Hudubar
Masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na 23/11/1437 Ah
Da
sheikh Abdulmuhsin Bin Muhammad Alkasim
Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun
tabbata ga Allah muna gode masa kuma muna neman taimakonsa da gafararsa, kuma muna
neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu , duk wanda
Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi, kuma wanda Allah ya batar da shi
babu mai shiryar da shi, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah
Shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, kuma na shaida Annabi Muhammad
bawansa ne kuma manzonsa ne,tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da
iyalansa da sahabbansa da aminci
tabbatace mai yawa.
Bayan haka:
ku ji tsoron Allah ya ku bayin
Allah yadda ya cancanci a ji tsoronshi, ku yi riko da igiya mai karfi na
musulunci,
Ya ku musulmai!
Allah ya kebanta da halittawa, da gudanarwa da zabi, zabinsa na nuni ne
ga rububiyyarsa da dayantakarsa
madaukaki,da cikar hikimarsa da iliminsa da ikonsa, Hakika Allah madaukaki ya fifita tsakanin wurare da
zatuttuka, da ayyuka da wattanni, da dararraki da ranaku.
Mafi alherin halittu shi ne Annnnabi muhammmad tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi, kuma mafi alherin aiki shine kadaita Allah da bauta , mafi
daraja daga cikin watanni shine watan
ramadan, kuma mafi daukakan dare shi ne
daren lailatul kadri, mafi alherin rana
shine ranar suka (Babbar sallah) kuma mafi alherin wuri a gun Allah kuma mafi
soyuwa a gareshi shine makkah,Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi, ya ce: ( Wallahi lalle ke ce mafi alherin kasar Allah kuma mafi soyuwar kasa a
gun Allah madaukakin sarki kuma ba don an fitar da ni daga cikinki ba da ban
fita ba) Ahmad ne ya rawaito shi ,
ita ce uwar alkaryu kuma waninta
na biye mata ne, Allah ya rantse
da ita, don nuni ne zuwa ga girmanta sai
yace :(Ubangiji na rantsuwa da wannan gari (Makka), tare da rantsuwa ya kira shi da gari amintacce, sai ya ce; (
Da wannan gari amintacce).
Masallacin makka ne mafi daukaka cikin masallatayya, shi ne dakin farko
mai albarka da aka sanya a doron kasa don shiryar da mutane, : ( kuma lalle
ne daki na farko da aka aza domin mutane hakika shi ne wanda ke Bakka mai
albarka kuma shiriya ga talikai) Ali Imran 95
Abu Zarri Allah kara yarda a gare shi yace:( ya manzon Allah: wani
masalllaci ne aka fara aza shi
a doron kasa? Sai yace :( Masallacin ka'aba), sai nace saannan sai wanne? Sai yace (masalllacin
Aksa) Bukhari da muslim ne suka rawaito.
Allah ya shiryar da Annai Ibrahim
zuwa ga gina dakin kaba, a cikinta, Allah madaukakin sarki ya ce (Kuma
a lokacin da muka iyakance wa Ibrahim wurin dakin ) Hajj 26
Sai ya daga shi da dansa Annabi Isma'ila, kuma khalilin Allah ya roki a
jefa son Makka a zukatan mutane da farin
ciki lokacin zuwa gare shi sai ya ce (sai ka sanya zukata daga mutane ta
dinga karkata izuwa garesu) ibrahim '37.
Allah ya zabe ta domin mafi
karamcin manzanninsa, a cikinta ne aka haifi Annabi muhmmad tsira da amincin
Alla su tabbta a gare shi kuma acikinta ya taso kuma acikin ta aka turo shi,
kuma a cikinta aka fara sauko da wahayi da alkur'ani, Manzon Allah ya rayu a cikinta sama da shekaru hamsin, daga
nan kira na musulunci ta taso, kuma a nan ne mafi alherin mutane bayan Annabawa
wato sahabbai suka taso, daga nan ne aka yi tafiyan dare da shi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi zuwa ga masallacin Aksa.
Manzon Allah ya so shi so mai yawa, an kuma fitar da shi daga garin
makkan a halin tilasci, yayin da ya
sauka madina ya kasance yana adu'a (ya
Allah ka jefa mana son madina kamar yadda ka sanya mana son makka ko sama da
haka). Buhari da Muslim,ne suka rawaito shi . Gari ne mai aminci Annabi Ibrahim yayi mar addua na neman aminci sai ya
ce : (ya ubangiji na ka sanya wannan
gari amintacce ) Bakara 126
Allah yayi ma garin baiwa inda yake cewa, (Asai basu ganin mun sanya harami amintacce kuma
ana kaiwa mutane hari a kewayenshi )Ankabut
67.
Malam kurdubi Allah ya masa
rahama yake cewa : " lalle makka bata gushe ba cikin aminci kuma cikin alhurma daga masu dagun kai da
girgizan kasa da kuma sauran abubuwa na fitintinu da ke sauka a kasa.
Duk wanda ya shiga Masallacinta zai samu aminci irin nata Allah (Mai
tsarki da daukaka )yake cewa : ( Duk wanda ya shige shi zai kasance
amintacce) Ali Imran 97.
Allah ya sanya mata alhurma tun
lokacinda ya halicci sammai da kasa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gareshi ya ce: (lallai Allah ya sanya ahurma wa makka tun randa ya
halicci sammai da kasa, sai ta kasance tsararriya ce da alhurman Allah har zuwa ranan Alkiyama) buhari
ne ya rawaito.
Annabi ibrahim shi ya bayyana wa
halittu alfarmarta kamar yadda manzon
Allah Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,yake cewa: (lalle Ibrahim
ya haramta garin makka) Bukhari da muslim suka rawaito.
Annabinmu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana
girmamata, a ranan hudaibiyya yake cewa :( na rantse da wanda raina ke
hanunshi baza su tambayeni wata kudda ba wanda suke girmama Alhurman Allah a cikinta sai na basu ita ) Bukhari ne ya rawaito
Na daga cikin Alhurmanta akwai cewa : Zubar da jini a cikinta ba tare da
hakki ba ya fi muni da alfarma akan watan ta.
Manzon Allah Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce : (Baya
halatta ga mutumin da yayi imani da Allah da ranan lahira da ya zubar da jini a
cikinta) Bukhari da muslim ne suka rawaito.
Ba a tsorata mutanenta ta hanyan rike makami a cikinta manzon Allah Tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce : ( Ba ya halatta ga dayanku
ya riki makami a makka )muslim ne ya rawaito.
Haka dabbobi ma amintattu ne da amincin Allah a farfajiya ko fili, su
kuma tsuntsaye suna masu tafiya ne cikin jeji ) kuma itatuwanta na kadawa da aminci ba a sare ta, kuma baa tsintuwan batattun dukiya a a cikinta kamar sauran garurruka manzon Allah Tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi, ya ce : (ba a
tsinke danyen itaciyarta haka nan kuma ba a yanke bishiyarta sa'annan kuma ba a
kora abin farawtarta haka nan kuma ba a tsintuwan abin tsintuwan cikinta sai ga
wanda zai nemi me shi)Bukhari da muslim ne suka rawaito.
Manzon Allah ya kamanta alhurman
dukiyoyi da mutunci da kuma jini saboda
girman hurumcinta Allah Madaukakin sarki ya ce : (lallai jininku da dukiyoyinku da mutuncinku haramtacce ne a gareku kamar
haramcin wannan rana naku a wannan gari naku kuma da wannan wata naku ) Buhari
da muslim ne suka rawaito.
wanda yayi niyyan aikata mummuna
a cikinta Allah zai azabtar da shi Allah Madaukakin
sarki ya ce : (wanda yayi nufin aikata aikin
ilhadi a cikinsa da zalunci zamu dandana masa daga wata azaba mai
radadi ) Hajji 25
Dan masud -Allah kara masa yarda
– " ya ce : Da wani mutum zai yi nufin ilhadi kuma yana garin Adan Da Allah ya dandana masa azaba mai radadi ".
kuma mai zalunci a cikinta shi ne wanda Allah yafi ki a cikin mutane, Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
) ya ce : (wanda Allah ya fi ki a cikin
mutane shi ne mai ilhadi a harami ) Buhari ne ya rawaito.
Saboda girman alhurmanta mushriki baya taka kasanta, sai Allah ya ce : (lallai mushrikai masu najasa
ne kar su kusanto masallacin harami)Tauba 28.
kuma dujjal shine ya kafurce wa
Allah yana fitinan mutane a addininsu, sai Allah
ya hana shi shiga makka da
madina,Manzon Allah (Tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ) ya ce (Babu
wani gari da dajjal baya takawa sai Makka da Madina )Bukhari da Muslim ne
suka rawaito.
Allah ya kiyaye makka kuma zata
cigaba da zama cikin kiyayewar Allah,
duk wanda ya nufe ta da mummuna Allah
zai halaka shi, mutanen giwaye sun nufe ta da sharri, sai Alla ya kangesu kuma ya sanya su suka zama
aya da darasi har zuwa ranar sakayya,
wasu mutane zasu yaki garin ka'aba har sai
idan sun kasance a wata sahara sai Allah ya kisfe na farkonsu har zuwa na karshensu) Bukhari ne ya rawaito.
Kamar yadda Allah ya sanya aminci a cikinta, ya yi falala ga mutanenta
da alhkairu da 'ya'yan itace, duk da cewa tana kwari ne a tsakanin duwatsu biyu
wanda ba shuki, duwatsu ne ke kewaye da
ita ta kowani gefe, kasar da gu ne da zaa tsammaci yunwa, sai Ibrahim ya yi
adua ga mutanenta da a azurta su da 'ya'yan itace, kamar yadda Allah ya azurta
garuruwa masu ruwa, da shuki, sai yace :
(kuma ka azurta mutanenta da yayan itace )Bakara 126.
sai Allah ya amsa da cewa (
shin bamu tabbatar musu da mallakr hurumi ba ya zama amintacce ana jawowa zuwa
gare shi 'ya'yan itace kowani irin bisa ga azurtawa daga garemu?)Kasas
57.
A'a ai Annabi Ibrahim ya mata adduan
albarka a cikin kwanon awunta da mudunta, wato cikin abin shanta da abincin ta,
Na daga cikin Adduar Annabi tsira
da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce (ya Allah ka sanya a madina
ribin Abinda ka sanya a makka na Albarka )Buhari da muslim ne suka rawaito.
Ya shayar da mutanen ta ruwan da ba irin shi a doron
kasa, wanda mutane na fatan samun ko dan kadan ne daga gare shi. Ruwan zamzam
ruwa ne mai albarka kuma abin ci ne Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce : :( lallai ruwa ne mai albarka kuma abin sha ne
mai dadano ) muslim ne ya rawaito
har ila yau waraka ne daga dukkan cuta manzon Allah Tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi, ya ce(zam zam abinci ne kuma abin sha ne waraka
ne kuma ga cuta ) Muslim ne ya rawaito.
Malaika ya tsaga kirjin Annabi tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya wanke shi da ruwan zamzam.) Bukhari ne ya
rawaito
Samuwar arziki da kuma aminci a
cikinta abubuwa ne da za su sa a bauta wa Allah shi kadai, Allah Madaukakin sarki ya ce: ( su bautawa
ubangijin wannan gida (kaba)* wanda ya ciyar da su (ya hanasu daga yunwa kuma
ya amintar da su daga wani tsoro )) kuraish 3-4
Allah zai tunkude sharri daga
mutanenta a dalilin girmama daki da suke yi a cikinta da kuma kadaita
Allah, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Allah
ya sanya ka'aba daki me alfarma rayuwa ga mutane ) Ma'ida 97.
Ibnu kasir ya ce : wato ze dauke musu mummuna sakamakon girmama
fiskantanta,
Makka gari ne mai albarka
alherinta gamamme ne, da na daga cikin
Albarkanta ribanya sallah a cikinta don (sallar mutum a masallacin ka'aba ya
fi sallah dubu dari a waninsa ) Ahmad ne ya rawaito, yin dawafi a dakin ka'aba ibada ne kuma ba za
a hana wani ba daga cikin mutane cikin dare ne ko wuni Allah ya ce (kuma suyi dawafi a daki
dadedde ) Hajj 29
wuraren nata alamomin addini ne kuma
wurarene na bauta ga musulmai, Allah ya wajabta
musu fiskantanta kuma ya sanyata
daya daga cikin rukunnan musulunci ,
matafiyi zuwa Masallacinta na samun lada, Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata agareshi ya ce : (ba a nika gari zuwa ga kowani masallaci sai guda uku masallacin ka'aba da masallacin
Manzon Allah da Masallacin aksa) Bukhari da muslim ne suka rawaito.
Babu wani wuri a doron kasa da
ake kewaya shi da sunan ibada sai dakin ka'aba haka kuma ba wani wuri a duniya
da aka shar'anta sumbatan shi, sai Hajarul
– Aswad, da ke ka'aba, rukunul yamani na ka'aba ake shafa wa.
Allah ya sanya ka'aba wurin neman
lada, da kuma wurin komawa kuma da
aminci gare ta ne mutane ke
cacarindo shekara bayan shekara daga
kowani sako mai zurfi, rayuka na begensa
kuma zuciya na kwadayin zuwa gare shi a duk lokacin da suka ziyarce ta sai begensu
ya karu zuwa gareta. Annabawa sun nufe
shi , Annabi Musa da Annabi Yunus da Annabi Muhammad sun yi hajji, Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gareshi ya ce; (kamar gani ina ganin Musa (Amincin Allah
ya tabbata a gare shi) yana sauka daga tsakanin duwatsu ya na mai kakan da kai
zuwa ga Allah da talbiya, kamar ina dubi zuwa ga yunusa dan matta Amincin Allah
ya tabbata agare shi ya na kan jar taguwa a halin yana mai talbiya) Muslim ne ya rawaito.
Allah ya daukaka wannan daki ya jingina shi zuwa gare shi,
kuma ya sanya shi wurin daukaka tauhidi da haskaka shi, ya yi umarni da a
tsarka ke shi daga dukkan wani abu da zai kishiyanci hakan na daga gumaka da
bauta musu, sai ya ce (ka tsarkake dakina don masu dawafi da masu tsayuwa da
masu yawan ruku'u da sujada) Hajj 26
Ya sanya zuwa gare shi ya zama kankara ne ga zunubai da
kusakurai da suka shude, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a
gareshi ya ce : (wanda yayi hajji a wannan dakin kuma bai yi jimai ba, kuma
bai yi fasikanci ba zai dawo kamar yadda mahaifiyarsa ta haife shi
) Bukhari da muslim ne suka rawaito.
Allah bai yarda da wani lada
ga wanda ya ziyarci ka'aba ba koma bayan Aljanna ba, Annabi Tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi, ya ce :( Daga umra zuwa wata umra kankara ne ga zunubai, aikin
hajjin da aka yi da'a bai da sakamako sai aljanna ) Bukhari da muslim ne
suka rawaito.
kuma shi ne
alkibila na mutanen doron kasa baki daya,kuma
dukkan musulmi na fiskantan shi sau da dama a kowani rana Allah Madaukakin sarki ya ce : ( sai ka
juya fiskarka wajen masallaci tsararre kuma inda duk kuka kasance to ku juyar
da fuskokinku jiharsa)Bakara 144.
Wanda ya mutu cikin musulmai za'a fiskantar da
kabarinsa zuwa gare shi.
Ubangiji mai
tsarki ya sanya masa alhurma ba a
fiskantan jihar shi yayin fitsari ko kuma ba haya, Manzon Allah Tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi, ya ce : (kada ku fiskanci alkibila da bahaya ko bawali
sai dai ku fiskanci gabas ko kuma yamma )Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
zuwa gareshi ne
ake kora hadaya da kuma abin da za a
nemi kusanci zuwa ga ubangiji Allah Madaukakin
sarki yake cewa : (sa'annan kuma wurin halatta ta zuwa ga dakin yantacce ne )
Hajj 33
A dakin kaba akwai ayoyi bayyanannu, lallai yana daga
cikin ginin Ibrahim, akwai Makama
ibrahima, Amincin Allah ya tabbata a gare shi, Allah ya ya umarce mu da mu mu
rike shi gurin sallah, a dakin Allah mai girma akwai Hajarul Aswad (ya sauko daga Aljanna a halin ya fi nono fari,sai
kusakuran bani adam ya bakanta shi) Ahmad ne ya rawaito shi.
shi dutse ne da baya amfanarwa ko kuma cutarwa, kawai dai ana sumbatan shi domin bin
sunna na Annabi Tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi, sayyidina Umar Allah ya kara masa yarda ya ce : (lallai
ni na san kai dutse nebaka cutarwa kuma baka amfanarwa ba don na ga Annabin Allah yana sumbattanka ba da ba zan sumbanceka
ba ) Bukhari da Muslim suka rawaito.
A Masallacin ka'aba akwai Safa da Marwa, suna daga cikin manyan alamomi na ibada
wajibi ne a girmamasu a kai komo a tsakaninsu.
A dakin Allah
akwai zamzam,abin lura ne kuma aya ne cikin yawansa da albarkansa da amfaninsa.
Kuma Bayan Ya ku Musulmai:
Dakin Allah an gina shi ne don bautawa Allah shi kadan shi
bashi da abokin tarayya, yana daga cikin
wuraren da ake karban tuba, kuma ake komawa zuwa ga Allah,
ga duk bawa ya nufi wannan masallaci na ka'aban
yana mai kankan da kai da rusunawa ga Allah yana mai neman kusanci zuwa ga mai
tsarki Madaukakin sarki don neman a yafe masa zunuban shi. Wajibi ne akan bayi
su girmama dakin Allah, don girmama abin
da Allah ya girmama na daga cikin tsoron Allah, a cikin hakan akwai gyaruwan Musulmai a cikin addininsu da duniyansu.
Duk wanda yayi hidima wa Masallatai biyu masu alfarma, da
alhazai da masu umrah da masu ziyara, to sakayyansa fa yana wurin Allah ne mai
girma, dukkan Masallatan biyu Annabi ne
ya gina su, kuma suna cikin guraren ibada a gurin Allah,
Ina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan abin
jefewa.
(Kace) An umarce ni in bautawa Ubangijin wannan
gari, wanda ya mayar da shi Hurumi, kuma yana da dukkan kome. Kuma an umarce ni
da na kasance cikin masu mika wuya.) Namli 91.
Allah mini albarka ni da ku cikin Alkur'ani mai girma,
kuma ya amfanar da ni da ku da abin da ke cikin shi na ayoyi da ambato mai
hikima, Ina fadin wannan bayanan nawa kuma ina neman gafarar Allah wa ni da ku
da dukkan musulmai daga dukkan zunubai, ku nemi gafararsa don lalle shi mai
gafara ne mai jinkai.
Huduba ta biyu
Dukkan yabo sun tabbata ga Allah bisa kyautatawarsa, da kuma godiya bisa ga
datarwan shi da baiwarsa, Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi
kadai bashi da abokin tarayya muna masu girmama sha'aninsa kuma na shaida lalle
Annabinmu Muhammadu bawansa ne kuma
manzonsa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da iyalansa da
sahabbansa kuma da tsira tabbatacciya mai yawa.
ya ku
musulmai:
A wannan gari mai albarka amintacce musulmai suna sauke
hajjinsu suna masu tsiraituwa daga dukkan wasu abubuwa na duniya da kwadaye
kwadayenta, suna mika kawunansu ga Allah kuma suna masu bauta mishi kuma suna
neman a 'yanta su, tawhidi ya hadasu kuma kuma Imani ya tausasa zukatansu ya
hada su, suna masu bayyana da'a ga Allah
madaukakin sarki suna masu kankan da kai
kuma suna jayuwa a tafarkin Allah, suna masu nuna talaucinsu ga Allah suna
neman bukata a wurin shi kuma suna rokon Allah, kuma suna masu yawan ambaton
Allah halin zaman gida ko tafiya.
A wurare na ayyukan ibada na aikin hajji akwai abin
lura da kuma wa'azuzuka, dukkan mutane a wurin Allah daya suke,ma' aunin shi ne tsoron Allah, haka nan kuma a wurin ihrami
da kuma tattaruwan mutane akwai tunatar
da su, game tattaruwan da zasu yi a matattara wato ranar alkiyama, wanda za'a
karbi nashi shine wanda ayyukansa ya kasance yayishi da ikhlasi don Allah bai
cakuda shi da shirka ba, ko riya ko
rashin bin sunnar Annabi, lokutan hajji
na da tsada, kuma wanda ya samu dace shi ne wanda ya ribaci wannan lokutan ta
hanyan yawaita ambaton Allah da kuma Ayyuka na kwarai.
Sa'annan ku sani lallai Allah ya umarce ku da salati da
aminci ga Annabinsa , sai yace cikin
Alkur'ani : ( Lalle Allah da Mala'ikunsa suna salati ga Annabi,
ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da sallama tabbatacciya.)
Ahzab 56.
Ya Allah ka yi salati da aminci da albarka bisa ga Annabinmu Muhammad,
Ya Allah ka yarda da khalifofinsa shiryayyu, wadanda suka yi shude akan gaskiya
kuma da ita suke hukunci: Abubakr, Umar, Usman, Ali, da sauran sahabbai baki
daya, ka hada mu da su cikin kyautar ka da karamcinka ya mafi karamcin masu
karamci.
Ya Allah ka daukaka musulunci da musulmai, ka kaskantar da shirka da
mushrikai, ka ruguza makiya addini, ka sanya wannan gari cikin aminci da
kwanciyar hankali da yalwa da suran
garuruwan musulmai.
Ya Allah duk wanda ya nufe mu ko ya nufi gidajenmu ko ya nufi musulmai
da mummunar manufa to ka shagaltar da shi da kansa, ka sanya kaidinsa a
makasansa, ka jefa tsoro cikin zuciyarsa ya mai karfi ya mabuwayi.
Ya Allah ka amintar da Alhazai da masu Umra, ya Allah ka sanya Hajjinsu
karbabbe, aikinsu abin godiya, da aikinsu
karbabbe, ya maabocin daraja da karramawa, ya Allah ka gyara musu
niyoyinsu da zuriyarsu, ka saukar musu da kwanciyar hankali da natsuwa, da
khushu'I da kankan da kai gare ka ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka gyara halin musulmai a ko ina, ya Allah ka amintar da
iyakokinmu, ya Allah ka karfafi zukatan sojojinmu, ya Allah ka datar da jifansu, Ya Allah ka basu nasara mai karfi,
ya ma'abocin daraja da daukaka.
Ya Allah ka datar da jagoranmu zuwa ga shiryarwarka, ka sanya aikinsa
cikin yardarka.
Ya Allah ka datar da masu hidima ga Masallatayya biyu masu alfarma, ka
daga ladansu, ka sanya su cikin masoyan bayinka, ya ma'abocin daraja da
daukaka.
(Ya Ubangiji ka bamu kyakyawa a nan duniya da kyakkyawa a lahira kuma ka
kare mu daga azaba na wuta.) Bakara 201
Ya ku bayin Allah: (Lalle Allah na yin umarni da adalci da kyautatawa da
bai wa ma'abocin zumunta. Kuma yana hani ga alfahasha da abin da aka ki da
zalunci, yana muku gargadi ko zaku waazantu). Nahl 90
Ku ambaci Allah mai girma da daukaka zai ambace ku, ku gode mishi bisa
ni'imominsa zai kara muku, kuma ambaton Allah ya fi girma Allah ya san abin da
ku ke aikatawa.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق