Hudubar Masallacin
Annabi 24/10/4137 Tare
da sheikh Salah dan Muhammad Albudair
HUDUBAR FARKO
Dukkan yabo da godiya
sun tabbata ga Mai karamci Mai yawan kyauta, Ya fifita tsakanin halittunsa
cikin fahimta da ilmuka da hankula da laduba, Ya haramta alfahasha da batsa da zagi,Na
shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin
tarayya, gare shi nake kira, kuma zuwa gare shi makoma ta.Na shaida Annabinmu
kuma shugabanmu Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa ne, tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi, kuma ga Alaye da Sahabbai baki daya.
Bayan haka, Ya ku
musulmai!
Ku ji tsoron Allah, to
duk wanda ya ji tsoron Allah ya rabauta a ranar sa ta yau da ta gobe, kuma
Musulmi shi ne wanda musulmi suka kubuta daga sharrin harshensa da na hanunsa, (
Ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah ku fadi magana madaidaiciya)
Ahzab 70.
Ya ku Musulmai:
Mumini na tunkudo
alheri , kuma yana tausayawa halittu,
Sauki a zance
da tattausawa a magana, da Taushi cikin tattaunawa, tafarki ne mikakke
da ake karkato da zukata, ta kan janye soye soyen rayuka daban daban, kuma ta
dawo da zukata da suka yi nesa, da ra'ayoyi mabanbanta,
Allah madaukakin sarki yace ga musa da Harun :
( Ku ce da shi zance mai taushi ko zai fadaka ko ya ji tsoro)
Ibnu kasir Allah ya
mishi rahama yace: "wannan aya
akwai abin lura mai girma, wanda ita ce Fir'auna ya kai kololuwa cikin sabawa
Allah da dagun kai shi kuma Musa zababben Allah ne na cikin halittu a wancan
lokaci, amma duk da haka aka yi mishi umarni da kar ya fiskanci fir'auna sai da
magana mai taushi da kuma tausasawa".
Ya ku Musulmai :
Zagi kan yada
fitintinu,kuma zagi bai dawo da gudajje,
kuma bai janyo abokin musu, sai dai kawai ya haifar da gaba da kiyayya da
kullin zuci, kuma ya kara wa mai jayayya dogewa da musu.
Duk wanda yake zagin
abokin adawarsa yana jifansa da
alfahasha, ya munana zance game da shi,ya aibata shi da kalamai marasa kyau, to ya dada kwambala ruwa akan tabo ne, ya kuma karawa cuta rashin lafiya ne (ma'ana
ya dada kamari da rikita al'amura kamar wanda ya karawa wuta fetur ne).
Ma'aboci mummunan hali
da zafin harshe mai yawan cin mutunci, mai sukan jama'a, mai kazafi ga wadanda
basu ji ba ba su gani ba, mai cin zarafin bayin Allah, mai yawan aibata mutane
da cin namansu, wanda bai furuci sai da alfahasha da zagi, ba zai taba zama mai
kawo gyara ko nasiha ba, ko malami ba.
Abubuwa na gaugawan
faruwa cikin al'uma, ba wani kara da mutane zasu ji ko faduwan wani abu, ko wata
wakia ta kusa ko ta nesa, face sun
garzaya ga yanar gizo wato internet, suna rikan wannan wakiar abin zagi da za su rika zagin juna da shi
suna bibiyar shi suna yada shi. Suna masu gaggawa zuwa ga hanyoyin sadarwa na
sada zumunta suna kai hari tsakanin mai
jifa da mai harbi , da mai suka da mai tsinuwa da mai zagi sai kadan daga
cikinsu wadanda Allah ya tarfawa garin su nono.
Ya ku wadanda ku ke
rubuta tsinuwa da zagi da sake tuhume –tuhume da hukunce – hukunce! Ku sani zaa
tambaye ku game da abinda ku ke rubutawa, a ranar da halittu za su tattaru a
cikinta, kuma a auna dukkan ayyuka, da mintuna da ka sarayar, ko wace rai za ta
zo da mai shaida da mai kora ta.
Ya wanda ya buya bayan
fiskar wayarsa ko naurarsa, ya wanda ya fake da suna na karya, ya yi nesa daga
idanuwa! Ya zame yana auna wa waninsa zagi da tsinuwa! Ka manta Allah ya na
ganinka ne? A halin kuwa yana sane da sirrinka da ganawarka.
Mumini ba mai suka ne
ko tsinuwa ko batsa da mummunar magana ba.
Annabi tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi bai kasance mai zagi ba ko mai maganar alfahasha ko
tsinuwa ba, ya kuma ce : (Lalle ni baa turo ni mai tsinuwa ba sai dai ni an
turo ni rahama ne.)
zagin musulmi fasikanci
ne) kuma yace ( Masu zagin junansu su biyu shaidanu ne, suna cin zarafin
junansu, kuma suna karya akan junansu).
Daga Jabir bin sulaim Allah yarda da shi lalle
yace ga Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata agare shi,: A sanar da ni abin da zan kiyaye shi na kuma
lizimce shi, : sai yace (kar ka zagi wani! ) yace :" Bayan haka ban
sake zagin kowa ba, da ne ko bawa,
rakumi ko akuya ba".
Manzon Allah tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da shi: ( Idan mutum ya zage ka,
ya aibata ka da wani abu da ya sani game da kai, to alhakin hakan na kan
shi,)Abu Dauda ne ya rawaito.
Ya kai bawan Allah!
Ka tuba daga abin da hannayenka
suka rubuta, ka goge zaginka da cutarwarka da ka yi wa wani.ka tuna fadin
Mahaliccinka Majibincinka :(kuma kace wa Bayi na , su fadi kalma wacce take
mafi kyau. Lalle ne shaidan yana sanya barna tsakaninsu. Lalle ne shaidan ya
kasance ga mutum makiyi bayyanane.)Isra'i
53.
Ya Allah ka mana
ilhaman shiriyarmu ka kare mu daga sharrin kawunanmu.
Ina neman gafarar Allah
ku ma ku nemi gafararsa, don shi Mai gafartawa masu komawa a gare shi ne.
Huduba ta biyu
Dukkan yaba da godiya
sun tabbata ga Allah da yace : ( kuma ku
fadi magana mai kyau ga Mutane)
Bakara 83. Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke
bashi da abokin tarayya, shahadar da muke
fatan samun rabauta da maikyau a dalilinta, Na shaida kuma Annabinmu
kuma shugabanmu Muhammad Bawansa ne kuma Manzonsa ne, zababben Annabi,kuma
Manzo zababbe, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da
sahabbansa, salati mai wanzuwa da aminci mai biyo wa da yawa.
Bayan haka, Ya ku
musulmai:
Ku ji tsoron Allah
hakika mai tsoron Allah ya rabauta, shi kuma Mai sabo ya yi hasara.
(Ya ku wadanda ku ka
bada gaskiya ku ji tsoron Allah, kuma ku kasance tare da masu gaskiya)Tauba
119.
Ya ku Musulmai:
Hakika Allah ya hani
muminai zagin abin bautan mushrikai,
sabo da kar zagin nasu ya zama sanadin zagin Allah madaukakin sarki.
To zagin abin bautansu
zai kara musu kafirci da sangarcewa da gujewa, to sai zagin nasu ya zama ya
sabawa manufan Allah game da kira da manufa na sakonsa.
Allah madaukakin sarkin
yace : (kuma kada ku zagi wadanda suke kira, baicin Allah, har su zagi Allah
bisa zalunci,ba da ilimi ba.)An'Am 108.
Lallai a kiyaye dukkan
kiyayewa! Kada ku riski bayin Allah da kaushi da tsanani, da suka da tsinuwa da
zagi har ku kai su su guje wa gaskiya da sunnah da halaye masu kyau.
Ku bayyana gaskiya ta
hanyar hujja da dalili, da bayani cikin hikma da tausasawa tareda basira, kawai abin da ya wajaba a gare ku shi
ne : Nasiha, da umarni da hani, baakan ku shiryar da su da tankwara su ba da gyara su ba, ,Hisabinsu na gun Allah ba a kanku
ba,haka ma sakayyansu.
Ku yi salati da sallama
bisa ga Ahmad Mai shiryarwa, mai yi wa dukkan mutane ceto, duk wanda ya mishi
salati guda to Allah zai mishi salati goma dalilinta.
Ya Allah ka yi salati
da aminci ga bawanka kuma Manzonka Muhammad, Ya Allah ka yarda da dukkan iyalai
da sahabbai, mu ma ka hada da mu tare da su ya mai karamci ya Mai yawan kyauta.
Ya Allah ka daukaka
musulunci da Muslmai , ka kaskantar da shirka da mushrikai, ka rusa makiya
addini,ka sanya aminci da kwanciyan hankali ga wannan gari da sauran garuruwan
Musulmai.
Ya Allah ka datar da
shugabanmu jagoran al'amarinmu cikin abin da ka ke so kuma ka yarda da shi, ka
ja shi zuwa ga biyayya da tsoron Allah, Ya Allah ka datar da jagororin
al'amuran Musulmai su yi hukunci da shariarka, kuma su bi sunnar Annabinka
Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Ya Allah ka tseratar da
masu rauni cikin Musulmai ya Ubangijin talikai, Ya Allah ka tseratar da masu
rauni cikin Musulmai ya Ubangijin talikai, Ya Allah ka tseratar da masu rauni
cikin Musulmai ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka kashe
kafurai da suke saddu ga tafarkinka, masu gaba da masoyanka, ka sanya musu
azabarka, Ya abin bauta na gaskiya Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka bawa marasa
lafiyan mu sauki,ka bada lafiya ga wanda ka jarabce shi a cikinmu, ka saki kamammu na gurin yaki, ka jikan matattunmu,
ka taimake mu kan wanda ya yi gaba da mu, Ya Allah ka kawo aminci a iyakokinmu,
ka kiyaye sojojinmu, ka basu karfin guiwa, ka taimake su kan makiyin ka kuma
makiyinsu, Ya Ubangijin talikai, Ya Allah ka karbi matattunsu cikin shahidai,
ka kawo waraka ga wadanda suka ji rauni a cikin su.ya Mai karbar adua. Ya Allah
ka sanya aduarmu ta zama karbabbiya, ka sanya kiranmu ta samu daukakuwa, Ya Mai
girma ya mai jinkai ya mai karamci.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق