الجمعة، 23 أكتوبر 2020

HIKIMAR JARRABAWA

 

ترجمة خطبة الشيخ حسين  آل الشيخ

  بالمسجد النبوي

اسم المترجم :أمين سعد

اللغة : الهوسا

التاريخ 29-2-1442هـ

Hudubar juma'a  na  masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na Shaikh Husain Bin Abdul'Aziz Al - Asshaikh  29-2-1442Ah

Hudubar farko:

Allah wanda tsarki ya tabbata a gare shi yana tunatar da mu sunnar rayuwa da yadda yake tafiyar da ita a cikin al'umomi, sai wanda shaninSa ya buwaya yace :( Ba mu tura wani manzo ba cikin wata alkariya face mun riki mutanenta da tsanani da cuta ko za su kankan da kai)

ABA'SA: shine tsanani da kunci irin na rayuwa,

ADDARRA:Dukkan cuta da  mawuyacin hali cikin sabuba na duniya.

Sai Allah ya bayyana hikimar faruwan hakan da sabubansa, don bayi su komo ga Ubangijinsu su rusunawa Mahaliccinsu, su dawo zuwa ga Allah abin bautansu su bar abin da zai fusata shi Allah Mabuwayi da daukaka ta hanyar tuba ta gaskiya zuwa gare shi, da lizimtar da'a gare shi, da rusunawa umarninSa da tafiya bisa tafarkin sharia.

Na daga cikin hikimomi na jarabawa da ma duk wani abu da ke samun mutum a rayuwa na tsanani da wahala, da abin da ke faruwa a gare shi na cuta a jikinsa da cututtuka.

Na daga cikin hikimar haka halittu su koma ga Ubangijinsu, su mika-wuya zuwa ga umarninSa tsarki ya tabbata a gare shi  su kama hanya zuwa ga shiriyarsu su gargadu daga bata da musu, ko sandararrun zukata za su lausasa, su waazantu su gyaru su shiryu su riki shiriya su kama hanya ta daidai,

Allah Madaukakin sarki ya ce :   ( kuma hakika mun tura zuwa ga al'umomi da suke gabaninka sai muka rike su da tsanani da cuta  ko za su kankan da kai).

    

Ya wajaba ga bayi su yiwa kansu hisabi a halin suna ganin jarabawowi daya – bayan daya su koma da gaskiya zuwa ga addinin Allah, su sabunta tuba ta gaskiya kuma su nemi gafarar Allah da gaske, su sake sabunta alkawari na tafiya bisa tafarki mikakke. Na daga cikin mafi girman musibu  jarabawowi su zo su wuce zukata basu tausasa ba, gabbai ba su koma ga Ubangijinsu ba. Allah Madaukakin sarki ya ce : (Ina ma da lokacin da tsananinmu ya je musu sun kankan da kai sai da zukatansu ta kekashe kuma shaidan ya kawata musu abin da suka kasance suna aikatawa)  

Mafi girman musibu kuma mafi munin sifa ta shakawa, a samu jarabawowi amma masu gafala suna dogewa cikin gafalarsu, masu demuwa suna baccinsu da wasanninsu da ayyukan sabo, mabarnata sun bace cikin barnansu da laifukansu.

Nu'man Bin Bashir Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :( Lalle Halaka dukkan halaka shine ka yi sabo a lokacin jarrabawa ) Ibnu Abi Shaiba ne ya rawaito

Allah Subhanahu wa Ta'ala yana mai gargadi game da sha'anin kafurai masu musu, (Hakika mun rike su da azaba ba su kaskantar da kawunan su ba gaUbangijin su ba su kasance suna rusunawa ba) ai mun jarrabe su da musibu daban daban da tsanani ba su rusuna ba ba su yi kushu'i ba ba su kwantar da kai ba zahiri da badini sai dai ma sun doge cikin batan su da barnan su.

Ya ku bayin Allah:

Lallai akwai laruran tuba mai tsanani da bukatuwa zuwa ga yiwa kai hisabi mai karfi, Allah Madaukakin sarki ya ce (mai Allah zai yi da azabtar da ku idan kuka gode ku ka yi imani? Allah ya kasance mai godiya kuma masani)

Musibu ba za su iya su koma ni'ima ba , tsanani da cuta su koma yalwa da yayewan bakin ciki sai ta hanyar  tuban bayi zuwa ga Ubangijin su da komawa zuwa ga mahaliccin su da haka ne Allah Mabuwayi zai jikan su ya yi ni'ima a gare su ya dauke bala'i da suke cikin da  abin da ya faru da su , lallai Allah yana jarabta bayin sa da tsanani da musibu da laifuka domin ya kwadaitar da su zuwa ga yin da'a gare shi kuma su dawo zuwa ga bangaren shi .

Allah Madaukakin sarki ya ce:(barna ta bayyana a doron kasa da kuma kogi sakamakon abinda hannayen mutane suka haifar don ya dandana musu wani sashi na abunda suka aikata ko za su komo).

Allah Subhanahu wa Ta'ala ya ce:(za mu dandana musu na daga azaba na kusa banda azaba mai girma ko za su juyo).

Allah Subhanahu wa ta'ala ya na cewa (muka jarrabe su da kyawawa da kuma munana ko za su juyo) , Malaman tarihi sun ambata cewa: a shekara ta dari bakwai da arba'in da tara wata annoba ta auku a Misra da Siriya (sham) wanda a dalilin ta mutane da yawa suka rasa rayukansu sai mutane suka hadu a masallatayya suka kankan da kai ga Ubangijinsu suka tuba daga zunubansu suka fuskanci Allah da nau'uka na sadakoki har zuwa lokacin gushewan bala'in cikin gaggawa,

Duk wanda Allah ya nufe shi da alheri kuma ya datar da shi sai su riki fadawa cikin musibu kamar wani abu ne na gargadi da wa'azi da kuma tunatarwa , Allah Madaukakin sarki ya ce (Hakika mun riki fir'auna da jama'an sa da tsanani da fari da tawaya na daga 'ya'yan itace ko za su wa'azan tu su tuna) ko su wa'azantu domin tsanani na ratsa zukata kuma tana kwadaitar da ita cikin abin da ke wurin Allah Mabuwayi da kuma komawa zuwa gare shi.

Ya ku bayi Allah

Babu samun abunda ake kwadayi rayi ta ke sha'awa babu tsira daga abunda ake tsoro zuciya ta ke kin shi sai ta hanyan tuba na gaskiya zuwa ga Allah Mabuwayi da daukaka, Allah madaukakin sarki ya ce:(ku tuba zuwa ga Allah gaba daya ya ku musulmai ko za ku rabauta)

Rahamar Allah ga halittunSa wanda ita ta ke yaye bakin ciki kuma ta gusar da wahalhalu ba ta tabbatuwa sai ta hanyan da'a ga Allah kuma da tsoron shi da bin shari'arSa da tafiya akan sunnan manzon Sa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Allah Madaukakin sarki ya ce: (ku tsaida sallah ku bada zakka ku yi da'a wa manzo ko za ku samu rahama ko za aji kan ku), Allah Madaukakin sarki ya ke cewa:(duk wanda ya ji tsoron Allah to Allah zai sama masa mafita)

Allah Mabuwayi da daukaka ya ke cewa (duk wanda ya ji tsoron Allah zai saukake mishi daga cikin al'amuransa)

To ku koma zuwa ga Allah Subhanahu wa Ta'ala ku gyara fadin ku da ayyukan ku ku lizimci abubuwa da su ke na hani da umarni za ku samu shiriya kuma ku rabauta, Allah Madaukakin sarki ya ce:(duk wanda ya aikata aiki na kwarai na miji ne ko mace a halin yana mumini to za mu raya shi rayuwa daddada mu sakanya mishi da ladan shi mafi kyan abinda ya ke aikatawa).

 

Huduba ta biyu:

A duk lokacinda al'umma suka tabbatar da imani tabbatarwa ta gaskiya ta zahiri da ta badini a kuma duk lokacinda suka kasance akan manhaji tafarki na Allah a dukkan al'amuran su da sha'anonin su da kai -komon su a rayuwan su to Allah zai bude musu albarkatu su rayu cikin yalwa da rayuwa daddada da kuma jin dadi wanda ba wani gurbata ko bakin ciki da zai cakudu da shi

Allah Madaukakin sarki ya ce:(da ace mutanen alkarya sun yi imani sun ji tsoro da mun bude musu albarkatoci daga sama da kasa sai dai sun karyata sai muka rike su da abinda suka kasance suna aikatawa).

  

      

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق