Hudubar Juma'a daga Masallacin Annabi
(SAW) 21/12/1437AH Na Sheikh
Husain Bin Alus shaikh
Lalle dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna gode masa kuma
muna neman taimakonsa, muna neman gafararsa, muna neman tsarin Allah daga
sharrin kawunanmu, da kuma munanan ayyukanmu,duk wanda Allah ya shiryar da shi
babu mai batar da shi, wanda ya batar kuma babu mai shiryar da shi, na shaida
ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya,
kuma na shaida Annabinmu Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne.
(Ya ku wadanda suka bada gaskiya ku ji tsoron Allah hakikar soronsa,kuma kada ku mutu face kuna
musulmai) Al Imran 102.
(Ya ku mutane ku ji tsoron ubangijinku, wanda ya halicce ku daga rai
guda daya, kuma ya halitta daga gare shi matarsa kuma ya yada daga gare su maza
masu yawa da mata, ku ji tsoron Allah da kuke rokon juna da (sunan) Shi, da
kuma zumunta, lalle Allah ya kasance mai kulawa
ne da ku.) Nisa'I 1
(Ya ku wadanda suka yi imani ! ku ji tsoron Allah ku fadi magana madaidaiciya.
Zai kyautata muku ayyukanku kuma ya gafarta zunubanku , kuma wanda ya yi daa ga
Allah da Manzonsa to lalle ya rabauta babban rabo mai girma.) Ahzab 70-71
Ya jama'ar Musulmi!
Mafi girman zunubai masu halakarwa kuma zalunci mafi muni da laifi mafi
girma shine Shirka ( Hada Allah - Mabuwayi da Daukaka- da wani a cikin bauta) ,
duk wanda ya auka cikin shi to ya halaka, wanda ya mutu yana yin sa zai shiga
wuta mai babbaka. Allah madaukakin sarki ya ce : (Lalle ne shi wanda ya yi
shirka da Allah, to lalle ne Allah ya haramta masa Aljanna) Alma'ida 72
Sabo da haka na daga cikin Aduar Shugaban HANIFAWA Badadayin
Mai Rahama Ibrahim Amincin Allah ya tabbata a gare shi :(Kuma ka nisanta ni,
ni da Diyana daga bautawa gumaka)
Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Duk
mutumin da ya mutu yana kiran wani koma bayan Allah a matsayin kishiya zai shiga wuta) Buhari ne ya rawaito.
Kuma yana cewa :(Duk wanda ya hadu da Allah bai hada shi da wani abu
cikin bauta to zai shiga Aljanna) Muslim.
Sabo da haka duk wanda ya nemi tsira da kubuta kuma ya nemi Alheri da
tsarkaka to ya kasance ya kiyaye fadawa cikin shirka da Kuma hanyoyinsa da
alamominsa na bayyane, da tafarkinsa , har ya zama cikin aminci da kwanciyar
hankali a duniya da lahira, : ( Wadanda
suka yi Imani basu gauraya Imaninsu ba da zalunci ba, wadannan suna da aminci,
kuma su ne shiryayyu)
Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Lalle
Allah ya haramtawa wuta duk wanda ya ce : Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah
ya na neman yardar Allah da hakan.) Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Duk
wanda ya hadu da Allah a halin bai hada shi da wani to zai shiga Aljanna)
Muslim ne ya rawaito
Kusaurara ,lalle Nauuka na shirka
da tushen shi shi ne a girmama wani
halitta kamar yadda ake girmama Allah
Madaukaki - ko da waye shi-. Ko kuma ka kudurta cewa suna da wasu
siffofin da Allah ya kebanta da su, kuma suna gudanar da al'amura, ko kuma suna
iya tunkude wani abu, Allah yace game da Annabinsa : (kace "ni mutum ne
kawai kamar ku ana yin wahayi zuwa gare ni cewa : Lalle ne abin bautawarku,
abin bautawa guda ne, sabo da haka wanda ya kasance yana fatan haduwa da
ubangijinsa, to sai ya yi aiki na kwarai, kuma kada ya hada kowa ga bautawa
Ubangijinsa).
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi :( Kar ku
ketare iyaka cikin yabo na kamar yadda
aka ketare iyaka cikin yabon Masihu dan Maryam lalle ni bawa ne kuce
bawan Allah kuma Manzonsa) Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Na daga cikin misalan hakan ka rantse da wanin Allah kana girmama abinda
ka rantse da shi kamar yadda ka ke girmama Allah. To wannan shirka ne Babba,
kuma yana rusa aiki amma in bai kai yadda ake girmama Allah ba to ya zama
karamar shirka, ya fi girma a kan manyan
zunubai, Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi yace : Duk wanda ya rantse da wanin Allah to
hakika ya yi shirka ) Abu Dawuda ya rawaito a wani lafazin ( Hakika ya kafirta
ko ya yi shirka)
Hakika Ibnu Abdulbar ya hakaito ijma'i
kan cewa ba ya halatta rantsuwa da wanin Allah, na daga cikin sifa na Babbar
shirka mai rusa aiki kuma mai dawwamarwa a wuta kudurta cewa wanin Allah na da
ikon gudanar da duniya kuma yana iya amfanarwa da cutarwa koma bayan Allah,
sabo da haka duk wanda ya kudurta kan wani sababi na da tasiri a kan
kanshi kamar wanda zai sa abin kariya
(Guru ko laya) ya kudurta cewa wannan abin kariyar zai iya kawo mishi wani amfani
ko tunkude mishi wani cutarwa to wannan
babbar shirka ce. Allah Madaukakin sarki yace : (Kuma idan Allah ya shafe ka
da wata cuta, to, babu mai yaye ta face shi, kuma idan yana nufin ka da wani
alheri, to, babu mai mayar da falalarSa.)
Na daga cikin nauoi na babbar shirka da ke faruwa a kaburbura akwai abin
da wasu ke yi na fiskantar matattu da rokon su fitarwa daga bakin ciki da yaye
bacin rai, suna kuma neman biyan bukatu daga gare su, kuma suna fata daga gare
su dauke damuwa da bakin ciki, wannan na daga cikin mafi munin hada Allah da
wani, wanda ya sabawa daawar Manzanni Amincin Allah ya tabbata a gare su, Allah
madaukakin sarki ya ce :( Ko wane ne yake karba wa mai bukata idan ya
kira shi kuma ya sanya ku mamayan kasa? Shin akwai wani abin bautawa tare da
Allah? Kadan kwarai kuke yin tunani)
Na daga cikin hasara mafi girma ka riki mafaka koma bayan Allah
Madaukaki, a duk lokacin da ka shiga matsatsi, ko wata musiba ta same ka sai ka
kira: " Ya wane" ka manta da
mai iko Mai girma kuma Ubangiji Mai
tausayi ( Lalle wadanda ku ke kira koma bayan Allah
bayi ne kamar ku)
To na daga cikin bata mai
girma da shirka bayyananne ka dukufa ga kabarin wani matacce wanda bai
mallakawa kansa wani anfani ko cutarwa ba, kana mishi sujada ko ka yi dawafi a
kabarinsa, ko ka yi yanka domin shi, ko
ka roke shi, kana fata daga gare shi to wallahi wancan nin ku shine babban kage, kuma babbar shirka ce,
Allah madaukakin Sarki ya ce: (kuma wane ne mafi bata daga wanda ke kiran
wanin Allah, wanda ba zai karba masa ba, har ranar kiyama, alhali su (wadanda
ake kiran shagaltattu ne daga kiransu) Ahkaf 5
Allah madaukaki ya ce: ( kuma kada ka kirayi baicin Allah abin da ba
ya amfananka kuma ba ya cutanka. To idan ka aikata haka, saanaan lailai,a
lokacin ,kana daga masu zalunci.) yunus 106
Ka kasance ya kai musulmi bawa Mai ikhlasi ga ubagijinka a wajen aduarka
da fatanka,da tsoronka da kaunarka da kankan da kanka da rusunawarka (Ka ce
" Lalle ne salla ta da baiko na da rayuwa ta da mutuwa ta na Allah ne
Ubangijin talikai. Babu abokin tarayya a gare shi kuma da wancan aka umurce ni,
kuma nine farkon masu sallamawa.) An'am 162-163
Daga nan ne Mafi girman masu kira zuwa ga tauhidi mai kare sassan shi ya
tsine wa masu rikan kaburburan Annabawansu
masallatai kuma ya ambata cewa sune mafi sharrin halitta a gurin Allah,
yace : " Ku saurara kada ku riki kaburbura masllatai don na hane ku
daga wannan.) Muslim ne ya fitar da shi
An karbo daga Abdullahi dan Abbas ya ce : " Manzon Allah ya
tsine wa mata masu ziyartar makabarta masu rikon sa gurin bauta suna kunna
fitilu," ) Abu Dauda da Tirmizi suka rawaito kuma ya ce Hadisi ne Hasan.
Na daga cikin kwadayinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na
kiyaye hakkin Allah mai girma shine Tauhidi tsarkakke gare shi madaukaki wanda
Annabi ya kwadaici kiyaye shi da dukkan magana da aiki da kauda kai domin bada
kariya a gare shi.
Ya roki Ubangijinsa kamar yadda Malik ya rawaito shi a mawadda, sai Mai
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: Ya Allah kar ka sanya
kabari na gurin bauta, fushin Allah ya tsananta
ga mutanen da suka riki kabarburan Annabawansu gurin bauta.
Kuma Manzon Allah ya toshe duk wata kofa da za ta kai ga shirka da Allah
madaukaki, sai yace: ( Kar ku sanya kabari na idi ku mi salati gare ni don
salatinku na riska na a duk in da ku ke) Abu Dauda ne ya rawaito, Marawitarsa
duk amintattu ne, Wato kar ku maida kabari na ya zama gurin kai komo, a
wasu sanannun lokuta.
Ya kai musulmi ka kiyaye wadannan musibu masu girma, da manyan zunubai masu halakarwa, ka sani shaidan na madakata
yana kawata wa bayi shirka da hanyoyin shi kuma yana yin shamaki tsakaninsu da
Tauhidi da haskensa.
Wasu malamai masu tantancewa
" Shaidan na batar da bani Adam da gwargwadon iyawarsa… har zuwa inda yake cewa hakanan
masu bautan taurari da gumaka wani sa'i ma shaidanu kan yi magana da su, su
sami wani sashi na bukatunsu , rokon wadan da basanan da kuma matattu na daga
cikin wannan babin , sai shaidan ya suranta musu siffar wannan da ake neman
agaji agunshi, don ya biya wani sashi na
bukatum me neman a gajin, har ya zaci cewa wannan mutuminne ko kuma mala'ika ne
a cikin suransa, alhali kuwa shaidan ne asalin shi ne lokacin da aka hada Allah da
wani kamar yanda shaidanu suka kasance sukan shiga cikin gumaka su yi magana da
mushirikai, kuma ya ce : ( a wasu lokatan shaidan yana fitowa mai rokon wanin
Allah a wani sifa, har ma yakan samu wani sashi na bukatunsa)
HUDUBA TA BIYU
Ita ibada hakki ne kebantacciya ga Allah, Allah madaukakin sarki ya ce a
farkon umarni da yazo cikin Alkur'ani : (( Ya ku mutane ! ku bauta wa
Ubangijinku, Wanda ya halicce ku, ku da wadan da suke daga gabaninku,
tsammaninku, ku kare kanku!.) Bakara 21
Manzonmu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
ya ce: ((kuma hakkin Allah akan bayi shi ne, su bauta mishi kar su hada shi
da wani)) Buhari da Muslim suka rawaito.
Ibada suna ne da ya tattaro dukkan wani abinda Allah yake so kuma ya
yarda da shi , na fadi ne ko aiki, na bayyane kamar sallah da zakka da azumi da
hajji da sauran abubuwa da aka yi umarni, da kuma na boye kamar tsoro da so da
firgici da fata, to duk wanda ya aiwatar
da wani abu na daga cikin wannan ga wanin Allah to hakika yayi shirka da Allah
madaukaki mabuwayi . To ka kiyaye ya kai
dan uwa musulmi na daga wannan, dukkan kiyayewa ,domin shi ne hadari mafi girma da cuta mafi
muni.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق