ترجمة خطبة الشيخ عبد الباري الثبيتي
بالمسجد النبوي
اسم المترجم :أمين سعد
اللغة : الهوسا
التاريخ 6-3-1442هـ
Hudubar
juma'a na masallacin Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi na Shaikh AbdulBari Bin
Awad Assubaiti 6-3-1442Ah
Hudubar
farko:
Sura ce da
ta sauka a zuciyar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,
sai ta debe masa kewa ta share masa radadin da yake ji ta wanke masa zafin da
ya ke ji, ta kuma jefa masa natsuwa a cikin zuciyarsa.
Wahayi ya
katse wa Manzon Allah na wani lokaci, sai masu dako na dako da masu shakku na
jefa shakku sai Allah ya saukar (Allah na rantsuwa da
walaha. Da dare idan duhu ya lullube shi. Ubangijinka bai barka ba kuma bai
kaurace ma ba).
Wannan Sura ta fito da matsayin Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da kaunar Allah da ya ke masa
da kusancin shi da falalar sa ,
sabo da ya kaunaci Allah da gaske
sai Allah ya kaunace shi
(Ubangijinka
bai barka ba kuma bai kyale ka ba)
ta yaya Ubangijin shi zai juya mishi baya zai juyawa zuciyan da ya ke samun nitsuwa da
shi da ganawa da shi yakan ji dadi da
ayoyinSa da maganganunsa wallahi ba zai yi nesa ba da bawanda da ya allaka
zuciyan shi da shi sai ma ya kusanto shi ya manna shi a jiki ya
daukaka sha'anin sa , ya bashi matsayi
Wannan ayan
tana magana ne da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi kuma tana magana ne da dukkan wani mumini da mumina wanda ya yi gaskiya tare da Allah
ana jefa a cikin zuciya wani
shu'uri na kaunan Allah da kuma kusancin
shi da kuma ma'iyyarSa wato kasancewa tare da shi kuma tana kwararo
wani abu na sa'ada da yarda da kuma jin dadi Allah madaukakin sarki yana cewa:- a
cikin hadisin kudusi (BawaNa ba zai gushe ba
yana kusanta na da nafilfilu har sai na
kaunace shi idan na so shi sai in kasance jin shi da yake ji da shi da ganin sa da yake gani da shi da hanunsa da
yake damka da shi da kafan sa da
yake tafiya da ita , idan ya roke ni zan bashi idan ya tambaye ni zan bashi in kuma ya tambaye ni zan biya mishi
bukatanshi.)
(Kuma lallai lahira ya fi
ma alheri akan duniya ), lallai wato karshen al'amari a gare ka shi ya fi ma alheri akan farkon shi manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bai gushe
ba yana haurawa darajoji na daukaka Allah yana karfafan shi da addinin sa kuma yana taimakon shi yana datar da shi a kowani halayen shi
har zuwa lokacin da ya rasu a
kowani rana da yake shudewa na rayuwarsa
Allah yana kara mishi daukaka da
buwaya a cikin shi kuma ya taimake shi da taimako akan
taimako da karfafa akan karfafa har lokacin da ya ga mutane sun shiga addinin
Allah tawaga-tawaga , to hakika ya gaskata
Allah Allah ya yiawa AnnabinSa
gaskiyan Alkawari da ya mi shi ta inda
ya bude masa garin makka ya yada
da'awarsa a gabashin duniya da yammacin
ta lallai lahira ya fi duniya , lallai karshe ita tafi alheri akan farko a dukkan abin da Allah ya kaddara
lallai bawa yana mu'amala ne tare
da Ubangiji mai karamci yana wa bayinSa
jarabawa sannan kuma ya yaye musu bakin
ciki al'amarin ya kare zuwa ga
yalwa dukkan wata hala da ta jinkirta
daga cikin yanayin ka to, lallai tana da falala bisa ga halin da ya gabta (Kuma lallai lahira
ya fi ma alheri akan duniya )
Allah
ya san cewa ManzonSa ya sancewa lahira ta fi
duniya a gare shi Allah
madaukakin sarki yana cewa na tattalawa
bayiNa salihai abin da idanuwa basu taba gani ba kunne ba ta taba ji ba zuciyan wani dan adam bai taba hararo shi ba
shi ne kuma ya ke cewa wurin da
ake ajiye bulala a aljanna ya fi alheri akan duniya da abin da ke cikin ta an bawa Annabi zabi a rashin lafiyar shi tsakanin
da ya rayu a duniya iya yanda
zai rayu, da kuma abin da ya ke wurin Allah sai ya zabi abin da ya ke wurin Allah duk wanda yake da hankali na shiriya ya
san cewa lahira ya fi alheri akan duniya , lallai
duniya mai karewa ne kuma
dukkan wanda ya ke doronta kuma
zai kare sai ya rage fiskan Ubangijin ka kadai zai wanzu ma'aboci daukaka da karamci
wannan ma'ana na asali
yana tunkuda musulmi zuwa ga ya
kyautata imanin shi ya ya gyara ayukan sa
ya tsarkake rayuwarsa kuma ya habaka ayukansa a lokutansa (Ubangijinka zai baka har sai ka yarda) ana karanta wannan aya a dukkan zamani da suka shude ana kuma kawata kunnuwa da shi zuciya na raurawa tana hakaito matsayin da ke lullube yana kuma hakaito matsayin wanda aka
bawa da kuma matsayin wanda ya ke bayarwa
wanda akan kanshi yana da ma'ana
da madalulin sa kyauta ne ,
madalla da irin wannan kyauta daga mai bada kyauta wanda baya saba alkawari ba kuma wani falala bayan kyautar sa ba wani kari
akan ladanSa kuma ba iyaka bisa
ga ni'imarSa,
Allah ya bashi wani matsayi madaukaki da sammai madaukaka ya kusantar da shi ga
Annabawa gaba daya ya sanya shi
cikamakin Annabawa ya sanya al'umarsa
mafificiyar al'umu ya sanya littafinshi da ya saukar zuwa gare shi shi ne mafi
darajan littatafai ya sanya shari'arsa kuma shi ne mafi alherin
shari'o'i ya daukaka ma'abotansa ya
daraja matayensa kuma ya bashi na daga
falala wanda ba za a iya iyakance shi ba
Allah madaukakin sarki ya ce tsarki ya tabbata ga wanda in ya ga dama zai sanya maka
wanda ya fi haka alheri daga gare shi gonakai wanda koramai na gudana a karkashin sa kuma ya sanya maka benaye ya bashi ceto
ga mutanen da suke a maukif har
lokacin da Allah zai yi hukunci a tsakanin su
da ceto kuma ga ma'abota Aljanna
har su samu su shiga .
Yarda da kyautan
Allah ga wanda ya fiskanto zuwa ga Allah
sai Ubangijinsa ya so shi , wanda Ubangijin shi ya so shi kuma zai
kusanto da shi ya kawo shi kusa kuma ya yardar da shi , ya bashi nitsuwa ta zuci da kwanciyar hankali, har zuciya da cikakken natsuwa da hutu
ya gusar mishi da bakin ciki da bacin rai amma kuma abin da ya ke lahira yana cikin rayuwa ne yardajjiya to ki koma
zuwa ga Ubangijin ki kina yardajjiya
abin yarda , kina mai yarda kuma abin yarda (ashe
Ubangijinka bai same ka maraya ba kuma
ya baka mafaka ya same ka batacce
kuma baka da shiriya kuma ya shiryar da kai , ya same ka kana talaka kuma ya
wadata ka) to kamar yanda ya
bashi mafaka yana matsayin maraya kuma ya shiryar da shi da wahayi to da wannan
kuma ya wadatar da shi da dukkan wani abin da ya sha-gabansa a dukkan matakai na rayuwarsa Allah ya wadata shi da tarbiyanSa, tarbiyan
Abu –Dalib ya yin da aka samu rashin Abu-Dalib sai Allah ya wadata shi da dukiyan Khadija , yayin da aka rasa wannan
sai Allah ya wadata shi da dukiyan
Abubakar , yayin da aka rasa hakan sai Allah ya
umarce shi da hijira ya wadata
shi da taimakon mutanen madina .
A cikin
wadannan ni'imomi wanda Allah ya yi
baiwada shi ga Annabin sa tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi idan
mai bakin- ciki yayi lura da ita
sai ya gusar mishi da musiba , ko kuma ya samu wasu matsaltsalu a kan
hanya da wasu musibu to lallai wannan za ta bude mishi kofofi
ne da suke na fatan alheri da kuma wani gun shiga abun sha mai
dadi na alhini kuma ya cika shi
da azama da aiki kuma ya kiraye shi zuwa
ga ya yarda duk wani yanke tsammani ko
yanke kauna ya yada duk wani abin da ke
ga zai kawo mishi rashin nasara ya samu
sakankancewa a dukkan tafiyan sa da
rayuwarsa sabo da gamayyan rahamar
Allah da kuma kyautanSa da bayida iyaka
amma shi maraya kada a fi karfin shi
amma kuma matambayi ba a tsawatar mishi
wadannan ayoyi suna isar da ma'ana ne na shiryayyen rayuwa wanda aka assasa ta akwai daukan nauyi da
tausayawa kuma kira ne ga dukkan wanda Allah ya yiwa ni'ima da matsayi bayan da
ya kasance ba a sanshi ba , ya bashi
mafaka bayan maraya ne ya wadata shi
bayan talaka ne ya daga sha'anin sa
bayan ya kaskanta da ya godewa ni'imar Allah
.
Kada ka yi
rinjaye kada ka fi karfin maraya kada ka walakanta shi ka tsawata mishi sai dai ka kyautata mishi ka tausasa mishi kar ka kasance ga masu rauni kana mai jabbaranci kada ka yi girman kai kada ka
zama mai zafin rai kana mai maida miskinai
ta hanyar rahama tausasawa da amma ga
ni'imar Ubangijinka to ka bada labari .
Huduba
ta biyu
rayuwa domin ka ga ni'imomin Allah a gare ka a
da can baka kasance komai ba har zuwa lokacin da ka wayi gari kana wani abu
abin abin ambato ni'imar Allah a ko wani kai komo da numfasawa ni'imar samarwa da ni'imar
shiryarwa da ni'imar lafiya da zaman lafiya da ji da gani da dukiya da zuriya
da ni'iman bacci da shiryarwa da fadaka ko farka da ni'imar Allah tun daga
kanka har zuwa tafin kafan ka , (A kawunan ku ashe
ba za ku yi lura ba) ka yi lura da ni'imomin Allah cikin abin da ya
hore maka na daga rana da wata da koramai da koguna da itatuwa da dabbobi da
dare da yini ka yi lura ka yi lura bisa
ga ni'imomin Allah ka labarta da su bisa ga hanyoyi na tabbatarwa da rusunawa
da yarda da kuma wafa'I domin wannan
ni'ima su dauwama falalan su kuma ya
dauwama , domin ka rika jin wannan ni'ima din tare da kai domin ka rika jin
falala na wannan ni'ima , kuma ka san hakkinSa sai halinka ya canza daga gafala
zuwa ga mai da'a daga kuma mai gajartawa zuwa ga mai godiya ka godewa Allah a
wurin fadi da aiki, a zuciya da gabbai sai Allah ya dada hore maka ni'imomin
cikin abinda Allah ya shar'anta maka .
(Ina rantsuwa da hantsi, da dare a lokacin da ya rufe(da
duhunsa)Ubangijin ka bai yi maka bankwana ba kuma bai ki ka ba , kuma lalle ta karshe ce mafi alheri a gare ka daga ta farko , kuma
lalle ne Ubangijinka zai yi ta baka kyauta har sai ka yarda , ashe bai same ka
maraya ba sa'annan ya yi maka makoma , kuma ya same ka ba kada shari'a sai ya shiryar da kai kuma ya same ka matalauci sai ya wadata ka sabo da haka , amma maraya to, kada ka rinjaye
shi , kuma amma mai tambaya kada ka yi
masa tsawa , kuma amma ni'imar Ubangijinka sai ka fada (domin godiya )).
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق