الأحد، 29 يناير 2017

TAUSASA ZANCE NA SHAIKH SALAH MUHAMMAD AL BUDAIR ( 24 SHAUWAL 1437 AH)

Hudubar Masallacin Annabi 24/10/4137 Tare da sheikh Salah dan Muhammad Albudair
HUDUBAR FARKO
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Mai karamci Mai yawan kyauta, Ya fifita tsakanin halittunsa cikin fahimta da ilmuka da hankula da laduba, Ya haramta alfahasha da batsa da zagi,Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, gare shi nake kira, kuma zuwa gare shi makoma ta.Na shaida Annabinmu kuma shugabanmu Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma ga Alaye da Sahabbai baki daya.
Bayan haka, Ya ku musulmai!
Ku ji tsoron Allah, to duk wanda ya ji tsoron Allah ya rabauta a ranar sa ta yau da ta gobe, kuma Musulmi shi ne wanda musulmi suka kubuta daga sharrin harshensa da na hanunsa, ( Ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah ku fadi magana madaidaiciya) Ahzab 70.
Ya ku Musulmai: 
Mumini na tunkudo alheri , kuma yana tausayawa halittu,
 Sauki a zance  da tattausawa a magana, da Taushi cikin tattaunawa, tafarki ne mikakke da ake karkato da zukata, ta kan janye soye soyen rayuka daban daban, kuma ta dawo da zukata da suka yi nesa, da ra'ayoyi mabanbanta,
 Allah madaukakin sarki yace ga musa da Harun : ( Ku ce da shi zance mai taushi ko zai fadaka ko ya ji tsoro)
Ibnu kasir Allah ya mishi rahama yace:  "wannan aya akwai abin lura mai girma, wanda ita ce Fir'auna ya kai kololuwa cikin sabawa Allah da dagun kai shi kuma Musa zababben Allah ne na cikin halittu a wancan lokaci, amma duk da haka aka yi mishi umarni da kar ya fiskanci fir'auna sai da magana mai taushi da kuma tausasawa".
Ya ku Musulmai :
Zagi kan yada fitintinu,kuma  zagi bai dawo da gudajje, kuma bai janyo abokin musu, sai dai kawai ya haifar da gaba da kiyayya da kullin zuci, kuma ya kara wa mai jayayya dogewa da musu.
Duk wanda yake zagin abokin adawarsa  yana jifansa da alfahasha, ya munana zance game da shi,ya aibata shi da kalamai marasa kyau,  to ya dada kwambala ruwa akan tabo ne,  ya kuma karawa cuta rashin lafiya ne (ma'ana ya dada kamari da rikita al'amura kamar wanda ya karawa wuta fetur ne).
Ma'aboci mummunan hali da zafin harshe mai yawan cin mutunci, mai sukan jama'a, mai kazafi ga wadanda basu ji ba ba su gani ba, mai cin zarafin bayin Allah, mai yawan aibata mutane da cin namansu, wanda bai furuci sai da alfahasha da zagi, ba zai taba zama mai kawo gyara ko nasiha ba, ko malami ba.
Abubuwa na gaugawan faruwa cikin al'uma, ba wani kara da mutane zasu ji ko faduwan wani abu, ko wata wakia  ta kusa ko ta nesa, face sun garzaya ga yanar gizo wato internet, suna rikan wannan wakiar  abin zagi da za su rika zagin juna da shi suna bibiyar shi suna yada shi. Suna masu gaggawa zuwa ga hanyoyin sadarwa na sada zumunta  suna kai hari tsakanin mai jifa da mai harbi , da mai suka da mai tsinuwa da mai zagi sai kadan daga cikinsu wadanda Allah ya tarfawa garin su nono.
Ya ku wadanda ku ke rubuta tsinuwa da zagi da sake tuhume –tuhume da hukunce – hukunce! Ku sani zaa tambaye ku game da abinda ku ke rubutawa, a ranar da halittu za su tattaru a cikinta, kuma a auna dukkan ayyuka, da mintuna da ka sarayar, ko wace rai za ta zo da mai shaida da mai kora ta.
Ya wanda ya buya bayan fiskar wayarsa ko naurarsa, ya wanda ya fake da suna na karya, ya yi nesa daga idanuwa! Ya zame yana auna wa waninsa zagi da tsinuwa! Ka manta Allah ya na ganinka ne? A halin kuwa yana sane da sirrinka da ganawarka.
Mumini ba mai suka ne ko tsinuwa ko batsa da mummunar magana ba.
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bai kasance mai zagi ba ko mai maganar alfahasha ko tsinuwa ba, ya kuma ce : (Lalle ni baa turo ni mai tsinuwa ba sai dai ni an turo ni rahama ne.)
zagin musulmi fasikanci ne) kuma yace ( Masu zagin junansu su biyu shaidanu ne, suna cin zarafin junansu, kuma suna karya akan junansu).
 Daga Jabir bin sulaim Allah yarda da shi lalle  yace ga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi,: A sanar da ni abin da zan kiyaye shi na kuma lizimce shi, : sai yace (kar ka zagi wani! ) yace :" Bayan haka ban sake  zagin kowa ba, da ne ko bawa, rakumi ko akuya ba".
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da shi: ( Idan mutum ya zage ka, ya aibata ka da wani abu da ya sani game da kai, to alhakin hakan na kan shi,)Abu Dauda ne ya rawaito.
Ya kai bawan Allah!
Ka tuba daga abin da hannayenka suka rubuta, ka goge zaginka da cutarwarka da ka yi wa wani.ka tuna fadin Mahaliccinka Majibincinka :(kuma kace wa Bayi na , su fadi kalma wacce take mafi kyau. Lalle ne shaidan yana sanya barna tsakaninsu. Lalle ne shaidan ya kasance ga mutum makiyi bayyanane.)Isra'i  53.
Ya Allah ka mana ilhaman shiriyarmu ka kare mu daga sharrin kawunanmu.
Ina neman gafarar Allah ku ma ku nemi gafararsa, don shi Mai gafartawa masu komawa a gare shi ne.



Huduba ta biyu
Dukkan yaba da godiya sun tabbata ga Allah da yace : ( kuma ku  fadi magana mai kyau ga  Mutane) Bakara 83. Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, shahadar da muke  fatan samun rabauta da maikyau a dalilinta, Na shaida kuma Annabinmu kuma shugabanmu Muhammad Bawansa ne kuma Manzonsa ne, zababben Annabi,kuma Manzo zababbe, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa, salati mai wanzuwa da aminci mai biyo wa da yawa.    
Bayan haka, Ya ku musulmai:
Ku ji tsoron Allah hakika mai tsoron Allah ya rabauta, shi kuma Mai sabo ya yi hasara.
(Ya ku wadanda ku ka bada gaskiya ku ji tsoron Allah, kuma ku kasance tare da masu gaskiya)Tauba 119.
Ya ku Musulmai:
Hakika Allah ya hani muminai  zagin abin bautan mushrikai, sabo da kar zagin nasu ya zama sanadin zagin Allah madaukakin sarki.
To zagin abin bautansu zai kara musu kafirci da sangarcewa da gujewa, to sai zagin nasu ya zama ya sabawa manufan Allah game da kira da manufa na sakonsa. 
Allah madaukakin sarkin yace : (kuma kada ku zagi wadanda suke kira, baicin Allah, har su zagi Allah bisa zalunci,ba da ilimi ba.)An'Am 108.
Lallai a kiyaye dukkan kiyayewa! Kada ku riski bayin Allah da kaushi da tsanani, da suka da tsinuwa da zagi har ku kai su su guje wa gaskiya da sunnah da halaye masu kyau.
Ku bayyana gaskiya ta hanyar hujja da dalili, da bayani cikin hikma da tausasawa tareda  basira, kawai abin da ya wajaba a gare ku shi ne : Nasiha, da umarni da hani, baakan ku shiryar da su da tankwara su ba da  gyara su ba, ,Hisabinsu na gun Allah ba a kanku ba,haka ma sakayyansu.
Ku yi salati da sallama bisa ga Ahmad Mai shiryarwa, mai yi wa dukkan mutane ceto, duk wanda ya mishi salati guda to Allah zai mishi salati goma dalilinta.
Ya Allah ka yi salati da aminci ga bawanka kuma Manzonka Muhammad, Ya Allah ka yarda da dukkan iyalai da sahabbai, mu ma ka hada da mu tare da su ya mai karamci ya Mai yawan kyauta.
Ya Allah ka daukaka musulunci da Muslmai , ka kaskantar da shirka da mushrikai, ka rusa makiya addini,ka sanya aminci da kwanciyan hankali ga wannan gari da sauran garuruwan Musulmai.
Ya Allah ka datar da shugabanmu jagoran al'amarinmu cikin abin da ka ke so kuma ka yarda da shi, ka ja shi zuwa ga biyayya da tsoron Allah, Ya Allah ka datar da jagororin al'amuran Musulmai su yi hukunci da shariarka, kuma su bi sunnar Annabinka Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Ya Allah ka tseratar da masu rauni cikin Musulmai ya Ubangijin talikai, Ya Allah ka tseratar da masu rauni cikin Musulmai ya Ubangijin talikai, Ya Allah ka tseratar da masu rauni cikin Musulmai ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka kashe kafurai da suke saddu ga tafarkinka, masu gaba da masoyanka, ka sanya musu azabarka, Ya abin bauta na gaskiya Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka bawa marasa lafiyan mu sauki,ka bada lafiya ga wanda ka jarabce shi a cikinmu, ka saki  kamammu na gurin yaki, ka jikan matattunmu, ka taimake mu kan wanda ya yi gaba da mu, Ya Allah ka kawo aminci a iyakokinmu, ka kiyaye sojojinmu, ka basu karfin guiwa, ka taimake su kan makiyin ka kuma makiyinsu, Ya Ubangijin talikai, Ya Allah ka karbi matattunsu cikin shahidai, ka kawo waraka ga wadanda suka ji rauni a cikin su.ya Mai karbar adua. Ya Allah ka sanya aduarmu ta zama karbabbiya, ka sanya kiranmu ta samu daukakuwa, Ya Mai girma ya mai jinkai ya mai karamci.

  

TUNANI GAME DA AYOYIN ALLAH(RANA) SHAIKH ABDUL MUHSIN ALKASIMI (17 SHAWWAL 1437 AH)

Hudubar Juma'a na  Masallacin Annabi 17/10/1437 tare da sheikh Abdulmuhsin Alkasim.
Hudubar farko.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah muna gode masa kuma muna neman taimakonsa da gafararsa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi, kuma duk wanda ya batar babu mai shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah,shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, na kuma shaida Annabinmu Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne, tsira da amincin Allah su tabbata gare shi da iyalansa da sahabbansa da aminci tabbatacciya mai yawa.
Bayan haka, ku ji tsoron Allah yadda ya dace a ji tsoron shi – ya ku bayin Allah- ku yi murakabarsa a boye da bayyane,
Ya ku musulmai:
Abu mafi kyau da mutum zai sadaukar da rai don shi, shine tunani a ayoyin Allah da abubuwan ban mamaki na aikinsa, da kaura zuwa taallakan zuciya da himmatuwa da Allah ba wani abu cikin halittansa ba,
Ayoyin  ubangiji sune dalilai da hujjojin da bayi zasu san Ubangijinsu da su da sunayensa  da siffofinsa da ayyukansa, da kadaita shi,
 Kuma Tunani a halittun Allah ibada ne, kuma shiriya ne, kuma  shine mafarin alheri da mabudinsa, da shi ne bawa zai girmama Ubangijinsa, kuma ya kara imani da sakankancewa, kuma ya bude basira ta zuci, ya fadakar da shi daga gafalarsa, ya gadar mishi da rayuwa da lura da kauna ga Allah da tunani.
Tunani a ayoyin  Allah na daga cikin abu  mafi daraja daga cikin ayyukan zuci kuma mafi  amfani, yana kira ga aiki kuma ya sanya ma'abocinsa mika - wuya,
 Sufyan dan Uyaina Allah jikansa yace: "Tunani mabudi ne na rahama, ase ba ka gani mutum kan yi tunani ya tuba"
Shi ne abu mafi Alherin abin da zaa yi wa'azi ga bayi da shi. Allah madaukakin sarki yace : ka ce ni kawai ina yi muku gargadi da kalma guda wato ku tsayu domin Allah, bibbiyu  da dai dai, sa'an nan ku yi tunani )Saba'I 46
Idan mutum na tunani  to a komai zai zama yana da abin lura, Alkur'ani mai girma na cike da kiran halittu zuwa ga tunani bisa ayoyin Allah, da dubi ga halittunsa, Allah madaukakin sarki ya ce:  ( shin basu yi dubi ba a cikin mulkin sammai da kasa da kuma abin da Allah ya halitta daga komai). Araf 185
A cikin halittun Allah akwai  abin lura da wa'azi  Allah ya yi umarni da tunani game da su, sai yace: "ka ce ku yi dubi me ke cikin sammai da kasa" yunus 101
Shekul  Islam Allah ya mishi rahama ya ce : '' kuma  dubi zuwa ga halittun sama da na kasa don yin tunani da lura  abu ne da aka yi umarni da shi kuma mustahabbi ne''
 Hankula cikakku masu wayo su ke gane abubuwa bisa hakikanin yadda suke,  Allah ya yabi masu tunani cikin halittunsakuma lalle suna cikin masu zurfin hankali,Allah madaukakin sarki yace : ( Lalle ne a cikin halittar sammai da kasa da sabawar dare da yini akwai ayoyi ga ma'abuta hankali. Wadanda suke ambaton Allah a tsaye kuma a zaune a bisa sasaninsu, suna tunani akan halittar sammai da kasa, ya Ubangiji baka halitta wannan a kan banza ba, Tsarkin ka sabo da haka ka tsare mu daga azabar wuta. ) Ali Imran 190-191.
Allah ya yi zambo ga masu kauda kai daga tunani sai yace  : (kuma da yawa wata aya a cikin sammai da kasa suna shudewa a kanta kuma su suna bijirewa daga gare ta.) yusuf 105
Na daga cikin ukubobin  Allah karkatar da ayoyin shi daga masu girman kai, sai ya ce:
:( za ni karkatar da wadanda suke yin girman kai a cikin kasa ba da wani hakki ba daga ayoyi na kuma idan sun ga dukkan aya ba za su yi imani da ita ba).A'araf 146
 Hasanul Basri yace :( Abin da ya  hana su tunani a ciknta.)
Rana na cikin manyan ayoyin Allah na yau da kullum, Allah madaukakin sarki ya ce:( kuma akwai daga ayoyinsa dare da wuni da rana da wata,) Fussilat 37
 Allah ya sanya ta ga duniya haske a sama kuma fitila mai tsananin haske. tana gudu ba tare da sauti ba duk da girman gangan jikinta, tana tafiya bisa kididdiga mai zurfi  cikin yalwataccen falaki, zuwa ajali abin ambato, (Rana ba ya kamata a gare ta ta riski wata kuma dare ba ya kamata a gare shi ya zama mai tsere wa yini, kuma dukkansu a cikin sarari guda suke yin  iyo) yasin 40
Allah ya hore ta ga bayin sa,  to hudowarta da faduwarta ke bada tsayuwar  dare da yini, ba don samuwarta ba da al'amuran wannan duniya ya rikirkice, a cikinta akwai hikimomi da maslahohin da halittu ba za su iya iyakance su ba, Allah ya kafa hujja da shi bisa kadaicinsa da uluhiyyarsa sai ya ce : (kuma lalle  Idan ka tambaye su wane ne ya  halitta sammai da kasa,kuma ya hore rana da wata ? lalle suna cewa ; Allah ne.) Ankabut 61
Kuma ya sanya ta aya ga mutane masu hankali, Allah madaukakin sarki ya ce :
(kuma  ya hore muku dare da wuni, da rana da wata,kuma taurari horarru ne da umarninsa, lalle ne a cikin wancan, hakika akwai, ayoyi ga mutane wadanda suke hankalta.)Nahli 12
Ya kuma kirayi bayi zuwa ga dubi  ga horewarta da yayi na ban al'ajabi.sai ya ce : ( Ashe ba ku ga lalle Allah, yana shigar da dare a cikin rana ba, kuma yana shigar da rana a cikin dare, kuma ya hore rana da wata.) lukman :29
Kuma da su ne halittu ke kidanya lokutansu, kuma su san  manyan alamomi na al'amuransu na yau da kullum (kuma ya sanya dare mai nitsuwa, da rana da wata bisa lissafi) An'am 96
Kuma  Allah yahalicci inuwa, ya kuma sanya rana ta zama mai nuni a gare ta.
Imamul Baghawi  - Allah mishi rahama ya ce : " Ma'anar nuni a gare shi shi ne  cewa : Ba don rana ba da ba a san inuwa ba, kuma ba don haske ba da ba a san duhu ba, abubuwa ana gane su ne da kishiyoyinsu." Allah ya ta'allaka tafiyarta a matsayin  alama na da yawa daga cikin ibadoji kamar sallah sai yace : ka tsayar da sallah a karkatar rana zuwa ga duhun dare) Isra 78
Game da mafificin lokuta na Ambaton Allah yace : ( Kuma ka yi tasbihi game da gode wa Ubangijinka a gabanin fitowar rana da gabanin bacewarta) K 39
 A azumi kuma mai azumi zai yi buda baki idan ta bace.., na daga cikin alamomin lailatulkadri (Rana tana bullowa  wayan garin daren lailatul kadri tana halin bata haske mai karfi, a wannan wunin nata.)Muslim ne ya rawaito.
A ranakun (Ayyamuttashrik) Alhaji zai yi jifa ne na jamara bayan zawali.
  Lokaci na datsewar ibada na tuba  na  na fara wa ne da bullowar rana daga yamma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Allah na shimfida hannayensa da dare don mai laifin wuni ya tuba, kuma yana shimfida hannunsa da rana don mai laifin dare ya tuba har zuwa  rana ta fito daga yamma)  Muslim ne ya rawaito,
Lalle Allah na shimfida  hannayensa da dare don mai laifin rana ya tuba, kuma yana shimfida hanunsa da rana don mai laifin dare ya tuba, har rana ta fito daga  mafadanta, Muslim ne ya rawaito,
Da salla kafin hudowar rana da kafin faduwarta Allah ya sanya lada  gare ta mai yawa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (lalle za ku ga ubangijinku kamar yadda ku ke  ganin wannnan wata.ba ku tumurmusa, a  wajen ganinsa, idan za ku iya kar sallah ta kubce muku, kafin hudowar rana (Asuba) da faduwarta(sallar la'asar) to ku aikata hakan). Buhari ne ya rawaito.
Kisfewarta tsoratarwa ne na Allah ga bayinsa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :( Lalle rana da wata ba su kisfewa  sakamakon mutuwar wani ko rayuwarsa, sai dai suna cikin ayoyin Allah ne. Allah na tsoratar da bayinsa da su, idan kun ga kusufi ku ambaci Allah har sai ya yaye).Muslim ne ya rawaito
Sabo da girman  halittarta da yawan amfaninta  Allah ya rantse da ita sai yace: ( Ina rantsuwa da rana da hantsinta).  Shams 1
Tare da wannan girma kuma Allah ne ke tafiyar da ita, ita tana tasbihi gare shi, Allah madaukakin sarki yace :(Ashe baka gani ba lalle Allah wanda ya ke acikin sammai da wanda ya ke a cikin kasa yana yin sujjada a gare shi da kuma rana da wata da taurari,da duwatsu da itace da dabbobi da kuma masu yawa daga mutane.) Hajj 18
A kowani rana tana sujada ga Allah bayan  faduwarta, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce ; ya Abu zarri! Ko ka san a ina rana ke faduwa? Sai nace : Allah da Manzonsa ne suka fi sani, sai yace : lalle Tafiya ta ke yi har ta yi sujada a karkashin Al'arshi) wannan shine fadin Allah madaukaki. (Kuma rana tana gudana zuwa ga wani matabbaci nata, wannan kaddarawar mabuwayi masani.) Yasin 38
Buhari ne ya rawaito.
Kuma  Baiwa ce ga Allah ba'a bauta mata, na daga cikin shirka a yi mata sujada  Allah ya ce yace:( kar ku yi sujada ga rana ko wata  ku yi sujada ga Allah in kun kasance shi kadai ku ke bautawa)Fussilat 37.  
Faduwarta salo ne daga cikin salon da Annabawa suka rika na kira zuwa ga tafarkin Allah.
 Annabi ibrahim  Amincin Allah su tabbata a gare shi ya kafa hujja bisa uluhiyyar Allah da rushewar bauta mata da faduwanta. Allah  madaukakin sarki yace:( sa'annan a lokacin da ya ga rana tana bayyana yace ; Wannan shine ubangiji na, wannan ne mafi girma) sa'annan a lokacin da  ta fadi yace : ya mutane na lalle ne ni barrantace nake daga abinda kuke yi na shirka)  Lalle ne na fuskantar da fuskata ga wanda  ya kaga hallitar  sammai da kasa ina mai karkata zuwa ga gaskiya kuma ba ni cikin  masu shirka ) Al An'am 78-79
An fitini da yawa da ga cikin halittu  sai suka bauta mata koma bayan Allah, Huda huda tace da Annabi sulaiman, tana mai hakaitowa, game da sarauniyar saba'I da mutanenta,  (Na same ta  ita da mutanenta suna yin sujada ga rana baicin Allah, Kuma shaidan ya kawata musu ayyukansu saboda haka sai ya karkatar da su daga hanya  sa'anan su basu shiryuwa)   Annaml  24.
Musulmi bai kirdadan faduwan rana ko hudowarta da sallar sa,  a wannan lokacin ne wasu kafurai ke mata sujada, a dalilin sujadan wasu mutane gare ta sai shaidan ya kafa bauta gare ta yayin bullowarta da yayin faduwarta, yana nuna shi suke yi wa sujada, sabo da toshe kofar bauta mata aka hana musulmi  da ya kirdadi sallah kafin  fitowar rana ko faduwarta,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: (kar ku kirdadi fitowar rana ko faduwarta da sallarku domin tana hudowa ne a kahon shaidan) Muslim ne ya rawaito.
A yayin zawali na rana a kowani wuni  akwai wa'azi ga mumini, domin ana zuga wuta a ruruta(ana kunna ta a cika ta) to sai aka hana sallah a wannan lokaci, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : A wannan lokaci ne ake zuga jahannama) Muslim ne ya rawaito.
 Fitowar rana daga ta inda ba ta nan ta saba fitowa ba alama ne na kusancin Tashin Alkiyama. Kuma umarni ne daga Allah da rushewar duniya. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Alkiyama ba za ta tsaya ba har sai rana ta fito da mafadarta, ida ta fito mutane suka ganta duk sai su yi imani,  wannan shine lokaci da imani ba zai amfanar da rayi ba.) Bukhari da muslim ne suka rawaito.
Kuma  farkon ayoyi da zai fito, fitowan rana daga yammacinta da fitawar dabba ga mutane da hantsi, kuma duk wanda ta riga dayanta fita to dayan ma na biye a kusa .
 kuma a matattara Allah yana hada mutanen  farko da na karshe a farfajiya guda,
  mai kira  na jiyar da su, kowa na ganin kowa, rana zata matsa kusa da halittu har ta kai tsakaninta da su kwatankwacin (Mel). Sulaim dan Amir Allah mishi rahama ya ce: "To wallahi ban san wanne yake nufi ba da mel na na auna kasa,ko  tsinken kwallin da ake sawa a ido ?"
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Mutane za su kasance cikin zufa kowa gwargwadon aikinsa, akwai wanda zai kai zuwa idon sawunsa, wani kuma zuwa guiwarsa, wani kuma zuwa kwankwasonsa, akwai wanda zai nuta cikin zufa, gumi ya kai  har zuwa bakinsa, ) Muslim ne ya rawaito,
  Mutane bakwai Allah zai musu inuwa a ranar da ba inuwa sai inuwarsa, son Allah ne da girmama shi ya hada su, sai Ubangiji ya yi yekuwa ya na cewa :(Duk wanda ya kasance yana bautawa wani abu to ya bi wannan abin, masu bautan rana sai su bi rana,sai a jefa su cikin jahannama, a wannan lokaci ne rana za ta dunkule haskenta ya tafi,kuma a jefa ta cikin jahima)
Allah madaukakin sarki ya ce: (Kuma idan aka shafe hasken rana)Takwir 1
Ibnu kasir –Allah mishi rahama- ya ce : "Abin da ake nufi da (kuwwirat):an tattaro sashenta aka hade da sashen sa'annan sai a nade ta a wurga ta, to idan an yi hakan da ita sai haskenta ya tafi.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Rana da Wata za'a shafe haskensu ranar alkiyama,) Bukhari ne ya rawaito.
A cikin Aljanna babu rana ko jaura, don ana haska ta ne da hasken Allah. Mafi girman ni'ima ga 'yan Aljanna  ita ce ganin Allah, za su gan shi -Tsarki ya tabbata a gare shi- kamar yadda mutane a duniya suke kallon rana a tsakiyar wuni ba tare da girgije ba.
Sahabbai sun ce ga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: shin ko za mu ga Ubangijinmu ranar alkiyama? Sai ya ce: ( shin kuna cutuwa ga (Kallon) rana yayin da babu gajimare? Sai suka ce : aa ya manzon Allah. Sai ya ce : ( To kamar hakan zaku gan shi)Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Bayan haka .. ya ku musulmai!
Dukkan halittu tun daga kwayar zarra har ya kai ga Al'arshi suna nuni ne akwai Allah,Duniya kuma na furuci ne da kadaitakarsa. Kallo  mai amfani shine wanda aka yi da idon basira ba da  tsurar ido kawai ba. Musulmi na aiki da hankalin sa da tunaninsa don ya yi wa kansa hisabi ya kuma gyara zuciyarsa.
Ku ambaci Allah ku girmama shi, ku fiskance shi da biyayya ku kadaita shi. Ku kiyaye daga gafala da bijirewa ku yi tasbihi a gare shi.
Ina neman tsarin Allah daga shaidan abin jefewa, (Wannan shi ne halittar Allah. To ku nuna mini , "Mene ne wadanda ba shi ba suka halitta? Aa, azzalumai suna cikin bata bayyananna") Lukman 11      
    Allah sa mini albarka ni da ku cikin Alkur'ani mai girma, Allah  ya amfane ni da ku da abin da ke cikinsa na ayoyi, da ambato mai hikima, iya abin da zan fadi ina neman gafarar Allah ga ni da ku da dukkan musulmai daga dukkan zunubai, ku nemi gafararsa shi mai gafara ne kuma mai jinkai.



Huduba ta Biyu

Dukkan yabo ya  tabbata ga Allah bisa kyautatawarsa, godiya a gare shi bisa datarwarsa da baiwarsa, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya sha'aninsa abin girmamawa  ne. Na shaida Annabinmu Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa ne,tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa  da aminci tabbatacce mai kari.
Ya ku Musulmai:
Hikimar Allah ta hukunta ya sanyawa rana daguwa da sauka wanda ke haifar da zafi da kuma sanyi, ya a zafin bazara akwai wa'azi ga muminai, tsananin zafin shi daga tururin jahannama ne, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Wuta ta koka wa Ubangijinta sai tace: sashi na na cin sashe, sai ya mata izini da numfasawa biyu, Numfasawa a cikin hunturu numfasawa a lokacin bazara, shine tsananin zafi da kuke ji a bazara da tsananin sanyi da kuke ji na jaura.) Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Duniya na gauraye ne da radadi da ni'ima, radadinta zai tuna mana radadin wuta kamar yadda ni'imarta zai tuna mana da jin dadi na aljanna. Jujjuyawarta daga sanyi zuwa zafi da kuma daga dare zuwa wuni dalili ne na karewarta da gushewarta.
Mumini wani abu ba zai raba shi da Allah ba, to zafi ba zai hana shi sallah ko azumi ba da biyayya da alheri, Allah ya zargi masu cewa :(kar ku fita a lokacin zafi) ya amsa da narko na azaba,(ka ce wutar jahannama ta fi tsananin zafi da sun kasance suna fahimta) Tauba 81
Abin mamaki ga mutumin da ya ke kare kansa daga zafin wutan duniya amma kuma bai karewa daga wutar Jahima?
Sannan ku sani Allah ya muku umarni da salati da aminci ga Annabinsa sai yace: a cikin Muhkamin littafinsa da ya saukar :(Lalle Allah da Malaikunsa suna salati ga Annabi. Ya ku wadanda suka yi imani ! ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi).Ahzab 56.
Ya Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka ga Annabinmu Muhammad,ya Allah  ka yarda da khalifofinsa shiryayyu, wadanda suka yi hukunci da gaskiya, kuma da shi suke adalci: Abubakar da Umar da Usman da Aliyu, da sauran sahabbai baki daya.mu ma ka yarda da mu tare da su da kyautarka da karamcinka, ya mafi karamcin masu karamci.
Ya Allah ka daukaka Musulunci da musulmai, ka kaskantar da shirka da mushrikai, ka ruguza makiya addini, ya Allah ka sanya aminci ga wannan gari da kwanciyar hankali da yalwa da sauran garuruwa na musulmai.
Ya Allah duk wanda ya nufe mu ko ya nufi gidajen musulunci da musulmai da mugun nufi, to ka shagaltar da shi da kan shi, ka maida mishi makircinsa cikin halakarsa, ka jefa tsoro cikin zukatansu, ya mai karfi mabuwayi.
(Ya ubangijika ka bamu mai kyau cikin duniya,da kuma mai kyau a cikin lahira, kuma ka tsare mana azabar wuta.) Bakara 201.
Ya Allah ka gyara halayen musulmai a ko ina, ya Allah ka sanya gidajensu gida ne na Aminci da yalwa, ya ma'aboci daukaka da karramawa.
(Ya Ubangijinmu! Mun zalunci kanmu, kuma idan ba ka gafarta mana ba, kuma ka yi mana rahama, hakika muna kasancewa cikin masu hasara.)Araf 23.
Ya Allah ka datar da jagoranmu da shiryarwarka,ka sanya aikin shi cikin yardarka.
Ka datar da dukkan jagorori na musulmai da aiki da littafinka, da yin hukunci da shariarka Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka amintar da iyakokinmu, ka sanya gidajenmu gidaje ne na imani da karfi da tauhidi ya ma'aboci daraja da daukaka. Ya Allah ka taimaki sojojinmu ka hada zukatarsu ka tabbatar da diga digansu, ka taimake su a kan makiya ya Mai karfi Mai buwaya.
Ya ku bayin Allah:
(Lalle Allah na yin umarni da adalci da kyautatawa da baiwa ma'abocin zumunta, kuma yana hani da alfahasha da abin da aka ki, da zalunci, yana muku gargadi ko za ku na tunawa.) Nahli 90.

Ku ambaci Allah Mai girma da daukaka zai ambace ku,ku gode mishi bisa ni'imominsa zai kara muku. Ambaton Allah shi ya fi komai, Allah ya san Abin da ku ke aikatawa.      

FALAL RANAKU GOMA NA FARKON ZUL HAJJI NA SHAIKH ALI ABDURRAHMAN ALHUZAIFI (7 ZUL HAJJ ) 1437

Hudubar Juma'a a Masllacin Annabi tare da sheikh Aliyu dan  Abdurrahman Alhuzaifi 7/12/1437
Hudubar Farko:
  Yabo da godiya  sun tabbata ga Allah,  (Dukkan Godiya da yabo  sun  tabbata ga Allah wanda ya halicci sammai da kasa ya kuma sanya duffai  da haske) An'ami 1,
 kuma ya shar'anta shario'i, rahama ga bayi domin lada ya yawaita ga talikai kuma ya tunkude musu ukuba da dukkan sharri, ina yabo ga ubangiji na kuma ina gode mishi kuma ina tuba gareshi, kuma ina neman gafaran shi, kuma na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ne bashi da abokin tarayya masani ga abin da ke cikin zukata, kuma na shaida Annabin mu kuma shugabanmu  Muhammad (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi)  bawansa ne kuma Manzonsa ne, mai kira zuwa ga dukkan aiki na biyayya. ya  Allah kayi salati da sallama da albarka wa bawanka kuma manzonka  muhammad da iyalansa da sahabbansa wadanda suka taimaki addinin Allah Madaukaki, har dukkan  mushrikai masu yawan kafurci su ka rusuna masa.
 Bayan haka : ku ji  soron Allah madaukaki, da gaggawa  zuwa  ga ayyukan Alheri, da nisantan haramtattun abubuwa, don shi Ubangiji madaukaki ya cancanci a kiyaye dokokin shi a  ji tsoron shi, ba wadanda zasu rabauta sai masu tsoron Allah, ba hasararru sai wadanda suka juya baya su ka sa shakku a addinin Allah.
Ya ku musulmai!
    Lalle kuna cikin ranaku masu albarka da falala, sauran kwanakin nan  goma  da Allah ke ribanya ladan ayyuka na kwarai, yana kyale tuntube da aka yi a cikin su, kuma yana karban uzuri daga wanda ya bada uzuri, kuma Allah na karbar tuban wadanda suka tuba, ya yafe zunuban masu neman gafara.
An karbo daga Abdullahi dan Abbas Allah kara musu yarda,yce ; Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce;  (Ba wasu ranaku da ayyukan alheri ya fi soyuwa a gurin Allah  kamar wadannan ranaku goma) sai su ka ce har da jihadi? Sai yace : har da jahadi, sai dai mutumin da ya fita da ransa da dukiyansa bai dawo da komai ba.) Buhari ne ya rawaito.
An karbo daga Abu Huraira Allah kara yarda a gare shi yace :  daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: ( Ba wasu ranaku da ya fi soyuwa ga Allah da a yi bauta a cikin su kamar goman farko na zulhajji, azumin kowani rana na daidai da azumin shekara, tsayuwan kowani dare na daidai da tsayuwan daren lailatul kadri,) Tirmizi da Ibnu maja da Baihaki,
 A cikin wannan goman akwai ranar arafa, wanda Allah ya yalwata alheri a cikinta, falala da albarka na sauka a cikinta, da rahama ga wanda ya halarce ta, kyautayin  Allah da karamcinsa na kwarara ga dukkan musulmai  a doron kasa, a wannan wunin,
An karbo daga Abu katada Allah kara yarda a gare shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: (an tambaye shi game da azumin ranar Arafa sai yace : yana kankare zunuban shekaran da ta gabata da mai zuwa,) Muslim ne da Abu Dawud  suka rawaito.
An karbo daga Aisha Allah kara yarda a gare ta, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (Babu wata rana da Allah ya ke yawaita 'yanta bayi daga wuta kamar ranar arfa, lalle Allah na kusantowa ya bayyana, sannan ya yi tinkaho da su a gaban mala'iku, sai ya ce: me wadannan ke bukata?) Muslim ne ya rawaito da Nasai.
Daga Abdullahi dan Umar Allah ya kara yarda a gare su, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: ( Idan yammacin Arafa ya yi ba wanda zai rage cikin wadanda akwai kwayan zarra na imani a zuciyarsa  face Allah ya gafarta masa, sai na ce ya manzon Allah ya kebanci mutanen Arafa ne kadai? Yace : a 'a , ga dukkan musulmai! ) Dabarani ya rawaito a Al- Kabir.
An karbo daga ubada dan samit  Allah ya kara yarda a gareshi  kan lallai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a greshi ya ce  : (Annabi ya ce a ranan arfa :ya ku mutane ! lallai Allah ya muku falala a wannan rana ya gafarta muku, sai dai nauyin wani da ke kan  wani a tsakaaninku (Hakkoki)  kuma yayi kyautan( ceton) masu musgunawanku ga masu kyautatawanku, ya bawa mai kyautatawanku abin da ya roka, to ku tunkude, idan ya kasance a muzdalifa sai ya ce :lalle Allah ya gafartawa na kwarai a cikin ku , kuma na kwaranku zasu yi  shafa'a ga na banzanku, rahama na sauka gare ku ta game su, sai a raba gafara a doron kasa sai ta sauka kan duk wanda ya tuba cikin  wanda ya kiyaye harcensa, da hannunsa,kuma  iblis da rundunarsa na kan dutsen Arafa, suna sauraron abin da Allah zai yi , idan an saukar da gafara sai ya yi yekuwa shi da rundunarsa suna ( wayyo azaba ta da Halaka, na kasance ina ingiza su wani lokaci, sannan gafara ta zo ta lullube su, sai su rarraba suna wayyo Allah mun boni mun lalace.) Dabarani ne ya rawaito a Al kabir.      Tsayuwan Arfa shi ne rukuni mafi girma a hajji, Ayyukan hajji da aduo'in  alhazai na game dukkan musulmai a doron kasa.  kai ai manyan Ibadoji da alamomi na hajji suna amfanar da kasa baki daya. Sai Allah ya tunkude azaba da ita ko ya sasssauta zunubansa. Allah madaukakin sarki ya ce:( Allah ya sanya ka'aba daki mai alfarma rayuwa ga mutane al'amarin addininsu na hajji yake mikewa sabo da shi,) Ma'ida 97.
Al Bagawi Allah ya jikan sa ya ce: Ai abin da zai mikar musu da addininsu da duniyarsu.
Allah madaukakin sarki ya ce : ( Kuma ba domin tunkudewar Allah ga mutane sashinsu  da sashe ba lalle ne da kasa ta baci, kuma amma Allah maabocin falala ne a kan talikai) Bakara 251
Al- Bagawi ya ce a tafsirinsa:  ba don tunkudewar Allah ga muminai masu biyayya ba daga kafurai da fajirai ba da kasa ta halaka da wanda ke cikinta, sai dai Allah na tunkudewa kafiri a dalilin muminai haka yana tunkudewa fasiki a dalilin salihin bawa.) ya tike.
Bayan Arafat akwai ranar babbar sallla da ranakun tashrik sune mafi alherin ranaku a gun Allah madaukaki, ya shar'anta ayyuka na kwarai da Allah ke ribanya lada da su, da kuma irin abin da Allah zai tseratar na daga azaba, A ranar babbar sallah Allah ya hada mafiya yawan ayyukan hajji a cikinsa, sune jifa da yanka da aski da dawaful ifada, kuma bisa wannan tsari ya fi, amma in da zaa fara gabatar da wani kafin wani, to ba laifi sai dai an bar abin da ya fi. sabo da manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a ranar babbar sallah baa tambaye shi ba game da wani abu da aka kaddamar ko aka jinkirta ba face ya ce ku yi ba laifi.
Kuma Allah ya ambaci ranar babbar sallah da Ranar babban Hajji.kuma yana cikin mafi alherin ranaku a gurin Allah madaukaki. Ranar sha daya ga wata ke bi masa, shi ake cewa  ranar ALKAR, da ranaku biyu da ke bi masa shine cikaton ranakun Attashrik , ya shar'anta sauran ayyukan hajji kamar yadda aka shar'anta yawan ambaton Allah ga alhaji da waninsa.
Daga Abdullah dan kurad Allah ya kara yarda a gare shi, daga Annabi  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:  Mafi alherin ranaku a gun Allah shi ne ranar suka, sai ranar Karr) Tabarani da Ibn  Hibban suka rawaito.
 Ku godewa Allah bisa abin da ya yalwata muku na ni'ima, da abin da ya shar'anta muku na sabuban rahama. Ku girmama albishirin da Allah ya yi mana, ku karbe ta da farin ciki da yakini, Alkawarin Allah mai kasancewa ne ba sabawa,  Allah madaukakin sarki yace : (saannan kuma abin bautawar ku Abin bautawa ne guda, sai ku sallama masa kuma ka yi bushara ga masu kankantar da kai. Wadanda su ke idan an ambaci Allah sai zukatansu su firgita da masu hakuri akan abin da ya same su da masu tsayar da sallah, kuma suna ciyarwa daga abinda mu ka azurta su ). Hajj 34-35.
Allah madaukakin sarki ya ce:  kuma ku gabatar da alheri sabo da kan ku, ku ji tsoron Allah kuma ku sani cewa lalle ne ku masu haduwa da shi ne, kuma ka yi albishir ga muminai)
Ku gaggauta ayyuka na kwarai kafin zuwan ajali, da katsewar ayyuka, domin duniya gida ne na rudi, matattara nena  musibu da sharri, ku dubi yanda ta yi da masu kwadayinta, da kuma yadda ta shelanta rabuwa da su, ba gida ne na dawwama ba, ko ni'ima na dindindin ba, gidan mumini ita ce gidan aminci gidan ni'ima da zama  wanda bai sauyawa ko gushewa, ku yi aiki don ita game da abin da Allah ya kira ku zuwa gare shi ku yi nesa da abin da Allah ya gargade ku ga me da shi, kamar ga ku da ranaku sun juya baya, ga lokacin mutuwa ya yi, to a wannan lokacin ne kowa zai yi da na shina, Me kyautatawa zai yi fatan ace ya kara aikin alheri, mai sabo zai yi kaito da nadama sakamakon tafiyarsa da ba guzuri, ya ku musulmi a wadannan ranaku, duk wanda Allah bai nufe shi da hajji ba, to Allah ya shar'anta mishi kofofi na da'a da ayyukan kwarai masu yawa  da zai riski wanda ya sha gaban shi, ko ya cin ma wanda ya yi mar fintinkau, da izinin Allah madaukaki, wanda aka datar da shi da yin hajji to ya godewa Allah madaukaki, ya kuma kyautata wa kansa ta hanyar aikata daa da barin abin da aka ki, ya zuba alheri nsa ya kame daga sharrinsa ya kiyaye dokoki na wannan farilla, kuma ya godewa Allah bisa abin da ya saukake masa na sabuba, da kuma irin baiwa da Allah ya yi wa Alhazai na daga aminci da imani, da saukin arziki, da saukake abubuwa masu wahala, to godiya ta tabbbata ga Allah bisa ni'imarsa na bayyane da na boye. Godiya tana gare shi a cikin duniya da lahira, Allah madaukakin sarki ya ce : ( sabo da haka Kuma ku ambace ni na ambace ku kuma ku yi godiya gare ni kuma kada ku butulce mini)  Bakara 152
Allah ya saka wa wannan kasa mafi alherin sakayya,  bisa abin da ta ke tashi da shi na hana kansu barci don Alhazai su samu hutu, haka ma masu umra da ziyara. Da kuma kulawa da take ba su ta bangaren lafiya. Da saukake musu duk wata hidima da kawo zaman lafiya, da abin da ake gani a kowace  shekara na daga tsare tsare da ta cin ma, na ban mamaki wanda ya bawa duniya mamaki,cikin ayyukan hajji don neman lada, muminai na farin ciki da haka,
Allah Madaukakin sarki ya ce : ( Ku yi gaggawa  zuwa ga gafara daga Ubangijinku da Aljanna da fadinta (daidai) da sammai da kasa ne, an yi tattalinta domin masu takawa. Wadan da suke ciyarwa a cikin sauki da tsanani, kuma suke masu hadiyewar fushi, kuma masu yafewa mutane laifi kuma Allah ya na son masu kyautatawa.) Al Imran 133-134.
Allah sa min albarka ni da ku cikin Alkur'ani mai girma.kuma ya amfanar da ni da ku da abin da ke ciki na ayoyi da ambato mai hikima, kuma ya amfanar da mu da shiryarwar shugaban Manzanni, da fadinsa mikakke, abin da na fadi kenan ina nemawa kai na da ku gafara daga dukkan zunubai. Da sauran musulmai daga dukkan zunubai, to ku nemi gafararsa don shi mai gafara ne mai jinkai.
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga maaboci buwaya da daukaka, maabocin girmame girmame, mai girma madaukaki, ina yabon Ubangiji na ina gode masa ina tuba zuwa gare shi, kuma ina neman gafararsa, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya,mai tsananin hila, na shaida Annabin mu muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wanda Allah ya tsamar da dan Adam  ta hanyarsa daga bata.
Ya Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammad da Sahabbai da Iyalai, bayan haka! Ku ji tsoron Allah madaukaki yadda ya dace a ji tsoronsa, duk wanda ya ji tsoronsa zai kare shi daga abubuwa masu halakarwa, a duniyarsa da lahirarsa,
Ya ku bayin Allah ! ku tuna abin da Allah ya muku na niima cikin farillai na hajji, na daga 'yan uwantaka na musulunci, da madauri na imani, da hadin kai na mafiskanta da ke kawo hadin kai na zuciya, da hadin kai na sahu  da ke haifar da yada rarrabuwa da sabani, Allah madaukakin sarki ya ce :( kuma  ku kankame   igiyar Allah gaba daya  kuma kada ku
Rarraba) Al imran 103.
Allah madaukakin sarki ya ce: (su muminai 'yan uwan junane a cikin addini) Hujurat 10.
Allah madaukakin sarki ya ce: (ya ku mutane hakika mun halicceku daga namiji da mace kuma muka sanyaku dangogi da kabiloli domin ku san juna lalle mafificinku daraja a wurin Allah shi ne  wanda yake mafificinku a takawa) Hujurat 13
. Kuma ku tuna wasiyoyin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shida hudubarsa a hajjin ban kwana : na daga cikin abin da aka kiyaye daga gare shi a wannan hajji tsira da amincin Allah su tabbata a gare  shi  fadinsa : Ku bauta wa ubangijin ku, ku yi sallolinku biyar, ku azumci watanku, ku yi biyayya ga mai jagorantar ku za ku shiga aljannar ubangijinku ) Ahmad ya rawaito daga hadisin Abu Umama Allah kara yarda a gare shi.
Ya ku bayin Allah !
( lalle Allah da malaikunsa suna salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce.
Ku yi salati da sallama ga shugaban mutanen farko da na karshe, kuma shugaban manzanni.
Ya Allah ka yi salati ga Annabi Muhammad da iyalan muhammmad kamar yadda ka yi salati ga Ibrahi da  iyalan Ibrahim, Lalle kai mai godiya ne kuma abin girmamawa.
Ka yi dadin tsira mai yawa.
Ya Allah  ka yarda da sahabbai baki daya. Da tabian da wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar hisabi,
Ya Allah ka yarda da mu tare da su da baiwanka da karamcinka da  rahamarka ya mai tausayin masu jin kai.
Ya Allah ka gafarta mana abin da muka gabatar da abin da muka jinkirtar da abin da muka boye da abin da muka bayyana da abin da kai ka fi mu sanin shi a kanmu, kai ne mai gabatarwa  kuma kai ne mai jinkirtarwa ba abin bautawa da gaskiya sai kai.
Ya Allah ka gafartawa matattun mu da matattu cikin musulmai,
Ya Allah ka gafartawa matattun mu da matattu cikin musulmai, da rahamarka ya mafi rahamar masu rahama.
Ya Allah muna rokonka maaboci daukaka da girmamawa,
Ya Allah muna rokon ka da ka dushe wutar fitina mai batarwa  tsakanin musulmai ya ubangijin talikai.
Ya Allah muna rokon ka da ka dushe wutar fitina mai batarwa  tsakanin musulmai ya ubangijin talikai.
Ya Allah ka hada zukatar musulmai ka gyara tsakaninsu.
Ya Allah ka azurta mu da musulmai fahimtar addini, Ya Allah ka azurta mu da musulmai fahimtar addini, da rahamarka ya mafi tausayin masu tausayi.
Ya Allah ka kyautata karshenmu a dukkan al'amura, ka kare mu daga walakancin duniya da azabar lahira, ya maabocin girma da karramawa.
Ya Allah muna neman tsari daga mummunar abin da aka kaddara, da kuma dariyan makiya, da kuma fadawa ramin tsiya, da matsanincin bala'I,
Ya Allah ka yaye bakincikin muminai  daga cikin musulmai, Allah ka biya bashi ga wadanda ake bin bashi cikin musulmai,
Ya Allah ka bada lafiya ga marasa lafiyan da marasa lafiyan musulmai, Ya Allah ka bada lafiya ga marasa lafiyanmu, ka taimake mu kan wadanda suka riki gaba da mu, da rahamarka ya mafi jinkan masu jinkai,
Ya Allah ka kare mu da zuriyarmu daga iblis da zuriyarsa da shaidanunsa,da rundunarsa da masoyansa, ya Ubangijin talikai, Ya Allah ka kiyaye mu daga sharrin kawunanmu, da munanan ayyukanmu, Ya Allah ka kiyaye musulmai da zuriyarsu daga Iblis da zuriyarsa, ya Ubangijin talikai, da rahamarka ya mafi jinkan masu jinkai,
Ya Allah ka kiyaye sojojinmu, Ya Allah ka kiyaye sojojinmu, kuma ka datar da su, Ya Allah ka kiyaye iyakokinmu, Ya Allah ka kiyaye kasarmu daga azzalumai masu ketare iyaka, da rahamarka ya mafi jinkan masu jinkai, ka kashe fitintinu masu batarwa,  ga musulmai ya Ma'abocin daukaka da karramawa,
Ya Allah ka kiyaye musulmai daga sharrin makiya musulunci, ya Ubangijin talikai, Ya Allah ka lalata shirin makiya musulunci, da suke kullawa musulunci da musulmai, ya maaboci girma da daukaka,
Ya Allah ka kame sharrin munafukai, domin lalle kana da iko ga dukkan komai,
Ya Allah muna neman tsarinka daga rarrabuwa da munafunci da munanan dabi'u,
Ya Allah ka jefa tsoron Allah a zukatanmu, ka tsarkake su kai ne mafi alherin wanda zai tsarkake su,
Ya Allah muna rokon ka aljanna da abin da zai kusantar da mu gare ta na fadi ko aiki,
Kuma muna neman tsarinka daga wuta da abin da zai kusantar  da mu gare ta na fadi ko aiki,
Ya Allah ka datar da Kadimul haramaini(shugaban kasar saudiya) cikin abin da ka ke so kuma ka yarda da shi, Ya Allah ka shiryar da shi zuwa ga shiriyarka, ka sanya aikin shi cikin yardardarka ya Ubangijin talikai, ya Allah ka taimake shi akan dukkan alheri, ka datar da shi ra'ayoyinsa ya Ubangijin talikai,
Ya Allah ka datar da mataimakansa guda biyu cikin abin da akwai alheri da daukaka ga musulunci da musulmai, ya Ubangijin talikai,
Ya Allah ka karbawa alhazai ayyukansu kuma ya Allah ka kiyaye su,ya Ubangijin talikai,
Ya Allah ka maida su garuruwansu cikin aminci da nasara suna halin ka gafarta musu zunubansu, ya Ubangijin talikai, kuma ka saukake musu al'amuransu.
Ya Allah muna rokonka ya ma'aboci daraja da daukaka, ka isarwa musulmai sharrin masharrata da makircin munafukai da mutanen banza, Ya ma'aboci daraja da daukaka.
Ya ku bayin Allah!
(Lalle Allah na yin umarni da adalci da kyautatawa, da baiwa ma'abocin zumunta, kuma yana hani da alfahasha da abin da aka ki da zalunci, yana muku wa'azi don ku wa'azantu.) Nahl 90.
Ku ambaci Allah mai girma da daukaka



  




السبت، 28 يناير 2017

SHIRKA NA SHAIKH HUSAIN AL ASSHAIKH (HUDUBAR 21 ZUL HAJJ 1437 AH)

Hudubar Juma'a daga Masallacin Annabi  (SAW)  21/12/1437AH Na Sheikh Husain Bin Alus shaikh
Lalle dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, muna gode masa kuma muna neman taimakonsa, muna neman gafararsa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da kuma munanan ayyukanmu,duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi, wanda ya batar kuma babu mai shiryar da shi, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, kuma na shaida Annabinmu Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne.
(Ya ku wadanda suka bada gaskiya ku ji tsoron Allah  hakikar soronsa,kuma kada ku mutu face kuna musulmai) Al Imran 102.
(Ya ku mutane ku ji tsoron ubangijinku, wanda ya halicce ku daga rai guda daya, kuma ya halitta daga gare shi matarsa kuma ya yada daga gare su maza masu yawa da mata, ku ji tsoron Allah da kuke rokon juna da (sunan) Shi, da kuma zumunta, lalle Allah ya kasance mai kulawa  ne da ku.) Nisa'I 1     
(Ya ku wadanda suka yi imani ! ku ji tsoron Allah ku fadi magana madaidaiciya. Zai kyautata muku ayyukanku kuma ya gafarta zunubanku , kuma wanda ya yi daa ga Allah da Manzonsa to lalle ya rabauta babban rabo mai girma.)  Ahzab 70-71
Ya jama'ar Musulmi!
Mafi girman zunubai masu halakarwa kuma zalunci mafi muni da laifi mafi girma shine Shirka ( Hada Allah - Mabuwayi da Daukaka- da wani a cikin bauta) , duk wanda ya auka cikin shi to ya halaka, wanda ya mutu yana yin sa zai shiga wuta mai babbaka. Allah madaukakin sarki ya ce : (Lalle ne shi wanda ya yi shirka da Allah, to lalle ne Allah ya haramta masa Aljanna) Alma'ida 72
Sabo da haka na daga cikin Aduar Shugaban HANIFAWA   Badadayin Mai Rahama Ibrahim Amincin Allah ya tabbata a gare shi :(Kuma ka nisanta ni, ni da Diyana daga bautawa gumaka)
Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Duk mutumin da ya mutu yana kiran wani koma bayan Allah a matsayin kishiya  zai shiga wuta) Buhari ne ya rawaito.
Kuma yana cewa :(Duk wanda ya hadu da Allah bai hada shi da wani abu cikin bauta to zai shiga Aljanna) Muslim.
Sabo da haka duk wanda ya nemi  tsira da kubuta kuma ya nemi Alheri da tsarkaka to ya kasance ya kiyaye fadawa cikin shirka da Kuma hanyoyinsa da alamominsa na bayyane, da tafarkinsa , har ya zama cikin aminci da kwanciyar hankali a duniya da lahira, : (  Wadanda suka yi Imani basu gauraya Imaninsu ba da zalunci ba, wadannan suna da aminci, kuma su ne shiryayyu)
Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Lalle Allah ya haramtawa wuta duk wanda ya ce : Ba abin bautawa da gaskiya sai Allah ya na neman yardar Allah da hakan.) Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : (Duk wanda ya hadu da Allah a halin bai hada shi da wani to zai shiga Aljanna) Muslim ne ya rawaito
Kusaurara ,lalle  Nauuka na shirka da tushen shi  shi ne a girmama wani halitta kamar yadda ake girmama Allah  Madaukaki - ko da waye shi-. Ko kuma ka kudurta cewa suna da wasu siffofin da Allah ya kebanta da su, kuma suna gudanar da al'amura, ko kuma suna iya tunkude wani abu, Allah yace game da Annabinsa : (kace "ni mutum ne kawai kamar ku ana yin wahayi zuwa gare ni cewa : Lalle ne abin bautawarku, abin bautawa guda ne, sabo da haka wanda ya kasance yana fatan haduwa da ubangijinsa, to sai ya yi aiki na kwarai, kuma kada ya hada kowa ga bautawa Ubangijinsa).
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi :( Kar ku ketare iyaka cikin yabo na kamar yadda  aka ketare iyaka cikin yabon Masihu dan Maryam lalle ni bawa ne kuce bawan Allah kuma Manzonsa)     Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Na daga cikin misalan hakan ka rantse da wanin Allah kana girmama abinda ka rantse da shi kamar yadda ka ke girmama Allah. To wannan shirka ne Babba, kuma yana rusa aiki amma in bai kai yadda ake girmama Allah ba to ya zama karamar shirka,  ya fi girma a kan manyan zunubai,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace : Duk wanda ya rantse da wanin Allah to hakika ya yi shirka ) Abu Dawuda ya rawaito a wani lafazin ( Hakika ya kafirta ko ya yi shirka)
 Hakika Ibnu Abdulbar ya hakaito ijma'i kan cewa ba ya halatta rantsuwa da wanin Allah, na daga cikin sifa na Babbar shirka mai rusa aiki kuma mai dawwamarwa a wuta kudurta cewa wanin Allah na da ikon gudanar da duniya kuma yana iya amfanarwa da cutarwa koma bayan Allah, sabo da haka duk wanda ya kudurta kan wani sababi na da tasiri a kan kanshi  kamar wanda zai sa abin kariya (Guru ko laya) ya kudurta cewa wannan abin kariyar zai iya kawo mishi wani amfani ko tunkude mishi wani cutarwa  to wannan babbar shirka ce. Allah Madaukakin sarki yace : (Kuma idan Allah ya shafe ka da wata cuta, to, babu mai yaye ta face shi, kuma idan yana nufin ka da wani alheri, to, babu mai mayar da falalarSa.)
Na daga cikin nauoi na babbar shirka da ke faruwa a kaburbura akwai abin da wasu ke yi na fiskantar matattu da rokon su fitarwa daga bakin ciki da yaye bacin rai, suna kuma neman biyan bukatu daga gare su, kuma suna fata daga gare su dauke damuwa da bakin ciki, wannan na daga cikin mafi munin hada Allah da wani, wanda ya sabawa daawar Manzanni Amincin Allah ya tabbata a gare su, Allah madaukakin sarki ya ce :( Ko wane ne yake karba wa mai bukata idan ya kira shi kuma ya sanya ku mamayan kasa? Shin akwai wani abin bautawa tare da Allah? Kadan kwarai kuke yin tunani)
Na daga cikin hasara mafi girma ka riki mafaka koma bayan Allah Madaukaki, a duk lokacin da ka shiga matsatsi, ko wata musiba ta same ka sai ka kira: " Ya wane"  ka manta da mai iko Mai girma kuma Ubangiji  Mai tausayi   ( Lalle wadanda ku ke kira koma bayan Allah bayi ne kamar ku)
 To na daga cikin bata mai girma da shirka bayyananne ka dukufa ga kabarin wani matacce wanda bai mallakawa kansa wani anfani ko cutarwa ba, kana mishi sujada ko ka yi dawafi a kabarinsa, ko ka yi  yanka domin shi, ko ka roke shi, kana fata daga gare shi to wallahi wancan nin ku  shine babban kage, kuma babbar shirka ce, Allah madaukakin Sarki ya ce: (kuma wane ne mafi bata daga wanda ke kiran wanin Allah, wanda ba zai karba masa ba, har ranar kiyama, alhali su (wadanda ake kiran shagaltattu ne daga kiransu) Ahkaf 5
Allah madaukaki ya ce: ( kuma kada ka kirayi baicin Allah abin da ba ya amfananka kuma ba ya cutanka. To idan ka aikata haka, saanaan lailai,a lokacin ,kana daga masu zalunci.) yunus 106
Ka kasance ya kai musulmi bawa Mai ikhlasi ga ubagijinka a wajen aduarka da fatanka,da tsoronka da kaunarka da kankan da kanka da rusunawarka (Ka ce " Lalle ne salla ta da baiko na da rayuwa ta da mutuwa ta na Allah ne Ubangijin talikai. Babu abokin tarayya a gare shi kuma da wancan aka umurce ni, kuma nine farkon masu sallamawa.) An'am 162-163
Daga nan ne Mafi girman masu kira zuwa ga tauhidi mai kare sassan shi ya tsine wa masu rikan kaburburan Annabawansu  masallatai kuma ya ambata cewa sune mafi sharrin halitta a gurin Allah, yace : " Ku saurara kada ku riki kaburbura masllatai don na hane ku daga wannan.) Muslim ne ya fitar da shi
An karbo daga Abdullahi dan Abbas ya ce : " Manzon Allah ya tsine wa mata masu ziyartar makabarta masu rikon sa gurin bauta suna kunna fitilu," ) Abu Dauda da Tirmizi suka rawaito kuma ya ce Hadisi ne Hasan.
Na daga cikin kwadayinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na kiyaye hakkin Allah mai girma shine Tauhidi tsarkakke gare shi madaukaki wanda Annabi ya kwadaici kiyaye shi da dukkan magana da aiki da kauda kai domin bada kariya a gare shi.
Ya roki Ubangijinsa kamar yadda Malik ya rawaito shi a mawadda, sai Mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: Ya Allah kar ka sanya kabari na gurin bauta, fushin Allah ya tsananta  ga mutanen da suka riki kabarburan Annabawansu gurin bauta.
Kuma Manzon Allah ya toshe duk wata kofa da za ta kai ga shirka da Allah madaukaki, sai yace: ( Kar ku sanya kabari na idi ku mi salati gare ni don salatinku na riska na a duk in da ku ke) Abu Dauda ne ya rawaito, Marawitarsa duk amintattu ne, Wato kar ku maida kabari na ya zama gurin kai komo, a wasu sanannun lokuta.
Ya kai musulmi ka kiyaye wadannan musibu masu girma, da manyan zunubai  masu halakarwa, ka sani shaidan na madakata yana kawata wa bayi shirka da hanyoyin shi kuma yana yin shamaki tsakaninsu da Tauhidi da haskensa.
 Wasu malamai masu tantancewa " Shaidan na batar da bani Adam da gwargwadon  iyawarsa… har zuwa inda yake cewa hakanan masu bautan taurari da gumaka wani sa'i ma shaidanu kan yi magana da su, su sami wani sashi na bukatunsu , rokon wadan da basanan da kuma matattu na daga cikin wannan babin , sai shaidan ya suranta musu siffar wannan da ake neman agaji agunshi,  don ya biya wani sashi na bukatum me neman a gajin, har ya zaci cewa wannan mutuminne ko kuma mala'ika ne a cikin suransa, alhali kuwa shaidan ne  asalin shi ne lokacin da aka hada Allah da wani kamar yanda shaidanu suka kasance sukan shiga cikin gumaka su yi magana da mushirikai, kuma ya ce : ( a wasu lokatan shaidan yana fitowa mai rokon wanin Allah a wani sifa, har ma yakan samu wani sashi na bukatunsa)
   HUDUBA TA BIYU
Ita ibada hakki ne kebantacciya ga Allah, Allah madaukakin sarki ya ce a farkon umarni da yazo cikin Alkur'ani : (( Ya ku mutane ! ku bauta wa Ubangijinku, Wanda ya halicce ku, ku da wadan da suke daga gabaninku, tsammaninku, ku kare kanku!.) Bakara 21
  Manzonmu  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: ((kuma hakkin Allah akan bayi shi ne, su bauta mishi kar su hada shi da wani)) Buhari da Muslim suka rawaito.
Ibada suna ne da ya tattaro dukkan wani abinda Allah yake so kuma ya yarda da shi , na fadi ne ko aiki, na bayyane kamar sallah da zakka da azumi da hajji da sauran abubuwa da aka yi umarni, da kuma na boye kamar tsoro da so da firgici da fata, to  duk wanda ya aiwatar da wani abu na daga cikin wannan ga wanin Allah to hakika yayi shirka da Allah madaukaki  mabuwayi . To ka kiyaye ya kai dan uwa musulmi na daga wannan, dukkan kiyayewa  ,domin shi ne hadari mafi girma da cuta mafi muni.
   

          

ALFAHARI NA SHAIK ABDUL BARI ASSUBAITI (HUDUBAR 9 ZUL KIDA 1437 AH

Hudubar Juma'a daga Masallacin Annabi 9/11/1437 Tare da Sheikh Abdulbari Al subaiti
Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya  sun tabbata ga Allah, Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, godiya mai yawa da tsarkaka da albarka a cikinta,dukkan godiya da falala tasa ce, kamar yadda ya tsarkake zukatan bayinsa da tausayawa juna, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, wanda ya sanya tunkudedeniya sunna ta rayuwa,na shaida shugabanmu kuma Annabinmu Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa ne, ya gargadi da jifan juna da kauracewa da alfahari, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa, wadanda babban sifa ta 'yan uwantakarsu akwai kawaici da yafiya ga juna,    
Bayan haka:
Ina muku nasiha da ni kai na da tsoron Allah, Allah madaukakin sarki ya ce :(ya ku wadanda suka bada gaskiya! Ku ji tsoron Allah ku kasance cikin masu gaskiya) Tauba 119
Yayin da muka yi lura da koyarwar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da rayuwarsa za mu samu ya yi nesa da dorawa kai nauyi da wuce gona da iri a maganganunsa da ayyukansa da abincinsa. kuma musulunci ya koyar da mu : cewa duk yadda ayyuka suka daukaka suka yi kyau to ba zai dace a yi alfahari da shi ba muddin ya rasa imani, Allah madaukakin sarki ya ce (: Shin kun sanya shayar da mahajjata da rayar da masallaci mai alfarma kamar wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, kuma ya yi jihadi a cikin hanyar Allah, ba su daidaita a wurin Allah) Tauba :19
Amma yin alfahari da kai da ambaton  kyawawan halaye da matsayi na kabila ko dangi da tinkaho da ta'adodi da ji da kai da bayyana niimomi da sunan isa, to sifofi ne ababan zarga, kuma naui ne na rauni irin na dan adam, kuma  dalili ne na raunin mutum da rashin cikan hankalinsa, Allah madaukakin sarki ya ce : ( Lalle Allah bai son dukkan mai takama mai alfahari) Lukman :18
Mafi hadarin sura na alfahari da ke  barazana ga akidar musulmi shi ne Riya, wanda Annabi ya siffanta shi da karamar shirka, shi ne mutum ya tashi ya na sallah sai ya kawata sallarsa sabo da sanin wani mutum na kallonsa,  )
Na daga cikin sifofi na alfahari akwai bayyana sabo, wanda zai haifar da mummunar karshe ga maabocinsa.
Alfahari da jiji da kai  ya bata sunan maana mai kyau da kararamci ke dauke da shi, ta hanyar sanya israfi da almubazzaranci har ya kai shi ga wauta da musu da kafurcewa niima, da almubazzaranci da musulunci ya hana.
Alfahari da isa ya hada da dagun kai da tinkaho,  wanda ya ginu akan ji da kai da riya da girman kai , Allah madaukakin sarki ya ce :(Alfahari da yawan dukiya da dangi ya shagaltar da ku,*Har kuka ziyarci kaburbura) Takasur 1-2.
Masu alfahari sun ta'allaka ne da abubuwa na zahiri, sakamakon juyawan maauni, da fadawa cikin wahamin cewa  karfi na ga abubuwan shigowa na kayan masarufi na rayuwan duniya mai juyawa da gushewa.
Ba ya boyuwa ga mai hankali cewa : dukiya da lafiya da kyau da matsayi kyauta ne na ubangiji Mabuwayi da daukaka, kuma suna juyawa, to ya wajaba ga mutum ya fiskance su da kankan da kai ba da tinkaho da alfahari ba.
Kur'ani ya bayyana  halin wadanda su ke alfahari da dukiyansu da 'ya'yansu sai ya ce :(Mu muka fi yawan dukiya da 'ya'ya kuma mu ba abin azabtarwa ba ne.) saba'I 35. sai Allah mabuwayi da daukaka  ya maida martani a gare su :(dukiyoyinsu da 'ya'yansu ba za su wadatar musu da komai ba daga Allah.) Ali Imran :10
Shuhura cuta ce mai tsanani, masu nemanta da kauna sune masu gudu bayan kawawainiya, basu damu ba ko da kuwa zai kai ga sabawa addini da kyawawan halaye, mai neman shahara na rayuwa ne a daure a gaban idunuwan wadanda zai burge, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Duk wanda ya sanya tufafi na shuhura ta Allah zai sanya mishi tufafi na kaskanci ranar alkiyama).
Na daga cikin gurbi mafi hadari da alfahari ke haifarwa akwai lalatawa musulmi  addini : domin addini na iya lalacewa sakamakon kwadayin daukaka na duniya. Musamman idan mutum ya nufi riya ko neman a san shi ko a ji shi. Wannan dabiar na haifar da kaskanci da walakanci da tozarci Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :( Duk wanda ya nemi a ji shi to Allah zai sa a ji shi kuma  wanda yayi riya da aikinsa Allah zai sa aga aikin nasa )   Bukhari ne ya rawaito
Kamar yanda alfahari a cikin ibada na tafiyar da albarkan aikin ya kuma lalatashi Allah madaukakin sarki ya ce (shin dayanku na son cewa wani lambu ya kasancewa a gareshi na dabinai da inabi koramu tana kwarara a cikinta yana da dukkan ya‘yan itaciya acikinta alhali tsufa ya riskeshi kuma yana da zuri'a rawnana kuma guguwa ta sameta da wuta take cikinta ta kone kurmus ) Bakara 266.
To wannan aiki na gari asalinshi  kamar gona ne me girma me yawan ya'yan itace, shi kuma bayyana aiki da nufin alfahari da riya kamar iska ne mai wuta aciki da ya afka ma gona zai gama da ita gamawa sai ya tafiyar da duk albarkatunta ya lalata ta.
Mutun ya kan zame a gidansa da kewayen iyalansa da wani abu na alfahari da isa ta hanyan bijiro da wasu abubuwa na zamantakewa da barna a shimfidi da kayayyakin gida da sura ko mutum mutumi, wanda haka ya kunshi  ketare iyaka a wurin sadaki da bukukuwan aure.
Alfahari yana zamar da  mutum ya fada  zuwa ga mantuwan  godewa mai ni'ima da yaba wa falalansa  Allah madaukakin sarki ya ce ( idan tsanani ya samu mutum sai  ya roki ubangijinsa  yana komar da alamarinsa zuwa gare shi sannan ida ya bashi ni'ima daga gareshi sai ya mance abinda ya kasance yana kira zuwa gareshi gabannin haka )Zumar 8.   wato zai rika takama da alfahari da ni'ima sai  ya manta da ubangijinsa da ya kasance yana bauta masa yana kankan da kai zuwa gare shi.
Alfahari : abu ne me tunkudawa zuwa ga rena wasu, kamar yadda haka ya bayyana a halin iblis cikin Fadinsa (ni na fishi alheri ka halicceni daga wuta kuma ka halicce shi da tabo)A'araf 12,  to sai  ya jingina zalunci zuwa ga ubangijinsa a nashi zaton cewa shi ne mafifici.
Dauka wa kai alfahari da tinkaho yana lalata tunanin musulmi game da sako na cigaba da raya kasa  :  gudu bayan da'awar banza da kuma abubuwa na zahiri wanda akwai yaudara a cikinsu  yana jefa  mutun musulmi ne zuwa ga sha'awe sha'awen rayuka da kuma nitso  cikin abin da bai da amfani na daga ayyuka.
Na daga cikin illolin alfahari yana rusa al'umma,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi  ya ce (kawai Allah yana taimakon wannan alumman ne saboda masu rawninta, kuma da adduoinsu da kuma sallolinsu da kuma tsarkake niyyarsu ) nasa'I ne ya rawaito
 Wannan yana bayyana cewa riya da kwadayin abubuwa na zahiri sababi ne na galaba akan al'umma.
A cikin alfahari da tinkaho da aikin alkhairi akwai  tunzura zuciyan musulmai  daga marasa galihu cikinsu wanda suke cikin kunci na rayuwa sakamakon rashin abin hanu, na daga cikin illoli na alfahari da tinkaho yaduwar hasada yayin da mutum yake magana akan ni'imomin da Allah yayi a gareshi  ta hanyan takama da alfahari da ruduwa, ko ta hanyan janyo hassadar mahassada.
   saboda haka kuma da waninsa  musulunci ya gandaya  ukuba mai tsanani akan yin alfahari da takama,da tinkaho da duk surorin shi da nau'ukanshi,  har a tafiya   Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce : (yayin da wani mutumi  yana alfahari yana tafiya a cikin tufafinsa kansa  na burge shi Allah sai ya nitsar da shi a kasa  yana nitso a cikinta har rana kiyama )  muslim ne ya rawaito shi
Allah sa mini albarka ni da ku ya amfane ni da ku da abin da ke cikinsa na ayoyi, da ambato mai hikima, iya abin da zan fadi ina neman gafarar Allah mai girma ga ni da ku da sauran musulmai daga dukkan zunubai, ku nemi gafararsa shi mai gafara ne kuma mai jinkai.



Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah da ya yi halitta ya daidaita, wanda ya kaddara kuma ya shiryar, ina gode masa – tsarki ya tabbata a gare shi- ina godiya a gare shi bisa ni'imominsa da ba za su kidanyu  ko akididdige su ba, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, Madaukaki kuma Mafi daukaka.Na shaida shugabanmu kuma Annabinmu Muhammad bawansa ne, kuma Manzonsa ne, wanda aka turo shi da haske a shiriya, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,da iyalansa da sahabbansa, wadanda suka biyo sawunsa.
Bayan haka:
Ina muku wasiyya da ni kai na da jin tsoron Allah – Mabuwayi da Madaukaki.
idan ni'imomi suka bayyana a tattare da mutum ba tare da nufin ya bayyana su  ba ko yayi dagun kai ga wasu ba  to wannan ba laifi  Allah ya ce : ( kace wanene ya haramta adon ubangiji wanda ya fitar da shi saboda bayi da dada'da na arziki) A'araf 32
An umurci musulmi da ya ambaci ni'imomin da Allah ya yi masa kamar yadda Ubangijinmu yake so ya ga alamar  ni'imarsa ga bawansa ta hanyan godiya a gareshi – Mai tsarki da daukaka - da kyakyawan yabo ba wai ta fiskan alfahari ba  Allah ya ce : (kuma amma ni'imomin ubangijinka sai ka fada (domin godiya) Adduha 11
babu laifi a shari'ance a boye ni'ima, kai shi ne ma asali idan har ma'abocinta  yana tsoron hasada da kambun ido,  Allah ya ce game da Annabi ya'akub (yace ya kai dan yaro na kada ka labarta mafarkinka ga yan uwanka kada su maka kaidi, kaidi hakika shaidan ga mutum makiyi ne bayyanenne )Yusuf 5
  kuma Manzon Allah tsira da amincin Alla su tabbata a gare shi ya ce (ku nemi cimma bukatunku ta hanyar boyewa domin duk wani ma'abocin ni'ima abin abin a yi mar hasada ne ).
Ku saura! Ku yi salati – ya ku bayin Allah-  ga Manzon Shiriya, hakika Allah ya umarce ku da hakan a cikin littafinsa sai ya ce: ( Lalle Allah da Mala'ikunsa suna salati ga Annabi, ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da sallama tabbatacciya.) Ahzab 56.
Ya Allah ka yi salati ga Muhammad da matayensa da zuriyarsa, kamar yadda ka yi salati Ibrahim da Alayensa, ka sa albaka ga Muhammad da matayensa da zuriyarsa, kamar yadda ka sa albarka ga Ibrahim da iyalansa.
Ya Allah ka yarda da khalifofi guda hudu shiryayyu: Abubakar da Umar da Usman da Aliyu da Iyalai kuma da sahabbai masu daraja, ka game  mu tare da su, a afuwarka  da karamcinka da kyautatawanka, Ya Mafi jinkan masu jinkai,
Ya Allah ka daukaka musulunci da musulmai, Ya  Allah ka daukaka musulunci da musulmai, ka kaskantar da kafurci da kafurai, Ya Allah ka rusa makiyanka kuma makiya addini, Ya Allah ka sanyawa wannan garin aminci da natsuwa, da sauran garuruwa na musulmai.
Ya Allah duk wanda ya nufe mu ko ya nufi musulunci da musulmai da mugun nufi to ka shagaltar da shi da kansa, ka sanya halakarsa cikin mugunyar shirinsa, ya Mai sauraron Adua.
Ya Allah mai saukar da littafi, Mai tafiyar da girgije, Mai ruguza runduna,ka rusa makiya musulunci, ka taimake mu akan su ya ubangijin talikai, ka taimake mu a kan makiyanka makiya addini, da rahamarka ya mafi jinkan masu jinkai.
Ya Allah muna rokonka shiriya  da takawa da kame kai da wadata.
Ya Allah muna rokonka dukkan alheri na gaggawansa da na nesa, wanda mu ka sani da wanda ba mu sani ba, muna neman tsarinka daga dukkan sharri, na kusa da na nesa, wanda muka sani da wanda ba mu sani ba.
Ya Allah muna rokonka Aljanna, kuma muna neman tsarinka daga wuta.
Ya Allah ka gyara mana addininmu,wanda shi ne tsari ga al'amuranmu, kuma ka gyara mana duniyarmu wanda rayuwarmu ke cikinta, ka gyara mana lahirarmu wanda gare ta zamu koma, ka sanya rayuwarmu kari ne ga dukkan alheri. Ka sanya mutuwa ta zama hutu ne gare mu daga dukkan sharri, ya ubangijin talikai.
Ya Allah ina rokon ka alheri mafarin shi da makuran shi,da matattarin shi, da farkon shi da karshen shi, na bayyane da na boye, muna rokon ka darajoji  madaukaka a Aljanna, ya Ubangijin talikai,
Ya Allah ka taimake mu kar ka taimaki wani akan mu, ka bamu nasara, kar ka bawa wani nasara akanmu, Ya Allah ka shirya mana yadda zamu iya maida makircin makiya akanmu, kar ka basu dama da zasu iya mana makirci, ka shirye mu kuma ka saukake sharia gare mu, ka taimake mu a kan wanda ya zalunce mu.
Ya Allah ka sanya mu masu anbatonka, masu godiya a gare ka. Masu kankan da kai gare ka, masu komawa da rusunawa gare ka.
Ya Allah ka karbi aduarmu.ka tafiyar da kullin zuci daga kirazanmu, ya Ubangijin talikai, Ya Allah ka jikan matattunmu, ka bada lafiya ga marasa lafiyanmu, ka jibinci al'amuranmu, ka yaye mana bakin-ciki.
Ya Allah ka kiyaye Mahajjata ga dakinka mai alfarma, Ya Allah ka kiyaye Mahajjata ga dakinka mai alfarma, Ya Allah ka kiyaye Mahajjata ga dakinka mai alfarma, ka nesantar da su daga sharri da zunubai.
Ya Allah ka maida su gidajensu lafiya, suna halin samun nasara da lada ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka sanya shi Hajji ne mabruri Wanda aka yi wa Allah biyayya a ciki. Kuma ka sa aikin su ya zama abin godiya  zunubansu kuma abin gafartawa, da aiki na kwarai karbabbe ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka datar da jagoran mu cikin abin da ka ke so kuma ka yarda da shi, ya Allah ka datar da shi zuwa shiriyarka , ka sanya aikin shi cikin yardarka  ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka datar da dukkan jagororin musulmai zuwa ga aiki da littafinka,da yin hukunci da shariarka, ya mai jinkan masu jinkai.
(Ya Ubangiji Mun zalunci kawunanmu muddin baka gafarta mana ka yi mana rahama ba lalle za mu kasance cikin hasararru) A'araf 22
(Ya Ubangiji ka gafarta mana da 'yan uwanmu da suka riga mu da imani, kar ka sanya kulli a cikin zukatanmu game da wadanda suka yi imani, ya ubangiji lalle kai mai tausayi ne kuma mai jinkai) Hashr 10
( Ya ubangiji ka ba mu kyakkyawa a nan duniya kuma ka bamu kyakkyawa a lahira  
Kuma ka kare mu daga azabar wuta) Bakara 201.
(Lalle Allah na yin umarni da adalci da kyautatawa da bai wa ma'abocin zumunta. Kuma yana hani ga alfahasha da abin da aka ki da zalunci, yana muku gargadi ko zaku waazantu). Nahl 90
Ku ambaci Allah sai ya ambace ku, ku gode mishi bisa ni'imominsa zai kara muku, ambaton Allah shi ya fi girma Allah ya san abin da ku ke aikata wa.