الجمعة، 25 سبتمبر 2020

FALALAN SALLAR JAM'I

 

 

ترجمة الخطبة بالمسجد النبوي

اسم المترجم :أمين سعد

اللغة : الهوسا

التاريخ 8-2-1442هـ

Hudubar juma'a  na  masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na Shaikh  Abdullah Abuaijan 8-2-1442.AH /25-9-2020AD

 

Hudubar farko:

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah muna gode masa kuma muna neman taimakonSa kuma muna neman gafararSa muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu,duk wanda Allah ya shiryar da shi to babu mai batar da shi duk wanda ya batar da shi babu mai shiryar da shi,

.

Na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah  shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya wanzuwa na shi ne  da yabo  kuma gudananar  da al'amura  a hanun shi ya ke da  hukunci  , yana tafiyar da al'amura zuwa doron kasa daga sama  yana aikata abin da ya so ,  ba abin da za ku so sai idan Allah ya so .

Na shida Annabi Muhammadu bawqnSa ne kuma ManzonSa ne ,  ya  isar da sako kuma ya sauke  amana  ya yi nasiha wa al'uma ya yi jahadi a tafarkin Allah cancancin jahadi , har mutuwa ta zo mi shi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi  da sahabbaan shi baki daya  .

Bayan haka:

Lallai littafin Allah shi ne zance mafi mikewa , shi ne kuma dalili  mafi  shiryarwa  kuma sunnan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  shi ne mafi alherin manhaji , kuma mafi adalcin tafarki  kuma abin koyi kyakkyawa  a wurin bi  kuma bata da kauce hanya na cikin kirkiran bidi'a  .

Ya ku bayin Allah   :

Ku ji tsoron Allah a cikin abin da ya yi umarni  , ku hanu daga abin da ya hana kuma ya tsawatar  (Ya ku wadan da kuka yi imani ku ji tsoron allah ku fadi  maganan da yake na daidai zai   gyara mu ku ayukan ku  kuma ya gafarta  mu ku zunuban ku ,  duk wanda  ya yiwa Allah da Mnzon sa da'a to hakika ya rabauta , rabauta mai girma)

Ya ku jama'ar Musulmi:

 Masallatayya dakuna ne na Allah  kuma mafi soyuwan bigire a gare shi an tanada su ne don bauta da sallah da ambaton Allah zuwa gare su wanda ya yi imani  da shi  kuma ya jibince shi  ya ke komawa (Lalle mai raya masallatan Sa shi ne  wanda y a yi imani da Allah da ranar lahira ,  ya tsaida sallah ya bada zakka bai ji tsoron wani ba face Allah ,  ya wuci wadancan   su kasance  cikin shiryayyu .)

Ba bu mai raya su sai muminai na gaskiya , Allah Madaukakin sarki ya ce :(Mushrikai ba su kasance da su raya masallatan Allah ba)

:(cikin wasu gidaje da Allah ya yi umarni da daukaka kuma a ambaci sunanSa cikin su, wasu mazaje suna tasbihi a gare shi safiya da maraice, kasuwanci bai shagaltar da su ko ciniki daga ambaton Allah da tsaida sallah da bada zakka suna tsoron wata ranar da zukata da ganai ke juyawa)

Allah ya yi alkawarin narkon azaba ga  wanda ya yi saddu ga tafarkin su  ya bata wuraren kiran sallan su da mihraban su  sai ya ce:- (Wa ya fi zalunci  sama da wanda ya hana masallatayyan Allah  da  a ambaci sunanSa a cikin su  kuma yayi aiki wurin rusa su  wadannan bai kasance ba a gare su da su shige su face suna halin tsoro ,  suna da wulakanci anan duniya a lahira kuma suna da azaba mai girma ) 

Ya ku bayin Allah :

Masallatai dakunan Allah ne , su ne mafifitan gurare da bigire, su ne makwancin wanda ke bautawa Ubangijinsa ya yi biyayya.

Daga wuraren kiran sallan su  ne ake maimaita shahadan tauhidi ko wace rana  bisa kunnuwa; na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah  na shaida Annabi Muhammadu Manzon Allah ne.

Daga wuraren kiran sallanta ne ake maimaita yekuwa zuwa ga sallah  kinshiki na musulunci , na  biyu daga   cikin rukunan sa masu girma , ku gaggauto zuwa ga sallah, ku gaggauto zuwa ga sallah , ku gaggauto zuwa ga babban rabo .

Daga mihirabansu  ne da mimbarorin su  sako na imani ya taso , ya bude zukata da kunnuwa , kuma ya goge duhun shirka da gumaka .

Su ne farkon makarantu na tarbiya da ilmantarwa a musulunci, tawaga irin na sahabbai masu  daraja daga nan su ka fito , sai suka kasance mafi cancantan mutane a ilimi da aiki.

Su ne farkon  tawagan da aka kafa  mimbari na da'awa , sai suka  yada musulunci dukkan duniya  da da'awa da jahadi da halaye .

Ya jama'ar musulmi:

Lallai mafifici kuma mafi daukakan ayuka a wurin Allah da girman matsayi awurin Allah  shi ne raya masallatayya  dakunan Allah (Abin sani kawai wadanda suka yi imani da Allah su ne ke raya masallatayyan Allah ).

Kuma raya masallatayya na  kasancewa ne ta hanyar gina su da bauta a cikin su   da fiskantar su don tsaida sallah da amsa kiran mai kira idan ya kira a gaggauto zuwa ga sallah .

An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi   ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gre shi ya ce :- (Da ace mutane sun san abin da ke cikin kiran sallah da sahun farko  sa'annan ba za su same su ba sai da kuri'a  to da sun yi kuri'a  kuma da ace sun san abin da ke cikin  diban garji  da sun yi tsere zuwa gare shi  da sun san abin da ke cikin isha'i da asubahi da sun zo mu su ko da da rarrafe ne ) Buhari da Muslim ne suka rawaito 

Ya ku bayin Allah:

Na daga cikin abin da ke daga darajoji ya kankare laifuka akwai yawan taku zuwa masallatayya,  An karbo da ga Abu Huraira yace :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : Shin bazan fada maku ba abin da zai kankare maku zunubanku ba,ya daukaka darajarku ba.sai yace:

"Yawan taku zuwa masallaci,kyautata alwala alokacin da ake kin taba ruwa, da zama jiran sallah bayan sallah, wannan shine ribadi wannan shine Ribadi) Muslim ne ya rawaito

An karbo da ga Abu Huraira yace :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Duk wanda yayi Sammako ko yayi yammaci zuwa Masallaci, Allah yayi masa tanadin mazauni a aljanna,duk lokacin da yayi Sammmako ko yammacin zuwa Masallaci).

Ya ku bayin Allah:

Ya ku mazowa dakunan Allah masu raya masallatan Allah, barkanku da samun mafi yalwan inuwa. Albishirinku da mafi kyau da cikan haske,  

An karbo da ga Abu Huraira yace :Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Mutum bakwai suna cikin inuwar Allah ranar da ba wata inuwa sai inuwarSa sai ya ambaci  da mutumin da zuciyarsa ke ta'allake da masallaci) Buhari da Muslim ne suka rawaito.

An karbo daga Buraida al aslami Allah ya kara yarda a gare shi yace : -Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  yana cewa:

(Ka yiwa masu yawaita tafiya zuwa Masallaci cikin duhu da wani haske cikakke a ranar  alkiyama).

Abu Dauda da Tirmizi.

Ku sanya wa gidajen Allah wani kaso na daga lokacin ku , haka nan kuma da ibadojin ku ku sanya  wani kaso  na farilla , ku gabatar wa ibadun ku abin da zai amfane ku kuma Allah ya daukaka ku da shi ranan alkiyama , (kuma abunda ku ka gabatar wa kawunan kuy na daga alheri za ku same shi wurin Allah mafi girma a lada ku nemi gafarar Allah , Allah mai gafara ne mai jin kai)

 

Huduba ta biyu

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa datarwarSa godiya a gare \Shi bisa datarwan Shi da kuma baiwansa na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya ina mai girmama Sha'anin Shi na shaida cewa Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma Manzon Sa ne mai kira zuwa ga yardar Sa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da sahabban sa da aminci tabbatacce mai yawa.

Ya ku bayin Allah:

Sauke garilla cikin jama'a yana cikin manya manyan alamomi na musulunci kuma alamomi na imani (ku yi ruku'u tare da masu yin ruku'u), sallan jama'a ya ku bayin Allah yana daga cikin mafificin ayyuka kuma mafi daukakan da'a kuma mafi tsarkakan ayyukan kusanci kuma darajoji an karbo daga Abdullahi dan Mas'ud Allah ya kara yarda a gare shi ya ce (Duk wanda zai burge shi da ya hadu da Allah gobe yana musulmi to ya kiyaye wadannan salloli din a yayin da ake kira zuwa gare su domin lallai Allah ya shar'anta wa Annabin ku tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wasu sunnoni na shiriya, lallai su din nan duk suna cikin sunnoni na shiriya, da ace za ku yi sallah a cikin gidajen ku kamar yanda wannan wanda bai samu jam'I ba aka barshi ya yi sallah a gida to da hakika kun bar sunnan Annabin ku da kuma kun bar sunnan Annabin ku da kuwa kun bata , ba wani mutumi da zai yi tsarki ya kyautata alola sa'annan ya nufi zuwa masallaci cikin wadannan masallatan face Allah ya rubuta mishi a ko wani takawa da zai yi za a rubuta mishi lada a daga shi daraja da ita a kankare mishi laifi dalilin ta , hakika ba wanda ya ke barin sallah a cikin mu face munafiki wanda aka san shi da munafinci , hakika mutum ya kasance ana zuwa da shi ana tagire gire da shi tsakanin mutane biyu har a zo a tarar da shi cikin sahu) Muslim ne ya rawaito

An karbo daga Ibnu Umar Allah ya kara yarda a gare shi shi da mahaifin shi cewa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (sallan jama'a yafi sallan mutum daya da daraja ashirin da bakwai ) Muslim ne ya rawaito.

An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:(sallan mutum a cikin jam'I tana ribanya sallan sa a cikin gidan shi haka nan a kasuwan shi da da ribi ashirin da biyarsaboda haka nema idan mutum ya yi  alola ya kyautata alola sannan ya fita zuwa  ga masallaci ba abin da ke fitar da shi sai sallah to ba zai yi wani taku ba face dawannan takun an daga darajan shi da ita kuma an kankaare mishi kuskuren shi da ita idan ya yi sallah mala'iku ba za su gushe ba suna mishi salati muddin yana wurin sallan sa suna cewa : Allah ka yi dadin tsira a gare shi ya Allah ka mishi rahama, dayan ku ba zai gushe ba yana cikin sallah muddin ya tsaya jiran sallah) Bukari ne ya rawaito.

Ya ku bayin Allah:

Hakika hudubar musiba ta korona ya girmama ga musulmai ya lalata sallan jam'i bakin ciki da bacin rai sakamakon ta'allukin  zuciya ke yi da masallaci  sai radadin da shaukin da kwadayin ya yawaita ga mutane .

Hakika Allah ya zo da yaye bakin ciki sai ya sanya mafita ga ko wani kunci  da dukkan wani damuwa ya sanya mishi farin ciki , to ga shi masallatai an bude kofofin su an kimtsa su farfajiyan su an shirya  su, ga dakunan Allah suna jiran masu raya su da masu ziyartan su an daga sautukan kiran sallan su suna kira ku gaggauto zuwa ga sallah ku gaggauto zuwa ga sallah ku gaggauto zuwa ga babban rabo ku gaggauto zuwa ga babban rabo .

Muna godewa Allah kuma muna kyautata yabo a gare shi muna rokon shi da ya dauke abin da ya saura na daga wannan annoba kuma ya tunkude shi daga gare mu dukkan wani bala'i  kuma  ya cika mana cikakken lafiya da waraka ku gaggauto ya ku bayin Allah zuwa ga dakunan Allah ku amsa kiran mai kiran Allah idan ya kiraye ku zuwa ga Allah da Manzon Sa idan ya kiraye ku zuwa ga abin da zai rayaku kuma ya sa ku cikin walwala ya shiryar da ku, ku tsaida fuskokin ku a dukkan wuraren masallataiyya, ku kiyaye farilloli ta inda duk lokacin da aka yi kira zuwa gare su , (abun sani wanda ya ke raya masallatayyan Allah shi ne wanda imani da Allah da ranan lahira kuma ya tsaida sallah ya bada zakka kuma bai ji tsoron kowa ba sai Allah ya wuci wadannan su kasan ce cikin wadanda su ke shiryayyu) .

   

Yak u bayin Allah Lalle ambaton ni'imar Allah na daga abin da ya yin a ni'ima da shi ga wannan kasa mai albarka na ni'imar tauhidi da hadin kai da zaman lafiya da kwanciyar hankali da hidima ga masallatayya biyu masu alfarma da masu zuwa gare su, da bada kulawa ga batutuwa da suka shafi musulmai, da irin ayyuka na jinkai a lokuta daban daban, da tabbatar da zaman lafiya na duniya tun lokacin da aka kafa wannan kasa har zuwa wannan lokaci da muke ciki. Wanda zai sa mu godewa Allah ga wadannan ni'imomi, da kiyaye amincinta da dukiyanta da tabbatar da hadin kai irin na addini da dunkulewa irin na kasa daya mubaya'a irin ta sharia da lizimtar jama'a da jagoranci da ji da bi da adua ga shuwagabannin kasanta ya datar da su, Allah ya kiyaye kasar mu da sauran kasashen musulmai daga duk wani abu mummuna da abin ki, lalle Shi mai ji ne mai amsawa.

 

  

 

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق