اسم
المترجم :أمين سعد
اللغة :
الهوسا
التاريخ
16/1/1442ه
Hudubar
masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na 16/1/1442 na
shaihk Husaini Al -Asshaikh
Hudubar farko:
An
karbo daga Mua'azu dan Jabal Allah ya kara yarda a gare shi daga Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:(ka
ji tsoron Allah a duk inda ka ke, kuma ka bi mummuna da kyakkyawa sai ta goge
ta, ka mua'amalanci mutane da kyakkyawar dabia'a) Ahmad ne ya
rawaito da Tirmizi kuma ya ce hadisi ne hasan, kuma da yawa daga cikin malamai
sun inganta shi lallai hadisi ne mai girma da ya kumshi wasiyya mai girma wanda
ya ke masu jumloli masu girma da ka'idoji muhimmai Ibnu hajar alhaisami ya ke
cewa: wannan hadisi ne da ya tattaro sauran hukunce hukunce na shari'a wasun su
sun ambace shi da uwar sunna ,aiki da shi ya kan kawo walwalan gidan duniya da
na lahira da rabauta a cikin su:
Tushe
na farko : akwai tabbatar da takawa ga Allah Mabuwayi da daukaka ta hanyan
lizimtan umarnoni da da'a da kuma nisatan sabo da laifuka a bayyane da kuma
boye .
Lallai
wasiyya ce da ta kan sa bawa duk inda ya ke ya lizimci kiyaye dokokin Allah
kuma ya yi nesa daga abubuwa na laifi da abubuwa da su ke muharramai , yana mai
daidaito a kan tafarki mekakke yana mai kulawa da shi a cikin dukkan sha'ani
Allah Madaukakin sarki ya ce :(ku ji tsoron Allah
kuma ku sani lallai Allah yana ganin abin da ku ke aikatawa)
Kuma
Allah Madaukakin sarki ya ke cewa(ku ji tsoron
rananda za ku koma zuwa ga Allah sa'an nan a cikawa ko wace rayi abunda ta
kasance ta ke aikatawa ba za ayi zalunce ku ba).
Ibnu
Abbas da Sa'id dan Jubair suka ce: wannan wasiyyar Allah ce ga bayinSa a a'aya
ta karshe da ta sauka a cikin alkur'ani , kuma Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce:(ka kiyaye
Allah sai ya kiyayeka). Lallai aiki da wannan asali yana hukunta
samun rabauta mai girma da kuma lada mai daraja.
Ya zo
cikin sahihain wato Bukhari da Muslim cewa Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce: (Mutane bakwai Allah
na musu inuwa a cikin inuwarSa ranar da ba wata inuwa sai inuwarSa, kuma ya
ambaci a cikinsu da mutumin da mace ma'abociya matsayi da kyawu ta neme shi sai
ya ce lallai ni ina tsoron Allah Ubangijin talikai)
Tushe
na biyu: biyar da kyakkyawa bayan mummuna, ita kyakkyawa kalma ce da ta tattaro
dukkan abin da zai kusantar zuwa ga Allah Mabuwayi Mai daukaka, mafi girman
kyawawan abin da su ke tunkude munana shi ne tuba da gaske da kuma neman gafara
ta gaskiya da kuma komawa zuwa ga Allah komawa ta gaskiya,
Imamu Ahmad ya rawaito daga Abu zarri ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (wani ya ce: ya Manzan Allah ka mini wasiyya sai ya ce:
idan ka yi aiki mummuna to ka biyo ta da kyakkyawa sai ta goge ta ,sai ya ce:
ya Manzan Allah na daga cikin kyawawa (la ilaha illallah)?sai ya ce ita ce
mafificiya a cikin kyawawa).
Aikata
ayyukan alhairi yana kankare zunubbai da
suka shude Allah Mabuwayi da daukaka ya ce:(kuma ka
tsaida sallah a gefe guda biyu na gini da wani yanki na daga dare lallai ne
ayyukan kwarai suna kore munanan ayyuka).
Allah
Madaukakin sarki ya ce:(idan za ku nesaci manyan
zunubai to za Mu kankare muku laifuka (kanana)), yazo a sahihu
muslim (salloli guda biyar da kuma juma'a zuwa
juma'a da ramadana zuwa ramadan suna masu kankare zunubban da ke tsakaninsu
muddin aka nesaci manyan zunubai).
Tushe
na uku: mu'amalantar halittu da kyawawan dabi'u da kuma kyawawan halaye da
kuma tafarki wanda ya ke mai kyau wannan kuma ta hanyan dadadawa halittu da
sake musu fiska da yalwata ayyukan ma'arufi gare su da kuma kamewa daga cutar
da su, asali shi ne ka yardarwa dan uwanka abin da ka yarda wa kanka na daga
maganganu kyawawa da ayyuka kyawawa da muamala na mutunci,Allah Madaukakin
sarki ya fada yana mai yabo ga ManzonSa tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi (lallai kana kan wasu dabi'u masu girma)
Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce: (mafi cikan mumini
imani shi ne wanda ya fi su kyakkyawan hali) Tirmizi ya rawaito kuma
ya ce hadisi ne hasan sahihi,Ibnu hibban da hakim sun inganta shi , Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:(lallai mumini yana riskan darajan mai azumi da mai
tsayuwa ta hanyan kyawawan halayensa) Abu dauda ne ya rawaito kuma
Ibnu hibban ya inganta shi.
Ka yi
kokari ya kai dan uwana musulmi a rayuwanka ka kasance cikin ma'abota kyawawan hali kuma masu bin abu buwa na yardan Allah wannan shi ne aiki
mai girma a wurin Allah kai Annabi tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kidanya haka ma cikin da'a mai sadarwa zuwa ga aljannan alkuld.
An
tambayi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi menene
biyayya kuma da laifi? Sai ya ke cewa:(Biyayya: ita
ce kyakkyawan hali, shi kuma laifi shi ne abin da ya sosa cikin zuciyarka kuma
ka kyamaci mutane su tsinkaye shi) Muslim ne ya rawaito.
Hakika
an tambaye shi kuma game da yawan abin da ke shigarwa aljanna sai ya ce (tsoron Allah da kyakkyawan hali) Tirmizi ne ya
rawaito kuma ya ce hadisi ne hasan sahihi , Ibnu hibban ingantashi
Ku
tabbatar - Allah ya muku rahama- wadannan ginshikai masu girma ku lizimce su
wadannan ka'idoji masu girma za ku samu rabauta ku samu walwala da nasara a
duniya da lahira .
Huduba ta biyu:
Na daga cikin kyawawa wadanda su ke goge
laifuka shi ne akwai kyautata wa mutane ta fiskoki daban daban, Allah
Madaukakin sarki ya ce (ku kyautata lallai Allah yana
son masu kyautatawa) ,
An
karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: wani mutumi ya ce
ya Manzon Allah : lallai wance tana yawaita sallolinta da sadakanta da azuminta sai dai
kawai tana cutar da makwabciyarta da harshenta sai Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: (tana
wuta) , sai aka ce ya Manzon Allah lallai wance ana
ambaton karancin azuminta da sallan ta
kuma tana yin sadaka da wani yanki na
cukui amma bata cutar da makwabtanta , sai Manzon Allah tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi ya ce (tana cikin gidan
aljanna) Ahmad ne da Bazzar suka rawaito da Ibnu hibban a cikin
sahihansu da hakim kuma ya ce hadisin sahihi ne isnadinsa da kuma wasu sashi na
daga malaman hadisi sun ingantashi.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق