Hudubar Masallacin
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi 2/1/1439 H
Na Sheikh Abdullah
Bin Abdurrahman Albuaijan
Hudubar farko
Dukkan yabo da godiya
sun tabbata ga Allah wanda sammai da kasa na shi ne, gare shi al'amura ke
komawa, godiya da yabo da kyakkyawan ambato da wanzuwa nashi ne, kuma gare shi
zaa koma, tsarki ya tabbata gare shi ya horar da rana da wata suna karbar juna
ya kuma hore muku dare da wuni kome gare shi a kaddare ya ke.
Na shaida ba abin
bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya mulki da
godiya na shi ne, yana rayawa kuma yana kashe wa kuma shi rayayye ne ba ya
mutuwa, alheri na hanunsa kuma mai iko ne ga dukkan komai.
Na shaida Annabi
Muhammadu cikamaki ne na Annabawansa da
Manzanninsa, an turo shi a lokacin da ba Manzanni sai ya isar da sako ya kuma bada amana ya yi
nasiha ga al'umma, ya yi jahadi don Allah hakkin jahadi har mutuwa ta zo mishi,
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da iyalansa da sahabbansa wadanda suka yi hijira daga gidajen su da
dukiyoyinsu suna neman falala na Allah da yarda.
Da Ansar da da suka mallaki gida da imani suna
son wadanda suka yi hijira zuwa gare su, basu jin wani bukata daga ransu cikin
abin da su bada ko sun kasace mabukata.
Da kuma wadanda suka bi
sawunsu su ka bi su da kyautatawa,da aminci tabbatacce mai yawa har zuwa ranar
alkiyama.
Bayan haka! Lalle mafi
gaskiyan zance shi ne littafin Allah mafi karfin abin riko shi ne kalmar
takawa, mafi alherin addini shi ne addinin Ibrahim, mafi kyan kissoshi shine
Alkur'ani, kuma mafi kyan shiryarwa shine shiryarwar Annabi tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi, mafi al'amura shi ne fararrunta, dukkan bidiah
bata ne.
Ya ku wadanda suka
yi imani ku ji tsoron Allah hakkin tsoronsa, kar ku mutu face kuna musulmai)
Ya ku bayin Allah!
Duniya gidan jarabawa ne
da karewa ita kuma lahira gida ce na
sakayya da wanzuwa, duniya jindadi ne na rudi, wasu sa'oi ne da kwanaki da
watanni da shekaru da zama shekaru na
karewa wasu zamuna n su zo su riska,
ranaku su shude, watanni su zo su wuce, Allah na juya dare da wuni, a hakan
akwai abin lura ga masu basira.
Zamani na karewa gurace gurace na karewa , kuma ajali na cika
( kuma duk wanda ke kan ta na kare wa, fiskan Ubangijinka ne zai wanzu ma'aboci
daraja da daukaka ).
*Wallahi duniya ba gidan wanzuwa ba
ne* A'a ko da mutane sun gina benayenta
*Shekaru na shan
banban sai dai * suna mai tsawon kwana da gajere na daidaita a yayin mutuwa.
Nesa ba kusa ba
gidan duniya ba gidan da ake fatan
wanzuwa ba ne , farin- cikinta bai cika, mutuwa abin buri ne ga dukkan rayuka *
ga mai hankali ba banbanci tsakanin benayenta da kaburanta
Yaku Musulmi!
Shekara ta kare, kuma
shekarun duniya na raguwa, ga ajali na kusantowa , an rufe ayyukanta, an nade takardunta, Madalla da barka ga wanda
ya ribaci damanta, ya ribaci lokacinsa. Ya gyara ayyukansa.
Ku saurara ga mu mun
shigo farkon sabuwar shekara , wanda
zai tattara mu zuwa kabari ya tunkuda mu zuwa ga ranar tadawa da
tattarowa.
To ya dace ga duk mai
zuciya da wanda ya kasa kunnen shi, ya ribaci dama ta rayuwarsa kafin nadama da
da na sani, da zubar da hawaye ya riske shi, (Kada wani rai ya ce ya nadama
ta akan abin da na yi sakaci a cikin
sashen Allah, kuma lalle na kasance hakika daga masu isgili,ko kuma
(kada) ya ce ; da Allah ya shiryar da ni da na kasance daga masu takawa, ko
kuma (kada) ya ce, a lokacin da ya ke ganin azaba da lalle ace ina da wata
komawa zuwa duniya.) domin in kasance daga masu kyautatawa).
Ya ku bayin Allah!
Lalle lokaci na shudewa
rayuwa na ta tafiya, kuma rayuwar lokaci ne kankani, ga wajibabbu sun taru, ga hakkoki
sun cunkushe mutum abin tambaya ne game da rayuwarsa yadda ya tafiyar da ita da samartarsa yadda
ya gudanar da ita. Kuma zaa yi mar bincike game da yadda ya sarayar da
rayuwarsa, da zamanin da ya daidaitar, duk yadda shekuru ya tsawaita to lokaci ne kankani, ( Ya ce nawa ku ka zauna acikin kasa na
kidayar shekaru? Suka ce , mun zauna a yini daya ko rabin yini sai ka tambayi
masu kidanyawa. Ya ce ba ku zauna ba face kadan da dai kun kasance kuna sani,
shin to kun yi zaton cewa mun halitta ku ne da wasa kuma lalle ku zuwa gare mu ba za ku koma ).
Ya ku bayin Allah !
Lalle Allah bai halicce
ku don wasa ba , kuma bai bar ku haka kawai ba, hakika ya halicci mutuwa da
rayuwa domin ya jarraba ku. Ya nuna waye daga cikinku ya fi kyawun aiki.
Ku saurara! Lalle mafi girman musiba , kuma mafi tsananin
wahala da kuma abu mafi tada hankali da
bakin ciki mafi firgitawa , shi ne ;
hasara bisa sarayar da lokaci , da kwacewan ajali da cudewan sa'o'I na zamani ba tare da aiki
ba , hasararta na farawa ne da nadamar
tata tun daga lokacin halartowar magagin
mutuwa , ( Har idan mutuwa ta je wa
dayan su sai ya ce : '' Ya Ubangijina ku mayar da ni ( duniya). Tsammani
na in aikata aiki na kwarai cikin abin
da na bari , kayya , lalle ne! ita kalma ce shi ne mafadinta alhali kuwa a baya gare su akwai
shamaki har ranar da za a tayar da su''.
''Ya ku wadanda suka yi imani kada dukiyoyin ku
da 'ya'yan ku su shagaltar da ku daga ambaton Allah , kuma wanda ya yi haka ,
to wadannan shu ne masu hasara , kuma ku
ciyar daga abin da muka azurta ku daga gabanin mutuwa ta je wa dayan ku har ya ce ya
Ubangijina don me ba ka yi min jinkiri
ba zuwa wani ajali makusanci, domin in gaskata kuma in kasance daga salihai
! kuma Allah ba zai jinkirtawa wani rai ba idan
ajalin sa ya zo kuma Allah masani ne
bisa abin da kuke aikatawa ''.
To lokacin rayuwa -bayin Allah- wata dama
ce na aiki kuma ni'ima ce da take wajabta yin godiya ( Idan za ku kidaya ni'imomin Allah ba za ku iya lissafa ta ba)
Mafi alherin cikin ku
shi ne wanda shekarun shi ya tsawaita
kuma ayyukansa suka kyautata, Mafi sharrin ku shi ne wanda ya yi tsawon rayuwa
kuma ayyukansa ya munana.
Ku saurara ! lalle na
daga cikin godiya ga ni'ima ribatan ni'ima na lokuta , da rayuwa cikin da'a wa
Allah mabuwayi da daukaka daidai yanda ya shasr'anta wa Annabin sa tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi.
A daya bangaren kuma yana daga cikin kafurcewa
ni'ima , da sababi na bala'I da azaba
da hasara da kuma nadama akwai tafiyar da lokaci da ruwa cikin sabawa
Allah , ko kuma cikin abin da Allah bai shar'anta ba , ( To wanda ya aikata (wani aiki) gorgodon nauyin
zarra na alheri zai gan shi . kuma wanda ya aikata gorgodon nauyin zarra zai ganshi .
Allah ya sa mini albarka ni da ku a cikin alkur'ani mai girma.
HUDUBA
TA BIYU
Dukkan yabo da
godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai ya kammala mana addini kuma ya cika mana ni'imomi , kuma ya yardar mana da Musulunci a matsayin addini
, na shaida ba abin bautawa da gaskiya
sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya , wanda ya hada Allah da wani
hakika ya bata , bata mabayyani.
Na shaida Annabi Muhammadu bawan sa ne kuma
Manzon sa ne , tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da
sahabban shi da aminci tabbatacce mai yawa.
YA KU MUSULMAI
Lalle farkon wata na
hijira na shekara shi ne watan Almuharram kuma wata ne mai alfarma Allah madaukakin sarki ya ce:
( lalle ne kidayan watanni a
wurin Allah wata goma sha biyu ne a cikin littafin Allah , a ranar
da ya halicci sammai da kasa , daga cikin su akwa hudu masu alfarma , wannanne addini madaidaici sabo da haka kada ku zalunci kawunan ku a cikin su )
An karbo daga Abu bakrata Allah ya kara yarda
a gare shi daga Annabi tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce: '' Lalle zamani ya juyo kamar siffan shi a ranar
da Allah ya halicci sammai da kasa shekara watanni goma sha biyu , cikin su akwai
guda hudu masu alfarma uku a jere su ke
:- Zulkada, Zulhijja da Almuharram, da
Rajab na MUDAR wanda ke tsakanin Jimada da sha'aban) Bukhari
da Muslim ne su ka rawaito.
Ya ku Bayin Allah!
Na daga cikin koyarwar
Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma na daga
cikin masu kankare zunubai da kuma godiya ga Allah , da kuma girmama shi , akwai
azumtar ranar ashura , shi ne goma ga watan Almuharram .
An karbo daga Dan Abbas Allah ya kara yarda a gare su, ya
ce: '' Ya yin da Annabi ya zo garin madina ya sami yahudawa suna azumin ashura sai ya tambaye su game da
hakan sai suka ce ; wannan rana ne da Allah ya bawa Annabi musa nasara da Banu Isra'ila a kan
Fir'auna , kuma mu muna azumtar shi don girmamawa gare shi sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce: '' mu muka fi dacewa da musa akan ku ,
sai Manzon Allah ya yi umarni da azumtar
shi ''. Buhari da Muslim ne su ka rawaito shi
Kuma daga gare shi ya ce :'' ban taba ganin
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi yana kirdadan azumin watarana ba ,
wanda ya fifita shi akan wanin shi ba face wannan ranan na ashura da wannan wata yana nufin watan ramadan ''. Buhari ne ya rawaito
Ya zo a cikin sahihu Muslim Annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : '' azumin ranar
Arfa ina fata Allah ya kankare zunuban
shekaran kafin shi , da kuma shekaran da
take bayan shi, da azumin Ashura ina fatan Allah ya kankare shekaran da take
kafin shi''.
Ya yin da
labari ya sami Annabi a karshen rayuwan shi , kan cewa yahudawa na rikan ashura a
matsayin idi , sai ya nufi ya azumci
tara da goma a shekara mai zagayowa , sai mutuwa ta shiga tsakani ,
An karbo daga
Abdullahi dan Abbas Allah ya kara yarda
a gare shi ya ce: a yayin da Annabi ya yi azumin ashura ya yi
umarni da azumtar shi sai suka ce
:'' ya Manzon Allah Yahudu da Nasara su na girmama shi , sai
Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbat a gare shi ya ce : idan Allah ya
kai mu badi za mu azumci tara ''. yana nufin tare da goma . ya ce : shekaran bata kewayo
ba har Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya
rasu.'' Muslim ne ya rawaito
Abin da ya fi falala shi ne a yi azumi
guda kafin shi, sabanin na yahudawa in hakan bai samu ba to a yi azumin ranar goma.
Ya Ku Musulmai !
Bidia fitina ce, fitina
kuma jarabawa ce, mafi sharrin al'amura
su ne fararrunta , dukkan bidi'a bata ce dukkan bata na wuta , to ku yi riko da igiya
mai karfi da tafarki mikakke, kada ku bi
hanyoyi , sai su kawar da ku daga
tafarkin
ku yi riko da littafin
ku da shiryarwar Annabin ku , to hakika an isar mu ku,.
(Sabo da haka ka yi riko ga abin da aka
yi wahayi da shi zuwa gare ka, lalle ne
kai kana kan hanya madaidaiciya. Kuma shi (Abin wahayin ) ambato ( na daukaka )
ne a gare ka da kuma ga mutanenka, kuma za a tambaye ku.)
Ya ku Musulmai !
Lalle abin nan da mabarnata suke shiryawa, mujirimai ke tsarawa, makirai
da mahassada ke gudanarwa, na daga makiyanmu da makiya addinin mu da
garuruwanmu wasu tawaga ne na 'yan
jarida da farfaganda irin na shaidan, da kai wa mummunan hari , da wani kazamin
makirci suna yi ne don karanbawul ga zaman lafiyanmu, da wargaza hadin kanmu,
da kunna fitina a garuruwanmu, a tsakanin sahun mu, da keta alfarmar
watanni masu alfarma, da warware alkawari,da janye mubaya'a
da fita daga da'a da barna a doron kasa, mun gani da idanuwarmu yadda kasashe makwabta suka koma, na daga rugujewa, to ku yi lura ya masu basira!
Ya Allah ka kiyaye
wannan gari ya zama cikin aminci da zaman lafiya, ya Allah ka kiyaye garin daga
fitintinu, ya Allah ka kiyaye shi daga makircin masu makirci, da sharrin
mabarnata, da sharrin makiya da
mahassada,
Ya Allah ka kiyaye
garin da sauran garuruwan musulmai, ya Ubangijin talikai,
Ya Allah ka taimaki
musulmai a Borma ka kare jinin su kuma ka suturce al'auran su , ka basu aminci
a abin da suke tsoro ka yi gaggawan yaye
musu bakin ciki .
Allah ka datar da jagoran al'amarin mu mai
hidima ga masallatayya biyu masu alfarma
da datarwarka , ka karfafe shi da
karfafanka.
Ya Allah ka datar da shi da mataimakin shi , da
abin da a cikin shi akwai gyaran garuruwa da bayi da abin da
a cikin shi akwai alheri ga musulunci da Musulmai , ya Ubangijin
talikai.
Ya Allah ka kiyaye mana
iyakan mu , ka bawa sojojin mu
nasara ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka warkar da
marasa lafiyan su , ka karbi matattun su, ka kiyaye su da kiyayewarka, ka kare
su da kariyarka .
BAYIN ALLAH ( Llle Allah
na yin umurni da kyautatawa, da bai
wa ma'abucin zumunta , kuma yana hani da
alfasha da abin da aka ki , da rarrabe
jama'a . Ya na yi muku gargadi,
dammaninku, kuna tunawa.
(Kuma ku cika da
alkawarin Allah idan kun yi
alkawari, kuma kada ku warware
rantsuwoyin ku a bayan karfafa su,
alhali kuma hakika kun sanya
Allah mai lamuncewa a kanku .
Kuma lalle Allah ne ya ke sanin
abin da kuke aikatawa) .
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق