اسم
المترجم :أمين سعد
اللغة :
الهوسا
التاريخ
2/1/1442هـ
Hudubar
masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na 2/1/1442 na
shaihk Ali dan Abdurrahman Alhuzaifi
Hudubar farko
Dukkan yabo da
godiya sun tabbata ga Allah Masanin gaibi Mai juya zukata Mai yawan gafarta
zunubai, kyautata yabo ga Ubangiji na kuma ina gode mishi bisa
ni'imominSa da wani bai iya kididdige su
in ba shi ba, na shaida ba abin
bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, da mulki
da godiya na shi ne kuma mai iko ne ga dukkan komai, na shaida Annabinmu kuma
shugabanmu Muhammad bawanSa ne, kuma manzonSa ne mai albishir mai gargadi, ya
Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka, bisa ga bawanka Muhammad da
iyalansa da shabbansa wadanda Allah ya jibince su to madalla da Majibinci kuma
madalla da Mataimaki.
Bayan
haka, ku ji tsoron Allah Mai tsarki a boyenku da bayyanenku, domin ya jibinci
lamuranku ya kuma gyara muku halayenku, Takawa ita ce tafarkin mutanen
kwarai masu rabauta rasa ta kuma shi ne
bayyananniyar hasara .
YA KU BAYIN ALLAH
Ku
kasance daga ma'abota basira da imani, ku bi tafarkin ma'abota hankula da kyautatawa, ma'abota hankula su ne
wadanda hankulan su ke lafiyayye
mikakke, masu lafiyayyan fidira su ne
wadan da suke amfana da wahayi kuma suke fahimtar abin da Allah ya saukar, bisa muradin Allah da kuma muradin Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi suna aiki da maganar Allah domin fatar lada
kuma suna tsoron ukubarSa .
Allah
Madaukakin sarki ya ce :-(Kuma wadan da
suka nisanci dagutu da su bauta masa
suka koma zuwa ga Allah, su na da kyakkyawan bishara, to, ka yi albishir ga
bayi Na, wadanda suke jin magana kuma su bi mafi kyau daga ciki, wadan nan su
ne wadan da Allah ya shiryar da su kuma wadan nan su ne ma'abota hankula ).
Lura
na daga cikin ayyukan masu hankali masu basira, na daga cikin ayyuka na basira
kuma da gwanancewa shi ne ; lura yana
shiryarwa zuwa ga rabauta da tsirata
daga abubuwa dake halakarwa, kuma yana datar da ma'abotan shi zuwa aiki na
kwarai ya nusar da ma'abotan shi
zuwa ga tafarkin mutane na gari masu neman gyara karshen shi kuma yakan koma ne zuwa ga
alheri, wanda aka haramta mishi lura to
wa'azi ma ba zai amfane shi ba, zai fada kuma cikin halaka kuma zai bi sha'awe
-sha'awen ransa zai bi tafarkin
mabarnata kuma ya zama ya yi nadama.
Lura
shi ne kaura daga hali na mushahada ko hali da ya shude wanda yake akwai ukuba
da azaba zuwa hali mai kyau abin a yaba
a hankalce da a shar'ance, ta hanyar nisatar sabuban ukuba da kuma azaba, ko
kuma kaura daga tarihin salihan bayi da abin da Allah ya karrama su da shi na
aiki da ayyukan su da kuma bin sawun su
ko kuma tuntuntuni cikin dabi'un halittu
da sanin sirrin da ke ciki da sifofin su ,
da hikiman da ya sa mahaliccin su ya halicce su, da kebantar da shi da tauhidi da da'a ga
Allah tabaraka wa ta'ala.
Hakika
Allah Mabuwayi da daukaka ya halicci halittu
ya sanyawa duniya wata sunnan da take tafiya a kai, sai ya sanya
biyayya sababi ne na dukkan alheri a nan
duniya da lahira, ya sanya kuma saba
mishi sababi ne na dukkan sharri a
duniya da lahira .
Shin
akwai wanda za ka ga ya tsiyace sabo da biyayya wa Allah ko kuwa za ka samu wanda ya samu rabauta sabo
da sabon Allah, hakika Allah ya bamu kissa tsarki ya tabbata a gare shi a cikin littafinSa kuma Manzon Allah ma tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi ya kissanta mana , daga kissoshi na halayen Annabawa da
Manzanni da muminai da abin da ke ciki na abin lura, da abin koyi ga wanda ke
bayan su, da kuma tsirata daga ukubobi,
da rabauta da dukkan alhairu
wanda a cikin shi za ka samu kyakkyawan karshe, da wanda a cikin su akwai akiba mafi kyau da
kuma darajoji Allah Madaukakin sarki ya
ce :-
(Hakika a cikin kissoshin su ya kasance akwai abin lura ga ma'abota hankula ).
Ba zance ne na kage ba, sai dai gaskatawa ne ga abin da ya
gabata da kuma bayani daki-daki na
dukkan komai da shiryarwa da rahama ga mutane masu imani
.)
Allah
Madaukakin sarki ya ce:- (Sa'annan muka tseratar
da ManzanninMu da wadan da suka yi imani
hakanan ne ya kasance hakki a gare mu da mu tsiratar da muminai).
Allah
Mai tsarki ya fadi game da masu karyatawa ( Ya
ce suka yi makirci muma muka mai da musu makircin su a halin ba su sani ba, to
ka dubi karshen makircin su yanda ya kasance;
shi ne Mun rusa su da mutanen su
baki daya wadancan gidajen su ne ba
komai sakamakon zalunci da suka yi
lallai a cikin wannan akwai abin lura ga
mutane da suka gane, muka tsiratar da wadan da suka yi imani kuma
sun kasance suna tsoron Allah).
Yayin
da Allah ya bamu kissoshi masu yawa na
daga Annabawa amincin Allah ya tabbata a gare su a cikin suratul Al-shu'ara sai
ya rufe kissan bayan tsiratan Manzanni
da muminai tare da su sai ya rufe kissan da fadinSa (Lallai a cikin haka akwai abin lura amma mafi
yawan su ba su kasance suna muminai ba• lallai Ubangijinka shi Mabuwayi ne kuma mai
jin kai.)
Ibnu
Kasir Allah ya mishi rahama yake cewa '' Lallai a cikin haka akwai aya, wato a wannan kissa
din da abin da ke cikin ta na ban mamaki
da kuma nasara da karfafan bayin Allah muminai, ta hanyar dalilai da hujjoji na yanke da kuma
hikima wanda takai kololuwa".
Lallai
Ubangijinku shi ne Mabuwayi ai Madaukaki da ya buwaya daga dukkan komai, kuma
mai yin galaba akan abun kuma ya rinjaye shi, ga rahama kuma wato ga halittun
sa baya gaggawa da ukuba ga wanda ya
saba mishi sai dai yana saurara mishi ya jinkirta mishi sannan ya damke shi damka irin na Mabuwayi Mai
iko.
Sa'id bin Jubair ya ke cewa Allah Mai jin kai
ne ga wanda ya tuba zuwa gare shi kuma ya komo zuwa gare shi , maganar ta tike.
A fadin Allah Madaukakin sarki a kissan
mutanen ludu tsira da amincin Allah su
tabbata a gare su.
(Lallai a cikin haka akwai ayoyi ga masu hankula). Katada ya ke cewa ; masu hankula ana nufin masu lura Albagawi shi
ya ambata shi a cikin tafsirinsa ba masu amfana da abubuwan da ke faruwa na
tarihi da hikimomi da ke ciki na yanayi face
wadanda suke masu lura masu
tunani wadan da suke koyi da ma'abota na
kwarai da mutane na gargaru, masu neman
gyara suna kyale mutanen barna da masu kawo barna, amma wanda baya lura baya
wa'azantuwa baya muhasaba wa kanshi baya aiki don lahiransa, addinin sa baya
hana shi hankalin shi baya hana shi yin abu mara kyau da laifuka to, wannan
kamar dabba ya ke, Allah Madaukakin sarki ya ce:- ( Ko kana zaton cewa mafiya yawan su suna ji ne ko suna
hankaltuwa , a'a su dinnan ba komai ba ne sai kamar dabbobi ne, kai sun fi ma dabbobi
bata).
Ya
zo a cikin Hadisi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi (Lallai mumini
idan ya yi rashin lafiya ciwo ya same shi sannan ya mutu zai kasance kaffara ne a gare shi game da
zunuban shi cikin abin da ya shude idan ya bashi lafiya sai ya kasance kaffara
ne cikin abin da ya shude da kuma wa'azi
ga abin da ya fiskanto lallai munafukai idan dayan su ya yi rashin lafiya
sannan aka warkar da shi to sai ya kasance kamar rakumi ne da iyalan shi suka
kunce shi sannan suka sake shi bai san
sabo da me aka sake shi ba, bai san kuma
sabo da me aka kunce shi ba Nasa'i ne ya rawaito).
Allah
bai ambaci tarihin Annabawa ba da Manzanni da cikamakinsu Annabinmu Muhammad ba
face don mu yi lura da tarihin nasu, mu
yi koyi da shiryarwar su da halayen su
mu bi tafarkin su hakika kuma Allah ya umarci Annabin mu Muhammad da ya yi koyi
da su sai yake cewa wadannan su ne Allah ya shiryar to ka yi koyi
da shiryarwar su Allah Madaukakin sarki ya ce :-(To
ka yi hakuri kamar yanda ma'abota azama
suka yi hakuri na daga Manzanni)
Allah Madaukakin sarki ya ce game da muminin
Yasin (Ya
ku mutanena ku bi manzanni ku bi wanda bazai tambaye ku lada ba kuma su dinnan
suna shiryarwa ne)
Cikamakinsu
Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, wanda da shi
ne Allah ya goge sauran shario'i gaba daya,ya turo shi da mafi kamalan addini
da sharia ta har abada, kuma Allah ya dauki nauyin duk mutumin da ya yi riko da
koyarwarsa da zai rayu rayuwa daddada a
duniya da lahira, kuma zai shigar da shi gidan aminci tare da mafi alherin
halittanSa, Allah Madaukakin sarki ya ce:(Duk wanda ya ke wa Allah da Manzo biyayya to wadannan suna
tare da wadanda Allah ya yi wa ni'ima na daga Annabawa da siddikai da shahidai
da salihan bayi, to madalla da wadannan abokan zama).
To
wani irin karramawa ne ya fi wannan? Wani
irin daukaka ne da zai yi kusa da wannan matsayi? Kuma kamar yadda Allah ya
kissanta mana kissoshin Annabawa amincin Allah ya tabbata a gare su, da wadanda
suka yi imani da su don mu yi koyi ne da su ne mu bi tafarkin tsira tare da su,
kuma mu yi lura da tarihin rayuwarsu, mu san irin halin da suka shiga, kamar
yadda ya bamu labarin wadanda suka karyata su, da wadanda suka ja da gaskiya
suka yi girman kai daga binsu, wadanda suka fifita rayuwar duniya akan lahira,
masu bin soye-soyen rayukansu da abubuwan jin dadin duniya, don mu yi lura da
ukubar da aka musu, kuma mu dauki izina da abin da ya faru da su na walakancin
duniya da azabar lahira, don mu kiyaye kanmu daga tsinuwar Allah da ta tabbata
a kan su, Allah Madaukakin sarki ya ce:(Da Adawa da samudawa alhali kuwa lalle alamun azaba sun
bayyana a gare su daga gidajensu, kuma shaidan ya kawata musu ayyukansu, sabo
da haka ya kange su daga hanyar Allah, kuma sun kasance masu basira. Kuma
Karuna da Fir'auna da Hamana, kuma lalle Musa ya je musu da hujjoji, sai suka
yi girman kai a cikin kasa, kuma basu kasance masu tserewa ba. Saboda haka
kowannensu mun kama shi da laifinsa: wato daga cikinsu akwai wanda muka aiki
iskar tsakuwa a kansa, kuma daga cikinsu akwai wanda tsawa ta kama, kuma daga
cikinsu akwai wanda muka birkice kasa da shi, kuma daga cikinsu akwai wanda
muka nutsar. Ba ya yiwuwa ga Allah ya zalunce su, amma sun kasance kansu suke
zalunta.
Allah
Madaukakin sarki ya ce:(kowannensu ya karyata
Manzanni sai Kyacewa ta tabbata).
Allah Madaukakin sarki ya ce game da kissar
Banu nadir :(To ku yi lura fa ya ma'abota basirori)
Tarihin
Manzanni amincin Allah ya tabbata a gare su tare da masu karyata su, masu saba
wa Allah da ManzonSa abu ne da mutane suka san shi, al'umar karshe sun san shi
daga al'umar da farko, kuma yana cikin hujjojin Allah mafi girma ga halittunSa
wurin karfafar gaskiya da ma'abotarta, sanin tauhidi da kira zuwa gare shi da
taimakawa masu kadaita Allah, haka kuma hujja ne wurin rusa karya (bata) da
shirka da yin gargadi game da shi, da ukubobi na mushrikai masu bijirewa, kuma
tarihi shine bigere ko mahallin lura da daukan izina ga daidaiku da iyalai da
dabakoki da al'umu da ma kasashe, duk wanda ya amfana da shi zai tsira, wanda
bai amfana da shi ba kuma sunnar Allah zata bi ta kan shi sai ya samu tawaya,
Allah Madaukakin sarki ya ce:(Sunnar Allah wacce
hakika ta shude cikin bayinSa kuma kafurai sun yi hasara a wancanninka).
Amma shi lura da dabiun halittu da binciko
hikimomin da ke cikinsu da sifofinsu, da tunani game da farar da halittarsu to
gayarsa da babbar manufarsa shine kadaita Allah
Mabuwayi da Daukaka da bauta masa da masa biyayya, wanda ya kadaita da
halitta shine abin bauta da gaskiya Allah Madaukakin Sarki ya ce : (kuma lalle ne kuna da abin lura a cikin dabbobin ni'ima
muna shayar da ku daga abin da yake a cikin cikunansu daga tsakanin tukar tumbi
da jini, nono tsantsa mai saukin hadiya ga masu sha.)
Allah Madaukakin Sarki ya ce : (kuma Allah yana juyar da dare da yini, lalle ne a cikin
wannan akwai abin lura ga masu basira).
Allah
Madaukakin Sarki ya ce : (ka ce ku dubi abin da ya
ke cikin sammai da kasa, kuma ayoyi da gargadi basu wadatarwa ga wadanda basu
yin imani).
Lalle tunani cikin halittun Allah ibada ne ga
musulmi, daukan izina ga wadannan halittu kuma yana kara imani ga musulmi da
tabbatuwar yakini, Allah Madaukakin Sarki ya ce :
(Lalle ne a cikin sammai da kasa akwai ayoyi ga masu imani).
To
tunani da lura na tabbatar da mai shakku, kuma yana raya zukata, yana haskaka
basira, yana daidaita halaye da dabiu, kamar yadda bijirewa tunani kan kekasar
da zukata, kuma yana haifar da gafala, yana jan ragama zuwa ga nadama ya kuma
jefa mutum cikin sabon Allah.
Daga Abu Huraira
Allah ya kara yarda a gare shi yace lalle Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi a lokacin da ya yi isra'i ya ce : ( Yayin da na sauko saman
duniya sai na dubi kasa da ni sai ga
wani irin iska da sauti da hayaki, sai nace : menene wannan ya kai
jibrilu? Sai yace wadannan shaidanu ne suke kona wuta a idon dan adam wai don
kar yayi tunani cikin mulkin sammai da kasa, ba don haka ba da sun ga abin
al'ajabi).Ahmad ne ya rawaito.
Allah
Madaukakin Sarki ya ce : (Lalle ne wadanda suka ji
tsoron Allah idan wani tashin hankali daga shaidan ya shafe su, sai su tuna
Allah sai ga su sun zama masu basira. Kuma 'yan'uwansu shaidanu suna taimakonsu
cikin bata Sannan basu gajartawa.)
Allah
ya sa min albarka ni da ku cikin Alkur'ani mai girma.
Huduba
ta biyu
Dukkan
yabo da godiya sun tabbata ga Allah,
wanda ya haskaka zukatan masoyanSa da Alkur'ani, ya kuma haskaka
basirarsu da Imani, ya kawata ayyukansu da kyautatawa, ina kyautata yabo ga
Ubangiji na kuma ina gode masa, bisa ni'imominSa da ba mai iya iyakance su in
ba shi ba, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bai da
abokin tarayya, Mulki da godiya na shi ne, Mai jinkai Mai rahama, kuma na
shaida Annabinmu kuma shugabanmu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, wanda
aka kebantar da shi da dunkulallun kalmomi gamammu da cikan bayani, Allah ka yi
dadin tsira da aminci bisa ga bawanKa kuma ManzonKa Muhammad da iyalan shi da
sahabban shi da wadanda suka biyo su da kyautatawa, bayan haka:
To
ku ji tsoron Allah Madaukakin sarki zai gafarta muku ya tattaro muku alheri a
rayuwarku da bayan mutuwarku.
Yaku
bayin Allah! Ku yi wa kanku hisabi kafin a muku hisabi, dayanku ya yi dubi zuwa
ga akibar al'amura, da karewar ajali duk wanda luransa ya yawaita to
kura-kuransa zasu karanta, wanda ya kiyaye sabawa Allah da laifuka to zai rayu
cikin aminci, kuma za a datar da shi zuwa ga kyakkyawan karshe, mai rabauta
shine wanda ya wa'azantu da waninsa, hasararre shine wanda da shi waninsa ya
wa'azantu.
Hakika
Allah Madaukakin sarki ya zargi wadanda suka bi son ransu ba su yi lura ba,
basu wa'azantu da labarai da suka zo musu ba, Allah Madaukakin Sarki ya ce : (kuma suka karyata suka bi soye- soyen rayukansu, alhali
kowani al'amari tabbatacce ne. Hakika labarai ya zo musu wanda cikinsa akwai
abin gargadi)
Ku saurara ! lalle Allah Madaukakin sarki
yana da wasu sunnoni a rayuwa wurin sakayya da lada ko ukuba, wanda ya nemi ja
da yin Allah sai sunnar rayuwa ta nesatar da shi ya dunkufe ya fado ya kaskanta, Allah Madaukakin Sarki
ya ce : (Hanyar Allah ga wadanda suka shude kafin
nan kuma ba za ka samu sauyi ba ga hanyar Allah).
Ya
zo a hadisi :(ku yawaita ambaton mai katse jin
dadi mutuwa).
Wanda
ya tuna mutuwa aikinsa zai yi kyau, wanda ya manta mutuwa aikinsa zai munana.
Ya
ku bayin Allah! (Lalle Allah da Mala'ikunSa suna
salati ga Annabi yaku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci
tabbatacce).
To
ku yi salati da aminci ga shugaban mutanen farko da na karshe kuma shugaban
manzanni.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق