الجمعة، 7 أغسطس 2020

YI WA KAI HISABI

 

 

اسم المترجم : أمين سعد عبد الله

اللغة : الهوسا

التاريخ : 17-12-1441هـ

Hudubar Juma'a a masallacin Annabi na Shaikh Abdul Muhsin  Al kasim 17-12-1441AH /  7-8-2020AD

 

Hudubar farko:

  Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin sarki  muna gode mishi kuma muna neman taimakonsa, muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar da shi babu mai batar da shi , duk wanda ya batar kuma babu mai shiryar da shi, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, kuma na shaida Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa  da sahabbansa da aminci tabbatacce mai yawa.

Bayan haka: ku ji tsoron Allah-

Ya ku bayin Allah,- cancancin tsoronSa, takawa ita ce mafi alherin abin ribata kuma kyauta mafi yawa.

Ya ku musulmi!

Na daga cikin juyawan watanni da shekaru ga bayi na daga cikin ni'imomin Allah masu yawa ga bayi, Allah Mai tsarki ya ce ; (Kuma ya hore muku rana da wata suna madawwama biyu, kuma ya hore muku dare da wuni. Kuma ya baku dukkan abin da kuka roke shi, kuma idan kun kidaya ni'imar Allah ba za ku lissafe ta ba. Lalle ne mutum, hakika, mai yawan zalunci ne mai yawan kafurci)

Allah ya tsawatar ga duk wanda bai ribaci lokacinsa ba  da abin da zai amfanar da  shi a lahira Allah mai tsarki ya ce:- (Ase bamu baku tsawon rayuwa ba  wanda ya ci ace  mai wa'azantuwa ya wa'azantu? Kuma ga mai gargadi ya zo muku)

  kuma ni'imomi biyu idan mutum bai ribace su ba yayi asara  kuma zai yi nadama game da su.

 Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :-( Ni'imomi guda biyu mutane suna asara a cikin su, su ne ; lafiya da kuma lokaci ) Buhari ne ya rawaito

Allah ya yi  rantsuwa a ayoyi da dama  a cikin littafinSa  da wani yanki na lokaci na daga dare da yini da  alfijir da asubahi da la'sar  da walaha, hakika ga shi muna kusa da bankwana da shekara wacce ta tattaro wani abu na rayuwarmu,  muna bankwana da ayyukan mu a cikinta, wanda za a shimfida su a ranar taro  a gaba gare mu,  abin mamaki da irin saurin abin da ya shude  ya tafi,  kuma abin mamaki da girman abin da ya tattaro .

Dararraki da ranaku wasu taska ne na ayyuka  kuma matakai ne na rayuwa  na shekaru  ana tsofar da abin da ya ke sabo  a kusantar da abin da ya ke nesa  ranaku na shudewa ga shekaru suna tafiya  al'uma  suna bin bayan juna ,  bisa tafiya zuwa ga lahira  wannan na fiskantowa wancan kuma na juyawa,  wannan na samun lafiya wani kuma na samun cuta,  duka zuwa ga Allah za su koma.  Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :- (Dukkan mutane suna wayan gari akwai mai saida kanshi, to, sai ya 'yantata  ko kuma ya  halaka ta ) Muslim ne ya rawaito

A cikin zamani  akwai wasu radadi da ke juyawa farin ciki, akwai kuma  farin ciki da ke juyawa bakin ciki  ranaku na wucewa ga ma'abotanta , kaman shekaru , shekaru kuma na wucewa ga ma'abotanta kamar ranaku mai hankali shi ne wanda ya riki wannan a matsayin abin lura, kuma abin wa'azantuwa  Allah Madaukakin sarki ya ce :-(Allah na juya dare da yini  lallai a hakan akwai abin lura ga masu basira ) Shekara  kan tafi  da abin da ke cikinta  abin da bayi suka aikata a cikinta na ayyuka,  za a bijiro  musu da ayyukansu , (Ana bawa mutum labari game da abin da ya kaddamar ko ya jinkirta a wannan ranar) Ka yi dubi zuwa ga takardun  ranakun ka da suka shude  wani abu ne ka adanawa kanka  a ciki don lahiran ka?  Ka kebanta da kanka ka  mata hisabi, hisabi  amintacce  wanda akwai  matsi a ciki,  Maimun dan Mihran - Allah ya mishi rahama- ya ce :-(Bawa ba zai zama mi takawa ba har sai ya kasance  yana mai tsanani ga rayinsa fiye da aboki ga abokin shi).

 Dare da yini na wucewa ne don su  nesatar daga duniya  su kusantar zuwa lahira, madalla da bawan da ya amfana da rayuwarsa  ya tsaya tare da ransa tsayawa na hisabi da kuma zargi yana gyara tafiyarsa  kuma yana riskan kusakuransa,  yakan bude shafi da daddare  na daga abin da ya aikata a wuninsa ,  idan ya kasance abubuwa ne masu kyau sai ya  doge a kan su,  idan kuma ya kasance ayyuka ne na zargi sai ya tuba daga gare su  sabo da shi matafiyi ne tafiyan da ba komawa 

 Abu Hatim Dan Hibban - Allah ya mishi rahama - ya ce:- ( Mafifitan masu hankali matsayi su ne wadan da suka dimanci  yiwa kansu muhasaba .

Tsinkaya bisa ga  aibobi na rayi   da kuma abubuwan da suke   tawaya gare ta   da laifukanta zai mata linzami daga zalunci, bawa ya san kan shi kuma ya san makomar shi zuwa ga kabari  yana haifar mishi da kankan da kai da kuma bautawa Allah,  ba zai yi alfahari da aikinsa ba duk yanda abu ya girmama,  ba zai kuma raina zunubai ba komin kankantan su.

 Abu Darda Allah ya kara yarda a gare shi yana cewa :- '' Mutum ba zai zama  cikakken fakihi ba  har sai ya kama mutane  da  laifi a hakkin Allah  , sa'annan kuma ya koma zuwa ga kanshi  sai ya kasance ya fi mata tsanani.

Idan ka zauna da mutane  ka kasance mai wa'azi ga zuciyarka ,  domin halittu suna murakaban zahirin ka ne , Allah  kuma yana murakaban badinin ka ,  duk wanda badinin sa ya yi kyau  ta hanyar murakaba da ikhlasi  to Allah sai ya zayyana zahirin shi  da kyau da rabauta.

Sanin hakkin Allah da  girman falalarSa da baiwarSa  da tuna yawan ni'imominSa  yana kira zuwa ga Allah ,  yana sa mutum kuma ya gane gajartawarsa wurin  godewa ni'imomin Allah  kuma  lallai  ya san cewa babu tsira sai da komawa zuwa gare shi,  ya dace a mishi da'a ba za a saba mishi ba  a gode mi shi ba za a butulce mishi ba.

Ibnul  Kayyim Allah ya mishi rahama ya ke cewa:- '' Farkon muhasaba shi ne mutum ya yi kiyasi tsakanin ni'imarSa mabuwayi da kuma  laifukansa  a wannan lokacin ne zai bayyana mishi lallai akwai banbanci  kuma ya san cewa lallai  ba don wani abu na afuwar Allah da rahamar sa ba  da halaka za a fada da kuma  musiba, nemar laifukan rayi yana  tsarkake ta  kuma ya gyara ta Allah Madaukakin sarki ya ce:-(Hakika wanda ya tsarkake ta ya rabauta, hakika kuma yayi asara wanda ya turbude ta )  

Malik dan Dinar ya ce :-''Allah ya yi rahama wa bawan da ya ke  cewa ransa  ase ke ba ma'abociya kaza-da – kaza ba?  Ase ba ke ce mai kaza-da-kaza ba?  Sannan sai ya sa mata linzami sannan ya sa mata birki  sannan ya lizimtar da ita da littafin Ubangijinta  sai ya kasance shi ne mai jan  ragamar ta .

Ba wani mai nisata wanda zai nisanci Allah  face sai da gafalarsa da mantuwarsa daga muhasabar sa ga Allah , Allah Madaukakin sarki ya ce (Lallai sun kasance ba su fatan hisabi)  wanda ya fada cikin munanan ayyuka  kuma ya dogara bisa  afuwar Allah da rahamarSa to hakika  ya yaudari kan sa lallai  mai karamci baya fuskantar ayyuka munana  (Ya kai mutum me ya rude ka game da Ubangijin ka Mai karamci )?  

Ibn Kasir Allah ya mishi rahama ya ce:-  (Me ya rude ka ya kai dan Adam  game da Ubangijin ka wanda ya ke mai karamci wato mai girma har ma  ka je zuwa ga saba mishi  ka fiskance shi da abin da bai dace ba ).

 Hisabi yana yin sauki ga mutanen da  suka yiwa kansu hisabi tun a duniya kuma ya kan yi tsauri ga mutanen da  suka riki wannan al'amari ba tare da muhasaba ba.

 Hasanul-Basari Allah ya mishi rahama ya ce :- '' (Baya dacewa ga mumini  face da ya rika yiwa kan shi zargi  yana mata mu'ataba  sai ya ce da ita me kike nufi da  kalma ta, me kike nufi da abinci na, amma fajiri zai shude ne  zai tafi ne  da kafansa baya zargin kansa, shi kuma mumini  yana mai tsayuwa a kansa yana mata hisabi).

Allah Madaukakin sarki ya ce :-(Lallai ne  wadanda suka yi takawa idan wani tashin hankali daga shaidan ya shafe su,  sai su tuna  (Allah)  sai ga su ,  sun zama  masu basira .

Taka-tsantsan  wurin afkawa cikin kuskure  da barin zunubai shi ne  ya fi sauki akan  neman tuba  kuma da zargin rayi bisa ga gajartawa cikin  da'a  domin ranaku a gare ka basu dauwama  kuma ba ka sani ba yaushe  ne  za ka kaura daga duniya  kuma ka yiwa kan ka magana  menene  kika gabatar a ranakun da su ka shude  kuma  wani shiri kike yi don ranaku masu fiskantowa?

Umar Dan Khaddabi Allah ya kara yarda a gare shi ya ce:- '' Ku yiwa kan ku hisabi  kafin a yi muku hisabi  ku aunata kafin a auna ku

  ka rika bibiyan ranka  a farkon  ko wani rana  wurin kiyaye sallolin nan guda biyar  a masallatayya cikin jam'i  tare da musulmai  kana neman guzuri na ilimi mai amfani tare da kai-komo wurin yada shi  da kuma ilmantar da shi  da kiyaye harshen ka daga abubuwan da suke muharramai da karya da rada  da batsa da alfasha  kuma ka kasance kana da tsantseni cikin abin da ka ke ci da abin da kake sha,  ka nisaci abin da baya halatta  ka yi kwadayin biyayya wa iyaye  ka sada zumunci,   ka yawaita ma'arufi da makusanta da na nesa  ka tsarkake zuciyan ka daga hasada  da gaba da kiyayya  ka kiyaye daga aukawa cikin mutuncin musulmai  ka yi kokari wurin tashi da wato  sha'ira na umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna  da bada hakkokin yara kuma da iyali  bisa ga fiskan da ya dace  mafi kamala  ka rintse idanuwan ka daga kallon abin da ya ke muharramai  sawa'un a hanyoyi ne ko wanin su.

 To dare da wuni  suna  nesantarwa ne daga duniya kuma suna kusantarwa ne zuwa ga lahira, madalla da bawan da ya amfana  da rayuwarsa  dukkan wayan gari  rana na faduwa  yana maka gargadi ne cewa fa wani  abu na shekarunka ya ragu  mai hankali shi ne wanda ya wa'azantu a jiyansa ya yi kokari a yau dinsa  ya shirya don gobensa  ka dauki mataki  na shiri  domin  tafiyan da take gaban ka, yi guzuri domin tafiyan ta kusanto ,  mafi alherin guzuri shi ne wanda a ka hada da tsoron Allah,  mafi darajan mutane a wurin Allah  shi ne wanda ya fi su tsoron shi .

 

Ina neman tsarin Allah daga sharrin shaidan abin jefewa

(Ya ku wadan da suka yi imani ku ji tsoron Allah kuma rayi ta yi dubi zuwa ga abin da  ta gabatar  don gobe . ku ji tsoron Allah lallai Allah Mai bada labarin abin  kuke aikatawa ne).

Allah ya sa mini albarka ni da ku a cikin Alkur'ani mai girma.

 


 

HUDUBA TA BIYU

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah bisa  kyautatawanSa,  godiya ta tabbata gare shi bisa  datarwanSa  da baiwanSa, na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya  ina mai girmama sha'aninSa na shaida Annabi Muhammad bawanSa ne kuma Manzon sa ne  tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabban shi da aminci tabbatacce mai kari .

Ya ku musulmi:-

 Shekarun dan adam a nan duniya na rayuwarsa su ne  kasonsa, idan ya kyautata ribatarsu a nan duniya  cikin abin da zai amfane shi a gidan lahira to ya ci riba a kasuwancinsa, to idan kuma ya munanta ribatan su ya yawaita sabo da laifuka to ya yi hasara a kasuwancinsa, mai dace shi ne wanda ya yi hisabi wa kansa kafin Allah ya masa, ya ribaci lokacinsa ya san maganinsa daga cutarsa, bai yi sake ba har a yi mishi sakiya, alheri na cikin da'a sharri kuma na cikin sabo.

Rayuwa fage ne mai fadi na kyawawan ayyuka, jinkirta aiki da cewa sai nan gaba bai haifar da wani abu sai nadama, tuba na goge kuskure, mai samun walwala shine wanda ya adana ayyuka na kwarai a tsawon rayuwarsa. Shakiyyi shine wanda gabbansa suka shaide shi da munanan laifukansa.

To ku kiyaye ranakun rayuwanku kafin ku kadaita a kabarinku, ku ribaci ranakun rayuwarku kafin kwacewar lokaci, ku girmama masaukinku na sabon rayuwa da da'a.

Sannan ku sani Allah ya umarce ku da salati da aminci ga AnnabinSa.    

 

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق