الجمعة، 28 أغسطس 2020

DAGA SHIRYARWAR SURATUL IKHLAS

 

اسم المترجم :أمين سعد

اللغة : الهوسا

التاريخ 9/1/1442ه

Hudubar masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na 9/1/1442 na shaihk Abdul Bari dan Awad Alsubaiti

 

Hudubar farko:

 Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah da iyalanSa da sahabbansa da wanda suka biyo su,,,,,, bayan haka:

wata sura ce mai girma, - dukkan surorin Alkur'ani kuma na da girma- gajeruwa ce a harufanta, amma tana da zurfin ma'ana a ma'anoninta, ta tattaro abubuwa da su ke na dabi'u masu kyau ta kebanta da girma na falaloli tana daidai da daya bisa ukun Alkur'ani , Allah Madaukakin sarki ya ce:(ka ce : Allah Shi daya ne) (Allah wanda ake komawa yayin bukata)(Bai haifa ba kuma ba a haife Shi ba )(kuma bai da wani da ya ke kininSa), kul huwa Allahu ahad,  Allah : wannan sunan shi ne sunan da yafi ko wanne cikin sunayen Allah kuma shi ne sunan da ya fi ko wanne a wurin biyayya da kuma wurin tattarowa, Allah : shi ne suna mafi girma , shi ne abin ambato mafi daukaka , jalalarSa ta cika sammai bakwai da abin da ke cikinsu kasaitarSa ta kewaye doron kasa da abin da ke kanta da abin da ke karkashinta da kuma abin da ke cikinta sanin Allah tushe ne na dukkan ilimi, kai shi ne sani mafi daukaka kuma mafi girma mafi kasaita Allah Madaukaki ya ce:(Shi ne Allah a cikin sama kuma a kasa)

Babu rayuwa ga zukata kuma babu farin ciki babu annashawa babu ni'ima babu debe kewa face na cikin sanin Allah , Malik dan Dinar ya ce: ''Miskinan gidan duniya sun fita daga gidan ba su dandani abu mafi dadi ba a cikinta sai aka ce da shi , menene abu mafi dadi a cikinta? Sai ya ce: sanin Allah da kaunarSa''

sani ne wanda ke tabbatar da wuyaye a masaukai na bauta da kankan da kai da rusunawa da kauna , Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:(lallai Allah na da sunaye  casa'in da tara, dari ba daya duk wanda ya kiyaye su zai shiga aljanna), duk wanda ya so Allah da sunayen Shi da siffofin Shi Allah zai kaunace shi idan ya so shi kuma zai debe kewa tare da ambaton shi kuma zai yi shauki zuwa gare shi kuma da zuwa haduwa da shi.

Gwargwadon sanin mutum gwargwadon girmamawan shi ga Alla Mabuwayi da daukaka, matakan mutane cikin bauta gwargwadon abin da ya dasu a cikin zukatan su ne na sanin Allah.

 kamar yanda halayen mutane ya dara juna a cikin salla da gwargwadon halartowan su da ma'anonin da sakon sanin Ubangiji.

Sanin Allah na sanya bawa ya halarto da kasancewan Allah tare da shi a dukkan halayen da ya ke ciki sai zuciyarsa ta samu natsuwa, ya samu kwanciyan hankali ya dogara zuwa ga Allah dogaro na gaskiya kuma ya samu sakankancewa da Allah bisa gaskiya ,Allah Madaukakin sarki ya ce: (wadanda suka yi imani zukatansu na natsuwa da ambaton Allah ku saurara da ambaton Allah ne zukata ke natsuwa).

Duk wanda ya san Allah cancancin saninSa zai ji dadi a sujjadarsa zai yi sallah sai ya yi kushu'i a tsayuwarsa da zamarsa kuma zai zama yayi yawo a malakutin sama ko a malakutai yana mai lura yana mai tafakkuri wato tunani harshensa zai zama yana furtawa da ''tsarki ya tabbata ga Allah… godiya ta tabbata ga Allah …Allah mai girma… ba abin bautawa da gaskiya sai Allah…''

Sunan Allah idan aka ambata a abin da ya ke dan kadan sai ya karu, idan aka ambata shi yayin shiga tsoro sai tsoron ya gushe, idan lokacin bakin ciki ne sai bakin cikin ya yaye, idan lokacin bacin rai da damuwa ne sai mutum ya samu farin ciki da walwala, idan lokacin kunci ne sai mutum ya samu yalwa, duk wanda ya san Allah zai ji kunyan Ubangiji ya same shi wurin da ya hane shi kuma ya rasa shi a wurin da ya umarce shi saboda yana tuna kasaitar Allah (ka dogara ga Mabuwayi Mai rahama) (wanda ya ke ganinka a lokacinda ka ke tashi) (da kai komonka cikin masu sujjada) .

Idan halarto da ma'anoni na sanin Ubangiji ya raunana to sai mabubbuga na imani ya bushe kututturen dadin biyayya sai ya dushe zuciya sai ta kekashe mutum ya fada cikin damuwa , damuwa ya yawaita a tare da shi ya rika shiga cikin tsoron abin da zai fiskanto da kuma arziki

(ka ce: Allah daya ne):Shi ne guda daya wanda ba Shi da makamanci ba wani wanda ya ke irin Shi a kudurarSa ne to Shi kadai ne a SiffofinSa Shi daya ne a zatinSa Shi ne Mahalicci Mai azurtawa, Mi rayawa, Mai kashewa Mamallaki, Mai sarrafa halittunSa yanda ya so, ba a neman agaji da taimako da tsari sai zuwa gare Shi, Shi kadanShi .

(Allahussamad): Shi Samadu Shi ne wanda ya cika a siffofinsa wanda dukkan halittu na bukatuwa zuwa gare Shi, wanda ya wadata daga dukkan kowa, wanda baya mutuwa , ba ya gadarwa amma duk abin da ya ke na sama da kasa dukka gadonSa ne wanda ba ya barci , ba ya mantuwa Shugaba wanda shugabancinSa ya kammala ya cika Mai girma a iliminSa da hikimarSa da hakurinSa da kusurarSa da buwayarSa da dukkan siffofinSa tsarki ya tabbata a gare Shi Madaukaki (Assamadu): Shi ne wanda halittu ke dumfara yayin bukatu a bukatunsu kuma ya gamsar da su, sunan Allah (Assamadu): yana sanya bawa ya rika jin wani karfi da izza da wadatuwa daga dukkan wani da ke koma bayan Allah Mabuwayi da daukaka sai ya sakankance ma'anar cewa Allah din nan ya ishi bawanSa tofa domin assamadu yana jin ganawarsa yana ganin wurinSa ko da dukk duniya ne suka tattaru dommi su cutar da shi ba za su iya cutar da shi ba da wani abu face sai abin da Allah ya rubuta a gare shi .

(lam yalid wa lam yulad): Shi ne rayayye wanda ba ya mutuwa Mai wanzuwa bayan karewan halittunSa Shi ne mai tsarki wadatacce daga da'a, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ke cewa : (Ba wani da ke mafi hakuri bisa cutarwar da ya ji shi kamar Allah, lallai suna sanya miSha da'a alhali kuwa yana azurta su kuma yana basu lafiya) .

(wa lam ya kun lahu kufwan ahad) ta yaya zai kasance yanada kini alhali kuwa Shi ya halicci dukkan komai? , ya samar da dukkan kowa Shi ya samar da kowa da kowa Shi ne babba Mai daukaka wanda Shi ne yafi dukkan komai kuma mafi girma ga dukkan komai, an karbo daga Anas dan Malik Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: (wani mutumi daga cikin ansar ya kasance yana jan mutane salla a masallacin kuba ya kasance a duk lokacin da ya fara karatun sura yana farawa ne da ita a cikin sallan da ke musu, sai ya fara da (kul huwa Allahu ahad) har ya kare da ita sannan ya karanta wata sura daban tare da ita ya kasance yana yin haka a ko wace raka'a mutanensa suka mishi magana sai suka ce kai kana bude salla da wannan suran sannan kuma ba ka ganin ita ta isar maka ba sai ka karanta wata ba? ko dai ka karantata ko ka barta ka karanta wata ,Sai ya ke cewa: ni ba zan barta ba, in kuna so na cigaba da limantanku ko jagorantan ku a salla to sai na yi in kuma kun ki ba kwa so to sai na barku  kuma suna ganin lallai shi ne ya fi su daraja, sai suka ki waninsa ya musu limanci , yayinda suka zo wurin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, su ka bashi labari da wannan labarin sai ya ce: ya wane : mai ya hana ka ka aikata abin da mutanenka ke umartanka da shi? Meyasa ka ke lizimtan karanta wannan sura a ko wace raka'a? sai ya ce: ni ina kaunanta ne sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: kaunar da ka ke mata ta shigar da kai Aljanna) Buhari ne ya rawaito .

Huduba ta biyu:

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ji wani mutum yana cewa : (Ya Allah ina rokonKa, lallai kai ne Allah Tilo, wanda ake dumfara yayin bukata wanda bai haifa ba kuma ba a haife Shi ba, bai  da wanda ya ke kininSa, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Hakika ya roki Allah da sunan Shi mafi girma wanda idan an roke Shi da shi zai bada, idan an yi adu'a da shi zai amsa) Ibnu Majah ya rawaito Albani ya inganta shi

  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce: ((kul huwallahu ahad) da(kul a'uzu ) guda biyu a yayin da aka wayi gari da yayin da aka yi yammaci sau uku sun isar maka ga dukkan komai) Abu Dauda ne ya rawato da isnadi ingantacce .

Gobe asabar ne  ranan ashura, hakika Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana kirdadan wannan rana na ashura kuma ya ce: (lallai ina fatan Allah ya kankare zunubin shekaran da ta gabata) Abu Dauda ne ya rawaito da isnadi ingantacce.     

 

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق