ترجمة الخطبة بالمسجد
النبوي
اسم المترجم :أمين سعد
اللغة : الهوسا
التاريخ 1-2-1442هـ
Hudubar juma'a na masallacin
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na Shaikh Salah Albudair
1-2-1442.AH /18-9-2020AD
Hudubar
farko:
Ya ku
musulmai:
Ilimin
likitanci na daga cikin ilmuka mafi daukaka da amfani, kuma yafi girma da
tasiri, kokari a cikin shi yana cikin dabi'u na masu daukaka, yin kasa da haka
kuma wata ukuba ce kamar sauke nauyin abu mai wahala a wurin wahalan haurawa
zuwa gare shi, ba gushewa mai neman ilimin likitanci yana mai haurawa zuwa gare
shi yana hauhawa daraja bayan daraja har ya isa zuwa ga matsayi madaukaki da
martaba mai daraja wanda ba kowa ya ke samunsa ba sai masu kokari tsayayyu, ba kuma mai riskansa sai wanda ya
dace kuma ya lizimci juriya.
Imamushshafi'i ya ce:'' ilimi iri biyu ne:
ilimin fikihu na addinai da kuma ilimin likitanci na jiki ''
Rabi'i
ya ce: na ji Shafi'i yana cewa: ban san wani ilimi ba bayan halal da haram da
yafi kyau kaman ilimin likitanci .
An ce:
kar ka zauna a garin da babu shugaba da zai baka kariya, babu ruwa da zai
shayar da kai, babu malami da zai baka fatawa babu likita da zai baka magani.
Musulunci
ya kula da harkan likitanci kwarai da gaske dukkan kulawa, ka duba littafi na
dibbu (likitanci) a cikin sahihulbukari da kuma babi na magani da rashin lafiya
da rukiya a cikin sahihu Muslim da kuma kitabuddibbi a cikin sunanu Abi
dauda, da littafi na dibbi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi a cikin sunanuttirmizi da kuma littafi na dibb a cikin sunanu kubra na
Nasa'i, da kuma littafin Addibb a cikin sunan Ibnu maja.
An rawaito
daga Ibnu Masawaihi likita lokacin da ya karanta hadisin Annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi da ya ke cewa (Ba
wata jaka da dan Adam zai cika ta zama sharri a gare shi fiye da cikin shi, ya
ishi dan Adam 'yan wasu lomomi da za su tsaida mishi kwankwason shi in ya
kasance ba makawa to ku kasa shi kashi uku, kashi daya na abincinsa, kashi daya
na abin shan sa, kashi daya na numfasawarsa).
Ya ce:
da mutane za su yi aiki da wannan kalmomi da sun kubuta daga rashin lafiya da
cututtuka, da ma an rasa asibitoci da shaguna na magani, kemes sun zama ba amfani.
Larabawa
suka ce: mafi alherin abin kalace shi ne na sassafe mafi alherin abin cin dare
shi ne ………
Likita
haziki kwararrae wanda ya ke ya kware suna amfani ne da magunguna wanda suke na
boye da suka rufe suka sa yanar ido , allah ya sanya damtsenSa ya zama rahama,
mishradansa ya zamana shafaka ciyakanSa ya zamana tsira sadarwanSa ya zamana
karba, ribadinSa ya zamana magani, magungunanSa kuma ya zamana waraka.
Larabawa
sun ambace shi da mai hikima mai tausayi saboda yana tausayawa ga mara lafiya
yana mar muladafa, yana mannashi a jiki, Allah Shi ne wanda ya ke warkarwa kuma
ya ke bada lafiya.
Likitoci
bas]u da iko koda sun hadu da su koro waraka ga mara lafiya face da izinin
Allah saboda Shi kadai ne mai bada waraka, wanda ya ke jarrabawa da cututtuka kuma
ya ke bada taimako da magun guna ya kuma rahama da waraka, likita na mun fatan
waraka ga idona*** shin akwai wani bayan Allah da ya ke likita?
Yayinda
waraka ya zama daga cikin tushe na ni'imomi wanda mara lafiya baya samu sai
daga wurin Allah ba wai daga wurin mai magani ba, Ibrahim alaihissalam ya ke cewa:
(idan nayi rashi lafiya Shi ya ke bani waraka)
An karbo daga suhaibu dan sinan arrumi Allah
ya kara yarda a gare shi( a kissan wannan yaron
wanda ya kasance yana warkarda makaho da kuma mai kuturta kuma yana bada magani
da sauran cututtuka da izinin Allah, sai
bafaden sarki ya ji shi bayan kuma da ya makance sai ya zo wurin wannan yaron
da wasu kyaututtuka masu yawa sai ya ce: menene wannan? Sai ya ce duka na
tattaro naka ne idan ka warkar da ni, sai yaro ya ce: ni bana warkarda wani sai
dai Allah ne ya ke warkarwa idan ka yi imani da Allah sai na ma addu'a sai ya
baka waraka, sai ya yi imani da Allah shi ke nan sai Allah ya bashi waraka ya
maida mishi ganinshi) Muslim ne ya rawaito.
** sai
na wayi gari bana rokon likita don ya bani waraka don likitancin shi***
** sai
dai ina kiranKa ne ya Mai saukar da ruwa***
Likitoci
da nasis sunada falala da zance ba zai iya tattaro su duka game su ba
** ka
sani wadatanka kyautanka ba'a iya sakanyawa ***
Shin ana
iya sakanyawa bisa ga abubuwa masu tsada na cikin kogi? ***
To ku
kiyaye wa likitoci matsayin su da malaman jinya ku kiyaye musu matsayin su ku
gode musu bisa kokarin su da irin bada lokacin su da suke yi, hakika sun tsaya
gaba dayan su wurin bada katanga mai
kariya madaukakiya, domin kiyaye mutane daga fadawa ga mutuwa .da dulmuyar korona
zuciyar da ba ta kokawa da farfajiya da ba a takawa.
Wasu
kamshi na busawa don dadin yabo
Irin nasu
a ko ina ana shakansa.
Mun
yabe su ba mu riska ba da yabon su
Ba mu bar wata magana ba.
Yabo
da rera waka ga irinku akwai dadi
To me zan
ce ne bayan ku din ku ne
Kun
fifita marasa lafiya a kan yaranku
Kauna da fifita wani akai ana sanin shi daga
gare ku
Ya
ku Musulmi!
Mustahabbi
ne neman magani, idan barinsa zai kai ga halaka to ya zama wajibi.
An
karbo daga Usama dan Sharik Allah ya kara yarda a gare shi yace : Manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace :(ku
nemi magani –ya ku bayin Allah- lalle Allah subhanahu bai sanya wata cuta ba
face ya sanya mata magani banda tsufa )
A wani
lafazi (face mutuwa ) ya na nufin
mutuwa. Ahmad da Ashabus sunan,
Idan al'amari
mukaddari tabbatacce ya sauka lokaci da a ka yanka mishi ya kare magunguna sai
su ki aiki dabaru su kare.
Hakika
mutane kafin mu sun rabu da masoya
Maganin mutuwa ya gagari duk wani likita.
Sau
dayawa halaka kan tsallake mara lafiya
Ya tsira likitan shi ya mutu da itacen
magani.
Likita
na cewa da kai maganinka na guri na.
Idan gwada
tafin hanu da zira'i
Da
ace likita ya san maganin cuta
Da zai maida mutuwa bai dandani
cece kuce ba
Mu kan
sanya sababi ga magani idan mun yi rashin lafiya
Shin magani na warkarwa daga mutuwa ne?
Muna
zaban likita,ko likita na iya
Jinkirta abin da aka hukunta
Numfasawarmu
ba wani abu bane face a kididdige
Kai komonmu ba wani abu ba ne face karewa
Ya
ku musulmai!
Ya
wajaba ga likita ya kwadaitar da mara lafiya ya sa musu tsammanin samun sauki,
ya tausasa musu a wajen zance, ya jefa musu farinciki, ya yelwa, da yaye mishi
bakinciki da sa mishi annashwa, da lausasa masa da gusar masa da tsoro, da damuwa
a kwantar masa da hankali da firgici, da tunatar da shi da sanya mishi natsuwa.
Hakika
an ce : Ludufi irin na likita shine rabin magani, dariya a fiskar mara lafiya
kan saukake mishi radadin ciwo,yana jefa farinciki a gare shi yana tasiri da
bai boyuwa, faruwan shi na ratsa jiki yana da fa'ida mai yawa.
Kuma likita
mai tsauri da kaushin hali ya kan gitta wa mara lafiya ne tamkar iska mai kai
hari ta tunbuke abin da ke gabanta tana rusa kyakkyawan fata irin ta zuciya,
wanda ya tsorata mara lafiya da cuta ta ba zata ba tare da ya yi wata shimfida ba ko mukaddima ko kankantar
wa ba to hakika ya kara bata lamari ne, ya dada illa ne ga cutar.
Ya
wajaba ga likita ya zama ya siffantu da hakuri da lura da hakkokin mara lafiya
ya karya abin da ya samu mara lafiya ya karfafe shi ya girmama kokawansa.
Ya ku likitoci ku riki hannayen marasa
lafiyanku daga kunci na zafi da radadi zuwa ga yalwa na fatan alheri da taku
irin na kunci zuwa ga farfajiya na yaye bakinciki.
Ya wajaba
ga likita ya riki mara lafiya tamkar kan
shi sai ya bashi kariya ya mutunta shi ya kiyaye sirrinsa ya boye laifin shi ya kame daga yada cutar da ya ke tare da
ita wanda a cikin yaye ta akwai cutuwa gare shi, Ya wajaba kada ya yaye
al'auransa sai idan ya kama na larura na bada magani.
Ya wajaba
ga likita ya kirdada sannan kuma ya kiyaye ya kuma jinkiri da kuma yi jinkiri
kar ya yi gaggawa wurin binciko cutan da kuma bada maganinta ya tabbatar daga
illa na wannan rashin lafiyan da kuma ya
nemi shawara cikin al'amura da suka rikice mishi kada ya yi gaggawa ya bar
abkawa ga abu muddin bai kware ba.
Ya haramta
mutum ya bada magani wanda baida iliminshi, wanda bayi da kwarewa ko gwanancewa,
a duk lokacinda mutum ya kekeren likitanci bisa jahilci ya bawa marasa lafiya
magani hakika ya ruudar da mutane kuma ya hujumi da gjahilcinsa bisa ga abin da
ya ke na lalata rayuka kuma ya bijiro zuwa ga abin da ya ke wato tahawwuri tare
da kuma munanta bada magani zowa ga cutarwa da gan gan to ya wajaba a ladabtar
da shi kuma abin da ya ellanta ya biya saboda hadisin Utbatu Umru dan Shu'aibu
daga babansa daga kakansa ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata
agare shi ya ce : (duk mutumin da yayi liktanci
bisa karya a hali bai san likitanci ba to shi din nan zai biya abin da ya lalata)
Abu dauda ne ya fitar da shi da Nisa'I a wurin darakutni kuma akim ya inganta
shi (duk wanda ya yi likitanci a kuma shi ba
likita ba bai iya likitanci ba sai ya kashe rayi ko kasa da haka to lallai shi
zai biya).
Baya halatta
ga mai yin likitanci bisa jahilci ko kuma shi likita wanda bai kware ba ya je
ya rika yin aikin tiyata ko kuma ya fiskance ta domin iya gudanar da ita hakika
ya dauka wa kanshi laifi kuma ya yi zalunci ya yi barna , kuma dole ya biya
abin da ya yi kuskure a ciki da abin da aka samu na matsala.
Shi likita
wanda ya ke ma'aboci sana'ansa likitanci idan hanunshi ya yi wani laifi ko ya kuskure
irin kuskurenda makamantanshi ba sa yin irinshi ko kuma ya yi sakaci ko kuma ya
gajarta ko kuma ya ketare gona da iyaka, to shi zai iya biyan asaran da ya
biyo.
Kaddabi
ya ce: '' ban san wani sabani ba cewa wanda ke bada magani idan ya ketare iyaka
ya laata mai rashin lafiya shi ne zai biya abin da ya lalata, haka nan wanda ya
ke bada magani a ilmance ko kuma a aikace bai sansu ba to mai ketare iyaka ne ,
idan ya haifar da wani abu sakamakon wannan abin da ya yi to dole ne ya wajaba
ya biya diyya ''
Shi kuma
likita jahili wanda zai iya haifar da mutuwa ya shuka abubuwa na tsoro, ya kai
ga halaka idan har ciwo ya kara ruruta to zai bayyana a nan irin sakaci irin na
likita.
***………………………………***……………………
ya haramta ga likita ya bada magunguna wanda
mara lafiya bai bukatanshi , ya haramta ya yiwa mara lafiya kari cikin abin da
ba zai sha ba ko ba za a markada ba ko ba za a yi allura ba kafun ya tantance
shi na daga wani illa kawai bisa ga zargi ko kuma bisa zato ko kuma kawai ya
raya irin maganin da za a bashi , cututtuka ba'a iya magance su da wahami ba
abun nufi shi ne gusarda rashin lafiyan ba sai don a gusar da shi ta fiskan
amuntacce wanda hakan ba zai haifar da wani cutan ba ko kuma wani illa yafi
tsanani ba.
Ya haramta
ribatan mara lafiya amishi wasu gwaje -gwaje da aune aune da diban jini wanda
ba bukatansu ko kuma ba wata fa'ida cikin tafiyar da su sai kawai kasuwanci ko
kuma kwace dukiyan marasa lafiya , tir da irin wannan dukiya din , dukiya ne da
bazai amfanu ba ba zai habaka ba sai bisa kasuwanci da radadin mara lafiya da
kuma wanda suke cikin halin zazzabi.
Na daga
cikin likitoci da kuma masu kemest wanda suke bada magani ga mara lafiya bisa
ga wani farashi tare da akwai wani madadin shi wanda yafi dacewa kuma mai sauki
a wurin farashi yana yin haka ne domin manufan ya habaka wa kamfani
magungunanta ko kuma domin ya samu wasu sashi na garabasan da kamfanin ke
gabatarwa saboda maslahansa a fifitata akan maslahan mara lafiya ba zai yi haka
ba sai wanda zuciyarsa ba rahama ko yana kusa da ya rasa rahama da kuma rashin
tsoron Allah da rashin alkawari da kiyaye amana.
An karbo
daga Anas ya cewa: ba sa'annin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi ya ke mana huduba face ya ce: (babu imani ga wanda ba yida amana babu addini ga wanda
bayi da alkawari) Baihaki ne ya fito da shi.
Ku kiyaye
dajjalai na daga 'yan tsubbu masu bada magani wadanda suke masu da'awan
likitanci wadanda suke bude wuraren asibitoci da akwai shubuha a cikin su suna
karban marasa lafiya ba tare da wani izini na hukuma ba kuma sunada ikon bada
waraka bisa ga wasu cututtuka suna saida kayakin aiki da suke akwai zamba a ciki ko algus.
Muna gargadan
musulmai kar su gaskata wadanda suke ba ma'abota fanni ba a likitanci wadanda
suna yada bayanai da siffantawa irin na likita ta hanyan kafafan sada zumunta suna saida rudu suna wasa da rayuwa na
marasa lafiya suna sadar da cutuwa bayyananne wanda ake da yakini a madadin
lafiyan mutane da kuma jikinsu.
Suna yada
abubuwa na mafi hadari kuma suna afkawa gidaje ku kiyaye su kar ku rudu da
wadannan azzalumai masu barna a doron kasa mujrimai a hakkin rayi na dan Adam
wanda musulunci ya zo domin kiyaye shi ya bashi kariya kuma ya haramta keta
alfarman shi.
Ya ku
musulmai:
Hakika
Allah ya dauke rayin Abatil abubuwa na bata irin na bokaye da hujjoji da
Alkur'ani, to ku kiyaye bokaye da kuma dajjalai da kuma masu buga kkasa ko
taurari da masu sha'awaza konkulomboto wadanda suna da'awan ilimin gaibi da
gano abubuwanda suke na zuciya da sanin abubuwanda suka boyo, to ku kiyaye
wadannan dajjalan masu bada magani wadanda sun fita daga magani na shari'a sun
kare akai suka shigarda wasu abubuwa na bidi'o'I wanda su ke masu laifi masu
fusatawa, ku kiyaye masu yaudara masu rufa ido makaryata wadanda suke da'awan
bada magani ga wanda aka ma sihiri da kuma wadanda suke aljani ya shafe su da
kuma wadanda suke masu farfadiya ta hanyan shakewa ko ratayewa ko daurewa ko
duka ko bada wasu dalasimai , da de wasu kulumboto suna saida wasu layu da kuma
wasu abubuwa dunkulallu da kuma tamima ,hatimai da kuma wasu kariya da suke yi
domin neman waraka da kuma abubuwa da ake daurewa da wasu rukiya na shirka wanda
suna habaka da barna da kurafa suna saida abubuwa da suke na wahami wanda bata
zayyanuwa a ganta sai ga ma'abota raunin hankali da akida An karbo daga Imran da Husan Allah ya kara
yarda a gare ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
ya ce (Baya cikin mu duk wanda ya yi shu'umanci
haka nan kuma ko wanda aka yima, kuma baya cikin mu wanda ya yi bokanci ko wanda aka mai
bokanci ko kuma ya yi sihiri ko yasa aka mishi sihiri, duk wanda ya yi kulle
kulle da wanda ya zoma boka ya gaskata shi cikin abin da ya ke fada to ya
kafurce abin da aka saukar wa Muhammad) Bazzar ne ya fito da shi.
Duk wanda
ya je wurin wadanan dajjalan to shi ma yana tarayya da su wurin alhaki saboda
bakinsu da muninsu ya yi yawa kuma suna habaka abin da suke na barnan su to ya
wajaba a isar da bangarori na tsaro don duba mataki da za su dauka ga wadannan
kazantattu , ya haramta a boye sha'anin su ko a musu shiru .
*** ya
fi mana sauki ba kusa ba da jikin mu ya cutu ***
***
mutuncin mu da hankalin mu ya tsira ***
Ina fadin
abin da kuka ji kuma ina neman gafaran Allah ni da ku da kuma sauran musulmai
daga dukkan zunubbai da kusakurai ku nemi gafaran Shi domin Shi mai gafara ne
ga masu komawa gare Shi.
Huduba ta biyu:
Ya ku
musulmai:
Halittu
ana nufansu da jarabawoyi, hakika an ce: muddin kana wannan gida, kar ka yi
mamakin faruwan abin da ya ke mai aukuwa
jirkitacce, kar ya kasance cikin wadanda idan wani abu na cuta ya same
su sai su firgita su gaza hakuri sai zuciyan su ya dare su yi nesa, yanke kauna
daga rahamar Ubangijinsa ya tuna fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi (lallai bawa idan yana da wani
matsayi a wurin Allah ba zai riske shi ba ta hanyar ayyukan shi sai Allah ya jarrabe
shi a jikin shi ko dukiyarsa ko kuma a
dan shi sa'annan sai ya sa shi ya yi hakuri bisa hakan don ya hadu da shi har
ya kai shi wani matsayi wanda Allah Ta'ala ya riga ya rubuta shi a gare shi) Abu dauda ya fitar da
shi.
Wani daga
cikin magabata ya ke cewa: '' ba don musimun duniya ba da mun zo kiyama muna
talakawa''
Kais binu
Ubad ya ke cewa:'' awowinda aka yi na wahala suna tafiyar da awowin da aka yi
na kusakurai ''
Kada mumini
ya yi fatan aukuwan ukuba sai dai ya roki Allah waraka , an karbo daga Anas da
Malik Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: (Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ziyarci wani daga cikin
musumai ya rame ya zama kaman wani dan tsako, sai Manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce da shi shin ka kasance kana addu'a da wani
abu ne? ko kana rokon Allah da shi? Sai ya ce e, na kasance ina cewa '' ya
Allah : muddin zaKa mini ukuba a lahira abin da zaKa min ukuba da shi a lahira
to ka sanya min shi a nan duniya sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce: Subhanallah! Ai Ba zaka iya shi ba inama ka ce: Ya
Allah ka bamu kyakkyawa a nan duniya ka bamu kyakkyawa a lahira ma ka kare mu
daga azaban wuta? Sai ya roki Allah da ya bashi waraka). Muslim ne
ya rawaito.
***Idan
ya yi rashin lafiya to hakurin shi ba zai yi rashi lafiya ba ***
***
idan yayi zazzabi to azaman sa ba zai yi zazzabi ba***
*** idan ya mika wuya to ba wai ya rage ba ne sai
dai ***
*** na
kubuta ni daga alhumam zuwa humam ***
Ku yi
salati da aminci ga Ahmad alhadi mai ceton dukkan halittu wanda ya yi salati a
gare shi guda daya Allah zai mishi salati guda goma.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق