Hudubar Juma'a na Masallacin Annabi na sheikh
Abdulbari Bin Awad Assubaiti 3/12/1438 AH
Hudubar farko
Allah ya halicci mutum
a cikin mafi kyawun tsayuwa, ya mar ni'ima da sura ta bayyane mai kyau, da na
ciki daidaitacce mai daraja.
Allah Madaukaki ya ce :
(Ya kai mutum me ya rude ka game da ubangijinka Mai karimci ? wanda ya
halitta ka sa'annan ya daidaita ka ya kuma tsakaita ka. A cikin kowace irin
sura ya so gina ka a kanta)
Cikan kyan dan Adam na
daga gyaruwan badinin shi, wanda ke bayyana kyan wajen shi. Tsabtatuwan ciki na
bayyana amfanin tsarkin waje.
Ko da ya ke mutane sun
fi damuwa da abu na bayyane don shi ne makurar sanin su, amma shi Allah ya fi
la'akari da na badini game da dan adam, Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce : (Lalle Allah bai dubi ga surorin ku ko dukiyarku,
sai dai yana dubi ne ga zukatanku
da ayyukanku)
A duk lokacin da aka fi
kyautata badini wurin karfin alaka
da Ubangiji sai a samu kauna da karbuwa, ba wani bawa da ya kyautata
cikinsa da son Allah Madaukaki face ya samu karbuwa ta zuci a sama da kasa, Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Lalle idan Allah ya so bawa sai
ya kira Jibrilu yace : Lalle ina son wane ta ka so shi! Sai Jibrilu ya so shi,
sannan ya yi yekuwa a sama, ya ce : Allah na son wane to ku so shi! Sai na
cikin sama su so shi, sai a sanya mishi karbuwa a doron kasa.)
A ranar Alkiyama ; za a
kwalkwale hisabi ciki da waje na bayi, Allah Madaukakin sarki ya ce : (kuma
kada ka bi abin da ba ka da ilimi game da shi, lalle ne ji da gani da zuciya
dukkan wadancan (Mutum) ya kasance daga gare shi wanda ake tambaya,)
Wannan fahimta mai
zurfi zai sanya musulmi ya gyara badinin shi, wanda ya ginu a kan tsarkaki
niyya ga wanda ake bautawa, don niyya ne sirrin bauta , kuma ginshikin
bautawa Allah na zahiri yana ga kyautatuwan bin Manzo da koyi da shi, Allah Madaukakin
sarki ya ce : (Ka ce idan kun kasance kuna son Allah to ku bi ni Allah ya so
ku, kuma ya gafarta muku)
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi ya ce : (Dukkan al'uma ta zasu shiga aljanna sai wanda ya ki, sai
suka ce ya Manzon Allah wa zai ki? Sai ya ce : Wanda ya bi ni zai shiga aljanna
wanda ya saba mini to hakika ya ki.)
Ibada na tarbiyantar
da musulmi a zahiri da badini, wanda ya
lura da koyarwar Annabi zai ga akwai kulawa da ciki da waje, na daga cikin haka
akwai tsayuwar musulmai gaba ga Ubangijinsa da daidaita sahu da la'akari da ita
na da ga cikin tsaida sallah, hakika ya tabbata daga gare shi ya kasance ya na
umartan mutane da daidaita sahu ya na
cewa ya ku bayin Allah ko dai ku daidaita sahun ku ko Allah ya rarraba
fiskoki.
Muna gani cikin ayyukan
hajji kulawa da tsarkake zahiri da tsaftace badini, to fitan
musulmi yana nufan yin hajji ya dumfari dakin Allah mai alfarma yana nuna mana mafi
girman sura na amsa kiran Allah ciki da waje, tufafi da niyya da talbiya da
ambaton Allah na dada tabbatar mana da hakan.
Allah Madaukakin sarki ya ce : (Hajji
watanni ne sanannu cikinsu to babu jima'I kuma babu fasikanci kuma babu jayayya a cikin hajji kuma abin da
kuka aikata daga alheri Allah ya san shi
kuma ku yi guzuri to mafi alherin guzuri yin takawa kuma ku bi ni da takawa ya
ma'abuta hankula سورة البقرة 197
Kamar yadda Manzon Allah Almusdafa
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fito da hakan a fili a
hudubarsa ta hajjin ban kwana inda ya bayyana mana matsayin abubuwa na badini a
musulunci, kuma shine abin da Allah ke sa ido akai, yana cewa : (Ya ku
mutane ! ku saurara lalle Ubangijinku
guda ne kuma mahaifinku daya ne, ku sani ba fifiko tsakanin balarabe da
ba'ajame haka farin fata bai fi bakar
fata ba haka jar fata bai fi bakin fata ba kuma bakin fata bai fi jar fata ba
sai da tsoron Allah)
Musulmi an umarce shi
da ya nesaci sabo na bayyane da na boye Allah Madaukakin sarki ya ce : ( Ka ce abin sani kawai Ubangijina ya hana
abubuwan al-fasha abin da ya bayyana daga gare su da abin da ya boyu ) سورة الاعراف 33
Lalle tsaftar zahiri da
tsarkake badini na kai wa ne ga tsaftace matattarar al'umar musulmi da kuma
sifantuwa da kyawawan halaye da kyautata dabi'u, Allah Madaukakin Sarki ya ce :
(Kuma Allah ne ya fitar da ku daga cikunan iyayenku ba da kuna sanin kome ba
kuma ya sanya muku ji da gannai da
zukata tsammaninku za ku gode سورة النحل 78
Duk wanda ya gyara zahirinsa ya tsaftace
badininsa to zai yi kokari kar ya saba
abin da yake kira a kansa na shiriya da halaye na mutunci da alheri, Allah
Madaukakin sarki ya ce :( Shin kuna umurnin mutane da alheri kuma ku manta
da kanku alhali kuwa kuna karatun littafi ? shin ba za ku hankalta ba) سورة
البقرة 44
Cikin alakar musulmi da
dan uwansa musulmi a zahiri da badini akwai ya fiskance shi da fara'a da
runguma sa'annan ya ya yi mishi adua na alheri a boye cikin tsarkin zuciya, ya
so wa 'yan uwansa alheri ya kuma bayyana
kauna tare tsarkake zuciya game da shi, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi ya ce : ( Ba wani bawa musulmi da zai yi adu'a ga dan uwan shi musulmi a
boye face Mala'ika ya ce : Kai ma kana da kwatankwacin hakan)
Musulmi shi ne wanda
musulmai suka kubuta daga sharrin harshensa da hanunsa a bayyane kuma suka aminta daga hasadarsa da kullinsa a zuci, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
ya ce :(kar ku yi hasada kar ku yi munajasha (cinikin ingiza mai kantu ruwa)
kar ku yi gaba da juna, kar ku yanke wa juna, kada wanin ku ya yi ciniki a kan
cinikin wani, ku zama bayin Allah 'yan uwan juna, Musulmi dan uwan musulmi ne
ba zai cuce shi ba, ba zai tabar da shi ba, ba zai yi mishi karya ba, ba zai
rena shi ba)
'Yan Uwantaka na hukunta taimakawa musulmi ga dan
Uwansa Musulmi da harshe da rubutu a
bayyane, a boye kuma a zuciya da tunani.
Ya wajaba ga dukkan
musulmi ya taimaka game da al'amuran musulmi da dukiya da matsayi da shawari da
adua, (Kuma lalle Mun aika zuwa ga
al'ummai daga gabaninka sai muka kama su
da tsanani da cuta tsammaninsu za su kankan da kai) سورة الانعام 42
Idan musulmi zai zartar da wani hukunci bai dace a gare shi ya yi ta
bibiyan sirrin mutane ba ko ya dora wa kansa nauyin haka ba ko farauto abin da
ya boyu daga gare su ba, to Allah shi ne mafi sanin abin da ya boyu, kuma
hisabin su na kan wanda ba abin da ke boyuwa a gare shi, Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : ( An umarce ni
da na yaki mutane har sai sun shaida ba abin bauta da gaskiya sai Allah kuma
Muhammadu Manzo ne na Allah su kuma tsaida sallah su bada zakkah, to idan sun
yi hakan to kare jininsu daga gare ni, sai da hakki na musulunci, kuma hisabin
su na kan Allah Madaukai).
Neman kutsawa cikin
badinin musulmai da hukunci game da abin da ke zukatansu keta alfarmansu ne, wanda hakan zai kai ga
sakaci game da mutunci musulmi da halasta jinin su, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
ya ce : (Gushewar duniya wallahi ya fi sauki gurin Allah a kan kashe mutum
musulmi,)
Hakika Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana muamalantar
munafukai da ke bayyana musulunci irin
muamalar musulmai kuma yana gudanar musu da hukunci na musulunci a zahiri duk da cewa ya san
wasun su a boye munafukai ne.
Alamu na imani na
bayyana a lokacin jarrabawa: ta hanyar
hakuri a zahiri da neman lada a badini, gabbansa ba za su wuce gona da
iri ba ko ya yi rashin ladabi ga Ubangijinsa kuma Majibincinsa. Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi ya ce : ( Lalle idanu na zubar da hawaye kuma zuciya na bakin
ciki amma ba za mu fadi wani abu ba sai abin da Ubangiji ya yarda da shi, kuma
lalle ya kai Ibrahim muna bakin cikin rabuwa da kai)
A wurin tsere zuwa ga
aljanna ba a yin nasara sai an gyara ciki tare da muhimmancin waje, to da
gyaruwan badini ne masu cin nasara suka yi fintinkau, masu isa suka haye suka
kai gaci, Allah Madaukakin Sarki ya ce :
(Lalle wadannan da suka ce Ubangijinmu shi ne Allah sa'an nan suka
daidaitu mala'iku na sassauka a kansu (a lokacin saukar ajalinsu suna ce musa )
kada ku ji tsoro kuma kada ku yi bakin ciki kuma ku yi bushara da Aljanna wadda kun kasance ana yi
muku wa'di da ita سورة فصلت 30
Huduba ta biyu
Bayan haka ! na daga
cikin yelwar rahamar Allah ya hore wa mutum
tasha ta karin imani da zai yi guzuri da abin da zai tsarkake badininsa
ya kuma habaka zahirinsa, na daga ciki akwai wadannan ranaku masu girma masu albarka
wanda lada ke ribanyuwa a ciki wato ranaku goma na zulhijja wanda ke da nunanun
fa'idoji ga daidaiku da al'uma, ya zo a falalansu fadin Allah Madaukakin sarki (Ina rantsuwa da Alfijri da daruruwa goma) da fadin Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ( Ba aikin da ya fi kamar na
wadannan ranaku goma ) sai aka ce har jihadi? Sai yace ( ko jihadi ne sai dai
mutumin da ya fita da ransa da dukiyarsa bai dawo da komai ba)Buhari ne ya
rawaito
Kamar yadda kabar bari
na saki waiwai sunna ne a goman zulhajji da sauran ranakun Sallah (Tashrik) tun
daga shigar watan zulhajji har zuwa ranar karshe na Attashrik, shi kuma kabarbari
kayyadaddu na fara wa ne tun daga asubahin ranar arafa har zuwa faduwar
rana na ranar karshe na ranaku
Attashrik.
Allahu Akbar Allahu
Akbar Allahu akbar La'ilaha illallahu Allahu akbar wa lillahil Hamd
Na daga cikin ayyuka da
a ke kusantar Allah da shi akwai yanka dabbar laiha, hakika Imam Attirmizi da Ibnu Majah
daga A'isha tana mai jingina shi ga Annabi (Ba wani aiki da dan adam zai yi
a ranar babbar sallah da ya fi soyuwa ga Allah da ya kai zubar da jini( wato yanka dabba ) don zai
taho a ranar alkiyama da kahonsa da abin alamarsa da kofotonsa, kuma jinin na
zuba a gurin Allah a wani wuri kafin ya zuba a kasa, to ku tsarkake kawunanku
da shi) Hakim ya inganta shi a Almustadrak.
Ya tike.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق