Hudubar masallacin
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na 22/9/1441 na shaihk Ali
dan Abdurrahman Alhuzaifi.
Da sunan Allah mai
rahama mai jin kai.
Huduban farko
:
Dukkan yabo da godiya
sun tabbata ga Allah ubangijin kasa da sammai a hanun shi ne alheru su ke , shi
ne kuma wanda ya ke gafarta zunubai yana tunkude mummuna da abinda aka ki ina
kyautata yabo ga ubangijina kuma ina gode mishi bisa ni'mominSa masu yawa wanda
ba mai iya kididdige su sai shi wanda
muka sani daga cikinsu da wanda ba mu sani ba shi ne ma'aboci falala da kuma
kyawawa ,na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba
shi da abokin tarayya mai amsa addu'o'i , na shaida cewa Annabin mu kuma
shugaban mu muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne mai kira zuwa ga Aljanna masu yawa wanda aka karfafe shi da
mu'jizozi, ya Allah ka yi dadin tsira da aminci bisa albarka ga bawanKa kuma
ManzonKa Muhammad da iyalanSa da sahabbanSa wadanda suka tsere zuwa ga ayyuka
na kwarai.
Bayan haka:
Ku ji tsoron Allah ta
hanyan kusantazuwa gare shi da ayyukan yardanSa da kuma nesatan fushinSa da
azabansa ta hanyan barin abubuwan da ya haramta.
Ya ku musulmai :
Hakika Allah ya kwarara
muku a wan nan wata albarkoki daga cikin albarkatu da alherori Allah ya yi baiwa a cikin shi da nau'uka
na biyayya masu yawa Allah kuma ya kiyaye ku daga abubuwan da suke muharramai
da kuma abinda aka ki da abinda Allah ya boye muku na daga lada bayan mutuwa
shi ne abunda zai faranta wa mumini rai kuma duk wani mai musabaka a cikin
alheri zai yi musabaka zuwa gare shi , Allah madaukakin sarki ya ce (ka ce da falalan Allah da rahamarSa saboda haka su yi farin
ciki shi ne ya fi akan abin da su ke tattarawa) sai suka bi kyawawa
da kyawawa to ku bi ayyuka na kyawawa da kyawawa ku kasance a kjarshen watan ku
kun dada tsananta kokari kun fa girmama neman daidai ku yi kuma nesa daga
zunubai da sabo wanda suke bata ayyuka na kwarai ko suke rage ladansu, Allah
madaukakin sarki ya ce: (ya ku wadanda suka yi imani
ku yi da'a wa Allah ku yi da'a wa ManzonSa kada ku bata ayyukanku)
a'aya ubangijin mu mai rahama mai jin kai ya shar'anta mana wasu kofofi na
falaloli da ayyuka na kwarai domin mu yawaita alheri dama da muka samu na
rayuwa baka san wani aiki ne Allah zai karba ba ya tsiratar da kai daga azaba
da shi , Allah Madaukakin sarki ya ce : (ya ku
wadanda suka yi imani ku yi ruku'u ku yi sujjada ku bauta wa ubangijinku ku
aikata alheri ko za ku samu rabauta)
An karbo daga Abi
zarrin Allah ya kara yarda a gare shi ya ce Mazon Allah tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi ya ce :(kar ka rena aikin
alheri komin kankantan shi ko da ma a ce ka hadu da dan uwanka ne da sakekken
fiska) Muslim ne ya rawaito , duk wanda ya nemi rabauta da tsira da
kuma rayuwa na dindin din cikin ni'ma dawwamammiya to ya yi aiki na kwarai a
cikin wadan nan ranaku masu falala da dararraki masu albarka domin lallai
abinda ya shude ba zai dawoba na daga lokaci masu daraja su ne lokaci na ayyuka
kuma da tabbatar da alherori na daga burace burace , an karbo daga Abu huraira
Allah ya kara yarda a gare shi ya ce :Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi ya ce:( ku gaggauta da ayyuka
abubuwa guda bakwai ,shin akwai
abinda ku ke jira facetalauci abin mantawa ? ko wadata abin ………? Ko kuma rashin
lafiya ? ko kuma tsufa ? ko kuma mutuwa shiryayyiya ? ko kuma dajjal to sharrin
abinda ya ke boye da ake jira ? ko kuma tashin alkiyama domin tashin alkiyama
shi ya fi zafi shi ya fi bala'I kuma shi ya fi daci )Tirmizi ne ya
rawaito kuma ya ce: hadisi ne hasan ku din nan ya jama'ar musulmai kuna goman
karshe na ayyukan albarkatoci da kuma
ayyuka ku sani abin la'akari shi ne karshen su kuma lailatul kadri na
kaura a cikin wan nan goman ne duk wanda aka datar da shi ya yi tsayuwan
darenta to za a gafarta mishi abinda ya gabata na daga zunuban shi , An karbo
daga Abu huraira Allah ya kara yarda a gare shi daga Annabi tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya ce: (duk wanda ya
yi tsayuwan daren lailatul kadri yana mai imani kuma da neman lada za a gafarta
mishi abinda ya gabata na daga zunubban shi) Bukari da Muslim ne
suka rawaito , alherin ta da albarkatun ta ko wani musulmi na iya riska bauta a
cikinta shi ne abinda ya fi na daga ibadan watanni dubu wanda ba a cikin daren
lailatulkadri ba Allah ya kebance wan nan al'umma da ita wan nan kuma falalan
Allah ne da ya ke bawa wanda ya so Allah ma'abocin falala ne mai girma,ya ku
musulmai : ku ku yawaita na daga adu'a da adauke bakin ciki daga al'umma hakika
Allah ya muku alkawarin amsa addu'a a wannan wata mai girma kuma ku yi
tawakkali zuwa ga Allah da ayyukan ku na kwarai domin lallai hakan na daga
cikin sabuba na amsa adu'a ku tsanannta wurin adu'a a wurin rokon Allah
ubangiji mai jin kai wurin dauke wan nan annoba
daga kasashe musamman ga kasashen musulmai , kuma ya dauke daga bayin
Allah domin Allah ubangijin dukkan komai ne amma dan adam sunada rauni suna da
gajiyawa ba su mallaki wani abu ba wa kansu na amfani ko na cutarwa Allah
Madaukakin sarki ya ce (Allah ya halicci mutum cikin
rauni) haka kuma Allah subhanahu wa ta'ala ya ce:(ku kirayi Ubangijinku
kuna masu kankan da kai da kuma a boye, lalle ne shi ba ya son masu wuce iyaka.
Kuma kada ku yi barna a cikin kasa a bayan gyaranta, kuma ku kiraye shi saboda
tsoro da kuma tsammani lalle ne rahamar Allah Makusanciya ce ga masu kyautatawa).
Allah ya sa min albarka
ni da ku a cikin Alkur'ani mai girma.
Huduba ta biyu
Dukkan yabo da godiya sun
tabbata ga Allah Mai rahama Mai jinkai Mabuwayi Mai hikima, ina kyautata yabo
ga Ubangiji na kuma ina gode masa bisa abin da ya kwarara a gare mu na daga
ni'imomi, da kuma tunkude musibu a gare mu da azaba na shaida ba abin bautawa
da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya Ma'aboci daukaka
da girma, kuma na shaida Annabinmu kuma shugabanmu Muhammad bawanSa ne kuma
ManzonSa ne, ma'aboci dabiu na karamci, to ya Allah ka yi dadin tsira da aminci
da albarka ga bawanka kuma ManzonKa Muhammad daiyalansa da sahabbansa wadanda suka
taimakawa wannan addini mikakke.
Bayan haka ku ji tsoron
Allah cancancin tsoronSa, ku yi riko da igiya mai karfi na musulunci.
Ya ku musulmai hakika
Ubangijinku ya kirayeku da fadinSa (Ya ku wadanda
suka yi imani ku tuba zuwa ga Allah tuba ta gaskiya, mai yiwuwa Ubangijinku ya
kankare muku miyagun ayyukanku, kuma ya shigar da ku gidajen Aljanna koramu na
gudana a karkashin su, a ranar da Allah bai kunyatar da Annabi da wadanda suka
yi imani tare da shi, haskensu yana tafiya gaba gare su da jihohin damansu). Kuma
Allah Madaukaki ya ce : ( ku tuba zuwa ga Allah gabadayanku ya ku wadanda suka
yi imani ko zaku samu rabauta)
Hakika Allah ya muku baiwa na tuba a wannan tsanani, lalle kuma Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (lalle Allah ya fi farinciki da tubar bawanSa sama da
mutumin da abar hawansa ta bace a cikin jeji ya neme ta har ya gaji sai ya kama
barci a karkashin wata bishiya yana farkawa sai ga dabbar tsaye a kan shi, sai
ya riki linzaminta ya ce : Ya Allah kai ne bawa na nine Ubangijinka ya yi
kuskure sabo da tsaban farinciki.) muslim ne ya rawaito daga hadisin
Anas Allah ya kara yarda a gare shi.
Kada ku warware tubanku
da abin da ke kishiyantar ta, ku yawaita tilawan Alkur'ani a watan Alkur'ani,
domin shi ne kalacen ruhi, zuciya na amfana da shi sama da komai a wannan wata,
domin shine anbato mai hikima kuma mai shiryarwa ga tafarki mikakke, shi ne mai
hukunci na gaskiya cikin abin da mutane suka saba a cikinsa.
Ya ku bayin Allah!
Lalle Allah da mala'ikunSa suna salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku
yi salati a gare shi da aminci tabbatacce mai yawa.
ليست هناك تعليقات:
إرسال تعليق