ترجمة خطبة المسجد النبوي
اللغة : الهوسا
المترجم : أمين سعد
التاريخ :23-1-1442هـ
Hudubar Masallacin Annabi Tare da shaikh
Abdullah bin Abdurrahman Albuaijan 23-1-1442AH 11-9-2020Ad
Hudubar farko:
Dukkan
yabo da godiya sun tabbata ga Allah
wanda ya cikamake manzancin sama da shari'armu ya kuma cikamake annabawa da
manzanni da Annabimmu ya sanya al'umar mu tsaka-tsakiya, mafi alherin al'umar
da aka fitarwa mutane
Na
shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai bashi da abokin
tarayya, yana halittan abin da yaso kuma yayi zabi, na shaidah cewa Annabi Muhammad
bawansa ne kuma Manzosa ne, mustafa kuma zababbe cikin zababbun zababbu.
Ya
isar da sako kuma ya sauke amana kuma yayi nasiha wa al'umah kuma yayi jihadi a
tafarkin Allah cancancin jihadi har yakini yazo mishi, tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi da iyalan shi da sahabban shi da wanda ya bisu da
kyautatawa har zuwa ranan sakayyah.
bayan haka:
lallai
mafi gaskiayan zance shine littafin Allah, mafi kyan shiryarwa shine shiriyar Muhammad
dan abdullahi, sharrin al'amura kuma sune fararrunta, dukkan wata fararriyar
abu bidi'a ce, dukkan bidi'a bata ce, kuma dukkan bata na wuta.
Yaku
wadanda sukai imani kuji tsoron Allah cancancin tsoronshi kuma kada ku mutu
face kuna musulmai
Ya
jama'ar musulmi, mutum yana tare da wanda yake kauna, kaunar Annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi sharadi ne a imani, kuma mafificin hanya
don kaunar Annabi sallallahu alaihi wa sallam, shine sanin rayuwarsa da halayensa
da dabi'unsa, to ku san Annabinku domin ku san kimansa da matsayinsa, sai a samu
kaunarsa ta samu da kuma da'a gare shi ba dayanku da zai yi imani har sai ya
kasance Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance mafi
soyuwa a gare shi akan kansa da dansa da mahaifinsa da ma dukiyarsa da mutane
baki daya.
Ya ku
bayin Allah:
Allah yana zaban manzanni cikin malaiuku da kuma a cikin
mutane ma hakika Allah ya zabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a
gareshi, daga mafi tsadar ma'adinai da mafi tsada da kyau, Allah ya karrama shi
kuma ya fifitashi akan sauran mutane, Allah Madaukakin sarki yace: (Hakika Manzo yazo muku daga cikinku yana mishi nauyi abin da
ya wahalar da ku, mai fata ne ga muminai kuma mai jin kai mai tausayi).
Ya
sanya shiryarwarsa ma'auni ne domin wurin falala da kamala, (Hakika ya kasance a gareku ga Manzon Allah abin koyi ga
wanda ya kasance yana fatan Allah da kuma ranar lahira.)
Allah
ya tsarkake shiryarwarSa da halittanSa da kuma iliminSa da hankalinSa da
fadinSa da aikinSa ,Allah ya tsarkake shi tsarkakewa cikakkiya a zahiri da
badini ya tsarkake shi a hankalinsa sai ya ce (sahibinku
bai bata ba kuma bai kauce hanya ba) ya tsarkake shi a ganinshi sai
ya ce:(gani bai kauce ba kuma bai wuce gona da iri
ba) ya kuma tsarkake shi a kirjinsa(zuciyarsa) sai ya ce (ase ba Mu fadada maka zuciyanka ba?) ya tsarkake
shi a ambatonsa sai ya ce:(sai Mu ka daga ambatonka
gareka) ya tsarkake shi a tsarkinsa sai ya ce:(Muka dauke maka laifinka) ya tsarkake shi a
gaskiyansa sai ya ce: (baya furuci bisa son rai)
ya tsarkak shi a iliminsa sai ya ce :(ma'abociai
tsananin karfi ne ya koyar da shi) , ya tsarkake shi a hakurinsa sai
ya ke cewa: (mai tausayi ne da jin kai ga muminai)
ya tsarkake shi a halitansa na gaba daya sai ya ce:(lallai
kana kan dabi'u masu daraja).
Ya ku
bayin Allah:
Lallai
Allah Ta'ala ya halicci bayinSa suna masu karkata zuwa ga addinin Annabi Ibrahim
gaba dayan su hakika sai shaidanu suka zo musu sai suka yi awon gaba da su daga
addinin su suka haramta musu abunda Allah ya halatta musu suka umarce su da su
yi shirka da Allah kuma cikin abin da Allah bai saukar da wani hujja ba lallai
Allah ya yi dubi zuwa ga doron kasa sai ya fusata da su ,larabawansu da
ajamawansu sai saura daga cikin mutanen
ahlil kitabi sai ya zabi a tsakaninsu mafi tsadan ma'adinai ma'abota izza da
daukaka mabubbuga na alheri da falala , ya karramasu ya tsarkake su mafi
karramansu da tsarkakansu shi ne Muhammad dan Abdullahi dan Abdulmuttalib
balarabe bakuraishe kuma bahashime uwarsa Aminatu 'yar wahab bakuraishiya .
Ya
zaba mishi mafificin wuri sai aka haife shi kuma ya taso aka turo shi a Makka
uwar alkaryu , kuma masaukan wahayi ya kasance haifuwarsa a Rabi'ul'auwal ne
shekaran giwaye, bayan haka da kwatankwacin shekaru dari shida da talatin da
biyu daga haihuwar almasihu Isa alaihissalam dan Maryam aka haifi Annabi Muhammad
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi , ya turo shi zuwa ga Makka a
shekarunshi ya dumfari arba'in ya mutu kuma yana sittin da uku na daga shekaru
.
Ya
jama'ar musulmai:
Manzon
Allah ya rayu ya dandani daci irin na maraici mahaifin shi ya rasu a halin shi
yana cikin mahaifiyarsa, mahaifiyar shi ta rasu yana kwatankwacin shekara shida
na daga rayuwansa, sai kakansa Abdulmuttalib ya dauke shi shekaru biyu har zuwa
ya rasu sai baffan shi Abu dalib ya jingina shi sai ya zama yana kewaye da shi
yana kiyaye shi yana bashi kariya har zuwa lokacinda ya rasu yana dan shekara
goma daga turowa manzanci .
Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance shi kadai ne a
wurin mahaifansa , bashi da wani dan uwa ko dan uwa hakika Allah ya tattaro
mishi siffofi na alheri da falaloli da ta'adodi da dabi'u kyawawa yayi harkan
kasuwanci ya fita zuwa sham ba so daya ba ya fita tare da baffanshi a kasuwanci
haka nan kuma ya fita kasuwancin Khadija matarsa 'yar Kuwailid kamar yanda ya
yi kiwon dabbobi bisa ga wasu silalla ga mutanen garin Makka .
Ya
auri Khadija 'yar kuwailid shekarunshi na ashirin da biyar , ita kuma ta
kasance mafificiyar me taimakawa da kuma bada gudumawa , ta haifa mishi dukkan
'yayanda ya ke da su maza banda Ibrahim shi uwarsa Mariya ce alkibdiyya .
Yayin da
ya kai shekaru arba'in Allah ya zabe shi kuma ya turo shi kuma ya cikamake Annabawa
da Manzanni da shi sai ya fara da'awan shi zuwa ga tauhidi da kuma yin nesa da
shirka ya kuma kwadaita zuwa ga kyawawan dabi'u na alheri da umarni da
kyakkyawa da hani da mummuna da zalunci da barna, yana Makka na tsawon shekaru
goma sha uku yana kira a boye da kuma a bayyane dare da wuni sai suka rinka
sanya hannayen su a kunnuwansu suna makirci makirci mai girma suka rufa
tufafinsu kuma suka doge suka yi girman kai girman kai suka ketare iyaka suka
yi musu suka karyata suka cutar kuma suka yi izgili suka tuhume shi da sihiri
da kuma kahana (bokanci) da kuma hauka , Allah ya girmama bala'I ga mabiyansa
da kuma masu taimakonsa sai mutanen Makka suka yita azabtar da su suka kokkore
su basu musu ukuba ba face sai don sun yi imani da Allah Mabuwayi abun godiya .
Ya ku
bayin Allah:
Allah
ya yi izini ga AnnabinSa da yayi hijira zuwa ga Daibatuddaiba (Madina) inda
zama ke yin dadi kuma gida na imani ta inda ya ke shi ne masulala na imani ta
inda rundunan Allah Ansarawa suke, wadanda suka mallaki gida kuma da imani
kafun su suna son wandanda suka yi hijira zuwa gare su kuma ba'a samun wani abu
a cikin zukatan su na bukata cikin abunda suka bada kuma suna fifitawa a kan
kansu koda sun kasance sunada haja duk wanda aka kare shi daga rowan kanshi to
hakika yana cikin wadanda suka rabauta.
Daulan
musulunci ta fara tana habaka tana tasowa a garin Madina aka assasata a dan
lokaci kankani , hukunce hukunce suka sauka sa'an nan sai ta rika tattaro
mutane ana jihadi a tafarkin Allah ana yakan duk wanda ya yaki Allah da
ManzanSa , aka kulla kulleleniya da alkawura da yarjejeniya da mawasik.
Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya cigaba da zama a ciki
shekara goma har zuwa lokacin da wasu abubuwa suka faru masu yawa da kuma
shari'o'i da kuma yake yake a doron kasa tunda Allah ya shinfidata kuma ya kafa
ta tarihi bai san wani farawanta ba har zuwa yau wasu alumma da suka fi gaskiya
da a'adalci akan tsayuwa akan tafarki mikakke kuma fi soyuwa zuwa ga Allah game
da wancan fatra da wancan jama'a .
Ina
neman tsarin Allah daga sharrin shedan abin jefewa, Shi ne wanda ya turo cikin
ummiyai Manzo cikinsu yana karanta a'ayoyinSa kuma yana tsarkake shi kuma yana
karantar da shi littafi da hikima ko da da sun kasance kafin haka suna cikin
bata mabayyane .
Huduba ta biyu:
Dukkan yabo da
godiya sun tabbata ga Allah mai bayyana gaskiya mai daukakata mai kaskantar da
karya kuma mai tunkude ta ya tura ManzonSa da shiriya kuma da addini na gaskiya
domin ya bayyana shi akan addinai gaba daya ko da mushrikai sun ki.
ya ku bayin Allah :
a
tsakanin shekaru goma na lokacin zaman Madina Allah ya cika addininShi , mutane
suka shiga addinin Allah tawaga tawaga musulunci ya shiga ko wani bangare na
yankin kasashen larabawa, mutanenta suka rusunawa musulunci suka mika wuya a
gare shi, wadannan watanni akwai abubuwa da suka faru a wannan lokaci
A
shekaran farko: na hijira Annabi tsira da am incin Allah su tabbata a gare shi
ya gina masallacinSa da kuma gidansa , ya hada 'yan uwantaka tsakanin muhajirun
da ansar ya shar'anta kiran salla.
A
shekara ta biyu: ya maida alkibla zuwa Ka'aba kuma aka farlanta azumin ramadana
a ciki ne kuma aka farlanta sadakatulfidr zakkan fidda kai .
A ciki
ne kuma aka yi yakin badar kuma a ciki ne Rukayyatu 'yar Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ta rasu a ciki ne kuma Annabi Allah tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi ya shiga da A'aisha , a ciki ne kuma
aliyyu Allah ya kara yarda a gare shi ya auri fadima 'yar Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi .
A
shekara ta uku : an yi yake yake daga ciki akwai yakin uhud akwai kuma yakin
banunnadir an haramta giya bayanta sannan kuma Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya auri Hafsa 'yar Umar dan kaddabi , Usman kuma ya auri
Ummu kulsum 'yar Manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi , kuma aka haifi Hasan dan aliyyu ga Fadima
A
shekara ta hudu: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya
auri ummu salama , aka kuma shar'anta taimama , aka ce kuma a wannan shekaran
ne aka yi yakin kandak da kuma zatu rika'a a ciki , haka nan kuma sallan tsoro
.
A
shekara ta biyar: aka yi yakin daumatuljandal da kuma kuraiza , aka shar'anta
kuma hijabi.
A
shekara ta shida :aka yi sulhul hudaibiya da kuma bai'atul ridwan da kuma yakin
banil mustalak, Rana kuma ta kisfe aka saukar da hukuncin zihari.
A
shekara na bakwai : ne aka yi yakin kaibar kuma umra na kada'a Annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi aure da Habiba da Maimuna da Safiyya
da Mariyal kibdiyya , kuma Abu huraira ya musulunta.
A
shekara na takwas: ne aka yi yakin mu'ta da zatussalasil , aka bude Makka a
Ramadana, aka haifi Ibrahim kuma Zainab 'yar Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ta rasu , a ciki ne kuma aka yi yakin Hunain.
A
shekara ta tara: a ciki ne aka yi yakin tabuka Annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi hajji da mutane , kuma Ummu kulsum
'yar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ta rasu , Najashi
ma ya rasu kuma runduna runduna na zuwa suka yawaita.
A
shekara ta goma Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya yi hajjin ban kwana, kuma Ibrahin dansa ya rasu,Allah ya
saukar da (idan nasara ya zo daga Allah da kuma budi)(ka ga mutane na shiga addinin Allah kungiya kungiya)(to ka yi tasbihi da godiya ga Ubangijinka kana mai neman
gafararSa, lallai Shi ya kasance mai yawan karban tuba ne).
Ya ku
bayin Allah:
(Dukkan rai zai dandani mutuwa,) (dukkan wanda ke doron kasa
kuwa zai kare) .
Ya ce
shi
mutuwa kan da ke sara baya kaucewa ya yi
ha'inci ***
Tabki
ne mai dafi duk wanda ya rayu zai sha
shi**
A
cikin Rabi'ul auwal ne a shekara na sha daya bayan hijira kuma hajjin ban kwana
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ji wani irin ciwo, na
bada fansa da mahaifina da kuma mahaifiyata a gare shi , Allah ya bashi zabi
sai ya zabi haduwa da Ubangijinsa ,
Ya
Allah Arrafikul A'ala, ya Allah Arrafikul A'ala , lokacin rabuwa ya yi sai aka
yi wasiyya kuma ya yi ban kwana, duniya
ta yi duhu sakamakon rabuwa da shi sai ga shi an shiga matsananci bakin ciki.
Wayyo
Allah , abin mamaki da irin girman wannan bala'in da tsananin wannan musiban
kai ba abin da ya kai wannan wahala ba wani lokaci da aka wuce shi mai nauyi
irin wannan , hakika wahayi ya yanke daga
kasa sakamakon rasuwan Annabi Allah tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi , duniya ta yi duhu .
(Muhammadu ba wani ba ne face Manzo hakika
Manzanni kafin shi sun shude).
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق