci da natsuwa, da sauran garuruwa na musulmai.
Ya Allah duk wanda ya nufe mu ko ya nufi musulunci da musulmai da mugun nufi to ka shagaltar da shi da kansa, ka sanya halakarsa cikin mugunyar shirinsa, ya Mai sauraron Adua.
Ya Allah mai saukar da littafi, Mai tafiyar da girgije, Mai ruguza runduna,ka rusa makiya musulunci, ka taimake mu akan su ya ubangijin talikai, ka taimake mu a kan makiyanka makiya addini, da rahamarka ya mafi jinkan masu jinkai.
Ya Allah muna rokonka shiriya  da takawa da kame kai da wadata.
Ya Allah muna rokonka dukkan alheri na gaggawansa da na nesa, wanda mu ka sani da wanda ba mu sani ba, muna neman tsarinka daga dukkan sharri, na kusa da na nesa, wanda muka sani da wanda ba mu sani ba.
Ya Allah muna rokonka Aljanna, kuma muna neman tsarinka daga wuta.
Ya Allah ka gyara mana addininmu,wanda shi ne tsari ga al'amuranmu, kuma ka gyara mana duniyarmu wanda rayuwarmu ke cikinta, ka gyara mana lahirarmu wanda gare ta zamu koma, ka sanya rayuwarmu kari ne ga dukkan alheri. Ka sanya mutuwa ta zama hutu ne gare mu daga dukkan sharri, ya ubangijin talikai.
Ya Allah ina rokon ka alheri mafarin shi da makuran shi,da matattarin shi, da farkon shi da karshen shi, na bayyane da na boye, muna rokon ka darajoji  madaukaka a Aljanna, ya Ubangijin talikai,
Ya Allah ka taimake mu kar ka taimaki wani akan mu, ka bamu nasara, kar ka bawa wani nasara akanmu, Ya Allah ka shirya mana yadda zamu iya maida makircin makiya akanmu, kar ka basu dama da zasu iya mana makirci, ka shirye mu kuma ka saukake sharia gare mu, ka taimake mu a kan wanda ya zalunce mu.
Ya Allah ka sanya mu masu anbatonka, masu godiya a gare ka. Masu kankan da kai gare ka, masu komawa da rusunawa gare ka.
Ya Allah ka karbi aduarmu.ka tafiyar da kullin zuci daga kirazanmu, ya Ubangijin talikai, Ya Allah ka jikan matattunmu, ka bada lafiya ga marasa lafiyanmu, ka jibinci al'amuranmu, ka yaye mana bakin-ciki.
Ya Allah ka kiyaye Mahajjata ga dakinka mai alfarma, Ya Allah ka kiyaye Mahajjata ga dakinka mai alfarma, Ya Allah ka kiyaye Mahajjata ga dakinka mai alfarma, ka nesantar da su daga sharri da zunubai.
Ya Allah ka maida su gidajensu lafiya, suna halin samun nasara da lada ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka sanya shi Hajji ne mabruri Wanda aka yi wa Allah biyayya a ciki. Kuma ka sa aikin su ya zama abin godiya  zunubansu kuma abin gafartawa, da aiki na kwarai karbabbe ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka datar da jagoran mu cikin abin da ka ke so kuma ka yarda da shi, ya Allah ka datar da shi zuwa shiriyarka , ka sanya aikin shi cikin yardarka  ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka datar da dukkan jagororin musulmai zuwa ga aiki da littafinka,da yin hukunci da shariarka, ya mai jinkan masu jinkai.
(Ya Ubangiji Mun zalunci kawunanmu muddin baka gafarta mana ka yi mana rahama ba lalle za mu kasance cikin hasararru) A'araf 22
(Ya Ubangiji ka gafarta mana da 'yan uwanmu da suka riga mu da imani, kar ka sanya kulli a cikin zukatanmu game da wadanda suka yi imani, ya ubangiji lalle kai mai tausayi ne kuma mai jinkai) Hashr 10
( Ya ubangiji ka ba mu kyakkyawa a nan duniya kuma ka bamu kyakkyawa a lahira  
Kuma ka kare mu daga azabar wuta) Bakara 201.
(Lalle Allah na yin umarni da adalci da kyautatawa da bai wa ma'abocin zumunta. Kuma yana hani ga alfahasha da abin da aka ki da zalunci, yana muku gargadi ko zaku waazantu). Nahl 90
Ku ambaci Allah sai ya ambace ku, ku gode mishi bisa ni'imominsa zai kara muku, ambaton Allah shi ya fi girma Allah ya san abin da ku ke aikata wa.


ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق