الجمعة، 6 أكتوبر 2017

FARAUTAR MATA DA KAI MUSU FARMAKI

HUDUBAR JUMA'A NA MASALLACIN ANNABI TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI NA  16-1-1439 NA SHAIKH ABDULBARI AL-SUBAITI
HUDUBAR FARKO:
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI
Bayan haka:
Musulunci ya karrama dan Adam  da  cikakken rayuwa ta natsuwa  da aminci da zaman lafiya da duk abin da ya kumsa,  shari'ar Musulunci ta siffantu da siffa ta kamala da gamewa na hukunce –hukuncenta ,  ta kuma kewaye al'umma da dukkan wata katanga da kyawawan halaye da dabi'u wanda zai kare ta daga dukkan bangarorin ta  ya janyo ta  zuwa ga kyawawan dabi'u  da ayyuka  nagari ,  wanda zai kauda ta ta yi nesa daga  munanan halaye da siffofi marasa kyau,  Allah madaukakin sarki ya ce : (( A yau na kammala muku addininku kuma na cika ni'ima ta a kan ku , kuma na yarda da Musulunci ya zamo addini a gare ku ))
   Koyarwar Musulunci  ya iyakance dukkan wasu laifuka ,   ta hanyar toshe sabubanta ,  da kuma hana abubuwan da za su janyo ta   , ya gama da ita tun tana karamarta ,  domin kariya da amincin al'umma ,  domin  kulawa  da hakkin daidaiku,  kamar yanda Musulunci   ya toshe kofofin bullan laifuffuka  ta hanyar bada tarbiya ga al'umma  bisa ga kyawawan dabi'u da halaye na gari  da kuma gina  kariya na fadawa ga tabarbarewan halaye ,  shari'a ta wajabta dokoki da kisasi  ,  da kuma   hukunci na horo don amincin al'umma gaba daya  Allah madaukakin sarki ya ce ((kuma kuna da rayuwa a cikin kisasi,ya ma'abuta hankula;   tsammaninku, za ku yi takawa)).
Na daga cikin manyan laifuka   da al'umma ke dandanan azabanta,  dukkan masu hankali sun yi tarayya bisa ga muhimmancin yaki da ita ko hana faruwanta  akwai  laifin  farautar mutunci 'yan mata da firgita su wanda zai kai   zuwa ga abin da aka haramta  ta hanyar batarwa ko cutarwa da yaudara ;  shi din wani banzan dabi'a ne   kuma barna ne  abin kyama ,  ana  amfani da shi wurin tafiyar da zuciya da tada sha'awa , wannan laifin na da illoli da suka kai makura ;  cutarwan ta mafi girma ya boyu ne cikin fadawa ga abin da Allah ya haramta , da kuma tada hankulan al'umma da kuma cututtuka irin na zuci  ga wanda abu ya shafa , wanda hakan yakan kai  zuwa ga fadawa   ga kololuwan sharri,   yakan zamar da mutum ya gangara da shi zuwa ga sharri mafi zurfi  ,  ko ma ya kai ga kashe kan shi .
 Tsawatarwa masu farautar mata da kai hari da farmaki  don keta mutuncinsu, masu isgilanci masu wasa , abu ne  da  ya ke na wajibi a shari'a  ,  kuma abu ne  da yake na tilas a zamantakewa . Allah Madaukakin sarki ya ce: (( Kuma wadan da suke cutar muminai maza da muminai mata, ba da wani abu da suka aikata ba , to lalle sun dauki  kiren  karya da zunubi bayyananne)).
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (( Lalle mafi sharrin mutane matsayi  a ranar alkiyama a wurin Allah  shi ne wanda mutane suka kyale shi ko suka guje shi  don tsoron alfashan shi )).
Rikan farautar mata da kai musu  farmaki a matsayin laifi , da kuma yakansa  aiki ne mai daraja , kuma akwai tsaida hukunci na Allah  ta hanyar tsoratar  da duk wanda ya ke so ya kawo barna a doron kasa  ,  da kuma kunna wutar fitina , da kawo tashin tashina  ga aminci  ya kuma doge cikin bata ,  hukuncin Allah na kiyayewa mutane mutuncin su  da sum'ar su da kuma karamar su ; Nasa'I da Ibn Maja sun rawaito daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi  , cewa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata  a gare shi ya ce : (( Haddi da za a tsaida a doron kasa ya fi alheri ga mutanen bisa a musu ruwa na kwana arba'in))
  Ga kira na Alkur'ani mai girma ga muminai , da su yi nesa da bin hanyoyin shaidan  Allah madaukakin sarki ya ce (( Kuma kada ku kusanci abubuwan alfasha  abin da ya bayyana daga gare ta  da  abin da ya boyu))
 (( ya ku wadanda suka yi imani kada ku bi hanyoyin shaidan ,    Kuma wanda ke bin hanyoyin shaidan ,  to, lalle ne shi  yana umurni da yin alfahasha da abin da  aka ki )).
Dukkan wannan domin a toshe kofofin sharri ne  da kuma wanda  da ya ke kokarin yada alfahasha   a cikin wadan da suka yi imani .
 Kai farauta da farmaki ga mata  mummunar sifa  ce  da a ke samun su daga wadanda suke masu raunin hankali kuma wawaye , marasa lafiyan zukata ,  masu illa a dabi'u  kuma marasa mutunci , wadan da suke aikata ayyukan assha.
Laifi irin na kai farauta da farmaki ga mata   yana da salo daban-daban masu yawa , da hanyoyi  iri-iri  wanda ana fara shi ne da lafuza na batsa , da maganganu na fitsara , wanda masu aikata shi  ke yin shi,  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (( Ina muku gargadi da ku nisanci batsa  domin lalle Allah baya son masu batsa, da kuma masu neman ayi alfasha))  kuma ya ce:  (( Mumini bai zama mai yawan zagi ba ko yawan tsinuwa ko alfasha ko kuma batsa ba )).
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce ((  Ga ko wani dan Adam akwai wani kaso na daga zina ,  idanuwa biyu suna yin zina ;  zinan su kuma shi ne kallo,  hannaye biyu suma suna zina; zinan su kuma shi ne damka , kafafuwa biyu suma suna zina ; zinan su kuma shi ne tafiya , baki ma yana zina ; zinan shi kuma shi ne sumba, zuciya kuma na dimauta cikin fatan hakan, farji kuma sai ya gaskata ko kuma ya karyata shi )). Ahmad ne ya rawaito da isnadi ingantacce bisa sharadin Muslim
Idan mutum ya sakarwa  harshen sa linzami , da ya yi wasa  to, zai kai kansa ne bisa ga saraya a duniya    da kuma tsiyacewa  a lahira, Allah Madaukakin Sarki ya ce : (Ba ya lafazi da wata magana face a like da shi akwai mai tsaro halartacce)
Kuma ya ce : (ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah  ku fadi magana madaidaiciya).
Kai farauta da harin taba mutuncin mata ; wani ciwo ne mai game dukkan guri, ya ke kwankwasa dukkan kofa, kuma yana kara bazuwa a sararin samaniya, ba iyaka na wuri ko zamani,  da wasu  irin dabaru da ba a saba  da su ba, da makircin da ba a sansu ba  sai ya  ratsa cikin zuciya yana barna ya kuma gurbata hankali , ya bata kyakkyawan tunani .
 Daga cikin nau'uka na kai hari akwai amfani da  wasu hotunan bidiyo  na batsa ,  a kafafen sada zumunta  na yanar gizo, wanda a ciki akwai yada sharri  da  alfasha,  da kwadaitarwa mai ban tsoro zuwa gare ta  da cutarwa mai tsanani wanda ba za a iya siffanta shi ba , ((Lalle ne wadan da ke son alfasha ta watsu  ga wadan da suka yi imani , suna da azaba mai radadi a cikin duniya da lahira . kuma Allah shi ne ya sani , alhali kuwa ku ba ku sani ba  )).
  Masu yada wadan nan hotunan bidiyo kuma  suna masu tashi da  tallata  ta , makomar su ba kyau  , kuma karshen su abin bakin ciki ne  mai radadi : Allah ya kare mu da ku daga mummunan karshe ,   Allah madaukakin sarki ya ce: (( Domin su dauki zunuban su cikakku aranar kiyama , kuma daga zunuban wadan da suke bautarwa ba da wani ilimi ba .  to, abin da suke dauka na zunubi ya munana )).
Allah madaukakin sarki ya ce : (( Kuma lalle suna daukan kayan nauyin su ,  da wadan su nauyayan kaya , tare da kayan nauyin su , kuma lalle za a tambaye su a ranar kiyama ,  game da abin da suka kasance suna kirkirawa  na  karya   )).
Hakika cutan kai hari ga mutuncin mata da farautarsu ya yadu ne sakamakon bayyana sabo da sakaci da alfahari da kawata mummunan  abu,   kamar yanda  rashin kwanciyar hankali a gida ya ke saka 'yan mata  da yara  da mata  su zama abin farauta , mafi sauki a gun  masu kai farmaki da hari ga mutuncin mata .
Ma'abota shari'a da tunani da ra'ayi mai kyau sun san cewa lalle mafificin hanya na  kariya daga wannan mugunyar cutan, shi ne a dasa  kariya na addini  da kuma karfafan imani  da kuma bin koyarwar kur'ani , da lazimtar tsoron Allah a fadi da kuma  dabi'a da kuma runtse ido da sanya tufafi mai suturcewa , da tsarkake rayi  ta hanyar kamewa da kuma tsoron Allah. Baya boyuwa  cewa matasa suna da wani karfi  da fisgan kai na samartaka , to, amma idan ya samu saiti da nusarwa  da jan ragama , sai ya dawo kan hanyar da ya dace , tunanin shi da natsuwan shi sai su daidaita, sai ya zama cikin masu kawo gyara da gini ga al'umma , wannan kuma yana taimakawa wurin bada kariya ga al'uma daga aikin  kai farmaki ga mutuncin mata .
 Kamar yanda aure da  wuri yana kosar da bukatu, ya kan hana zaman banza kuma yana bada kariya daga munanan halaye , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (( Ya ku taron matasa  wanda yake da ikon yin aure  a cikin ku , to, ya yi aure , domin shi din ya fi bada kariya ga runtsa ido da katange farji )).
Gina alaka mai karfi da amincewa tsakanin iyaye da yara ,  yana gina mutum akan halin da yake kai nakwarai  ya kuma ba shi karfin gwuiwa  akan kyawawan dabi'un sa , kuma ya  gina mishi mazantakan shi ya cire mishi irin  dabi'un  mata , yana tarbiyantar da 'yan mata bisa ga kamun kai da suturcewa  da hijabi , amma iyalan gidan da ba su damu da  dulmuya acikin matsalolin zamani da  cin karon al'adu  da rarrabuwa kawuna ba , to   kamar wani sarari ne na shanya da masu farautar mata da kai farmakin suka samu  don kai farmakin  



    HUDUBA NA BIYU:
 Yana daga cikin abin da ya dace   a yi tsokaci a kai  kula da ba da muhimmanci kan tarbiyan yara  da kuma  rashin sakaci da su , musamman  lokacin da a ka hangi wasu munanan halaye da ake shakku a kansu.
  lalle yaki da farauta  ko farmaki ga mata da dukkan laifuka nauyi ne da ya rataya a kan kowa ,  a cikin al'uma ,  duk wanda bai ji tsawatarwan kur'ani ba da kira na imani ba to fa dole ne a wannan lokaci  ayi anfani da bulala ta hukuma.
 Hakika ya zo daga Usmanu Allah ya kara yarda a gare shi, ya ce : Lalle Allah na tsawatarwa da karfin mulki irin tsawatarwan da baya yi da kur'ani

        
    

.
  

   

الخميس، 21 سبتمبر 2017

RIBATAR DAMA A RAYUWA TA HANYAR BIYAYYA GA ALLAH

Hudubar Masallacin Annabi  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi 2/1/1439 H
Na Sheikh Abdullah Bin Abdurrahman Albuaijan
Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda sammai da kasa na shi ne, gare shi al'amura ke komawa, godiya da yabo da kyakkyawan ambato da wanzuwa nashi ne, kuma gare shi zaa koma, tsarki ya tabbata gare shi ya horar da rana da wata suna karbar juna ya kuma hore muku dare da wuni kome gare shi a kaddare ya ke.
Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya mulki da godiya na shi ne, yana rayawa kuma yana kashe wa kuma shi rayayye ne ba ya mutuwa, alheri na hanunsa kuma mai iko ne ga dukkan komai.
Na shaida Annabi Muhammadu cikamaki ne na Annabawansa  da Manzanninsa, an turo shi a lokacin da ba Manzanni  sai ya isar da sako ya kuma bada amana ya yi nasiha ga al'umma, ya yi jahadi don Allah hakkin jahadi har mutuwa ta zo mishi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da iyalansa da sahabbansa  wadanda suka yi hijira daga gidajen su da dukiyoyinsu suna neman falala na Allah da yarda.
 Da Ansar da da suka mallaki gida da imani suna son wadanda suka yi hijira zuwa gare su, basu jin wani bukata daga ransu cikin abin da su bada ko sun kasace mabukata.
Da kuma wadanda suka bi sawunsu su ka bi su da kyautatawa,da aminci tabbatacce mai yawa har zuwa ranar alkiyama.
Bayan haka! Lalle mafi gaskiyan zance shi ne littafin Allah mafi karfin abin riko shi ne kalmar takawa, mafi alherin addini shi ne addinin Ibrahim, mafi kyan kissoshi shine Alkur'ani, kuma mafi kyan shiryarwa shine shiryarwar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, mafi al'amura shi ne fararrunta, dukkan bidiah bata ne.
Ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah hakkin tsoronsa, kar ku mutu face kuna musulmai)
Ya ku bayin Allah!
Duniya gidan jarabawa ne da karewa  ita kuma lahira gida ce na sakayya da wanzuwa, duniya jindadi ne na rudi, wasu sa'oi ne da kwanaki da watanni da shekaru  da zama shekaru na karewa  wasu zamuna n su zo su riska, ranaku su shude, watanni su zo su wuce, Allah na juya dare da wuni, a hakan akwai abin lura ga masu basira.
Zamani na karewa  gurace gurace na karewa , kuma ajali na cika ( kuma duk wanda ke kan ta na kare wa, fiskan Ubangijinka ne zai wanzu ma'aboci daraja da daukaka ).
*Wallahi duniya ba gidan wanzuwa ba ne* A'a ko da mutane sun gina benayenta
*Shekaru na shan banban sai dai * suna mai tsawon kwana da gajere na  daidaita  a yayin mutuwa.
Nesa ba kusa ba gidan duniya ba gidan da ake  fatan wanzuwa ba ne , farin- cikinta bai cika, mutuwa abin buri ne ga dukkan rayuka * ga mai hankali ba banbanci tsakanin benayenta da kaburanta
Yaku Musulmi!
Shekara ta kare, kuma shekarun duniya na raguwa, ga ajali na kusantowa , an rufe ayyukanta,  an nade takardunta, Madalla da barka ga wanda ya ribaci damanta, ya ribaci lokacinsa. Ya gyara ayyukansa.
Ku saurara ga mu mun shigo  farkon sabuwar shekara , wanda zai  tattara mu zuwa kabari  ya tunkuda mu zuwa ga ranar tadawa da tattarowa.
To ya dace ga duk mai zuciya da wanda ya kasa kunnen shi, ya ribaci dama ta rayuwarsa kafin nadama da da na sani, da zubar da hawaye ya riske shi, (Kada wani rai ya ce ya nadama ta akan abin da na yi sakaci a cikin  sashen Allah, kuma lalle na kasance hakika daga masu isgili,ko kuma (kada) ya ce ; da Allah ya shiryar da ni da na kasance daga masu takawa, ko kuma (kada) ya ce, a lokacin da ya ke ganin azaba da lalle ace ina da wata komawa zuwa duniya.) domin in kasance daga masu kyautatawa).
 Ya ku bayin Allah!
Lalle lokaci na shudewa rayuwa na ta tafiya, kuma rayuwar lokaci ne kankani, ga wajibabbu sun taru, ga hakkoki sun cunkushe mutum abin tambaya ne game da rayuwarsa  yadda ya tafiyar da ita da samartarsa yadda ya gudanar da ita. Kuma zaa yi mar bincike game da yadda ya sarayar da rayuwarsa, da zamanin da ya daidaitar, duk yadda shekuru ya  tsawaita to lokaci ne kankani,  ( Ya ce nawa ku ka zauna acikin kasa na kidayar shekaru? Suka ce , mun zauna a yini daya ko rabin yini sai ka tambayi masu kidanyawa. Ya ce ba ku zauna ba face kadan da dai kun kasance kuna sani, shin to kun yi zaton cewa mun halitta ku ne da wasa  kuma lalle ku zuwa gare mu ba za ku koma ).
Ya ku bayin Allah !
Lalle Allah bai halicce ku don wasa ba , kuma bai bar ku haka kawai ba, hakika ya halicci mutuwa da rayuwa domin ya jarraba ku. Ya nuna waye daga cikinku ya fi kyawun aiki.
Ku saurara! Lalle  mafi girman musiba , kuma mafi tsananin wahala  da kuma abu mafi tada hankali da bakin ciki mafi firgitawa  , shi ne ; hasara bisa sarayar da lokaci  ,  da kwacewan ajali   da cudewan sa'o'I na zamani ba tare da aiki ba ,  hasararta na farawa ne da nadamar tata  tun daga lokacin halartowar magagin mutuwa , (   Har idan mutuwa ta je wa dayan su sai ya ce : '' Ya Ubangijina ku mayar da ni ( duniya). Tsammani na  in aikata aiki na kwarai cikin abin da na bari , kayya , lalle ne! ita kalma ce shi ne  mafadinta alhali kuwa a baya gare su akwai shamaki har ranar da za a tayar da su''.
''Ya     ku wadanda suka yi imani kada dukiyoyin ku da 'ya'yan ku su shagaltar da ku daga ambaton Allah , kuma wanda ya yi haka , to wadannan  shu ne masu hasara , kuma ku ciyar daga abin da muka azurta ku daga gabanin mutuwa  ta je wa dayan ku har ya ce ya Ubangijina  don me ba ka yi min jinkiri ba zuwa wani ajali makusanci, domin in gaskata kuma in kasance daga salihai !    kuma Allah ba zai jinkirtawa wani rai ba idan ajalin sa  ya zo kuma Allah masani ne bisa abin da kuke aikatawa ''.
     To lokacin rayuwa -bayin Allah- wata dama ce na aiki  kuma  ni'ima ce da take wajabta yin godiya   ( Idan za ku kidaya  ni'imomin Allah ba za ku iya lissafa ta ba)     
Mafi alherin cikin ku shi ne wanda shekarun shi  ya tsawaita kuma ayyukansa suka kyautata, Mafi sharrin ku shi ne wanda ya yi tsawon rayuwa kuma ayyukansa  ya munana.
Ku saurara ! lalle na daga cikin godiya ga ni'ima ribatan ni'ima na lokuta , da rayuwa cikin da'a wa Allah  mabuwayi da daukaka daidai  yanda ya shasr'anta wa Annabin sa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
 A daya bangaren kuma yana daga cikin kafurcewa ni'ima ,  da sababi na bala'I da  azaba  da  hasara da kuma nadama   akwai tafiyar da lokaci da ruwa cikin sabawa Allah , ko kuma cikin abin da Allah bai shar'anta ba , (  To wanda ya aikata (wani aiki) gorgodon nauyin zarra   na alheri zai gan shi .  kuma wanda ya aikata    gorgodon nauyin zarra zai ganshi .
 Allah ya sa mini albarka ni da ku a cikin alkur'ani mai girma.
    HUDUBA  TA  BIYU
Dukkan yabo da godiya  sun tabbata ga Allah  Ubangijin talikai ya kammala mana addini  kuma ya cika mana ni'imomi ,  kuma ya yardar mana da Musulunci a matsayin addini , na shaida ba  abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya , wanda ya hada Allah da wani hakika ya bata ,   bata mabayyani.
 Na shaida Annabi Muhammadu bawan sa ne kuma Manzon sa ne , tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabban shi da aminci tabbatacce mai yawa.
 YA KU MUSULMAI
Lalle farkon wata na hijira na shekara shi ne watan Almuharram kuma wata ne mai alfarma  Allah madaukakin sarki  ya ce:  ( lalle   ne kidayan watanni a wurin Allah wata goma sha biyu ne a cikin littafin Allah ,  a ranar  da ya halicci sammai da kasa , daga cikin su  akwa hudu masu alfarma , wannanne addini madaidaici    sabo da haka  kada ku zalunci kawunan ku a cikin su )
 An karbo daga Abu bakrata Allah ya kara yarda a gare shi  daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: ''  Lalle zamani ya juyo kamar siffan shi a ranar da Allah ya halicci sammai da kasa  shekara watanni goma sha biyu , cikin su akwai guda hudu masu alfarma  uku a jere su ke :- Zulkada, Zulhijja da Almuharram,  da Rajab  na MUDAR  wanda ke tsakanin Jimada da sha'aban) Bukhari da Muslim ne su ka rawaito.
Ya ku Bayin Allah!
Na daga cikin koyarwar Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma na daga cikin masu kankare  zunubai da kuma  godiya ga Allah , da kuma girmama shi , akwai azumtar ranar ashura  , shi ne goma  ga watan Almuharram .
 An karbo daga  Dan Abbas Allah ya kara yarda a gare su, ya ce: '' Ya yin da  Annabi ya  zo garin madina ya sami yahudawa  suna azumin ashura sai ya tambaye su game da hakan sai suka ce ; wannan rana ne da Allah ya bawa  Annabi musa nasara da Banu Isra'ila a kan Fir'auna , kuma mu muna azumtar shi don girmamawa gare shi   sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata  a gare shi  ya ce: '' mu muka fi dacewa da musa akan ku , sai  Manzon Allah ya yi umarni da azumtar shi ''. Buhari da Muslim ne su ka rawaito shi
 Kuma daga gare shi ya ce :'' ban taba ganin Annabi  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana kirdadan azumin watarana ba ,  wanda ya fifita shi akan wanin shi ba face wannan ranan    na ashura da wannan wata  yana nufin watan ramadan ''.  Buhari ne ya rawaito
 Ya zo a cikin sahihu Muslim Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : '' azumin   ranar Arfa ina fata Allah ya kankare  zunuban shekaran kafin shi ,  da kuma shekaran da take bayan shi, da azumin Ashura ina fatan Allah ya kankare shekaran da take kafin shi''.
 Ya yin da  labari ya sami  Annabi   a  karshen rayuwan shi  , kan cewa yahudawa na rikan ashura a matsayin idi  , sai ya nufi  ya azumci  tara da  goma a shekara  mai zagayowa ,  sai mutuwa ta shiga tsakani , 
An karbo daga Abdullahi dan Abbas  Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: a yayin da Annabi ya yi azumin ashura   ya yi  umarni da azumtar shi sai suka ce  :'' ya Manzon Allah Yahudu da Nasara su na girmama shi  ,  sai Manzon Allah tsira da  amincin Allah su tabbat a gare shi ya ce  : idan Allah ya kai mu badi za mu azumci tara ''. yana nufin tare da goma   .  ya ce : shekaran bata kewayo ba har Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya rasu.''   Muslim ne  ya rawaito
 Abin da ya fi falala shi ne a yi azumi  guda kafin shi, sabanin na yahudawa  in hakan  bai samu ba to a yi azumin ranar goma.
Ya Ku Musulmai !
Bidia fitina ce, fitina kuma jarabawa ce,  mafi sharrin al'amura su ne fararrunta , dukkan bidi'a bata ce    dukkan bata na wuta , to ku yi riko da igiya mai karfi da tafarki mikakke,  kada ku bi hanyoyi ,  sai su kawar da ku daga tafarkin 
ku yi riko da littafin ku da shiryarwar Annabin ku , to hakika an isar mu ku,.
 (Sabo da haka ka yi riko ga abin da aka yi  wahayi da shi zuwa gare ka, lalle ne kai kana kan hanya madaidaiciya. Kuma shi (Abin wahayin ) ambato ( na daukaka ) ne a gare ka da kuma ga mutanenka, kuma za a tambaye ku.)
Ya ku Musulmai !
 Lalle abin nan da mabarnata  suke shiryawa, mujirimai ke tsarawa, makirai da mahassada ke gudanarwa, na daga makiyanmu da makiya addinin mu da garuruwanmu  wasu tawaga ne na 'yan jarida da farfaganda irin na shaidan, da kai wa mummunan hari , da wani kazamin makirci suna yi ne don karanbawul ga zaman lafiyanmu, da wargaza hadin kanmu, da kunna fitina a garuruwanmu, a tsakanin sahun mu, da keta alfarmar watanni  masu  alfarma, da warware alkawari,da janye mubaya'a da fita daga da'a da barna a doron kasa, mun gani da idanuwarmu  yadda kasashe makwabta suka koma,  na daga rugujewa, to  ku yi lura ya masu basira!
Ya Allah ka kiyaye wannan gari ya zama cikin aminci da zaman lafiya, ya Allah ka kiyaye garin daga fitintinu, ya Allah ka kiyaye shi daga makircin masu makirci, da sharrin mabarnata, da  sharrin makiya da mahassada,
Ya Allah ka kiyaye garin da sauran garuruwan musulmai, ya Ubangijin talikai,
Ya Allah ka taimaki musulmai a Borma ka kare jinin su kuma ka suturce al'auran su , ka basu aminci a abin da suke tsoro  ka yi gaggawan yaye musu bakin ciki .
 Allah ka datar da jagoran al'amarin mu mai hidima ga masallatayya biyu masu alfarma   da datarwarka , ka karfafe shi da karfafanka.
Ya  Allah ka datar da shi da mataimakin shi , da abin da a cikin shi akwai gyaran garuruwa da bayi  da abin da  a cikin shi akwai alheri ga musulunci da Musulmai , ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka kiyaye mana iyakan mu , ka bawa sojojin mu  nasara  ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka warkar da marasa lafiyan su , ka karbi matattun su, ka kiyaye su da kiyayewarka, ka kare su da kariyarka .
BAYIN ALLAH  ( Llle Allah  na yin  umurni da kyautatawa,  da  bai wa ma'abucin  zumunta , kuma yana hani da alfasha  da abin da aka ki , da rarrabe jama'a . Ya na yi muku gargadi,  dammaninku,  kuna tunawa.
(Kuma ku cika da alkawarin  Allah idan kun yi alkawari,  kuma kada ku warware rantsuwoyin ku a bayan karfafa su,  alhali kuma hakika kun sanya  Allah mai lamuncewa a kanku .  Kuma lalle Allah ne  ya ke sanin abin da kuke  aikatawa) .  


  

الخميس، 7 سبتمبر 2017

TUSHEN KARBAR AIKI IKHLASI

Hudubar Jumaa a Masallacin Annabi  na Sheikh Abdul Muhsin Alkasim 17 ga zulhijja 1438 AH
Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah muna gode masa kuma muna neman taimakonsa muna neman gafararsa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu da kuma munanan ayyukanmu, Duk wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi, wanda ya batar babu mai shiryar da shi, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, na shaida Annabi Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa ne tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa da aminci tabbatace mai yawa.
Bayan haka!
Ku ji tsoron Allah ya ku bayin Allah hakkin tsoronsa,ku yi riko da igiya mai karfi na musulunci.
Kadaita Allah da bauta shine manufa na halittawa da umarni, Allah Mai tsarki da daukaka ya ce :(Ban halicci Aljani da mutane ba face su bauta min) Da hakan ne za a raya kasa, kuma dan Adam ya samu walwala, Allah Madaukakin sarki ya ce :  (wanda ya yi aiki na kawarai na daga na miji ko mace  yana mumini to zamu raya shi rayuwa na jin dadi  kuma mu sakanya mishi da mafi kyan abin da suka kasance suna aikatawa )
Yana yarda da aiki na kwarai ya amince da shi, Allah Mai tsarki ne bai karba sai mai tsarki,
Tushen karbar aiki shi ne Imani da Allah da yin aiki don neman yardarsa, Allah Mabuwayi da daukaka ya ce : (kuma wanda ya nufi lahira kuma ya yi aiki sabo da ita irin aikinta alhali kuwa yana mumini, to wadannan aikin su ya kasance godadde.)
 Aikin kafiri a lahira abin mayarwa ne ko da wani irin aiki ya yi, Allah Madaukakin sarki ya ce :(kuma muka gabata zuwa ga abin da suka aikata daga aiki sai muka sanya shi kura watsattsiya )
A duniya zaa ciyar da shi da kyakkyawan ayyuka da ya aikata, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :(Amma shi kafiri zaa ciyar da shi da kyakkyawan abin da ya aikata don Allah a nan duniya, har idan ya koma lahira sai ya zama bai da wani aikin lada guda da zaa saka mishi.) Muslim ne ya rawaito.
Aisha Allah kara yarda a gare ta ta ce :Ya Manzon Allah! Dan Jud'an ya kasance a lokacin Jahiliyya ya na  sada zumunci kuma yana ciyar da miskinai ko wannan zai amfane shi? Sai ya ce : Ba zai amfane shi ba,sabo da bai taba cewa :" ya Allah ka gafarta min kusakurai na a ranar sakayya"  ba ko da rana daya )  Muslim ne ya rawaito.
Wanda ya bayyana Musulunci ya boye sabanin haka a zuciyarsa ba zai amfana ba da abin da ya bayyana ba kuma zaa maida masa da aikinsa ba zaa karba ba. Allah Madaukakin Sarki ya ce game da halin munafukai : (Ku ciyar bisa kuna so ko akan tilas ba za a karba daga gare ku ba lalle ne ku kun kasance ne mutane fasikai. Kuma ba bu abin da ya hana a karbi ciyarwarsu daga gare su face domin su sun kafirta da Allah da Manzon sa.)
Kaiwa da komowar ibada ya dogara ne a kan niyya da aiki, kuma sharadin karbarta ita ce tsarkake niyya da kyautata aiki, da Ikhlasi ne manufa ke yin kyau  da bin sunna ne ayyuka ke daidaituwa, Allah Madaukakin sarki ya ce : (sabo da haka wanda ya kasance yana fatan haduwa da Ubangijinsa to sai ya yi aiki na kwarai, kuma kada ya hada kowa ga bautawa Ubangijinsa).
Kuma addinin Musulunci an gina shi a kan tushe ne guda biyu, : da a bauta wa Allah shi kadai ba shi da abokin taryya, kuma mu bauta masa da abinda ya shar'anta, shi ne abin da Manzon Allah ya zo da shi, tsira da amincin Allah sau tabbata a gare shi. Kuma wannan shine hakikanin shahada biyu, kuma sune rukunai biyu na karbabbun aiki.
Jarabawa a duniya ya doru ne bisa tabbatar ikhlasi da bin sunna, Allah Madaukakin sarki ya ce :(Allah wanda gudanar da Mulki ya ke ga hannunsa, ya tsarkaka kuma shi mai iko ne akan kome. Shi ne wanda ya halitta mutuwa da rayuwa domin ya jarraba ku, ya nuna waye  daga cikin ku yafi kyawun aiki) wato wanda ya fi ikhlasi da yi daidai, Fudail dan Iyad Allah ya mishi rahama : " Lalle aiki idan ya kasanceAllah kadai aka nufa amma ba a kawo shi daida da koyarwar sharia ba to ba zaa karba ba, haka kuma idan an yi shi daidai amma ba ikhlasi to ba za a karba ba, ba za karba ba har sai ya hada ikhlasi da bin sunna, Taceccen aiki shi ne wanda aka yi don Allah, shi kuma daidai: shi ne idan an yi shi bisa koyarwar Annabi.
Hakikanin ikhlasi shi ne bawa ya nufi yardar  Allah a biyayyarsa, Allah Madaukakin sarki ya ce :(Ka bauta wa Allah kana mai tsarkake addini a gare shi)
To duk abin da musulmi  ya ke yi na da'a  an umarce shi  ne da ya aikata shi tare da tsarkake shi ga Allah Ubangijin talikai,ba zai nemi sakayya ko godiya daga wani halitta ba, Gyaruwan zuciya shi ne tushe gurin karbar aiki, aiki na gyaruwa ne idan niyya ta yi kyau, niyya ce uwa uba na wadannan aiki ita ce niyya , kuma mutum niyyarsa na kai shi inda aikin shi ba zai kai shi ba, ta iya yiwuwa aiki karami amma niyya sai ta maida shi babba, ko kuma aiki babba amma niyya ta mai da shi karami.
Yahya Bin Abi kasir Allah ya mishi rahama ya ce : (ku koyi niyya don tafi tasiri bisa aiki)
Dukkan ibadar da baa yi ikhlasi ba da kyakkyawar badini ba to ba a karbar ta, ikhlasi bai haduwa a zuciya tare da kaunar yabo da kyakkyawan ambato, da kwadayin abin da ke hanun mutane, bin Annabi sharadi ne a gun karbar aiki, in an rasa shi to aikin abin maidawa ne ga mai shi, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Duk wanda ya aikata aiki ba umarnin mu a ciki to an maida mishi da kayansa).Bukhari da Muslim ne suka rawaito.
Sa'id Bin Jubair Allah ya mishi rahama  ya ce : (Ba a karbar fadi sai da aiki, ba za a karbi aiki ba sai da fadi, ba za a karbi fadi da aiki da niyya ba sai da bin sunna )
Sanya tsoron Allah a cikin ayyuka na daga sababi na karbar ayyuka Allah Madaukakin sarki ya ce : (Allah na karba ne daga masu takawa) 
Musulmi na da tsananin tsoro ga kan sa,kada ya zama bai cikin su,ba za a karbi aikinsa ba,wannan shi ne halin magabata, Abu Darda Allah ya kara yadda a gare shi ya ce : (Da na samu yakinin Allah ya karba sallah ta guda   yafi min duniya da abin da ke cikinta sabo da Allah na cewa : " Allah na karba ne daga masu takawa".
Wanda  ya ji tsoron Allah da ikhlasin aikinsa  da kuma bin sunna, to ya dace Ubangiji  mai karamci ya karbe shi.)  Sheikhul Islam Allah ya mishi rahama ya ce : (A gun Ahlussunna waljama'a ana karbar aiki daga wanda ya ji tsoron Allah a cikinsa  ya yi da ikhlasi don Allah yana bin daidai da umarnin Allah,duk wanda ya ji tsoronsa a wani aiki to zai amsa masa ko  da yana sabo a waninsa, wanda bai ji tsoron shi ba a cikinsa ba zai karba masa ba ko da yana mishi biyayya a waninsa.)
Yin da'a bayan da'a alama ce ta karbarta, Allah Madaukakin sarki ya ce :(Kuma wadannan da suka nemi shiryuwa (Allah) ya kara musu shiryuwarsu kuma ya basu (sakamakon takawarsu).
Alhasan AlBasri Allah ya mishi rahama ya ce : (Na daga sakayyar kyakkyawa a bi ta da kyakkyawa, na daga ukuba ta mummuna a bi ta da mummuna,  abin mamaki da kyakkyawa  ta biyo mummuna don za ta goge ta, tir da aikata mummuna bayan kyakkyawa don zata lalata ta, ta debe albarkarta. Wanda bai kasance cikin kari na da'a ba to kuwa yana cikin ragi
Saukin ibada ga ma'abocin shi  da kaunan aikin alheri albishir ne na duniya,Allah Madaukakin sarki ya ce: (To amma wanda ya yi kyauta kuma ya yi takawa, kuma ya gaskata kalma mai kyau, to za mu saukake masa har ya kai ga sauki)
Tsayuwa a kan aiki da tabbatuwa akan da'a dalili ne na alheri da dace,Ibnu kasir Allah ya yi mishi rahama: ( Allah na tafiyar da al'adarsa cikin karamcinsa bisa wanda  ya rayu a kan abu zai mutu a kai,in har ya mutu a kan wani abu to  za a tashe shi a kai ranar Alkiyama.)
Na daga koyarwar Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi akwai  dawwama a kan aikin alheri  ya kasance yana cewa : (Mafi soyuwar aiki a gun Allah shi ne wanda aka dawwama akai ko dan kadan ne.)Bukhari da Muslim ne suka rawaito
Gyaruwar gabbai da daidaituwarta na daga cikin fa'ida na karbuwar aikin daa , da kaunar ma'abocinta, Allah Madaukakin sarki ya ce  a hadisin Alkudsi : (Ba abin da bawa na  zai kusance ni da shi da ya fi soyuwa a gare ni kamar abin da na  farlanta mishi bawa na ba zai gushe yana kusanta na da nafila har na so shi,idan na so shi sai na zama jin shi da ya ke ji da shi da ganin shi da ya ke gani da shi da hanun shi da yake damka da shi da kafarsa da ya ke tafiya da ita kuma idan ya roke ni zan ba shi, in ya nemi tsari na zan bashi tsari )Bukhari ne ya rawaito.
Shanin mumini kokari cikin ibada da ganin aikin shi kankani, idan ya kammala wani biyayya sai ya sadar da wata ibada,bai nunawa ga Ubangijin shi yawan aikin sabo da in an kwatanta da abin da ya yi mar na ni'ima ya bashi kadan ne,) Allah ya ce : (kada ka yi kyauta kana neman kari) Duk wanda ya shaida hakikanin rububiya da hakikanin Ubudiyya, ya san Allah Ubangijinsa zai bayyana a gare shi, shi ,ba kome ba ba ne, ba wanin mu da shiga Aljanna a cikin mu don aikin shi sai dai da falalar Allah da karamcin sa da rahamarsa. Ibnu Abu Mulaika Allah ya mi shi rahamayace : " na riski  talatin daga cikin sahabbai kowannen su na tsoron munafunci a kansa, ba wani daga cikinsu da ke cewa yana da imani irin na Jibrilu da Mika'il "
Istigfari bayan da'a da bayyana gajartawa hali ne na bayin Allah masu ikhlasi, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Sun kasance a lokaci na dare kadan su ke yin barci,kuma alokacin asuba suna ta yin istigfari)
Ibnul kayyim Allah ya mishi rahama ya ce : (Alamar karbar aikin ka shi ne ka rena aikin naka ka kankantar da shi, ka kalle shi karami a zuciyarka har ya kai wanda ya san Allah zai rika neman gafara a karshen aikin sa na daa).
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kasance  idan ya sallame daga sallah yana neman gafarar Allah sau uku"
Kuma Allah ya umarci bayin sa bayan aikin hajji da neman gafara, ya kuma ya yabe su sabo da neman gafara a karshen tsayuwan dare, Manzon Allah ya shar'anta a karshen Alola tuba da istigfari, duk wanda ya shaida wajibin Ubangijinsa da gwargwadon aikinsa,da laifin kansa to dole ne  ya nemi  gafarar Ubangijinsa daga gare shi ya kuma rena kansa da aikinsa ya dauke su ba komai ba  ya rena kansa.
,    Allah ya yabi bayinsa da fadinsa  :( Da wadanda ke bayar da abin da suka bayar alhali kuwa zukatarsu  suna tsorace domin suna komawa  zuwa ga Ubangijinsu  )
Aisha ta ce ya Manzon Allah ! shin su ne su ke shan shan giya suna sata, sai yace a'a ya 'yar siddik sai dai su ne wadanda suke azumi suna sallah suna sadaka amma suna tsoron kar baa karba musu ba (Wadancan suna gaggawar tsere a cikin ayyukan alheri  alhali kuwa suna masu tserewa zuwa gare su(Ayyukan alheri)Tirmizi ne ya rawaito
Shi Mumini yana hada Ihsani da tsoro, Abdul'Aziz Dan Abi Rawad (Na riske su su na kokari cikin ayyukan kwarai idan su aikata shi sai su shiga damuwa na shin ko za'a karba musu ko a'a,)
Na daga cikin abu mafi girma na sababin karbar aiki da samun biyan bukata akwai rokon Allah hakan, to Ibrahim daIsma'il Amincin Allah ya tabbata a gare su a halin suna daga tubalin dakin ka'aba kuma suna rokon Allah, (Ya Ubangijin Mu ka karba daga gare mu lalle ne kai kai ne Mai ji Mai sani,)
To 'yar Imrana ta yi bakancen abin da ke cikin ta don hidima ga Masallacin Aksa, ta kasance tana adu'a  tana cewa : ( ya Ubangiji na lalle ne ni na yi bakancen abin da ke cikin ciki na gare ka ya zama 'yantacce, sai ka karba daga gare ni.lalle ne kai kai ne mai ji , masani ).
Annabi ya yi laiha sai ya ce : Ya  Allah ka karba daga Muhammad da Iyalan Muhammad    da kuma daga Al'umar Muhammad) Muslim ne ya rawaito.

 Godiya tafarki ne na karbar aiki, kuma kofa ne na kari Allah ya ce : (kuma alokacin da Ubangijinku ya sanar Lalle ne idan kun gode ina kara muku)
Kuma bayin Allah na cewa  :( Ya Ubangiji na ka kange ni domin in godewa ni'imar wadda ka ni'imta a kai na da kuma a kan Mahaifa na biyu, kuma domin in aikata aikin kwarai, wanda ka ke yarda da shi, kuma ka kyautata mini a cikin zuriya ta, lalle ni na tuba zuwa gare ka kuma lalle ni ina daga masu sallamawa  (ga umarninka)
Sai Allah ya musu alkawari da fadinsa  ( Wadancan ne wadanda muke karba daga gare su, mafi kyawun abin da suka aikata kuma muke gafarta mafi munanan ayyukansu,(suna ) a cikin 'yan Aljanna akan wa'adin gaskiya wanda suka kasance ana yi musu alkawari (da shi).
 Musulmi na kodayin a karba masa aikinsa kuma ya na kokari don  tabbatar da haka kuma yana taka tsantsa don tsananin  tsoron lalacewan aikin da rushewansa,  ba wai ya tsaya a aiki kadai ba a'a amma al'amarin ya hada da kiyaye aikin  bayan gama shi daga abin da zai bata shi ya rusa shi, mafi girman shi shi ne hada Allah da wani, Allah Madaukakin sarki ya ce :(Da sun yi shirki da hakika abin da su ka kasance suna aikatawa ya lalace )
Mutuwa cikin ridda na rusa aiki, Allah Mabuwayi da daukak :(Kuma wanda ya yi ridda daga gare ku ga barin Addinin sa,har ya mutu alhali kuwa yana kafiri to wadannan ayyukansu sun baci a cikin duniya da lahira)
Kuma kin addini na rusa aikin mai shi, Allah Madaukakin sarki ya ce : (wannan sabo da lalle su sun ki abin da Allah ya saukar domin haka ya bata ayyukansu).
Kafirci da Allah da haduwa da shi na sanya laacewar aiki Allah Madaukaki ya ce : (kuma wadanda suka karyata game da ayoyin mu da gamuwa da lahira ayyukansu sun baci )
Duk wanda ya bi abin da zai fusata Allah ya ki neman yardarsa Allah zai saka masa da ga irin aikin sa sai ya rusa aikinsa Allah Madaukakin sarki ya ce : (wannan domin lalle su sun bi abin da ya fusatar da Allah kuma sun ki yardarsa sabo da haka ya bata ayyukansu)
Kuma munafunci aiki ne mai mummunan karshe da sharri, Allah ya ce : (wadannan basu yi imani ba sabo da haka Allah ya bata ayyukansu ).
A cikin sabawa Manzo Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ta hanyan saba umarninsa akwai bata aiki da rusa shi Allah Madaukakin sarki  ya ce : ( Lalle ne wadanda suka kafirta kuma suka kange daga tafarkin Allah kuma suka sabawa Manzonsa abayan shiriyar ta bayyana a gare su ba za su cuci Allah da kome ba kuma zai baita ayyukansu.)
Kuma daga sauti a gaban Annabi na bata ayyuka. (yaku wadanda suka yi imani kada ku daukaka saututtukanku bisa sautin Annabi kuma kada ku bayyana sauti gare shi a magana kamar bayyanawar sashin ku ga sashe, domin kada ayyukanku su bacialhali kuwa ku baku sani ba)
Alfahari da aiki da shisshigi  ga Allah,  yana suka ne ga bangare rububiya Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace ga da wanda yace da wani Wallahi Allah ba zai gafarta ma wane  ba, sai Allah ya ce   : wane ne ya ke yi min shisshigi  kan cewa ba zan gafarta wa wane ba to ni lalle na gafarta masa kai kuma na rusa aikin ka).Muslim ne ya rawaito
Riya na lalata aiki Allah Madaukakin sarki ya ce a hadisi kudsi: (Ni na wadatu daga abokan tarayya duk wanda ya yi wani aiki ya hada ni da wani na a ciki to na bar shi da shirkarsa)Muslim ne ya rawaito.
Duk wanda ya zo gurin boka  ya tambaye shi wani abu to ba za a karba mishi sallan kwana arba'in ba) Muslim ne ya rawaito.
(Duk wanda ya bar sallar la'asar to aikin ka ya rushe) Bukhari ne ya rawaito
(Zalunci duhu ne ranar alkiyama).
Manzon Allah tsira da amincin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,ya ce : ( Tsiyatacce wanda aka yi wa wasoso shi ne wanda zai zo ranar Alkiyama da sallah da azumi da zakka kuma ya zo yazagi wannan ya yi kazafi ga wane ya ci dukiyan wane, ya zubar da jinin wane ya duki wane, sai a bawa wannan dag kyawawan shi wancan ma daga kyawawan shi, idan kyawawan shi sun kare kafin a biya bashin da ke kansa, sai a dauki kusakuransu sai a dora mishi sannan a jefa shi a wuta.) Muslim ne ya rawaito.
Zunuban  boye na goge kyawawa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Na san wasu mutane magana cikin al'umata za su zo ranar alkiya ma da kyawawa  sun kai girman dutsen tihama   da hasken sa sai Allah ya maida shi Turbaya tarwatstse
Sauban Allah ya yarda da shi ya ce : ya Manzon Allah siffanta su gare ka fayyace mana su ka mu kasance cikinsu ahalin ba mu sani ba, sai ya ce : ( Ai su 'yan uwanku ne masu irin fatar jikin ku, suna rikan kamar yadda ku ke yi na daga dare, sai dai su mutane ne da idan sun kebanta da abin da aka haramta sai su keta alfurmarta) Ibnu Maja ne ya rawaito.
(Wanda ya riki kare inba na kare dabbobi ba ko farauta ko kare shuka ba za a rage a kowani rana ladan sa da ya kai kiradi.)Bukhari ne ya rawaito.
(Duk wanda ya sha giya to Allah ba zai karba masa salla ba na safiya na arba'in ) Ahmad ne ya rawaito.
Makurar hasara shi ne mutum ya zaci yana kan aiki mai kyau a halin yana kan sabanin hakan. Allah Madaukakin sarki ya ce : (kace ko mu gaya muku game da mafifita hasara ga ayyuka?(wadanda aikinsu ya baci a cikin rayuwar duniya ,alhali kuwa suna zaton lalle ne su suna kyautata (abin da suke gani)aikin kwarai?)
Bayan haka ya ku musulmai :
To Ita ibada da  kiyaye ta abin nema ne a musulunci, dawwama akanta har zuwa mutuwa tushe ne a sharia, Allah Madaukaki ya ce : ( Kuma ka bautawa Ubangijinka har mutuwa ta zo ma)
Ya wajaba akan musulmi kada ya guji duk wani aikin alheri,ko da dan kadan ne, ya kuma nesanci dukkan munana ko da karama ce don bai san wace kyakyawan ce Allah zai jikan shi a dalilinta.bai kuma san wace mummunar ce Allah zai yi fushi da shi akan ta ba, ya wajaba ga Musulmi da ya tafi cikin ibadar sa yana mai tsakanin fata da tsoro, yana raya zuciyar sa da kaunar Allah da kyautata masa zato,
Ina neman tsarin Allah daga shaidan abin jefewa.
(Ka ce lalle ne salla ta da yanka na da rayuwa ta da mutuwa ta na Allah ne Ubangijin talikai, babu abokin tarayya a gare shi, kuma da wancan aka umarce ni, kuma ni ne farkon masu sallamawa)
Allah ya sanya min albari ka ni da ku a cikin Alkurni Mai girma,
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa kyautatawarsa.godiya ta tabbata bisa datarwarsa da baiwarsa, Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya muna girmama shaninsa, kuma na shaida Annabi Muhammad bawansa ne kuma Manzon sa ne, tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa,
Ya ku Musulmai!
Ku kasance kun fi kula da karbar aikin akan shi kan shi aikin, ku kiyaye abin da zai tafiyar muku da da'a  daga abin da zai lalata shi ko ya rage shi, duk wanda yayi aiki mai kyau to ya godewa Allah da ya datar da shi zuwa ga aikata  wannan aiki, kuma ya roke shi tabbatuwa da dogewa a kai,kuma kiyaye da'a ya fi aikata ta. Kuma bin lura shine na karshe, shi wanda ya san Allah yana kuma bauta masa zai sanya a cikin biyayyar sa wani abu da zai rika tsarkake mishi rayinsa ta hanyar lazimtar ibada,
Da gaskiya da kubutaciya kuma  da kankan da kai lafiyayyar zuciya,da kyawawan dabiu zai so alheri ga waninsa kamar yadda ya ke so wa kansa, kada ya aminta daga Makru na Allah kuma kada ya yanke kauna daga rahamar Allah.

Sannan ku sani Allah ya  umarce ku da salati ga Annabinsa.   

الخميس، 24 أغسطس 2017

Gyaran zahiri da badini (Ciki da Waje

Hudubar  Juma'a na Masallacin Annabi na sheikh Abdulbari Bin  Awad  Assubaiti 3/12/1438 AH

Hudubar farko
Allah ya halicci mutum a cikin mafi kyawun tsayuwa, ya mar ni'ima da sura ta bayyane mai kyau, da na ciki daidaitacce mai daraja.
Allah Madaukaki ya ce : (Ya kai mutum me ya rude ka game da ubangijinka Mai karimci ? wanda ya halitta ka sa'annan ya daidaita ka ya kuma tsakaita ka. A cikin kowace irin sura ya so gina ka a kanta)
Cikan kyan dan Adam na daga gyaruwan badinin shi, wanda ke bayyana kyan wajen shi. Tsabtatuwan ciki na bayyana  amfanin  tsarkin waje.
Ko da ya ke mutane sun fi damuwa da abu na bayyane don shi ne makurar sanin su, amma shi Allah ya fi la'akari da na badini game da dan adam, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Lalle Allah bai dubi ga surorin ku ko dukiyarku, sai dai yana dubi  ne ga zukatanku da ayyukanku)
A duk lokacin da aka fi kyautata  badini wurin karfin  alaka  da Ubangiji sai a samu kauna da karbuwa, ba wani bawa da ya kyautata cikinsa da son Allah Madaukaki face ya samu karbuwa  ta zuci a sama da kasa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Lalle idan Allah ya so bawa sai ya kira Jibrilu yace : Lalle ina son wane ta ka so shi! Sai Jibrilu ya so shi, sannan ya yi yekuwa a sama, ya ce : Allah na son wane to ku so shi! Sai na cikin sama su so shi, sai a sanya mishi karbuwa a doron kasa.)
A ranar Alkiyama ; za a kwalkwale hisabi ciki da waje na bayi, Allah Madaukakin sarki ya ce : (kuma kada ka bi abin da ba ka da ilimi game da shi, lalle ne ji da gani da zuciya dukkan wadancan (Mutum) ya kasance daga gare shi wanda ake tambaya,)
Wannan fahimta mai zurfi zai sanya musulmi ya gyara badinin shi, wanda ya ginu a kan tsarkaki niyya ga wanda ake bautawa, don niyya ne sirrin bauta , kuma ginshikin bautawa Allah na zahiri yana ga kyautatuwan bin Manzo da koyi da shi, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Ka ce idan kun kasance kuna son Allah to ku bi ni Allah ya so ku, kuma ya gafarta muku)
 Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Dukkan al'uma ta zasu shiga aljanna sai wanda ya ki, sai suka ce ya Manzon Allah wa zai ki? Sai ya ce : Wanda ya bi ni zai shiga aljanna wanda ya saba mini to hakika ya ki.)
Ibada na tarbiyantar da  musulmi a zahiri da badini, wanda ya lura da koyarwar Annabi zai ga akwai kulawa da ciki da waje, na daga cikin haka akwai tsayuwar musulmai gaba ga Ubangijinsa da daidaita sahu da la'akari da ita na da ga cikin tsaida sallah, hakika ya tabbata daga gare shi ya kasance ya na umartan mutane da daidaita sahu  ya na cewa ya ku bayin Allah ko dai ku daidaita sahun ku ko Allah ya rarraba fiskoki.
Muna gani cikin ayyukan hajji kulawa da tsarkake zahiri da tsaftace badini, to fitan musulmi yana nufan yin hajji ya dumfari dakin Allah mai alfarma yana nuna mana mafi girman sura na amsa kiran Allah ciki da waje, tufafi da niyya da talbiya da ambaton Allah na dada tabbatar mana da hakan.
 Allah Madaukakin sarki ya ce : (Hajji watanni ne sanannu cikinsu to babu jima'I kuma babu fasikanci  kuma babu jayayya a cikin hajji kuma abin da kuka aikata daga alheri Allah  ya san shi kuma ku yi guzuri to mafi alherin guzuri yin takawa kuma ku bi ni da takawa ya ma'abuta hankula  سورة البقرة 197
 Kamar yadda Manzon Allah Almusdafa  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fito da hakan a fili a hudubarsa ta hajjin ban kwana inda ya bayyana mana matsayin abubuwa na badini a musulunci, kuma shine abin da Allah ke sa ido akai, yana cewa : (Ya ku mutane ! ku saurara  lalle Ubangijinku guda ne kuma mahaifinku daya ne, ku sani ba fifiko tsakanin balarabe da ba'ajame  haka farin fata bai fi bakar fata ba haka jar fata bai fi bakin fata ba kuma bakin fata bai fi jar fata ba sai da tsoron Allah)
Musulmi an umarce shi da ya nesaci sabo na bayyane da na boye Allah Madaukakin sarki ya ce : (  Ka ce abin sani kawai Ubangijina ya hana abubuwan al-fasha abin da ya bayyana daga gare su da abin da ya boyu ) سورة الاعراف 33
Lalle tsaftar zahiri da tsarkake badini na kai wa ne ga tsaftace matattarar al'umar musulmi da kuma sifantuwa da kyawawan halaye da kyautata dabi'u, Allah Madaukakin Sarki ya ce : (Kuma Allah ne ya fitar da ku daga cikunan iyayenku ba da kuna sanin kome ba kuma ya  sanya muku ji da gannai da zukata tsammaninku za ku gode  سورة النحل 78
     Duk wanda ya gyara zahirinsa ya tsaftace badininsa  to zai yi kokari kar ya saba abin da yake kira a kansa na shiriya da halaye na mutunci da alheri, Allah Madaukakin sarki ya ce :( Shin kuna umurnin mutane da alheri kuma ku manta da kanku alhali kuwa kuna karatun littafi ? shin ba za ku hankalta ba)  سورة البقرة 44
Cikin alakar musulmi da dan uwansa musulmi a zahiri da badini akwai ya fiskance shi da fara'a da runguma sa'annan ya ya yi mishi adua na alheri a boye cikin tsarkin zuciya, ya so wa 'yan uwansa alheri  ya kuma bayyana kauna tare tsarkake zuciya game da shi, Manzon  Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Ba wani bawa musulmi da zai yi adu'a ga dan uwan shi musulmi a boye face Mala'ika ya ce : Kai ma kana da kwatankwacin hakan)
Musulmi shi ne wanda musulmai suka kubuta daga sharrin harshensa da hanunsa a bayyane kuma  suka aminta daga hasadarsa da  kullinsa a zuci, Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(kar ku yi hasada kar ku yi munajasha (cinikin ingiza mai kantu ruwa) kar ku yi gaba da juna, kar ku yanke wa juna, kada wanin ku ya yi ciniki a kan cinikin wani, ku zama bayin Allah 'yan uwan juna, Musulmi dan uwan musulmi ne ba zai cuce shi ba, ba zai tabar da shi ba, ba zai yi mishi karya ba, ba zai rena shi ba)
'Yan Uwantaka  na hukunta taimakawa musulmi ga dan Uwansa  Musulmi da harshe da rubutu a bayyane, a boye kuma a zuciya da tunani.
Ya wajaba ga dukkan musulmi ya taimaka game da al'amuran musulmi da dukiya da matsayi da shawari da adua,  (Kuma lalle Mun aika zuwa ga al'ummai daga  gabaninka sai muka kama su da tsanani da cuta tsammaninsu za su kankan da kai) سورة الانعام 42
 Idan musulmi zai zartar da wani hukunci bai dace a gare shi ya yi ta bibiyan sirrin mutane ba ko ya dora wa kansa nauyin haka ba ko farauto abin da ya boyu daga gare su ba, to Allah shi ne mafi sanin abin da ya boyu, kuma hisabin su na kan wanda ba abin da ke boyuwa a gare shi,   Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( An umarce ni da na yaki mutane har sai sun shaida ba abin bauta da gaskiya sai Allah kuma Muhammadu Manzo ne na Allah su kuma tsaida sallah su bada zakkah, to idan sun yi hakan to kare jininsu daga gare ni, sai da hakki na musulunci, kuma hisabin su na kan  Allah Madaukai).
Neman kutsawa cikin badinin musulmai da hukunci game da abin da ke zukatansu  keta alfarmansu ne, wanda hakan zai kai ga sakaci game da mutunci musulmi da halasta jinin su, Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Gushewar duniya wallahi ya fi sauki gurin Allah a kan kashe mutum musulmi,)
Hakika Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana muamalantar munafukai  da ke bayyana musulunci irin muamalar musulmai kuma yana gudanar musu da hukunci  na musulunci a zahiri duk da cewa ya san wasun su a boye munafukai ne.
Alamu na imani na bayyana a lokacin jarrabawa: ta hanyar  hakuri a zahiri da neman lada a badini, gabbansa ba za su wuce gona da iri ba ko ya yi rashin ladabi ga Ubangijinsa kuma Majibincinsa. Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( Lalle idanu na zubar da hawaye kuma zuciya na bakin ciki amma ba za mu fadi wani abu ba sai abin da Ubangiji ya yarda da shi, kuma lalle ya kai Ibrahim muna bakin cikin rabuwa da kai)
A wurin tsere zuwa ga aljanna ba a yin nasara sai an gyara ciki tare da muhimmancin waje, to da gyaruwan badini ne masu cin nasara suka yi fintinkau, masu isa suka haye suka kai gaci, Allah Madaukakin Sarki ya ce :  (Lalle wadannan da suka ce Ubangijinmu shi ne Allah sa'an nan suka daidaitu mala'iku na sassauka a kansu (a lokacin saukar ajalinsu suna ce musa ) kada ku ji tsoro kuma kada ku yi bakin ciki kuma ku yi  bushara da Aljanna wadda kun kasance ana yi muku wa'di da ita   سورة فصلت 30

Huduba ta biyu
Bayan haka ! na daga cikin yelwar rahamar Allah ya hore wa mutum  tasha ta karin imani da zai yi guzuri da abin da zai tsarkake badininsa ya kuma habaka zahirinsa, na daga ciki akwai wadannan ranaku masu girma masu albarka wanda lada ke ribanyuwa a ciki wato ranaku goma na zulhijja wanda ke da nunanun fa'idoji ga daidaiku da al'uma, ya zo a falalansu fadin Allah Madaukakin sarki  (Ina rantsuwa da Alfijri  da daruruwa goma) da fadin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ( Ba aikin da ya fi kamar na wadannan ranaku goma ) sai aka ce har jihadi? Sai yace ( ko jihadi ne sai dai mutumin da ya fita da ransa da dukiyarsa bai dawo da komai ba)Buhari ne ya rawaito
Kamar yadda kabar bari na saki waiwai sunna ne a goman zulhajji da sauran ranakun Sallah (Tashrik) tun daga shigar watan zulhajji  har zuwa  ranar karshe na Attashrik, shi kuma kabarbari kayyadaddu na fara wa ne tun daga asubahin ranar arafa har zuwa faduwar rana  na ranar karshe na ranaku Attashrik.
Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu akbar La'ilaha illallahu Allahu akbar wa lillahil Hamd
Na daga cikin ayyuka da a ke kusantar  Allah da  shi akwai yanka dabbar  laiha, hakika Imam Attirmizi da Ibnu Majah daga A'isha tana mai jingina shi ga Annabi (Ba wani aiki da dan adam zai yi a ranar babbar sallah da ya fi soyuwa ga Allah da ya  kai zubar da jini( wato yanka dabba ) don zai taho a ranar alkiyama da kahonsa da abin alamarsa da kofotonsa, kuma jinin na zuba a gurin Allah a wani wuri kafin ya zuba a kasa, to ku tsarkake kawunanku da shi) Hakim ya inganta shi a Almustadrak.

Ya tike.

الجمعة، 11 أغسطس 2017

KUNYA A MUSULUNCI

Hudubar Juma'a  a Masallacin Annabi  19-11-1438AH sheikh Abdullah bin Abdurrahman Albuaijan
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah da ya raba halaye a tsakaninku kamar yadda ya kasa arziki a tsakaninku ya sanya kyakyawan hali shine ma'uni na fifiko a tsakaninku                                                             na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya yana da kyawawan sunaye da kuma siffofi madaukaka.
Na shaida Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bawansa ne kuma Manzonsa ne, ya isar da sako, kuma ya sauke amana, ya yi nasiha wa alumma, ya yi jahadi don Allah yadda ya dace a yi jahadi har lokacin da mutuwa ta zo mishi .
Ya Allah ka yi dadin tsira da aminci a gare shi da iyalansa da sahabbansa da wanda  ya bi shiryarwarsa  ya kuma yi riko da sunnarsa har zuwa ranar sakayya.
Ya ku bayin Allah ku ji tsoron Allah, Mabuwayi da daukaka,domin takawa daukaka ne a nan duniya kuma guzuri ne a lahira.
(ya ku wadanda suka yi imani! In kun ji tsoron Allah zai sanya muku mararraba kuma ya kankare kananan zunubanku kuma ya gafarta muku. Kuma Allah ne Ma'abucin falala Mai girma)
Lalle duk da sabawan harshen su da launin su ko da kuwa sun kasance daga  Uba guda,to su kamar ma'adinai ne (da ake tonowa a kasa) wani na da fifiko kan wani haka wani nau'in ya dara wani, sabo da dabiu ne maauni na kyawawan halaye, kuma shi ne mizani na al'umu, kuma tsani zuwa ga daukaka, da kaiwa kololuwa, Manzon Allah ya yi gaskiya da ya ce :(Lalle zababbun ku su ne mafi kyan halaye a cikinku) Bukhari ne ya rawaito.
Ya ku bayin Allah ! Lalle addinin da muke dangantuwa gare shi addini ne na kyawawan dabiu. Kuma AnnabinMu Muhammad an turo shi ne don ya cika kyawawan dabiu, kuma biyu bisa ukun farfajiya na duniyan musulmai sun karbi musulunci ne ta hanyar kyawawan dabiu.
      kunya ne sarkin halaye nagari kuma, ba sabani kan  kunya ne abu mafi kyau da ado  a cikin kyawawan dabiu,                                                                                                                                                                                                             ya ku bayin Allah  kunya ita ce tushen kyawawan dabiu'kuma ita ce mabubbugan kyawawan halaye dukk wata falala ta boyu a cikin kunya wanda ya siffantu da ita  musuluncinsa ya yi kyau, haka nan kuma dabiu'.
Ita  za ta daukaka mutum ta sa ya  yi nesa daga sabo domin jin kunyan ubangijin shi dabia' ce mai daraja wanda ke haifar da aikata dukkan wani aiki mai kyaw ya hana mutun aikata aiki dukkan mara kyaw yasa mutun ya yi nesa daga dukk wani  aiki na kunya muna na da kuma ya yi nesa da abubuwa na minkari lalle shi din nan dalili ne da ke nuna girman hali da tsarkakan zuciya ga mutun kunya na tunkude mutun daga  aikata aikin ashshakuma kuma ya kare mai mutuncin shi ya dasa mishi kame kai a zuciyan shi shi kama wani ma'dini ne  mai tsada wanda ba mai siffantuwa da shi sai zukatanda suke na ayaba kuma kaman wani ado ne na annabawa an karbo daga abu masu'd Allah ya kara mishi yarda  ya ce: manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce''Na daga cikin abinda mutane suka riska na maganganun Annabawan farko  akawai " in baka ji kunya ba to ka aikata abin da ka so ) Bukhari ne ya rawaito   
 kunya  alami ne na musulunci ko wani addini yanada wasu dabiu'                                       
Na daga cikin dabi'u na musulunci  akwai kunya,Ibnu maja ya rawaito kuma Albani ya inganta shi a cikin sahihuhu aljami 
Imani  yanki saba'in da dori ne kuma kunya  daya daga cikin yanki  ne na imani muslim ne ya rawaito
 Manzon Allah ya wuce wani mutumi yana zargin dan uwan shi sabo da yawan   kunya sai ya ke cewa lalle kai din nan kana jin kunya sai yana cewa har kaman hakan ya maka illa sai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yake cewa kyale shi domin lalle kunya na daga cikin imani kuma babu imani ga wanda ba yi da kunya Bukhari ne ya rawaito
Kuma na daga cikin sirri ya ku bayin Allah da ke sanya kunya ta zama  a cikin imani saboda dukkan imani da kunya sun kasance suna kira ne zuwa ga alheri kuma suna kusantarwa zuwa gare shi kuma suna tunkudarwa daga sharri kuma suna  nesatarwa daga gareshi  kunya kofa ne daga cikin kofofin alheri.
An karbo daga Imran dan Husain Allah ya kara yarda a gare shi ya ce Annabi tsira da amicin Allah su tabbata a gare shi ya ce (Ita kunya bata kawo wani abu sai alheri ) kuma ya ce (kunya alherine dukkaninta ) muslim ne ya rawaito
Ya ku bayin Allah hakika manzon Allah ya tattaro dukkan siffofi  na mutanen farko da na karshe ya siffantu da dukkan sifa mafi daukaka da daraja har Allah ma ya ke ce da shi (lalle kai din nan kana kan dabiu' masu girma).
Manzon Allah ya  kasance mafi jin kunya a kan budurwa da ta ke cikin kafunta idan yaga wani abu da ya ki sai  a ga kin a fuskar shi ta hanyan kunya  ya lullubeshi
 ya ku musulmai lalle kunya daya daga cikin surori ne da darajoji mafi kololuwa a wurin Allah ta inda za ka ji kunyan a ganka wurinda ya haneka hakika kuma shi ya halicceka kuma ya daidaita ka kana jin kunyan ka yi amfani da ni'marsa da ya baka wurin saba mishi , Manzon Allah ya kwadaitar bisa ga kunya kuma cewa kunya daga Allah ne sai ya ce (ku ji kunya ya ku bayin Allah yanda ya dace a ji kunya sai suka ce ya manzon Allah dukkan mu muna jin kunya Ahamdu llillahi sai ya ce ba shi a ke nufi ba ana nufin jin kunya daga Allah yanda ya dace da  cancancin jin kunyarsa) wato kayi ya kiyaye abunda ya tattara ciki ya kiyaye abinda ya kumsa kuma a tuna mutuwa da karewa duk wanda ya nufi lahira zai bar kawan rayuwan duniya wanda ya yi haka to hakika ya ji kunyan Allah bisa cancancin kunyarsa  ) Hakim ne a mustadrak ya rawaito kuma ya inganta shi zahabi ya mar muwafaka kunya daga malayiku masu daraja da kuma masu kiyayewa masu rubutu da su shaida a gareka wato daga dama da hagu suna zaune ba abin da zai ambata  ko ya furta na fadi face  akwai mai kulawa tare da shi kunya na mutane shi ne ka keta dokan Allah da ya suturta a gare ka ka bayyana sabo a gabansu Annabi ya ce dukkan alummana ana basu lafiya suna kubuta sai wadanda su ke masu bayyana sabo kunya daga rayi daga gabbai domin su din nan sune zasu zama shaida a gareka sun yi musu da kai ranar alkiyama Allah ya ce ( ranarda harsunansu  za su shaida musu da hannayensu da kafafuwansu da abinda suka kasance suna aikatawa a wannan ranar ne Allah zai cika musu addininsu na gaskiya kuma su san cewa lalle Allah shi ne gaskiya kuma bayyananne )




 HUDUBA TA BIYU
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mai kunya kuma mai suturcewa ya sanya daga cikin dabiu' masu daraja da kuma ya cika kyawawan dabiu' ta hanyan turo mai albishir kuma mai gargadi wato fitila mai haskakawa annabin mu muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da aminci tabbatacce mai yawa ya ku musulmai lalle muna rayuwa acikin wata marhala na halaye wanda suke na kunci muna karshen zamani wanda wadan nan munanan dabiun sun yi rinjaye kuma sun yawaita shubuhohi dabin soye soyen rayuka sun yadu abunda da ya kasance  a jiya sanennen abune a yau ya zama shi ne  abin ki abunda kuma ya kasance abin ki a jiya ya zama shi ne abin so abinda aka saba da shi munanan dabi' sun sulale su shigo cikin gidaje ta hanyoyin nau'urorin  sadarwa  na zamani a wannan yanayi gashi ana fiskantanmu to ya wajaba mu  tarbiyyantar da masu tasowa kuma mu katangesu da akida na musulunci kyawawan dabiu' daga Allah ne kuma su din nan katanga ne daga cikin katanga wanda suke masu bada kariya kuma da aminci ga tarbiyya da tsarkake zukata da kuma murakaban Allah .
Ya ke musulma ya ke yar uwata mai daraja lalle kunya ko da ya kasance abu ne da ake nema a hakkin maza sai de kuma ya fi wajabta a kan hakkin mata a bangarenta yafi karfi domin lalle matanda ta ke bautawa  Allah da kyawawan dabiu'nta tana neman lada kuma tana jin tsoron ukubarsa  lalle kunya na daga cikin kyawawan dabiu' na addini kuma da ake tada mutane a kansu wanda ke lullube mace a cikin kafunta da shi tana ci tana sha kuma tana tufata shi kuma ta ke kai komo fita ta tafi tare da shi lalle kunya ga mace musulma shine hanun jarinta kuma kuma shi ne daukakanta kuma shi ke kiyaye karamarta kunya na janyo wa ya mace aminci da kuma daukaka da kuma kawa dalili ne kuma na nuna cewa ita kamemmiya ce haka nan kuma wani katanga ne mai katangewa mai karfi ya ke musulma Allah ya yi nuni a cikin littafinsa da kunya mace a kissan musa alaihi assalam ayayinda ya zo diba daga ruwan madyana  ta inda wata mace daya daga cikin diyar shua'ibu ta zana mana mana siffa daga cikin siffofi na kunya na daga ciki abinda annabi musa ya yi la'kari da shi na irin kame kanta da kunyanta da rashin cakudedeniyansu da mutane sai ya shayar da su Allah madaukakin sarki ya ce game da annabi musa  (kuma a lokacin da ya isa mashayar madyana ya sami wata jam'ar mutane suna shayarwa kuma a bayansu ya sami wadansu mata biyu suna korar (tumakinsu ).ya ce menene sha'ninku ? su ka ce ba za mu iya shayarwa ba sai makiyaya sun fitakuma uban mu tsoho ne mai daraja ) (sai ya shayar da su )
Shi kunya da kame wana daga cikin abubuwa ne na kunya kuma alamane na musulma kuma  dalili ne na kyakyawan tarbiyya ayan nan mai girma ta nuna mana misali daga cikin kyawawan dabiu shi wato kunya da kuma nitsuwa a dukkan kai komo  da zance Allah ya yabi daya daga cikinsu  , lokacin da ta dawo gare shi , sabo da abin da ta siffantu da shi na kunya, ba ta yi wani rangaji ko kwarkwasa ba , ba ta bayyana kwalliyanta ba kuma bata  rausaya murya ba, (  sai dayansu ta je masa  tana tafiya akan jin kunya ta ce: Ubana yana kiran ka domin ya sakanya  maka  ladan abin da ka shayar )

 YA KE MUSULMA :
Ga mahaifiyarki kuma abin koyin ki Aisha uwar muminai tana buga misali mafi kaye game da kunya , don ta kasance tana jin kunya har ma ta suturce daga rayayye da matacce ,  tana cewa :- na kasance na kan shiga dakin da aka binne Manzon Allah  tsira da amincin Allah su tabbata agare shi tare da Abubakar a cikin shi, ba tare da tufafi ba ,  sai nake cewa wannan  miji na  ne wannan kuma mahaifi na  ,   to a yayin da aka binne Umar wallahi ban shiga dakin ba face da tufafi na a daure a kai na sabo da kunya da nake ji na Umar .
 Kuma ta kasance idan ta zo daura da mahaya  a halin tana ihrami sai ta  sake jalbabinta a kan fiskanta .
Kuma ta kasance tana dawafi a dakin ka'aba  kamar  yanda ya zo a cikin littafi mai inganci  ba ta cakudaidainiya da su , a yayin da wata 'yar gidan ta take cewa da ita , na yi dawafi bakwai a dakin ka'aba kuma      na taba rukuni sau biyu ko uku sai Aisha ta ce, kar Allah ya baki lada , kina tuttunkude maza, ase ba za ki yi kabbara ba kawai ki wuce .
 YA KE MUSULMA :
Hijabin mace da kamun kanta na cikin addininta kuma yana cikin kyawawan  halayen ta , to, idan har fidiranta ya juya , ta shakala yin addinin ta sai ta yada kwarjallenta , ta yi wurgi da mayafinta , ta bayyana adonta  wuraren da za ta sa a fitinu da ita , tofa ta yi hasarar addinin ta kuma ta sarayar da amananta , an karbo daga Abu Huraira ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (nau'I biyu na mutane suna cikin 'yan wuta ban gansu ,   sai ya ambata daga cikin su , Matayen da suke sanya sutura amma suna cikin tsiraici , suna kuma jan hankalin mutane , masu karkatarwa ne kuma karkatattu, kayukan su kamar tozon rakumi , wanda suka karkace ,  ba za su shiga Aljanna ba ba za ma su ji kamshin ta ba , kuma a hali kamshinta a na jin shi tun daga tafiyan kaza da kaza ).

YA KU MUSULMAI :
(Dukkan ku masu kiwo ne , kuma dukkan ku abun tambaya ne bisa ga kiwonsu ,  na miji me kiwo ne akan iyalan gidan shi  kuma  abin tambaya ne game da  su ,  haka ma mace mai kiwo ne a kan gidan mijinta da kuma 'ya'yan shi ,   kuma ita abin tambaya ne game da su ,  ku saurara ! dukkan ku masu kiwo ne kuma dukkanin ku abin tambaya ne bisa ga kiwon da aka ba ku) Muslim ne ya rawaito
 Ya  Allah ina rokonka kunya da zai tsare ni daga saba maka ,
Ya Allah ka shiryar da mu bisa ga mafi kyan halaye ba mai shiryarwa  zuwa gare su sai kai , ka tunkude mana munanansu daga  gare mu , domin  ba mai tunkude munanan daga gare mu sai kai.
 Ya Allah muna rokon ka shiriya da takawa da kame kai da wadata .
 Ya Allah ka daukaka Musulunci ga musulmai ka kaskantar da shirka da mushrikai, ka taimaki bayinka masu Tauhidi ,