الجمعة، 22 مايو 2020

BANKWANA DA WATAN RAMADANA

Hudubar masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na 29/9/1441

 

Hudubar farko:

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah tsira da amincin Allah su tabbata ga manzonSa

Bayan haka :

watan ramadana ya kare , wanda Allah ya bamu labari cewa wasu 'yan kwanaki ne kididdigaggu sai gashi ya wuce kaman kyabtawan ido, ya wuce kaman hasken walkiya, hakika zukata sun kasance sun yi shaukin zuwan shi, ga shi a yau kuma yana shelanta tafiya kuma yana juyawa yana mai ban kwana, ba abin mamaki ba ne a samu zuciya ta samu nau'uka daban daban na abin da ta ke ji na daga cikin labaran zuciya, muna jin falalan Allah a gare mu da ya shiryar da mu zuwa ga musulunci kuma ya sanar da mu alkur'ani, kuma ya riskar da mu ramadana ya taimake mu zuwa ga azumi da kuma tsayuwa, shi ne mai ni'imtarwa mai yawan kyauta, Allah Madaukakin sarki ya ke cewa:(suna goranta maka don sun musulunta ka ce kar ku min gori bisa musuluncin ku sai dai Allah Shi ne zai goranta muku saboda ya shiryar da ku zuwa ga imani) wan nan shi ne halin masu tafiya zuwa ga Allah suna shelantawa da dukkan ladabi mai girma da daukaka da rusunawa da jingina ni'ma zuwa ga ma'bocinta (sai ya ce wannan falala ne na Ubangijina) wan nan shi ne abin da ya dace duk wasu ayyukan kwarai a rufe da su, a fiskanci ayyukan girmamawa da su (Dukkan godiya a gare shi ta ke a duniya da kuma lahira hukunci  ma naShi ne kuma gare shi za ku koma) lallai Shi Madaukaki mai falala na hakika da dukkan wani abu mai kyau ga halittunSa ,

An karbo daga Anas Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (Ba wani ni'ma da Allah zai yiwa bawa sai bawan ya ce godiya ta tabbata ga Allah face sai abin da aka bashi zai fi abin da ya rika) wan nan shi ne yanayin halin 'yan aljanna a lokacin da suka kai kololuwa gurin buri da samun yardan Allah sannan suka shiga aljanna harsunan su na daga murya da godiyan Allah Madaukaki suna cikamake adu'arsu da shi da ayyuka na kwarai , Allah Madaukakin sarki ya ke cewa (sai suka ce dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah da ya tafiyar mana da bakin ciki lallai Ubangijin mu mai yawan gafara ne kuma mai yawan godiya)(wanda ya bamu masauki a gidan dawwama daga cikin falalanSa , ba wani gajiya ko wahala da zai shafe mu)

Gaggautawa zuwa ga godiyan Allah da kyautata yabo bisa ga ni'mominsa a yayin kammala wannan watan falala shi ne manhaji na musulunci da kuma taujihin alkura'ani , Allah Madaukakin sarki ya ce: (Domin ku cike adadin kuma ku girmama Allah bisa ga abin da ya shiryar da ku ko za ku gode) ya zo a hadisi wanda Bukari da Muslim suka rawaito shi daga Abu huraira Allah ya kara yarda a gare shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :(Mai azumi nada farin ciki guda biyu , farin ciki guda yayin shan ruwansa farin ciki guda kuma yayin haduwa da Ubangijinsa )

 Tabbatar da ma'ana ta yabo da godiya ta watan ramadana alama ce ta kyautata zaton bawa ga Allah da kuma fatansa cewa Allah ya karba mishi abin da ya yi na da'a kuma ya kankare mishi tawaya da aka samu a aiki da kuma gafala na daga halaka da kuma jahilci , yayin sauke nauyi , hakika ya zo a hadisul kudusi (Ni ina inda bawa na ya zaceNi) idan bawa ya kyautata zato ga Ubangijin shi to ya lizimta a gare shi da ya yawaita addu'a don Allah ya karba mishi da'an shi yana mai ladabi tare da Allah da neman tabbatar da zaton shi da gaskiyan fatan shi.

Hakikanin godiya a karshen watan ramadan shi ne gyaruwan aikin bawa da lazimtan shi ga da'a ga Ubangijin shi da gaggautawa zuwa ga wurin samun yardar Allah , Allah Mabuwayi da daukaka ya ke cewa(ku yi aikin godiya ya ku mutanen Dauda , kadan ne daga cikin bayi Na su ke masu godiya) Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kan yi tsayuwan dare har kafafuwarsa su kumbura sai a ce da shi kai da Allah ya gafarta maka abin da ya gabata na daga zunubanka da abin da ya jinkirta? Sai ya ce : (Ashe ba zan zama bawa mai yawan godiya ba ?).

Musulmi wanda Allah ya haskaka zuciyarsa a cikin watan ramadana ya kara fadada da imani ya sha daga mabubbuganSa, ya koshi daga tabkinSa, ya yi tsayuwan daren Sa , ya azumci wuninSa , to ba zai gushe ba yana tsere zuwa ga ayyuka na da'a har bayan watan ramadana, ba zai yi sakaci ba wurin neman ayyuka na ganima wanda ya ci daga dadinta a cikin azumin shi da kuma sallarsa da biyayyarsa, duk wanda ya dandani dadin ganawa da Allah ya kuma dandani dadin imani a ramadana natsuwa da kwanciyar hankali ya kwararo a cikin zuciyarsa to ba zai  yi sakaci ba wurin barin wannan sa'ada din ya tsere mishi, zai zame ne zuciyarsa  na ta'allake da Ubangijin shi kuma zai zame yana ta debe kewa da Ubangijin shi, kuma tare da Allah kuma zuwa ga Allah, idan lokacin ramadana ya kare lallai lokuta na alheri na bibiyan juna falaloli na Mai rahama ba a'a iya iyakance su lokuta na da fifiko wurin kima da kuma lada a duk lokacin da aka samu nunfasawa na wani lokaci da  dama ta samu to mai hankali zai yi gaggawa ne ya tashi zuwa gare ta, mai komawa zuwa ga Ubangijin shi zai ribace ta, Allah Madaukakin sarki ya ce: (ka yi sujada ka kusanto)

A dukkan safiya da gari zai waye fage ne na yin hailala da kuma godiya da kabarbari da kuma istigfari.

 A dukka yammaci in ya sake duhun shi  to lokaci ne na ganima wanda zai  farauce shi, wanda ya san kimanta shi ne masu yawan ibada a cikin dare wanda sassan su ke nesatan makwanci suna rokon Ubangijinsu suna bisa halin tsoro da  kuma tsammani.

 Wadanda suka san hakikanin rayuwa da kuma kimanta suna da iko lokutan su su zama duka lokuta ne na ayyukan alheri, za su kuma rika  kai komo cikin nau'uka na mubadara ta hanyan ayyuka na kwarai da, yada ilimi da taimaka wa mabukaci da girmama bako da kuma shafa kan maraya da kuma gyara da gina masallaci da kuma yalwata nasiha da karfafan tsangayoyi  na alkur'ani  da tarayya wurin gidauniya  na alheri da kuma aiki bisa habaka kasa da kuma daga al'uma, Allah Madaukakin sarki ya ce: (Duk wanda ya ke son lahira kuma ya yi aiki don ita irin aikinta a halin yana mumini to wadan nan ayyukan su za su zama abin godiya).

Musulmi ya kan hadu da wani nau'i na bala'i ko annoba a zuciyansa ko iyalansa idan ya godewa Allah kuma ya nemi ladan musiban a wurin Allah ya yi imani da abin da Allah ya hukunta ya kaddara to Allah sai ya girmama mishi ladan shi, ya maida mishi da mafi alheri kuma ya rubuta masa rahama da gafara da shiriya Allah Madaukakin sarki ya ce:( lallai za mu  jarabe ku da wani abu na tsoro da yunwa da tawaya na daga dukiya da rayuka da 'ya'yan itace, ka yi albishir ga masu hakuri wadanda idan musiba ta same su sai su ce : ga Allah muke kuma gare shi za mu koma, wadan nan suna da wani kyakkyawan ambato daga Ubangijinsu da kuma rahama kuma lallai wadan nan su ne shiryayyu)

Haka na zuwa ne a wani yanayi na annoba wanda ya sanya abu mai motsi ya zama ya natsu ya mosta kuma abin da ya ke zaune gu daya, ya yi yawo a doron kasa ya sanya zukata cikin tsoro da  idanuwa kuru kuru na daga abin da jiki ke kwanta dama, da abubuwa da ke faruwa na kamuwa da cututtuka daya bayan daya da ake gani a wan nan yanayi na kunci mai tsanani akan fiskanci ludufin Allah boyayye  rahamomin Allah su kewaye mu sai Allah ya kiyaye bayi daga wan nan annoba mai ragargazawa ya katange kasa daga rashin lafiya mai halakarwa ya dauke bakin ciki daga al'uma tasirin shi a doron kasa ya zamana dan kadan ne san nan ya tunkude shi da falalanSa ga Ubangiji wani abu ne da ba mai wahala ba.

wannan shi ne yaye bakin ciki mai girma, zai sanya idin mu ya zama zai zo gare mu nan kusa cikin mafi kyan idi kuma wanda ya fi farin ciki da kuma jin dadi domin tufafin da za mu sa sabo a cikin idi shi ne na tsoron Allah da kuma lafiya, abin hawa mai laushi da za mu hau shi ne na aminci da zaman lafiya shakatawa da walwala shi ne mu shaki tacecciyar iska wacce ta kubuta daga wan nan annoba da kuma farin ciki na haduwan iyalai da 'yan uwa da makusanta da kuma makwabta, shi ne a samu labarin suna cikin koshin lafiya suna cikin ni'ma, shin bayan wannan ganima akwai wani abu kuma na nema ? ku tafi a doron kasa ku yi dubi zuwa ga halin da wadan su su ke ciki, domin ku san kaye na hali da daukaka da ni'ima a kuma kima na ludufi, abin mamaki da girman Allah da rahamarSa Mahalicci, lallai  halarto da ni'ima da gode wa Allah da harshe da zuciya yana sanya karin samun rahama da ludufi .

Huduba ta biyu:

Musulmi yana cika watan ramadana ne yana mai godiya da farin ciki saboda riskan cikan shi yana lullube da rahamar Allah yayin shan ruwan shi ni'man Allah da falalanSa yana mai gaggawa zuwa ga jefa farin ciki a al'umansa, sai ya fitar da zakkan fidda kansa domin tsarkakewa ga mai azumi daga kazanta da wasa kuma ya farantawa talakawa rayi ya wajaba ga musulmi haka kuma ga duk wanda musulmi ke daukan nauyin shi, mikdarin shi shi ne sa'i daga cikin abincin gari.

An karbo daga dan Umar Allah ya kara yarda a gare shi shi da mahaifin shi ya ce :(Manzon Allah ya wajabta zakkan fidda kai sa'i guda na dabino ko kuma sa'i guda na sha'iri bisa ga bawa da da na miji da mace da kuma yaro da babba na daga musulmai kuma ya umarni da a fitar da shi kafin fitan mutane zuwa sallah). Ya halatta gabatar da shi da rana daya ko rana biyu saboda abin da aka rawaito daga ibnu Umar cewa sun kasance suna badawa kafun fita eidi da rana daya ko rana biyu.

Tare da dakatar da sallah da aka yi a masallatai da kuma wuraren sallah na idi saboda wannan annoban an shar'antawa musulmai sallan idi a gidajensu a jama'a ko kuma a daidaiku, kuma za a fara kabarbari ne tun daga faduwan ranar daren idi sannan idan aka sallace ta a gida to sai a yanke kabarbarin tare da shiga salla. Ana sallatanta sifanta ne rak'a biyu ba tare da huduba ba za a yi kabbaran harama a farko sannan a yi kabarbari guda shida bayanta, a rak'a ta biyu kuma za a yi kabbara na tashi sannan kuma a yi kabarbari guda biyar bayanta , lokacin sallar idi na fara shigowa ne tun daga bayan hudowar rana da kuma bullowanta da mikidarin mashi biyu ko kuma da mikidarin abin da bai gaza minti ashirin ba kuma zai ci gaba lokacin nata har zuwa lokacin sallan walaha kafin shigan lokacin sallan azahar da kusan sulusin sa'a, hakika hani ya zo daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na hani ga sallah a lokacin da rana ke hudowa. 

Allah ya karba mana ayyukanmu na kwarai da ayyukan ku na kwarai.            

      

 


ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق