الأحد، 29 يناير 2017

FALAL RANAKU GOMA NA FARKON ZUL HAJJI NA SHAIKH ALI ABDURRAHMAN ALHUZAIFI (7 ZUL HAJJ ) 1437

Hudubar Juma'a a Masllacin Annabi tare da sheikh Aliyu dan  Abdurrahman Alhuzaifi 7/12/1437
Hudubar Farko:
  Yabo da godiya  sun tabbata ga Allah,  (Dukkan Godiya da yabo  sun  tabbata ga Allah wanda ya halicci sammai da kasa ya kuma sanya duffai  da haske) An'ami 1,
 kuma ya shar'anta shario'i, rahama ga bayi domin lada ya yawaita ga talikai kuma ya tunkude musu ukuba da dukkan sharri, ina yabo ga ubangiji na kuma ina gode mishi kuma ina tuba gareshi, kuma ina neman gafaran shi, kuma na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ne bashi da abokin tarayya masani ga abin da ke cikin zukata, kuma na shaida Annabin mu kuma shugabanmu  Muhammad (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)  bawansa ne kuma Manzonsa ne, mai kira zuwa ga dukkan aiki na biyayya. ya  Allah kayi salati da sallama da albarka wa bawanka kuma manzonka  muhammad da iyalansa da sahabbansa wadanda suka taimaki addinin Allah Madaukaki, har dukkan  mushrikai masu yawan kafurci su ka rusuna masa.
 Bayan haka : ku ji  soron Allah madaukaki, da gaggawa  zuwa  ga ayyukan Alheri, da nisantan haramtattun abubuwa, don shi Ubangiji madaukaki ya cancanci a kiyaye dokokin shi a  ji tsoron shi, ba wadanda zasu rabauta sai masu tsoron Allah, ba hasararru sai wadanda suka juya baya su ka sa shakku a addinin Allah.
Ya ku musulmai!
    Lalle kuna cikin ranaku masu albarka da falala, sauran kwanakin nan  goma  da Allah ke ribanya ladan ayyuka na kwarai, yana kyale tuntube da aka yi a cikin su, kuma yana karban uzuri daga wanda ya bada uzuri, kuma Allah na karbar tuban wadanda suka tuba, ya yafe zunuban masu neman gafara.
An karbo daga Abdullahi dan Abbas Allah kara musu yarda,yce ; Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce;  (Ba wasu ranaku da ayyukan alheri ya fi soyuwa a gurin Allah  kamar wadannan ranaku goma) sai su ka ce har da jihadi? Sai yace : har da jahadi, sai dai mutumin da ya fita da ransa da dukiyansa bai dawo da komai ba.) Buhari ne ya rawaito.
An karbo daga Abu Huraira Allah kara yarda a gare shi yace :  daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: ( Ba wasu ranaku da ya fi soyuwa ga Allah da a yi bauta a cikin su kamar goman farko na zulhajji, azumin kowani rana na daidai da azumin shekara, tsayuwan kowani dare na daidai da tsayuwan daren lailatul kadri,) Tirmizi da Ibnu maja da Baihaki,
 A cikin wannan goman akwai ranar arafa, wanda Allah ya yalwata alheri a cikinta, falala da albarka na sauka a cikinta, da rahama ga wanda ya halarce ta, kyautayin  Allah da karamcinsa na kwarara ga dukkan musulmai  a doron kasa, a wannan wunin,
An karbo daga Abu katada Allah kara yarda a gare shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: (an tambaye shi game da azumin ranar Arafa sai yace : yana kankare zunuban shekaran da ta gabata da mai zuwa,) Muslim ne da Abu Dawud  suka rawaito.
An karbo daga Aisha Allah kara yarda a gare ta, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Babu wata rana da Allah ya ke yawaita 'yanta bayi daga wuta kamar ranar arfa, lalle Allah na kusantowa ya bayyana, sannan ya yi tinkaho da su a gaban mala'iku, sai ya ce: me wadannan ke bukata?) Muslim ne ya rawaito da Nasai.
Daga Abdullahi dan Umar Allah ya kara yarda a gare su, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: ( Idan yammacin Arafa ya yi ba wanda zai rage cikin wadanda akwai kwayan zarra na imani a zuciyarsa  face Allah ya gafarta masa, sai na ce ya manzon Allah ya kebanci mutanen Arafa ne kadai? Yace : a 'a , ga dukkan musulmai! ) Dabarani ya rawaito a Al- Kabir.
An karbo daga ubada dan samit  Allah ya kara yarda a gareshi  kan lallai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a greshi ya ce  : (Annabi ya ce a ranan arfa :ya ku mutane ! lallai Allah ya muku falala a wannan rana ya gafarta muku, sai dai nauyin wani da ke kan  wani a tsakaaninku (Hakkoki)  kuma yayi kyautan( ceton) masu musgunawanku ga masu kyautatawanku, ya bawa mai kyautatawanku abin da ya roka, to ku tunkude, idan ya kasance a muzdalifa sai ya ce :lalle Allah ya gafartawa na kwarai a cikin ku , kuma na kwaranku zasu yi  shafa'a ga na banzanku, rahama na sauka gare ku ta game su, sai a raba gafara a doron kasa sai ta sauka kan duk wanda ya tuba cikin  wanda ya kiyaye harcensa, da hannunsa,kuma  iblis da rundunarsa na kan dutsen Arafa, suna sauraron abin da Allah zai yi , idan an saukar da gafara sai ya yi yekuwa shi da rundunarsa suna ( wayyo azaba ta da Halaka, na kasance ina ingiza su wani lokaci, sannan gafara ta zo ta lullube su, sai su rarraba suna wayyo Allah mun boni mun lalace.) Dabarani ne ya rawaito a Al kabir.      Tsayuwan Arfa shi ne rukuni mafi girma a hajji, Ayyukan hajji da aduo'in  alhazai na game dukkan musulmai a doron kasa.  kai ai manyan Ibadoji da alamomi na hajji suna amfanar da kasa baki daya. Sai Allah ya tunkude azaba da ita ko ya sasssauta zunubansa. Allah madaukakin sarki ya ce:( Allah ya sanya ka'aba daki mai alfarma rayuwa ga mutane al'amarin addininsu na hajji yake mikewa sabo da shi,) Ma'ida 97.
Al Bagawi Allah ya jikan sa ya ce: Ai abin da zai mikar musu da addininsu da duniyarsu.
Allah madaukakin sarki ya ce : ( Kuma ba domin tunkudewar Allah ga mutane sashinsu  da sashe ba lalle ne da kasa ta baci, kuma amma Allah maabocin falala ne a kan talikai) Bakara 251
Al- Bagawi ya ce a tafsirinsa:  ba don tunkudewar Allah ga muminai masu biyayya ba daga kafurai da fajirai ba da kasa ta halaka da wanda ke cikinta, sai dai Allah na tunkudewa kafiri a dalilin muminai haka yana tunkudewa fasiki a dalilin salihin bawa.) ya tike.
Bayan Arafat akwai ranar babbar sallla da ranakun tashrik sune mafi alherin ranaku a gun Allah madaukaki, ya shar'anta ayyuka na kwarai da Allah ke ribanya lada da su, da kuma irin abin da Allah zai tseratar na daga azaba, A ranar babbar sallah Allah ya hada mafiya yawan ayyukan hajji a cikinsa, sune jifa da yanka da aski da dawaful ifada, kuma bisa wannan tsari ya fi, amma in da zaa fara gabatar da wani kafin wani, to ba laifi sai dai an bar abin da ya fi. sabo da manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a ranar babbar sallah baa tambaye shi ba game da wani abu da aka kaddamar ko aka jinkirta ba face ya ce ku yi ba laifi.
Kuma Allah ya ambaci ranar babbar sallah da Ranar babban Hajji.kuma yana cikin mafi alherin ranaku a gurin Allah madaukaki. Ranar sha daya ga wata ke bi masa, shi ake cewa  ranar ALKAR, da ranaku biyu da ke bi masa shine cikaton ranakun Attashrik , ya shar'anta sauran ayyukan hajji kamar yadda aka shar'anta yawan ambaton Allah ga alhaji da waninsa.
Daga Abdullah dan kurad Allah ya kara yarda a gare shi, daga Annabi  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:  Mafi alherin ranaku a gun Allah shi ne ranar suka, sai ranar Karr) Tabarani da Ibn  Hibban suka rawaito.
 Ku godewa Allah bisa abin da ya yalwata muku na ni'ima, da abin da ya shar'anta muku na sabuban rahama. Ku girmama albishirin da Allah ya yi mana, ku karbe ta da farin ciki da yakini, Alkawarin Allah mai kasancewa ne ba sabawa,  Allah madaukakin sarki yace : (saannan kuma abin bautawar ku Abin bautawa ne guda, sai ku sallama masa kuma ka yi bushara ga masu kankantar da kai. Wadanda su ke idan an ambaci Allah sai zukatansu su firgita da masu hakuri akan abin da ya same su da masu tsayar da sallah, kuma suna ciyarwa daga abinda mu ka azurta su ). Hajj 34-35.
Allah madaukakin sarki ya ce:  kuma ku gabatar da alheri sabo da kan ku, ku ji tsoron Allah kuma ku sani cewa lalle ne ku masu haduwa da shi ne, kuma ka yi albishir ga muminai)
Ku gaggauta ayyuka na kwarai kafin zuwan ajali, da katsewar ayyuka, domin duniya gida ne na rudi, matattara nena  musibu da sharri, ku dubi yanda ta yi da masu kwadayinta, da kuma yadda ta shelanta rabuwa da su, ba gida ne na dawwama ba, ko ni'ima na dindindin ba, gidan mumini ita ce gidan aminci gidan ni'ima da zama  wanda bai sauyawa ko gushewa, ku yi aiki don ita game da abin da Allah ya kira ku zuwa gare shi ku yi nesa da abin da Allah ya gargade ku ga me da shi, kamar ga ku da ranaku sun juya baya, ga lokacin mutuwa ya yi, to a wannan lokacin ne kowa zai yi da na shina, Me kyautatawa zai yi fatan ace ya kara aikin alheri, mai sabo zai yi kaito da nadama sakamakon tafiyarsa da ba guzuri, ya ku musulmi a wadannan ranaku, duk wanda Allah bai nufe shi da hajji ba, to Allah ya shar'anta mishi kofofi na da'a da ayyukan kwarai masu yawa  da zai riski wanda ya sha gaban shi, ko ya cin ma wanda ya yi mar fintinkau, da izinin Allah madaukaki, wanda aka datar da shi da yin hajji to ya godewa Allah madaukaki, ya kuma kyautata wa kansa ta hanyar aikata daa da barin abin da aka ki, ya zuba alheri nsa ya kame daga sharrinsa ya kiyaye dokoki na wannan farilla, kuma ya godewa Allah bisa abin da ya saukake masa na sabuba, da kuma irin baiwa da Allah ya yi wa Alhazai na daga aminci da imani, da saukin arziki, da saukake abubuwa masu wahala, to godiya ta tabbbata ga Allah bisa ni'imarsa na bayyane da na boye. Godiya tana gare shi a cikin duniya da lahira, Allah madaukakin sarki ya ce : ( sabo da haka Kuma ku ambace ni na ambace ku kuma ku yi godiya gare ni kuma kada ku butulce mini)  Bakara 152
Allah ya saka wa wannan kasa mafi alherin sakayya,  bisa abin da ta ke tashi da shi na hana kansu barci don Alhazai su samu hutu, haka ma masu umra da ziyara. Da kuma kulawa da take ba su ta bangaren lafiya. Da saukake musu duk wata hidima da kawo zaman lafiya, da abin da ake gani a kowace  shekara na daga tsare tsare da ta cin ma, na ban mamaki wanda ya bawa duniya mamaki,cikin ayyukan hajji don neman lada, muminai na farin ciki da haka,
Allah Madaukakin sarki ya ce : ( Ku yi gaggawa  zuwa ga gafara daga Ubangijinku da Aljanna da fadinta (daidai) da sammai da kasa ne, an yi tattalinta domin masu takawa. Wadan da suke ciyarwa a cikin sauki da tsanani, kuma suke masu hadiyewar fushi, kuma masu yafewa mutane laifi kuma Allah ya na son masu kyautatawa.) Al Imran 133-134.
Allah sa min albarka ni da ku cikin Alkur'ani mai girma.kuma ya amfanar da ni da ku da abin da ke ciki na ayoyi da ambato mai hikima, kuma ya amfanar da mu da shiryarwar shugaban Manzanni, da fadinsa mikakke, abin da na fadi kenan ina nemawa kai na da ku gafara daga dukkan zunubai. Da sauran musulmai daga dukkan zunubai, to ku nemi gafararsa don shi mai gafara ne mai jinkai.
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga maaboci buwaya da daukaka, maabocin girmame girmame, mai girma madaukaki, ina yabon Ubangiji na ina gode masa ina tuba zuwa gare shi, kuma ina neman gafararsa, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya,mai tsananin hila, na shaida Annabin mu muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wanda Allah ya tsamar da dan Adam  ta hanyarsa daga bata.
Ya Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammad da Sahabbai da Iyalai, bayan haka! Ku ji tsoron Allah madaukaki yadda ya dace a ji tsoronsa, duk wanda ya ji tsoronsa zai kare shi daga abubuwa masu halakarwa, a duniyarsa da lahirarsa,
Ya ku bayin Allah ! ku tuna abin da Allah ya muku na niima cikin farillai na hajji, na daga 'yan uwantaka na musulunci, da madauri na imani, da hadin kai na mafiskanta da ke kawo hadin kai na zuciya, da hadin kai na sahu  da ke haifar da yada rarrabuwa da sabani, Allah madaukakin sarki ya ce :( kuma  ku kankame   igiyar Allah gaba daya  kuma kada ku
Rarraba) Al imran 103.
Allah madaukakin sarki ya ce: (su muminai 'yan uwan junane a cikin addini) Hujurat 10.
Allah madaukakin sarki ya ce: (ya ku mutane hakika mun halicceku daga namiji da mace kuma muka sanyaku dangogi da kabiloli domin ku san juna lalle mafificinku daraja a wurin Allah shi ne  wanda yake mafificinku a takawa) Hujurat 13
. Kuma ku tuna wasiyoyin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shida hudubarsa a hajjin ban kwana : na daga cikin abin da aka kiyaye daga gare shi a wannan hajji tsira da amincin Allah su tabbata a gare  shi  fadinsa : Ku bauta wa ubangijin ku, ku yi sallolinku biyar, ku azumci watanku, ku yi biyayya ga mai jagorantar ku za ku shiga aljannar ubangijinku ) Ahmad ya rawaito daga hadisin Abu Umama Allah kara yarda a gare shi.
Ya ku bayin Allah !
( lalle Allah da malaikunsa suna salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce.
Ku yi salati da sallama ga shugaban mutanen farko da na karshe, kuma shugaban manzanni.
Ya Allah ka yi salati ga Annabi Muhammad da iyalan muhammmad kamar yadda ka yi salati ga Ibrahi da  iyalan Ibrahim, Lalle kai mai godiya ne kuma abin girmamawa.
Ka yi dadin tsira mai yawa.
Ya Allah  ka yarda da sahabbai baki daya. Da tabian da wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar hisabi,
Ya Allah ka yarda da mu tare da su da baiwanka da karamcinka da  rahamarka ya mai tausayin masu jin kai.
Ya Allah ka gafarta mana abin da muka gabatar da abin da muka jinkirtar da abin da muka boye da abin da muka bayyana da abin da kai ka fi mu sanin shi a kanmu, kai ne mai gabatarwa  kuma kai ne mai jinkirtarwa ba abin bautawa da gaskiya sai kai.
Ya Allah ka gafartawa matattun mu da matattu cikin musulmai,
Ya Allah ka gafartawa matattun mu da matattu cikin musulmai, da rahamarka ya mafi rahamar masu rahama.
Ya Allah muna rokonka maaboci daukaka da girmamawa,
Ya Allah muna rokon ka da ka dushe wutar fitina mai batarwa  tsakanin musulmai ya ubangijin talikai.
Ya Allah muna rokon ka da ka dushe wutar fitina mai batarwa  tsakanin musulmai ya ubangijin talikai.
Ya Allah ka hada zukatar musulmai ka gyara tsakaninsu.
Ya Allah ka azurta mu da musulmai fahimtar addini, Ya Allah ka azurta mu da musulmai fahimtar addini, da rahamarka ya mafi tausayin masu tausayi.
Ya Allah ka kyautata karshenmu a dukkan al'amura, ka kare mu daga walakancin duniya da azabar lahira, ya maabocin girma da karramawa.
Ya Allah muna neman tsari daga mummunar abin da aka kaddara, da kuma dariyan makiya, da kuma fadawa ramin tsiya, da matsanincin bala'I,
Ya Allah ka yaye bakincikin muminai  daga cikin musulmai, Allah ka biya bashi ga wadanda ake bin bashi cikin musulmai,
Ya Allah ka bada lafiya ga marasa lafiyan da marasa lafiyan musulmai, Ya Allah ka bada lafiya ga marasa lafiyanmu, ka taimake mu kan wadanda suka riki gaba da mu, da rahamarka ya mafi jinkan masu jinkai,
Ya Allah ka kare mu da zuriyarmu daga iblis da zuriyarsa da shaidanunsa,da rundunarsa da masoyansa, ya Ubangijin talikai, Ya Allah ka kiyaye mu daga sharrin kawunanmu, da munanan ayyukanmu, Ya Allah ka kiyaye musulmai da zuriyarsu daga Iblis da zuriyarsa, ya Ubangijin talikai, da rahamarka ya mafi jinkan masu jinkai,
Ya Allah ka kiyaye sojojinmu, Ya Allah ka kiyaye sojojinmu, kuma ka datar da su, Ya Allah ka kiyaye iyakokinmu, Ya Allah ka kiyaye kasarmu daga azzalumai masu ketare iyaka, da rahamarka ya mafi jinkan masu jinkai, ka kashe fitintinu masu batarwa,  ga musulmai ya Ma'abocin daukaka da karramawa,
Ya Allah ka kiyaye musulmai daga sharrin makiya musulunci, ya Ubangijin talikai, Ya Allah ka lalata shirin makiya musulunci, da suke kullawa musulunci da musulmai, ya maaboci girma da daukaka,
Ya Allah ka kame sharrin munafukai, domin lalle kana da iko ga dukkan komai,
Ya Allah muna neman tsarinka daga rarrabuwa da munafunci da munanan dabi'u,
Ya Allah ka jefa tsoron Allah a zukatanmu, ka tsarkake su kai ne mafi alherin wanda zai tsarkake su,
Ya Allah muna rokon ka aljanna da abin da zai kusantar da mu gare ta na fadi ko aiki,
Kuma muna neman tsarinka daga wuta da abin da zai kusantar  da mu gare ta na fadi ko aiki,
Ya Allah ka datar da Kadimul haramaini(shugaban kasar saudiya) cikin abin da ka ke so kuma ka yarda da shi, Ya Allah ka shiryar da shi zuwa ga shiriyarka, ka sanya aikin shi cikin yardardarka ya Ubangijin talikai, ya Allah ka taimake shi akan dukkan alheri, ka datar da shi ra'ayoyinsa ya Ubangijin talikai,
Ya Allah ka datar da mataimakansa guda biyu cikin abin da akwai alheri da daukaka ga musulunci da musulmai, ya Ubangijin talikai,
Ya Allah ka karbawa alhazai ayyukansu kuma ya Allah ka kiyaye su,ya Ubangijin talikai,
Ya Allah ka maida su garuruwansu cikin aminci da nasara suna halin ka gafarta musu zunubansu, ya Ubangijin talikai, kuma ka saukake musu al'amuransu.
Ya Allah muna rokonka ya ma'aboci daraja da daukaka, ka isarwa musulmai sharrin masharrata da makircin munafukai da mutanen banza, Ya ma'aboci daraja da daukaka.
Ya ku bayin Allah!
(Lalle Allah na yin umarni da adalci da kyautatawa, da baiwa ma'abocin zumunta, kuma yana hani da alfahasha da abin da aka ki da zalunci, yana muku wa'azi don ku wa'azantu.) Nahl 90.
Ku ambaci Allah mai girma da daukaka



  




ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق